Zee Baby Book 1 Page 42

Advertisement

 

 

*👉🏻42*

 

 

….cikin sassarfa ya karaso gareta ya riketa ya mannata jikinsa yana buga bayanta” zainab ki tsaya mana kukan me kike babu inda zani shiru tayi ta kwanta kirjinshi ta d’ago da kanta tana kallonsa murmushi ya sakar mata” my kanwas murmushi ta sakar masa hawaye nabin kumcinta cikin sanyin murya tace”my kanwas lumsassun idanunsa ya zuba mata zuciyarsa na wata irin bugawa ya tallabo kanta hawaye yacika masa idanu ya lakuto. hawayen fuskarta ya lasa” my zainab meyasa zakimun haka me haka yake nufi menene ya faru dake please idan wasane kike ki dainamun kinji murmushi ta Saki ta zuba masa manyan idanunta ta beka hannuta ta shafo hawayen fuskarsa ta lashe ta rike fuskarsa ta maimaita abunda ya fada mata da sauri ya Mike ya cire mata na’uran da ya jona mata ya zaunar da ita ya juya ya nufi gun wata na’ura aikuwa ta fashe da kuka da Sauri ya dawo ya ware mata hannunwasa tazo gareshi Sam batasan

 

hakanba Dole yazo ya Sanya hawansa ya dauketa kamar baby ya rungumeta ” to yi shiru kallonsa take tana shashekar kuka tace”my Kanwas” Na’am my Kanwas please kimun rai kibar kukan ahaka tana jikinsa ya nufi gun Na’uran ya kunna ya dawo bakin gadon ya kwantar da ita harzata fara kuka taga ya zauna tayi shiru jona mata Na’urorin wayarsa ya dauka ya kira Daddy bugo daya ya daga da sallama “assalamu alaikum Dr Allah yasa muji alkhairi”Daddy” please kuzo yanzu hospital harda momyna da ummi duk kuzo kuga hukuncin Allah ya sake sabka akanmu Allah yasake Dora mana wata jarabtar arikice daddy yace” Sardauna meke faruwane? ” Daddy sai kunzo kitt ya tsinke kiran ya kwantar da zee da ta tsareshi da idanu ya shiga duba lafiyarta,  su Daddy sunzo suna waje saida ya kwashe awa daya cur ko ina na jikinsa rawa yakeyi sai sunayen Allah yake kira ya cire abun da ya jona akunnesa dabas ya zauna ya cire mata na’uran ya zuba mata idanu kukanma ya kasa Nabeel ne ya kirasa awaya su Daddy sun matsu suga zainab yace ya kawosu,  kofar aka turo da sallama ya amsa ghaisha da ummi da gudu sukayi gun zee ai tana daga kwance taga mutane na nufota akidime ta Mike zaune ta fashe da kuka ta fada jikin Sardauna tana karkarwa ta boye kanta acikin kirjinshi

 

tana kiransa” my kanwas rungumeta yayi yana buga bayanta ya Kara boyeta jikinsa sosai tamkar cinyeta zasuyi hankalinsa atashe yace” baby yi shiru bari kukan lafewa tayi jikinsa ta rikeshi gam tayi shiru ta lumshe idanunta ya kalli su daddy ” wlh Daddy akwai babbar Matsala batasan kowa ba fah ayanzu sai ni sabode tayi losing memory ta mance kowa da komai nata na baya sai Wanda za’a koya mata yanzu da ita da Wanda aka Haifa yau basuda banbanci Nima abinda yasa ta yarda dani saboda tana bude idanunta nita fara gani ita atunaninta babu kowa cikin duniya sai mu biyu daddy yace “innahlillahi wa’innailaihi Raji’un Allah mun gode maka kuma mun amshi jarabawar da kake bamu ummi Raiyan fashewa tayi da kuka ghaisha ta rungumeta”kiyi hakuri Raiyan zata samu sauki da yarda Allah kinsan bawa baya wuce kaddarasa Daddy yace”Raiyan don Allah kiyi hakuri zata warke insha Allah daddy yazo bakin gadon ya zauna “Dr yanzu yaya za’ayi fitar da ita za’ayi k’asar waje ko yayane?” Daddy zata warke insha Allah akwai maganin da zan dorata akai da yarda Allah lokacin da yaso zata dawo haiyacinta koda yaushene babu yau babu gobe ghaisha taja hannun ummi Raiyan ta zaunar da ita saman kujera ta nufi gun Sardauna ta dafa kafadunsa”Dr Sardauna yanzu ya zamuyi momy ta saba damu ta yarda murika koya mata abubuwa?  Daddy yace tashin hankalin kenan, ai

