Advertisement
(Yau Laraba/11/ ga watan Rabi’ul Auwal 1809. Karni na goma sha takwas)
Da gudu Mahayi ya shigo masarautan tare da rike wasikar hannun shi, ya shiga har farfajiyar masarautan. Tsare shi sarkin Fada yayi tare da cewa.
“Ilu dan Audu, Audu dan Uwaisu. Farin me farin aniya, baka zama jakadan alkhairi sai ta sharri”
Dira yayi a kan dokin sannan ya wuce fada Sarkin fada yana biye da shi. Ilu dan Audu, dan sako ne duk wani sakon da zai zo fada toh ta hannun shi yake zuwa, kasancewar masarautan sun tafi yaki da wasu kabilar da take gabashin masarautan kuma babban abun damuwa shine karfin da wadancan kabilar suke da shi idan suka samu karfin ta hanyar kabilar Fulani waɗanda ake kiran su Rumada.
Kasancewar suma Rumada bayin Fulani ne, kuma suna da matukar tasiri da karfi amma basu cika shiga abinda babu ruwan su ba, abinda ya kuma fusata masarautar Gobir ba kome bane sai yadda kabilar da suke kara samun ƙarfi sama da kowacce ƙabilar. Kasancewar su din kabilar sun fito daga kwararrafa ne, ana da yakinin Banza Bakwai ne, da suke da makotaka da Zamfara. Kafin Gobirawa su kwaci mulkin Sarkin Zamfara. Wanda shi da wadannan kabilun guda uku suka cure domin yaki da gobirawa.
Zubewa yayi a gaban Sarkin rikon kwarya, wato Sarki Bello na biyu.
“Allah ya taimaki mai martaba! A can filin dagga ana fama da yaki kamar yadda Yayanka mai Martaba sarki Ibrahim ya tafi wakilta wannan masarautan.” Shiru yayi lokacin da Zakaria ya shigo. Sunkuyar da kai tayi kafin ya d’ago kai yana kallon Sarkin Bello me rikon kwarya ya ce.
“Sai hakuri, domin sarki Ibrahim ya kwanta dama” a wani irin zabure mai martaba sarki Bello ya Mike. Jikin shi yana rawa.
“Karya kake bawa! Karya kake bawa! Taya Jarumin sadauki irin mahaifina ba zai mutu a banza ba” wani irin kuka ya sake tare da kallon Sarki Bello cikin shashekar kuka ya ce.
“Wallahi ba zan yafe hakkin mahaifina ba” riko shi sarki Bello yayi cikin matsanancin tausayi yana bubbuga bayan shi yana cewa.
“Kayi hakuri, Allah ya gafarta mishi.”
Abin tausayi baki daya masarautan ta kare yaran kabilar Gobir da suke mulki sun kare sabida yakin da suke da kuma faffatawa.
“An binne shi a can, amma mun samu nasarar farattakar mayakan da maciya amana, sannan mun dauko wasu yan tawaye zamu tawo dasu da bayin da aka kama”
Cikin wani irin shashekar kuka Zakaria,.ya mike tare da nufar cikin gidan sarautar. Wanda izuwa yanzun labarin mutuwar mai martaba sarki Ibrahim ya karade cikin gidan. Kasancewar yana da ƙarancin shekaru yasa ta zama abin tausayi. Mikewa Sarki Ibrahim yayi sannan ya kalli Chiroma.
“Idan kome ya lafa zan ba shi mulkin shi tunda na shine ni rikon kwarya nake” ya fada cikin sansayar murya wanda dama halin shi.
“A’a Mai Martaba, idan har kai aka bawa mulkin muna da yakinin yaki ya kare, idan kuma aka bawa wani tabbas yanzu aka fara domin yakin bai kare ba” inji Galadima. Domin yakin har da Wazirin masarautan aka tafi.
“Wannan maganar gaskiya ce, matukar muka sake ka bar mulkin baki daya masarautan Gobirawa zai zama tarihi. Amma idan muka barka akan mulkin nan ba mamaki zamu samu salama da nutsuwa, sannan Allah ya albarkaci da abubuwan cigaba. Idan kuma aure kake bukata zamu nima maka auren daga ya’yan manyan masarautu. Da suke zagaye da mu har ketaren mu.” Inji Chiroma.
Advertisements
Duk yadda Sarki Bello ya so kauce musu, haka suka mishi dabaibayi da mulkin. Har aka dawo da mutanen da suka tafi yaƙi. Inda aka dawo da Waziri cikin wani mugun hali. Domin kuwa ya jikata sosai dan dole aka kai shi gidan shi Jinya.
