KALLABI 10

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*<Babi Na Goma>*

_Gaisuwar wannan shafin naki ne Mrs Sadauki Mom Nasmah sakon ki ya iso Nagode sosai_

“An gama Allah ya baka nasara” Galadima ya fada a sanyayye, domin ya jima bai ga fushi ko fusata a idanun shi ba, balle ya ji maganar b’acin rai.
“Kayi hakuri.” Cire rigar shi yayi tare da juya bayan shi.
“Subhanallahi! Kana bukatar kulawa fa”
“Kar bashi ka nimo masu laifin” ya fada bayan ya mai da rigar, fita Galadima yayi ya turo masu maganin masarautan amma fir Mai Martaba ya ki bada ciwon a duba mishi, kuma guba ce domin sake rura fatar shi take. Haka ya fito ya nufi shashin Fulani Aminatu da zazzaɓi ya rufe ta.

Tana barci ne amma sai firgita take, tana matse hannun ta. Yana zuwa ya zauna a inda take ya riko hannun ta, sannan ya kalli Innayoh.
“An zo an duba ta?”
“Eh an zo” ta fada cikin girmamawa, fita suka yi aka bar su a wurin, abu ya ciro a cikin rigar shi ya saka mata a kasar matashinta, sannan ya fita. Dakyar ya isa kofar shi kafin ya zube akan gwiwar shi yana dafe kirjin shi. Ai kuwa amai ya fara wani irin bakin jini. Kakarin aman shi masu tsaron shi suka jiyo sai gasu da gudu, kafin kace me har sun kinkime shi sai turakar shi. Suka kwantar da shi a kife sabida nuna musu bayan shi da yayi.

Sarkin gida ya tafi har gidan galadima ya kuma kiran shi.
“Amma dai Bello akwai dan banzan taurin kai kamar arnan farko sai da na hana shi fita ya tsaya a kawo mishi magani” har suka isa turakar fada yake, sannan ya saka aka yaga rigar aka zuba mishi magani.
“Sarkin gida ina zan samu danyen madara”
“Ba za a rasa a wurin Innayoh ba, domin daga gidan gonar masarauta ana kai mata.” Sarkin gida ya fada yana kallon Galadima.
“Maza amso min”
Fita yayi da sauri ya amso madaran, yadda ya gayawa Innayoh halin da mai Martaba yake ciki ya d’aga mata hankali, domin gani take kamar laifin ta ne da ta bar Fulani Aminatu ta fita.

Har wurin magariba Mai Martaba bai dawo hayacin shi ba. Shigowar Waziri Zakaria ya saka suka zuba masa ido.
“Ya jikin Baffana yake?”
“Sai godiya amma ba a magana domin bai san wanda yake kan shi ba” inji Sarkin gida. Galadima kan bai d’ago kai ba, sai da ya samu Mai Martaba ya shanye madara da maganin nan, ko dakika dari da ashirin ba a dauka ba, ya fara kokarin amai, saka mishi wani tasa aka yi bayan ya mike zaune, ya shiga amai sosai sai da ya fitar da gubar. Sannan ya kalli galadima ya ce mishi.
“Ya Fulani Aminatu?” Sannan ya koma ya kwanta. Sai barci me nauyi yayi gaba da shi.

Ajiyar zuciya suka yi sannan galadima ya umarci Sarkin gida da ya kula da shi. Sannan suka fita baki daya suna jajjanta abinda ya faru, dake a shashinsa aka yi sallah la’asar magariba kuma Galadima ya wuce masallaci a can ake sake jajjanta mishi abinda ya faru.

Bayan ya idar da sallah Yarima Yakubu ya ce.
“Dake ragon maza ne shi yasa ta kare mishi”
“Ce maka aka yi jarumta kamar niman bayi mata ne da wasu suke amfani da matsayin su?” Waziri Zakaria ya tambaye shi.
“Eh na yarda da haka duk ranar da na samu dama sai na fille kan kowa” Yarima Yakubu ya faɗa yana kad’e rigar shi.

Kallon juna suka yi Galadima da waziri, cike da mamaki domin da alamu Zakaria ya Haukace.

**
Sanyin asuba ya rab’e shi kasancewar an bar tagogin a bude, yasa shi buɗe idanun shi yana sauke ajiyar zuciya.
Tashi yayi zaune yaji garau. Murmushi yayi yana kallon tagar. Sannan ya hango Sarkin gida yana ta sharan barci. Ban daki ya shiga ya zauna yana me kallon tagar. Tunanin jikin Fulani Aminatu yake, ya jima a wurin kafin yayi wanka. Ya fito a hankali ya shirya. Ya saka kayan sakin shi sannan ya gabatar da sallah da ya rasa, kafin ya nufi filin bayan gidan Fulani Aminatu, ya shiga wasa jinin shi. Kiran sallah ya tsayar da shi ya tafi sallah, bayan ya dawo ya cigaba.