Advertisements

 

Sardauna ya furzar da iskar bakinsa ya kalli zainab da tayi luf ajikinsa idanunta arufe ta rikeshi gam kamar zai gudu murmushin karfin hali yayi”Daddy muje gida yanzu sai nasamu nayi Mata yan dabaru ta yarda da ummi saboda ta Rika koya Mata abubuwa idan yaso zan kasance ina bata abunci da magani mu dage dayi mata Addu’a zata warke Dr Nabeel yace” Dr ayanzu yarinyarnan bazata iya rayuwa da kowaba sai dakai saboda kaika dai take gani mutum Dan uwanta Sardauna ya kalli Dr Nabeel “Dr kaje ka dubo mun irin magugunan da ya dace mu dorata akai ka kawomun kai Nabeel ya d’aga ya fice ghaisha kukan tausayin zeey ne ya kufce mata Sardauna yace”momy kiyi hakuri Adfu’a zaku mata ba kuka ba janyeta Sardauna yayi daga jikinsa ta bude idanunta ta saka masa kuka”baby tare zamu yi hakuri sabkota yayi daga saman gadon ya shidota k’asa ya rike hannuta boyewa tayi abayansa tana rike da rigarsa daddy yace”Allahu Akbar

 

Allah ya baki lafiya Sardauna yace”Amin ya kwashe wayoyinsa ya kalli iyayan  nasa” Daddy mutafi gida asamu tayi wanka taci abunci mik’ewa sukayi Sardauna yana rike da hannuta ya rigasu fita waje zainab na rike da rigarsa har suka fito yana jiran Nabeel kafarta ya kalla ba takalmi ya cire na kafarsa ” baby bari nasamiki nawa sakarmun Riga idanu ta zuba masa dan bata gane me yake fadiba ahankali ya cire hannunta daga rigarsa ya sunkuya gabanta ya kamo hannuta ya dora akafadarsa ta rike tana dariya ya kamo santaleliyar kafarta fara tas tamkar ta jarirai dan taushi ya saka mata takalminsa sun mata yawa sosai murmushi yayi ya Mike  tsaye ya dagota dariya tayi ta fada saman faffadan kirjinshi tace”my kanwas? rungumeta yayi”Na’am my kanwas kallonsa take tana murmushi shima kallonta yake baima San iyayansu sun fito ba da kallo suka bisu daddy ya jinjina kansa yanajin dadin yada Sardauna yake kula da zeey Dr Nabeel ne ya ISO

 

da leda ya hado Wanda suka samu dafa kafadar Sardauna yai “Dr gasu kallon Nabeel yayi ya beka hannu ya amshi maganin”OK zan duba idan mun isa gida thanks Dr murmushi Nabeel yayi” ai munatare uban gidanmu kai Sardauna ya girgiza ya kalli daddy” my dady mu tafi ya janye zainab ya kama hannunta ummi Raiyan hawaye ya cika mata idanu yau gata ga zainaba amma batasan taba Sardauna yace” dady kuje gamunan zansa takalmi a Office “to sai kunzo Dr hannuta yaja suka nufi Office d’insa ya ciro makullai ya

 

bude yana rike da hannunta suka shiga idanu take zarowa tana kallon ko ina na Office d’in sakin hannuta yayi yaje yasa takalmi da gudu ta biyoshi ta rungumeshi ta baya tace “my kanwas” Ya Salam ya fada yana juyo da ita gabansa ya rike kafadunta ya zuba mata tsumammun idanunsa”baby babu inda zani takalmi zansa kai ta langwabe tana turo baki sakinta yayi ya kama hannunta sukaje yasa, takalmin ya riko hannuta suka fito ya rufe Office d’in suka fito tana rike dashi gam har gurin mota ya bude ya zaunar da ita agaba ya rufe da ya zagaya ya shiga idanunta har sun tara kwalla yana zama ta kifa kanta saman cinyarsa ta fashe da kuka tana kiransa”my kanwas”Ya

 

