Zee Baby Book 1 Page 22

Advertisement

👉🏻22*

 

 

….”naga tana nunawa wai karta shigo sunkuyowa Daddy yayi yana mata Addu’a “Mahabeer inaga kamar Aljanunta fah basason Mariya ne bakinta ya fara fitar da kumfa abinda ya tsorota Nisha ta fado kanta tana kuka gaisha ta janyeta hafeeza ma kuka takeyi Daddy ya buga musu tsawa” Mahabeer ko muje asibitine?? “Daddy ba  ciwon hospital bane Addu’ar sukaci GABA da mata cikin ikon Allah tayi wata irin atishawa mai firgitarwa da ihu mai uban karfi saida khalisat da hafeeza suka gudu amma nisha na gunta tana hawaye tana tofa mata Addu’a Mahabeer yasa nisha ta kawo ruwa ya karanta suratul yasin ya tofa aruwan ya dura mata da karfi tasha ya shafa mata ajiki ta kuma atishawa da hamma tai lamo jikin Mahabeer sai bacci  Daddy yace”Alhmdllh tayi bacci kai momy Allah ya rabaki da Aljanun nan sun dameki Mahabeer kaita ka kwantar da ita mik’ewa yai ya dauketa ya nufi bedroom d’insu yaje ya kwantar da ita ya lulubeta ya fito ghaisha harda kwalla tausayi Mahabeer zama yai kusan ghaisha yayi tagumi kansa ta shafa “kayi hakuri ba komai bane zataji sauki tana tashi lfy zata tashi amma abun yabani mamaki irin wannan lamarin watarana sai sunga abinda bai musu bane ba suke haka Mahabeer yace” wlh nima nayi mamaki Daddy yace babu abin mamaki sharrin jinnu yawane dashi “Khadija ina mariya wai? “naga fah ta nufi kofa da gudu inajin tsorata tayi kofar Daddy ya nufa abin dariya yabashi da taji tsoron zee yana fitowa ya ganta rab’e ya nufi gunta “haba mariya saikace wata yarinya tsoron Aljannu kara matse Jakarta tayi ta tataro nutsuwarta dan kar yagano itace sila”Daddyn nanah wlh tsoron Aljannu nakeyi gashi aljannunta basu sona dariya yayi ya kamo hannuta “mujeto ga yarki can yar k’arama da ita ta tsaya a parlo tana zaune gun ghaisha shiru tayi yana rike da hannuta har parlo ya saketa wuff ta shige d’aki ta boye maganin ta fito parlo

 

“Aunty ghaisha sannu da gida? ” mariya kece da sannu ya mama da jikinta? ” Alhmdllh tana gaisheku ya jikinta momy? “tayi bacci” Allah bata lfy hira suka ci gaba dayi Daddy yace”khadija abamu abunci mana Dariya tayi ta Mike ta kalli mahabeer ta kamo hannusa”muje kaci abunci kayi hakuri zata tashi lfy mariya tashi muje kuci abunci khalisat kirawo Aisha da hafeeza maza kuci abunci mik’ewa tayi ta nufi bedroom suko suka nufi kan dining khalisat na shiga taga Nisha rumgume da zee gam idanunta arufe tace”hafeeza Nisha bacci takene?” idona biyu meye ai duk uwarkice taja mata tunda ita takebi hafeeza ta rufe mata baki”yi hakuri Nisha tashi muje kici abunci? ” banaci na koshi mik’ewa tayi suka fito itako tana kwance rumgume da zee,  Dr Sardauna yana fita ya shiga motarsa yabar gidan danma karsu nemesa ya dubata kai tsaye gidansu mashakurah ya tafi,  yau har cikin ya shiga da motarsa ya kirata ta fito suka shiga ya gaishe da iyayanta ta kaishi parlon baqi inda suke zama sai surutu take zuba masa kallonta yayi”wai meyene yanzu kika koyi rufe rufen jiki kina wani sunne kai sweet baby ko shirin amarcin ne? ” kai my Dr wlh ba haka bane nafiso karka sake ganin kome nawa sai na shiga gidanka baki ya tab’e daga baya Kenan ya fada cikin rainin hankali ya dan jima sosai sun dan tab’a hira ya Mike ta rakoshi harda shagwab’arta dariya ma ta bashi ya lallabata ya shiga mota yamata key direct gidansu Ahmed ya nufa har parlon su umma ya shiga ya gaishesu tukun ya fito ya nufi bangaran Ahmed yaga arufe yayi mamaki dan umma tace yananan baki Sardauna ya ciza”shege munafuki ko ina ya tafi adaranan ya fada yana wucewa mota ya shige ya bata wuta ya nufi gida kida ya kunna ya kure sauti wakar ethiopia ce dan yana mugun son wakokinsu sigari ya kunna yana zugarta yana kada kansa saida ya biya shopping mall yayi tsince tsince abubuwa ya kashe kudi ba kadanba kan kayan ciye ciye da turaruka masu uban tsada,  yana zuwa gida part d’insu ya shige ya nufi bangaransa ya bude hadaddan d’akinsa sai uban kamshi ke tashi carpet malale ko ina ga manyan kujeru tamkar d’akin Amarya bed d’insa kadai abun kallone ledojin hannusa ya ajiye harda su ghaisha yama sayaya amma bashida niyar komawa part d’insu ayau yayi niya sai gobe kayan jikinsa ya cire ya daura towel ya nufi bathroom shower ya kunna yasakarwa kansa