A cikin gidan sarauta kuwa akwai yaran Sarki Ibrahim marigayi, uku mace daya, maza biyu Zakaria shine Babba mahaifiyar shi me Suna Gambo, baiwa ce kafin sarki Ibrahim ya yantatta. Sai matar shi Ajuji wacce ya haifi yara mata biyu. Fulani Kyauta domin an tabbatar da ta jima kafin ta haihu har ana mata gorin haihu. Sai na biyun su Yakubu ana kiran shi sarkin yaki,. kasancewar an haife shi ne a wani rangadin da Sarkin yakin sarkin musulmi yazo Zamfara zai wuce sokoto. Shine ya tsaya a masarautar Gobir. Inda yana isa aka ce ai mai dakin sarki tana kan gwiwa. Shine yayi tofi aka kai mata ai kuwa tana sha ko minti ɗaya ba a kara ba ta haifu danta namiji. Koda aka kawo yaron fada, Sarkin yakin sarkin musulmi yayi mishi addu’a. Sannan ya wuce anan mai martaba da manyan fada suka yanke hukuncin yiwa Sarkin yakin sarkin musulmi wato Sarkin Bauchi a lokacin.
Sai sauran dakunan kuwa kwarkwarori ne, kuma basu haihu ba.
Duk wannan yanayin da aka gaya musu labarin yasaka jikin kowa yayi sanyi musamman da masu kishin akan danta ne zai yi mulki, sai gashi an fitar da sanarwar labarin Sarki Bello za a rantsar. Kasancewar Yarima Zakaria shekarun shi sha takwas ne, sai Yakubu me Shekara sha biyar, Fulani Kyauta. Tana gab da za a aurar da ita ne.
Wannan tsarin da akayi ya fitar da tashin hankalin da ake samu tsakanin Gambo da Ajuji, dan dole suka rungume ƙaddara. A lokacin Sarki Bello yana da shekaru talatin a duniya, babban damuwar shi yayi rayuwa ta yanci da walwala yana son koda zai yi aure baya son ya auri yar mulki domin zata iya saka shi ya bukaci mulki shi kuma abinda ya tsaya nake nan.
Bayan wasu watanni aka shirya bikin nadin sarautar sarki Bello, wanda aka kai gayyata ga sarakunan yankin gaɓar kogi Chadi zuwa bainuyo, sannan aka kai har zuwa kwara kasancewar tarihi ya tabbatar akwai milawa Fulani ne kuma Gobirawa ne, sannan aka kai yankin kasar Gombe inda Sarki Muhammad kwairanga yake mulki.
Sannan aka kai masarautar Kano, zuwa Yola inda Modibbo Adama yake mulki. Sannan aka kawo Bauchi ga Sarkin yakin sarkin musulmi. Kafin aja wuce da na zaria, domin shine nadin sarautar da za ayi na Muhammad Bello na biyu. Wannan nadin sarautar ya tara al’ummar sarakuna daga manyan yankunan arewacin kasar. Sannan an kai sakon gayyata har maradi domin can ma akwai wata masarautan Gobirawa. Kuma sun tabbatar zasu zo ayi bikin da su.
Lokacin da za ayi nadin Sarkin Musulmi da kan shi, ya halarci taron nadin sarautar, yadda mutanen Fada suka gayawa sarki Bello, sun roke shi da ya fada ba zasu kuma yaki ba, idan ma za ayi yakin toh sai ta hanyar yad’a kalmar Allah. Wato jahadi.
Haka kuwa ya kasance, mulki aka bashi bayan nadin sarautar da kwanaki Allah ya amshi rayuwar Wazirin sarki Ibrahim,me suna Musa dan Musa. A lokacin yaran Waziri sun so a basu sarautar gidan su, amma kasancewar akwai sauran sarakuna sai suka bada shawarar a bawa Zakaria waziri duk da lokacin shi din Yaro ne, haka Sarki Bello ya janyo shi har cikin fadar. Sannan yaki kallon Zakaria a matsayin dan Yayan shi, kallo yake mishi irin na wa da kani.
Shima kuma Zakaria yana mugun ganin girman Sarki Bello, idan ka cire Yakubu da kiri kiri yake adawa da sarki Bello. Tare da gaya kishi cewa.
“Ka bar murna karen ka ya kama kura! Inda rai da rabo wata rana kallo zai koma sama shawo ya dauki giwa” domin wani irin masifaffen kishin sarki Bello yake sannan ba iya shi ba hatta dan uwan shi Zakaria. Sai da Yakubu ya farmake shi kamar zai kashe shi.
Wannan yasa aka saka Idanu akan Yakubu domin adawar shi tana kazamta. Sannan bai da burin da ya wuce ya nufi Katangar bayi ya saka ana ware mishi kyawawan yan mata ana kai mishi dakin shi. Yana tarayya da shi kuma mai Martaba yaji labarin bai da ikon ya hukunta shi domin a cikin wannan yanayin baya son a samu rabuwar kai…
_____________________________________
Hello’ Fanmily dama na gaya muku zaku iya samun posting kafin Azumi… Karku manta labarin FREE BOOK ne… Comments da Voting shine price na labarin.
And inshallah zai na zuwa muku sau uku a sati Daya.. Saturday. Monday. Thursday inshallah…. Sabida ina da abubuwa dayawa kuma ina typing paid book so.
#Freestory
#mai_Dambu….
Advertisements
GIPHY App Key not set. Please check settings