Allah gani gareka baby ya zanyi Dole fah zamu rabu tunda ba guri dayaba zamu rinka kwana dake ba please ki daure kisaba da rashina ah irin wannan lokacin jikinsa ya janyota yana bubbuga bayanta yakai bakinsa kunnenta” yi shiru baby nine nataba Habibty shiru bazan sake barinki ba ina tare dake baccine zai rika rabamu lafewa tayi jikinsa tanajin dadin maganar da yake mata akunnenta ta lumshe idanunta ta kamo hannunsa ta rike cikin nata gam jin tayi shiru yayi murmushi ya janye bakinsa ya gyara mata kwanciya jikinsa ya tashi motar ya nufo bakin get horn yai aka bude masa get ya fice ana ta daga masa hannu driving yake cikin nutsuwa zuciyarsa babu dadi damuwa tayi masa yawa ga zainab cikin halin da take ayanzu tana bukatar kulawarsa hannusa da ta rike janye  ya dora saman kanta ya shafi gashinta” my baby kanwas kara shigewa jikinsa ta d’ago da kanta tana lumshe masa idanu muryata can k’asa tace”my baby kanwas kallota yayi ya daga mata

gira ya maida hankalinsa kan driving ta maida kanta kirjinshi ta lumshe idanunta Nisha ta kirasa,har sau biyu bai dagaba ahaka har suka ISO gida horn yayi aka bude masa get ya shige da motar nan tskiyar harabar gidan yai parking ya kashe motar,

 

Advertisements

ya dagota”My Baby Kanwas Oya mushiga ciki murmushi tayi ta dora hannunta saman dogon karan hancinsa tanaja kai ya girgiza ya janyeta jikinsa ya bude motar ya fito da ita shima ya fito ya zagayo ya kama hannuta da ido takebin gidan har suka shiga parlon da sallama hafeeza ta taresu da gudu zata riko zee tayi tsale ta makale Sardauna  tana ihu. janyeta yayi ya nufi gun ummi ya zauna zee na daga gefe tana makale dashi sai wani irin kallo takema su Najib da su minata da Tuwusai Sardauna yace” ummi kuje ki gwada mata wanka da sallah da sauran abubuwa agyara mata gashinta kufito ina jiranku na bata abunci da magani sai natafi mik’ewa ummi tayi Sardauna ya mikar da zeey tsaye”baby kuje agyaraki tsaresa tayi da idanu tsaye ya Mike ya kama hannunta yajata har kofar d’aki yaba ummi ita fur taki tafiya ta fara kuka daurewa yayi ya had’e fuska ya daka mata tsawa wuce maza ku tafi nace cikin rawar jiki ta labe bayan ummi tana kiransa”my baby kanwas kai ya kauda”ummi kuje ki nuna mata ya fada yana juyawa ya

 

dawo kan kujera ya zauna kusan ghaisha ya kwantar da kansa kafadarta ya lumshe idanunsa zee ko Dole tabi ummi suka shiga da ta rike mata hannu fizgewa tayi suna shiga ta shiga bathroom ta hada ruwan zafi tazo tajata tana tirjewa harda kuka tana Kiran my kanwas haka tajata ummin kanta hawaye take daket ta cire mata kayan jikinta ta nasata cikin ruwan gumin tana zuba mata ruwan har kanta da kanta tayi mata wanka har dukanta take amma saida ta wanke tas har gashinta bayan ta gama mata ummi ta tube ta kunna shower ta dauki soso da sabulu tana wanka zee ta fito itama ta tsaya gaban shower ta amshi soson tayi duk yada ummi tayi tana murmushi towel ummi ta d’aura itama ta d’aura ummi tayi Alwalla zee ma tayi suka fito tana karda gashinta tana dariya gaban dressing mirror ta janyota ta tsane mata gashinta ta shafa mata man gashi ta dauré mata da Ribbon yada ummin tayi abaya mai kyau ummi ta dauko mata ta bata ummi ta dauko tasaka itama ta saka tayane mata kanta da mayafin abayar

 