 

ruwa yajima sosai kafin yayi wanka ya dauro Alwalla ya fito dan bacci yakeji sosai yau ga gajiya  jikinsa ya goge ya murza maiyukansa masu kamshi da dadi yasaka jallabiya ya shimfida darduma ya tayar da sallah wayoyinsa har biyu sai ringing suke atare,  raka’a hudu yayi ya dauki Alqura’ani ya fara karatu yajima sosai dan yafi awa guda yana karatu akinrasa yafi so goma sujada yayi nanma yajima yana tasbihi ga ubangijinsa yana nema gafara Allah yana kara neman kusanci ga Allah subahanahu wata’alah yanama Annabinmu Muhammad s,w,a kirari Yajima sosai ya dago ya daga hannuwansa sama yashiga kwararo Addu’a ya shafa ya Mike ya nufi gun wayarsa yana dubawa Wanda suka kirasa yaga bandar yamasa kira uku mashakurah kira hudu Daddy kira biyu Ahmed kira uku sai number da babu suna kansa ya dafe”oh sweet baby ko miyene kiranta yayi wayar akashe kin Kiran Ahmed yayi yana murmushi ya kira bandar shima akashe wayar kiran Daddy yayi bugo daya ya daga”Faisal ina ka shiga bakaci komai ba”Daddy gidansu Ahmed naje da nazo bacci ya daukeni” to maza fito ko tea kasha ko coffee maza mu har mun kwanta dare yayi” to Daddy ganinan”yauwa Dr dariya Sardauna yai ya kashe wayar ya nufo parlo Mahabeer na zaune   da casbi ahannusa Dr ya kallesa “bro bakayi bacci ba har shabiyu? ” wlh tunanin halin da zeena take ciki ya hanani bacci baki ya tab’e “ni na tafi cikin gida nasha coffee nazo na kwanta wlh bacci nakeji mik’ewa Mahabeer yayi”muje naga ko ta tashi ko tea na hada mata baiwar Allah bataci komaiba Dr Sardauna baice komaiba suka fito can ko lokacin da Sardauna yakira Daddy d’akin Aunty Amarya yake tanajin yana maganar Sardauna yazo yaci wani abu kar ya kwanta haka zuwat ta Mike ta saci kallon Daddy taga baya kallon gefenta cikin rawar jiki ta nufi idan ta boye maganin ta dauko ta shiga toilet ta ciro Wanda Sardauna zai tsallaka ta fice daga dakin direct dakin su khalisat ta nufa cikin sa’a taci Karo da khalisat ta fito shan ruwa ta kirata suka lab’e ta sinto ledar ta  maganin “amshi babu lokaci da safe namiki bayani kiyi maza kije kofar parlo ki Barbada maganin wannan Sardauna zai shigo yanzu kinga darene babu Wanda zai shigo yanzu ki badeshi baki daya “momy na menene?? ” kece zaki San ko nameye nan gaba badai sonsa kikeba? ” eh momy”to maza jeki ba lokaci ta fada tana komawa

 