Advertisements

“Fulani tashi asuba tayi.” Innayoh ta tashe ta,
“Innayohhh!” Ta fada a sangarce,
“Tashi lokaci ya kure, zaki kaiwa Baffa’m ɗinki madara” da sauri ta tashi zaune tana raba idanun.
“Innayoh! Gaskiya ba zan je ba zai min fada”
“Me kika mishi?”
“Babu” ta fada tana wani tura baki. Kallon ta Innayoh tayi, ta dauke kai tana me sauka a gadon.
“Fulani kin shiga kin mishi bar…”
“A’a fa, ban shiga wurin shi ba” ta fada da ƙarfi tana shiga ban daki.
“Allah ya kintsa ki” inji Innayoh,

Bayan yayi alola tazo innayoh na kallonta, har ta idar da sallah sannan ta fita can sai gata dauke da magani da kuma madara.
“Innayoh kullum sai na sha magani nan ne? Ba dadi” ta fada kamar zata yi kuka, yadda Innayoh ta b’ata rai yasa ta amshi maganin ta sha, sannan ta dauke madaran ta shanye tass. Wannan shine al’adar Innayoh kenan.

Kwanciya tayi bayan Innayoh ta saka ta tayi wanka, ta shirya ta cikin wasu kaya masu kyau, an jera mata kayan kwalliya irin na matan sarakuna. Sannan ta kwanta. Baki daya ta manta da batun dan dalago barcin ta kawai take, bayan kusan awa guda. Taji karar takuba. A hankali ta tashi fita tayi babu wanda ya sani ta nufi inda take jin sautin. Daga nesa ta hango shi dan dalago yana cin ya’yan itaccen da aka yanka mishi a wani tire. Da wani irin farin ciki ta karta a guje ta dauke shi tana faɗin.
“Dan dalago na” ta wani rungume shi, yana jinta bai juya ba ya cigaba da abinda yake, wurin shi ta nufa tana kallon shi.
“Baffa’m!” Sauke takobin yayi, ya kalle ta da wutsiyar ido.
“Nagode da ka kula min da Babban abokina, da ya mutu da nima na…” Kura mata ido yayi yana jiran yaji me zata ce.
“Da ban san ya zan yi ba nima, Hamma Buba ne ya bani tun yana dan karami. Ina kewar shi sosai” ta fada idanun ta,yana zubda kwalla. Haka kawai ya tsinci kan shi da tambayar ta.
“Me ya kawo ki masarautan nan tunda kina kewar hammanki?” Kallon shi tayi sannan ta tab’e baki ta ce mishi.
“Ban san dalilin da yasa aka kawo ni ba, Innayoh ta ce idan na girma nayi hankali zan fahimta, amma karka gayawa kowa dan tace babu kyau na fadawa wani” ta fada cikin shahshanci da shirme.
“Ai daga ni sai dan dalago muka ji idan ma kin ji labarin a wani wurin toh ga wanda ya faɗa!” Ya nuna mata dan dalago.
“A’a yana magana ne?” Ta tambaye shi, tana zare ido alamar a tsorace take.
“Kwarai tunda ai ba ni na baki ba? Kuma zai gayawa Hammanki duk abinda ya faru, dan haka ki yar da shi domin munafuki ne” k’amk’ame dan dalago tai tana kuma kallon shi.
“A’a ba zan yarda shi ba, Hamma na ne ya bani shi tun yana jariri”

Share ta yayi domin ya lura ba zata tab’a yarda ta rabu, da dan dalago ba, shima kuma bai san ya akayi yake son ta rabu da zomon ba. Ajiye dan dalago tayi ta zauna tana kallon yadda ya dauki baka yaja. Sannan ya sake a jikin mutum mutumin ciyawa da aka ayi. Kallon shi tayi ta ce mishi.
“Baffa’m!”
“Hmm!”
“Ka koya min nima” ta fada tana mishi kwal-kwal da idanu.
“Aikin maza ne ba na mata ba” ya fada yana cigaba da harbawa.
“Don Allah” ta fada cikin wata irin murya, sake kwarin yayi ya juya yana kallon ta.
“Kin ci abinci kuwa?”
“Na ci”
Zuwan su Innayoh wurin ya sata juyawa.
“Innayoh kice ya koya min” sumkuyar a kai Innayoh tayi da sauran bayi matan.
“A kula da ita ta daina fitowa da rana ko da sassafe”
“Baffa’m” ta fada hawaye na zuba mata, bai kula da ita ba. Ya cigaba da abinda yake yi har aka wuce da ita. Sakata suka yi a tsakiyar su, a hankali ta juya tana kallon shi yana abin shi. Juyawa tayi ta cigaba da tafiya, sai lokacin ya juya yana bin su da idanu. Bayan ya gama horon ya koma sashensa yayi wanka sabida zufar da yake karyo mishi.