Darduma ta shimfida itama zee tazo ta tsaya gaban ummin tana kallon tana turo baki tace”my kanwas ta fada tana nuna kofar daki janyota tayi suka kalli alkiblah ummin ta tayar da kabarar sallah duk abinda ummin tayi cikin hukuncin Allah shi zee takeyi sukayi sallah isha’i bangaran Sardauna ghaisha ta shafi kansa”Auta kayi hakuri kafara cin abunci ansan mutuwa da ciwo amma babu yada muka iya daddy yace”Faisal ka dauré muyi ta wakali mu amshi kaddara kaga yada Allah ya sake jarabamu ta fannin zainab minata ta share hawaye tace”wlh ina tausayinta sosai baiwar Allah sai abinda aka koya mata Sardauna jinsu kawai yake dan basu fishi shiga damuwaba dauriya yake ga rashin d’an uwansa na ragargazar zuciyarsa ghaisha ya kalla”momyna kanshi ta kuma shafawa”Na’am Autana me kakeso? ” babu komai ya fada yana murmushin karfin hali” zakasha coffee?  su ummi ne suka fito zee tasha abaya mai kyau da mayafi da gudu tayi kan Sardauna fuska ya had’e ganin yada yayi yasa ta karasa anutse ta zauna kusansa tana kallonsa ta matsa ta kwantar da kanta kafadarsa”my baby kanwas daddy kallonsu kawai yakeyi janyeta yayi ya Mike ya kama hannuta ya dauki ledar maganin

 

ya nufi kan dining.kujera yaja ya zaunar da ita ya dauki plate ya zuba mata abunci jalof d’in shinkaface taji busashen kifi shi ba ciba yake amma Dole ya zuba ya zauna ya dauki spoon ya ya tsakuro yakai bakinsa murmushi tayi ta dauki spoon d’in ta tsakuri abuncin takai bakinta tana kallonsa kai ya daga mata” Oya baby ci sake daukowa tayi tanaci ganin tanaci ya ajiye spoon din hannusa itama ta ajiyewa tai” baby kici mana kafada ta makale tana kallonsa dauka yayi ya tsakuro yana bata da kansa tako amsa tanaci ta matsa ta kwanta jikinsa ahaka ya bata abuncin har ta koshi ya bude robar ruwa ya dago kanta ya kafa mata robar ta rika sha saida yaga ta dan sha mai yawa ya barta ledar maganin ya bude ya duduba ya b’aballosu ya tallabo kanta ya zuba mata cikin baki ya dauki robar ruwan ya kafa mata abaki tasha saida ya tabbatar ta shanye ya ajiye ya rungumeta yana shafa kanta sanin maganin yanzu zai fara aiki don bayaso tayi kuka idan zai tafi d’ago da kanta tayi tana kallonsa hannuta saman dogon hancinsa tana Ja tana murmushi gira ya daga mata yana hura mata iskar bakinsa yana shafa lallausan gashinta suna kallon junansu idanu ta lumshe yada yake hura mata iskar bakinsa ta kara rikeshi gam. ganin alamun bacci sun fara baiyana ya mikar da ita ya dauki ledar maganin ya riko hannuta sai lumshewa take ya ratso ta parlon suka shige dakin ummi ya kwantar da ita ya zauna yana shafa kanta kin kwanciya tayi ta tashi ta kwanta cinyarsa barinta yayi yana buga bayanta ko 5 minute batayi ba tayi bacci ya kwantar da ita ya rankwafa ya sakar mata kiss saman lips d’inta da

 

goshinta ya shafi fuskarta”my zeener da sonki zan mutu wlh ina mugu mugun sonki da kaunarki amma babu damar zama dake tabbas nasan sai sonki ya kasheni zuwa GABA zuciyata inada yakinin zata buga akanki nayi miki alkawalin tsayawa na kula da rayuwarki har Allah ya baki lfy ki warke na zaba miki miji nagari ki aura rungumeta yayi yana wani irin sabke ajiyar zuciya”my zainba i love you kece bugun numfashina ina sonki sonki kasheni zaiyi nan GABA kadan sosai ya rungumeta da karfi yana sabke Numfashi da karfi saida ta motsa tana kiran “my kanwas tana rungumeshi “Na’am bugun numfashina janye jikinsa yayi ya tofa mata Addu’a yaja blanket ya lulubeta