bangaranta da gudu khalisat ta nufi kofar parlo cikin rawar jiki ta barbade kofar parlon zuciyarta fari tas tana murna kuma daidai lokacin tajiyo murya Sardauna na tafe yana waya da gudu ta nufi hanyar bedroom tana cikin farin ciki Karo sukayi da Nisha”ke lfy me ya fito dake kuma kike irin wannan dariyar yawa zarara batace komai ba ta rab’e ta shige ciki Nisha kuwa ta nufi kitchen don hadama zee tea ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ko da khalisat ta shigo zee tana bathroom Dan haka ta haye bed ta shige cikin blanket hafeeza ma bacci takeyi Dr Sardauna ko suna fitowa suna dab da shiga bandar ya kira Sardauna ya daga rike hannu Mahabeer yai “bro ka jirani mana murmushi yai ya jirasa suna ta hirasu da bandar Akan yana tafe insha Allah nan da kwana biyar mahabeer ganin hirasu ba mai karewa baceba ya janyo hannu Sardauna “muje mana ciki wai kuyi wayar kiyawa Sardauna yai mahabeer ko ya fizge hannusa”to Nima kabarni naje naga Rabin raina ya fada yana murmushi ya nufi parlon yana sanyo kafarsa kansa ya Sara gabansa ya fadi da Sauri ya furta” Auzubillahi minal shaidaninr Rajim bismillahir Rahamanir la’ilaha innah anta subahanaka inni kutum minal zalumin ya fada yana shiga tsakiyar parlon kamar cira qaya yaji bayajin faduwar gaban sai kasala kadan kadan parlon shiru alamun kowa yayi bacci motsi yaji a kitchen ya nufin kitchen din Nisha na kokarin hadama zee tea ganin irin kayan dake jikinta yayi maza ya juyo ya fito ya lab’e”Nisha zee ta tashi ne?? dariya tayi “bro yo meye na labewa eh ta tashi tea ne zan kaimata ka ajiye hankalinka tana lfy dariya yayi”yauwa kanwata nagode ki gaishemun ita sai da safe na koma ya fada yana tafiya lokacin Dr Sardauna ya shigo akofar parlo suka hadu Mahabeer yace da ka hakura da coffeen mun koma? ” haba wlh sai na hada nasha Daddyna fah yace nazo nasha kafada mahabeer ya daga yana dariya ya fice Dan yasan Nisha najin motsinsa zata Ari ta kare ficewa yayi Sardauna ya shigo direct kitchen ya nufa Nisha ma ta hada tea ta dauko ta nufo kofa ita zata fito shi zai shiga Karo sukayi saida tea din ya Dan zubar masa akirji saboda tsabar tsorata da kaduwa kasa motsi tayi tsawar da ya buga matane yasa ta Saki cup d’in ya tarwatse ak’asa jikinta ya dauki rawa ta rumtse idanunta”Dan ubanki me kike nema awanan Daren idanu ta bude jikinta na rawa”yaya kayi hakuri wlh ban San kana hanyaba ta fada fitsari na kwararo mata daga k’asan cinyoyinta idanu yazo ganin tana tsiyayar da fitsari dama rigar yar guntuwace cinyoyinta duk awaje saboda tsabar bakin ciki da haushinta wai fitsari take atsaye yasa ya Kara marinta ya harbata da Kafarsa ta fadi k’asa ya taketa ya wuce yabar kitchen din ya fasa shan coffeen ya fice daga parlon fashewa tayi da kuka ta Mike tana jamasa Allah ya isa toilet din parlor taje ta wanko jikinta ta dawo ta sake hadama zee wani tea tana hawaye. ta kawo mata zee zaune take ta kunna wakar larabci Tasha sirot da kwaya ba kadanba Nisha ta shigo tana matsar kwalla zee tace “ke dawa? ” wlh yaya Dr ya dokeni zee cikin masifa tace”Allah ya isarmiki shege Dan iska halan matsarki yajeyi kika kiya ya manmareki ta fada azafafe tanama Nisha wani mugun kallo idanunta sunyi jajir? Idanu Nisha ta zaro” wlh A,A Dan na zuba masa tea ban ganiba ne wlh Allah bai tabani ba shi ba Dan iska bane ajiyar zuciya zee ta sabke ta rumgume nisha ta amshi tea din Tasha suna hira Nisha taje ta sake wanka ta canza rigar bacci suka kwanta suna hirasu har zee ta fara maye tana sambati tana kiran Sardauna Nisha ta Rumgumeta tana mata Addu’a jinta ko Aljanunta ne zasu motsa ahaka har bacci ya dauketa itama Nisha baccine ya dauketa suna rumgume da juna Asuba ta gari,  Dr Sardauna na komawa ya saka kayan bacci yasha lemo guda ya haye saman bed ya shige blanket bai jimaba bacci ya daukesa mahabeer ma yana zuwa yayi alwalla ya fara sallahr nafila sai kusan karfe biyu ya gama yanama zee dinsa Addu’a Allah ya rabata da jinnu yajima kafin ya Mike yai shirin kwanciya bai jimaba da kwanciya barci ya daukesa asubah ta gari,

Advertisements

 

**********************************

 

*Bayan kwana ukku*

 