…..
Wajen hantsi aka fito da wasu bayi mata biyu, sun ki magana kawai sun amince da sune suka turo macijin. Shiru fada yayi kafin ya bude baki kamar ba zai magana ba ya ce.
“A kashe su.”

“Mai Martaba! Babu kuskure a hukuncin ka?” Inji Chiroma,
“Me zan musu? A cikin gidana a da’irar sansanina suka farmaki matata?” Ya fada,
“Haka ba zai kara kome ko ya rage kome ba, sai dai tarin bakin jini da ita Fulani Aminatu” Yarima Yakubu ya faɗa bayan ya mike zai bar fadar.
“Wannan shine mafi munin yanayi a tarayyar ka da Yarinyar da aka alakanta rayuwar ka da ita” ya sakai yafita.

**
Zauren Fulani Aminatu.

Jakadiya Rama ce a bayan Ajuji, bata zauna ba tana tsaye tana kallon kyawun zauren Fulani Aminatu.
“Lalle maraba da zuwa, yau muke shirin kai Fulani taga Yayunta”
“Ba zuwan tattaunawa nayi ba, an san Fulbe da kunya da kawaici sai ga labari yana yawo a cikin gidan Fulani Aminatu ta yarda da al’adar su tana bin Mai Martaba har turakar shi? Koda yake taya yar kwarkwara zata yi kunya! Kamar yadda kika saba turata ki turata ta hana shi idda nufin shi na kashe bayin da basu ba basu gani ba. Idan tayi hakuri zata isa inda yake, karki manta a nan macen da ta isa mace take rike kambunta ba kwaila ba”

Har ta juya zata tafi, Innayoh ta ce mata.
“Mace da ta isa mace ita Jarumin sarki ke bada rayuwar shi domin kare nata, idan har kwarkwarah tana da bakin magana toh tabbas matar sarki idan ta tashi magana ba za a ji muryan kowa ba! Ba zan raba had’in da Allah yayi ba, sai dai maki gani zai iya mutuwa”

“Ke baiwa!” Ajuji ta daka mata tsawa, murmushi Innayoh tayi sannan ta ce mata.
“Fusatar na me? Kin ji haushi ne? Idan rana tafito tafin hannun bai kare shi. Iya yau gare mu gobe ta Allah ce kiyi shiru ki ja bakin ki koma gefe kiyi kallon abin da zai faru ga sarki da Kwailar matar shi, barin da ba zai tab’a goguwa ba a tarihin masarautar nan labarin da zai zauna daram a zukatan al’ummar wannan yankin. Mun iya magana amma mun fiso ayi maganar mu haka zai karawa shukar mu yabbanya”

Kasa magana Ajuji tayi ta saka kai ta fita, sannan ta juya ta kalli Fulani Aminatu, da tayi tsuru-tsuru tana kallon su. Baki daya ba zata ce ga inda Maganar ya dosa ba.
Dan dukawa kaɗan Innayoh tayi tana kallon Fulani Aminatu.
“Daga yau ba zaki kuma fita ba, ki zauna anan, amma zan tura ayi magana da Baffa’m ki roke shi da ayi musu afuwa”

Hannun ta Innayoh ta rike, tana kallon ta kamar zata yi kuka.
“Innayoh yaushe zamu bar nan bana son nan mu koma gida” murmushi Innayoh tayi sannan ta ce.
“Zan kika fara zaman nan”

Advertisements

Mikewa tayi ta saka aka kira mata sarkin gida, can sai gashi ya zo.
“Fulani tana son ganawa da Mai Martaba ka gaya mishi”

“An gama” sannan ya fita, har fada anan kan tattauna batun abinda ya faru jiya, sarkin gida ya gaya mishi sakon Fulani Aminatu. Babu musu ya mike. Gyara murya Waziri Zakaria yayi ya ce.
“Baffa’m” cak ya tsaya kunya ta kama shi sam ya manta ko zai tashi sai an sanar yau sai gashi ya mike. Komawa yayi ya zauna, yana muzurai. Take sarkin fada ya fara kokarin mikewa yana faɗin.
“Gyara kintsi! Mai martaba zai tashi aikin gaggawa” watsawa Waziri harara yayi, yana tashi ya nufi shashinsa, Waziri da Galadima suna biye da shi. Yana shiga ya cire kayan baki daya ya sauya. A zauren shi ne farko ya gansu zaune dauke kai yayi kamar bai gan su ba.
“Baffa’m” inji Zakaria,
“Ban san yaushe na zama kakanka ba, amma zan hukuntaka zan baka aikin kula da bakin da zasu shigo da fita na masarautar nan baki daya daga yau aikin ya fara”
“Baffa sabida kawai nayi abu karami za a mai dani duba gari” Galadima bai ce uffan ba, sai da ya fita ya mike shima yana faɗin.
“Yawwan duba gari idan ka fita”
“Kawu har da kai?”
“Toh na daina”