Ya Mike ya fice daga d’akin ya fito parlo Daddy yace “Allah ya biyaka Sardauna yace”Ameen daddy yayima iyayansa sallama ya tafi hafeeza ta Mike ta nufi dakin tana hawaye tuwusai tace”bawan Allah wlh dauriya yake yaron yanada damuwa ghaisha ta share hawaye tace”ai Dole rabuwa da dan uwa rabuwa ta har abadan ga el uwasa cikin mawuyacin hali ummi tace “khadijah hakuri zamuyi mu amshi kaddara daddy yace” mutumin da Allah baya jarabarsa ai ba mutum bane yayi kuka da kansa minata tace” niko Abdulmutallab inada magana amma bari naga Daddah tukun da mai ran karfe?  kai ya jinjina” to Allah ya kaimu goben saboda dare yayi kowa ya Mike ya nemi makwancinsa ummi tana shiga tayi shirin kwanciya kafin karfe biyu ta tashi sallah ta kalli hafeeza da ta rungume zainab hawaye ya bushe kan fuskarta har bacci ya dauketa saman gadon ta hauro ta kwanta gefen guda ta rungume zee tana shafa kanta tana tofa mata Addu’a” hafeeza yau jikin el uwa akayi bacci Allah sarki ta fada tana goge hawaye tana tunanin yaranta da iyayanta kullum burinta mahaifinta da mahaifiyarta su dawo gareta da ‘ya’yanta ahaka har bacci ya dauketa Asubah ta gari,

 

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

 

Sardauna lokacin da ya isa gida Nisha tana parlo tana jiransa hankalinta atashe sai sunturi take ta kasa, zaune takasa tsaye ta hada cikin kayan bacci farare tas Riga da wando knocking taji anyi da gudu nufi kofar ta murza key ta bude yana sayo kafa ta fada jikinsa ta fashe da kuka ta rungumeshi”my heartbeat ina kashiga ina kiranka baka dauka rungumeta yai yana buga bayanta yakai bakinsa kunnenta”My Neesher Sorry ki yafemun naga kiranki banida nutsuwane yi shiru bari kuka my Neesher ina cikin koshin lfy kinji matata shiru tayi ta kara shiga jikinsa tana sabke ajiyar zuciya daukarta yayi cak” muje ki kwanta ya babyna?  fuskarsa ta shafa ta sakar masa kiss ” my Dr inajin sonka kamar zai kasheni ta fada tana lasar fuskarsa “no maman babyna muna tare insha Allah inason zama dake ya fada yana shiga bedroom d’insa da ita saman makeken royal bed d’insa ya zaunar da ita ya lakaci hancinta”Nessher Dr kinci kaza ko naje na kawo miki? ” naci sai da safe “gud ya fada yana cire kayansa bathroom ya shiga ya santalo wanka ya fito daure da towel yana goge jikinsa ya murza maiyuka masu kamshi Nisha ta dauko masa kayan bacci masu kyau ta saka masa yana kallonta bayan ta saka masa ta dauko turarensa mai masifar kamshi ta fesa masa” thanks my Neesher murmushi tayi kwanciya sukayi ya kashe wutar dakin ya janyota jikinsa ya lulubesu ya dora hannusa saman cikinta yana shafawa” my Dr? ” my Neesher Oya muyi bacci ya fada yana kara shigar da ita jikinsa dan sam bashida nutsuwar da zai iya Saduwa da ita lamo tayi jikinsa hannunta saman fuskara tana shafawa” Dr ina sonka sosai kanta ya tallabo ya sakar mata kiss ya lalubo bakinta yana tsotsa yana shashafata jikinta ta sakar masa tana lumlumshewa har ya rikitata bacci ya dauketa bakinsa ya zare anata ya rumgumeta yana tofesu da Addu’a bai jimaba  bacci shima ya daukesa ransa babu dadi sam baya cikin kwanciyar hankali jarumata kawai yake saboda shi Mutumne mai dakiya da tawakali Asubah ta gari Sardauna and Nisha…………✍🏻

 

 

*Bazan gaji da Mika muku godiyata ba bisa irin gudumuwar da kuka bada wajan yin Addu’a akan batan Fareesa har Allah yaji kanmu ya fito da ita lokacin da muka cire rai da samunta kwana da yini har yanzu kukan farin ciki da tausayin yarinyata nakeyi Allah nagode maka suko Allah ya Toni asirinsu😭😭😭😭😭😭*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 32

Advertisement *page 32* ********************* Hafsa suna tafe a cikin mota, Abba yana ta bata hakuri akan ta kwantarda…
KALLABI
Read More

KALLABI 4

Advertisement *<Babi Na Huɗu>* _Soyayyar gaskiya tana faru ce a bisa wasu manyan ginshikai! Imma ƙaddara ta haɗa…
KALLABI
Read More

KALLABI 8

Advertisement Babi Na Bakwai>* *Godiya da fatan alkhairi son so daga Mai Daraja😍🔥* Barka da Juma’a# Masarautar Gobir.…