Bayan wannan lokacin abubuwa sun faru kamar su gabar Sardauna da zee baby ta dore Dan ko dawasa baya kallon inda take itama haka saidai ita rashinsa na mugun daga mata hankali har ta Dan rame sha’awarsa tana damunta ta rasa ya zatayi ta gaji da rashin Sardauna tana bukatarsa tanason gumin jikinsa tanason kamshinsa da sauraron zazagar muryasa da sweet d’in lips dinsa amma haka ta daure ta basar yada ya basar da ita suke rayuwa cikin k’unci da takura Nisha ko tun wahegari da sasafe ta gudu gidansu tace bazata iya rayuwa dukaba dama saboda zee ta matsa abarta ta dado tarinka zuwa makaranta daganan Najib ya kaita gida mahabeer dai yananan ras babu abinda ya samesa soyayyarsu da zee sai abunda yaci gaba suna kula da junansu zee said sangarta take maza iri iri zee ko ita da Aunty amarya basa wani shirin duk da ita zee sam batasan abinda ya faruba ranar amma washe gari fur ta hana ta zaman parlo gashi malam yace karta kuma nemansa sai wa’adi ya cika ita da khalisat farin ciki sukeyi Sardauna ya tsallaka magani jiran lokaci kawai sukeyi na wajan Daddy kuwa tun washe gari da zata hada masa babban aminin mairan karfe Alhaji Nuhu ya rasu a daura daga zuwa ganin dangi dama jikin tsofa ba lfy bace dashi gabaki dayansu mazan suka dunguma daura har Dr amma shi da mahabeer basu kwana ba su Nuhune suka kwana Daddy ko na can shine ya saka bata bashi maganin ba sai yaune zata bashi khalisat yaune zata wanke fuskarta da magani,

 

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

 

da misalin karfe shida na Yamma Dr Sardauna ya bari asibiti ya nufo gida yana zuwa yayi parking ya fito ya rufe motar cikin takunsa na isa da kasaita   ya yake tafiya cike da kuzari waya manne akunnesa sanye yake cikin suit bakake sunyi masifar yi masa kyau gashinsa ya Dan sabko wuyansa said zuba uban kamshi yake ya nufi part d’insu ghaisha  a parlo kuwa baby kowa said zee baby zaune tana game awayarta su Aunty amarya ko tana kitchen Ana k’ulla mugun Abu sai nanah da nawwara na kallon Tv da sallama ya shigo parlon yana waya sai murmushi yake aciki na amsa sanin darajar sallama ko kallo bata ishesaba ya wuce ta gabanta ya nufi kujerun can nesa da ita Wanda ko kallon juna basayi ya zauna tunda na kallesa na dauke kaina zuciyata na bugawa da karfi saboda irin kalaman da na tsinto yana fadama mashakurah ga muryasa ta kashe mun jiki ga kamshinsa kasala naji ta kamani daurewa nayi naci gaba da sha’anina cikin dauriya kiran ya katse dama hira irin kayan da take sone sukeyi dan asatinan zai hado akwatina ganin ita dayace a parlon yasa ya Mike yana kiran ghaisha shiru bata amsaba ya nufi d’akinta  zee tashi tayi jikinta amce tabar parlon bedroom ta shige Nawwara tace”yayamu mama tana gidan Daddah sai Aunty amarya a kitchen juyowa yayi ya nufi kitchen d’in har ya shiga kuma ya fito ya juya zai fita kenan khalisat ta fito daga d’akin Aunty Amarya fuskarta sharf da ruwa cikin farin ciki ta karasa”Yayamun Dr………….✍🏻

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 88

Advertisement *Page 88*   ********************   Ab’angaren maryam kuwa, su Gwaggo suna fita tsohuwar tayi mata wani kallon…
KALLABI
Read More

KALLABI 60

Advertisement BABI NA SITTIN CIF _Assalamun Alaikum yan uwa Barka da warhaka, Nagode sosai Alhamdulillahi jiki an murmure,…
Read More

TARTSATSI 99

Advertisement *Page 99* ********************** Acikin farin ciki ta shige gida, Kai tsaye ta shige d’akin su, ta dannawa…
INAYAH
Read More

INAYAH 33

Advertisement 33_* *_Arewabook@Mamuhgee_* Da zazzabin ta tashi da safe Dan haka sallah kawai ta iya Yi Takoma ta…
IDON NAIRA
Read More

IDON NAIRA 7

Advertisement *_Arewabooks@Mamuhgee_* 7 _ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA…
INAYAH
Read More

INAYAH 15

Advertisement 15_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Cikin damuwa umma yaganah tace” Ga irinta Nan ai Nima Dana biyewa roqonku aka biyo…