Shi kuwa yana fita ya nufi shashinta ta, tun daga babban zauren ya fahimci yar sakalcin tana daki, yana shiga ya same ta, da dan dalago.
“Yawwa dan dalago, yaushe samu tafi gida na gaji da nan” gyaran murya yayi U shiga cikin dakin. Gyara zama tayi tana kara daura zomon kan cinyarta.
Shiru yayi yana jin tana zuba shirme da dan dalago.
“Tashi” ya fada mata, mikewa tayi ya kalle ta da kyau sannan ya ce mata.
“Baki iya kawo ruwa bane ga bako?” Ajiye zomon tayi, ta fita tana faɗin.
“Ai Innayoh ta gaya min” ta fada bayan ta nufi wani daki na musamman da aka ajiye kayan Abincin da aka tanada, wani tire ta dauko ta kawo dakin, an saka dan gamon da ake sakawa a kasan kwarya ya rike yar kamar ƙwaryar da yake rufe da damammen fura da nono. Sai kamshi kanumfarin da masoro da citta yake.

Dauka tayi ta mika mishi, tana faɗin.
“Baffa’m amsa ka sha?” Ba musu ya amsa, ya dama a hankali sannan ya fara sha, yana kallon ta komawa gefe tayi can ta zauna tana wasa da dan dalago.
“Zo kisha”
“A’a na koshi”

“Toh zaki dauki kayan ki” a hankali ta taso, tana kallon shi kafin ta ce mishi.
“Me yasa ba zaka sha ba?”
“Ban iya cin abinci ni daya ba”
Zama tayi sannan ta ce mishi.
“Innayoh ta hana ni cin abinci da wani”
“Ni ne wani?”
Sunkuyar da kai tayi tana matse hannun ta.
“Waye ni?”
“Baffa’m”
“Toh daga yau ni ba baffa’m bane, Nima ina son zama abokin ki kamar yadda kike daukar dan dalago”

Sake baki tayi tare da cewa.
“Toh ai kai ba zan iya daukar ka ba, kayi kato” ta fada kamar zata yi kuka.
“Toh lallai dole kiyi abokata dani”
“Ayya taya zan dauke ka kamar dan dalago?”

*Da alamu idan aka kwana biyu kallon dan dalago zata maka ka yanke dan banza ka huta, domin shi ya hana ka samun kanta*

“Toh shi kenan, me yasa kika tura a kira ni.” Shiru tayi tana kallon kasa ta rasa me yake mata dad’i domin ta manta yadda suka yi da Innayoh.

“Baki ji bane?” Da sauri ta d’ago kai tana kallon shi kafin abin ta dawo mata rai, d’ago kai tayi tare da amsar ludayin hannun shi. Tana sha tana magana baki daya jikinta rawa yake ta ce mishi.
“Baffa’m! Ka gayawa Mai Martaba ayiwa su Hakama da Arewa afuwa ba zasu kuma ba. Idan aka kashe su ba zai kawo karshen kiyayyar ba. Haifar da shi zaka yi a madadin a haifi da me idanu ba. Baffa’m rayuwa da mutuwa duk na Allah ne muke sayan kiyayya muke sayan soyayya. Idan har mae martaba ya musu afuwa zai iya wucewa. Amma kiyayya tana iya rayuwa na tsawon karninnika a dakatar da kiyayyar tun Yanzun!” Murmushi yayi tare da kallon ta sannan ya ce mata…..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 11

Advertisement Babi Na sha ɗaya>*   *Fatan Alkhairi gare ku Yan uwa da abokan arziki Nagode sosai 😍🥰🤩🔥*…
KALLABI
Read More

KALLABI 26

Advertisement BABI NA ASHIRIN DA SHIDA Muryan shi na rawa ya rike hannun ta. “Zai fi kyau ki…
Read More

TARTSATSI 38

Advertisement page 38* ******************** Salma da d’inbin mamaki, ya taru ya sauka k’arara, akan fuskarta tace , “Ke…
Read More

TARTSATSI 55

Advertisement *Page 55* ******************** Koda mutane suka samu suka saka Hafsa motarsu, sai faman sharara gudu sukeyi saida…
Read More

TARTSATSI 99

Advertisement *Page 99* ********************** Acikin farin ciki ta shige gida, Kai tsaye ta shige d’akin su, ta dannawa…