KALLABI 11

KALLABI
KALLABI

Advertisement

Babi Na sha ɗaya>*

 

*Fatan Alkhairi gare ku Yan uwa da abokan arziki Nagode sosai 😍🥰🤩🔥*

 

“Me kike so?” Ya tambaye ta cikin tattausar harshe. Goge kwallar da yake zubo mata tayi har lokacin jikinta rawa yake.

“Baffa’m a yafe musu” ta furta bakinta yana rawa, saka hannu tayi ta rufe bakin, domin wannan ne karo na farko da ta samu kanta da rokon wani  , kuma baffa’m ba wani ba ko mahaifinta bata tab’a samun damar zama da shi haka ba. Kallon ta yake a hankali shekarunta basu kai rike abinda ya fada ba, girman ta bai kai shi ba.

 

Dan bata da wannan girman,

*Innayoh*  zuciyar shi ta furta, kenan .

“Toh zan gayawa mai Martaba, amma zaki yi abu daya?” Da sauri ta d’ago kai tana kallon shi. Hararan dan zomon ta yayi da yazo kusa da ita.

Advertisements

“Zaki mai dani abokin ki?” Ya fada yana kallon cikin idanunta, itama shi take kallo, lashe bakin ta tayi tana me ƙoƙarin janye idanun ta daga kallon shi da ya mata kwarjini. Da sauri ta dauke kai tana kallon dan dalago.

 

“Kai fa Baffa’m” hannun shi ya kai saman labbenta, a hankali ya d’ago fuskarta da daya hannun shi, yana shafa kyawawan labbanta. Sosai ya janyo ta jikin shi yana kallon kwayar idanun ta. Kafin ya kai kai shi zuwa kunnen ta.

“Abotar mu babu karya, babu cikin amana gaskiya zamu kulla. Sannan zamu tafi ko ina tare kin yarda domin har wajen masarautan nan zan kai ki” kamar wata gunki haka ta tsaya yana magana da ita, a hankali ya mike ya barta durkushe da gwiwowin ta, sai da ya isa bakin kofar ya juya yana kallon ta. Murmushin gefen baki yayi sannan ya fita a dakin.

 

Zubewa tayi tana ajiyar zuciya, domin baki daya ya saka ta wani irin yanayi.

 

Tunda ya fita ya nufi shashinsa, ya rubuta sako zuwa ga mutanen fadar sannan ya badda umarnin a dakatar da kashe su hakama da arewa, sun samu afuwa daga Fulani Aminatu,  dan haka wannan ba aikin shi bane, ita tayi musu afuwa kuma shima yayi musu, dan haka ayi kokarin kiyayye abinda da zai kuma had’a su.

 

**

Wurgi yayi da kofin hannun shi tare da fasa ihu yana faɗin.

“Ba haka nake son mulkin ba, ba haka nake so, so nake ayi mulkin da ko kasa taji takun mu sai ta girgiza. So nake talakawa su ji tsoron mu, kamata yayi mu addabi kowa da yaki wancan mutumin ya hana. Dole mulki ya dawo hannuna domin mune muka cancanta.”

Advertisements

 

“Karka manta jarmai yayi mutu, yanzun saura tsinbura, idan har muka yi hakuri lokacin da ya fada na zuwa mana”

 

Kallon madubin gaban shi yayi, bai san lokacin da ya dauki kofin da yake shan ruwa ya wurgi madubin da shi. Yana ƙara faɗin.

“Lokaci-lokaci lokaci lokaci! Yaushe lokacin zai yi ne?” Ya fada da karfi, dafe goshinsa yayi sannan ya kwanta.

 

**

Shekaru goma sha tara.

1789

Masarautar Sahil.

 

Masarauta ce ta suke tsakiyar sahara, masarauta ce da take da karfin mulki da ta tsafi. Musamman camfe  sunyi imani da camfe.

 

Masarautar an wani gari ne aka ganta a wannan wurin da Alummomin ta, sun shafe sama da karninnika a wurin, basu tab’a fita yaki ba, amma kuma babu tsuntsun da ya isa ya gifta ta masarautar.  Suna da wata gunki da suka sassaka shi da itacce me suna hil ita wannan gunki siffatar kamar mace ce da goyon daya, gefen wuyar ta kuwa kamar an sare ta, a duk bayan shekara biyar ana sadaukar da jinin wasu kabilu masu suna Na.

 

Wadannan kabilun sun kasance wasu shashi na larabawa makiyaya da suka yo hijira daga wata Alkarya da take tsakanin kogin Nile da kasar Habasha, kasancewar ana samun rashin zaman lafiya da kabilun yankin wurin. Cikin dare suka fada masarautar Sahil. Koda gari ya waye aka ga baki nan aka tafi masarautan inda aka samu sarki Arkhan aka gaya mishi. A lokacin sarki yana cikin matsanancin damuwan rashin da namiji.

 

Ana gaya mishi ya tura a kira bokan shi me suna zeela, kafin dan aiken ya iso bokan ya bayyana.

“Ka sani Ya mai Martaba, kukan ka ma shekaru arba’in zai kare ne da zaran ka samu daya daga cikin yan matan da suka yo gudun hijira, ka yi tarayya da ita kafin kusfewar rana da wata. D’igon ruwan da zai shiga jikin ta shi zai haifar maka da namijin duniya. Zaki kuma gamzaki wanda zai zama fasa taro. Idan aka samar da shi dole jinin uwar ya zama sadaukarwa ga Hil uwa mabada mana.  Kafin nan bari na gaya maka sawaye mutane nan nan. Su din mabiya wata addini ne masu dabi’ar dukawa. Sannan suna da wata baiwa na musamman na iya sarrafa maganin kowacce ciwo, sannan suna da wata irin karfin da ya fi na sihiri. Sadaukar da jinin uwar zai karawa masarautar mu karko da nisan kwana. Dan kuma zai kasance gaggarabadau. Sai dai tasirin su yana faruwa ne daga daren da rana da wata suka yi kusufe. Idan kuma namiji ya aure su, suna iya kara Mishi karfin mulki karshe mulkin yana iya dawowa hannun su, ba zan yarda da wannan yanayin ba shi yasa nake kallon Gara ka ajiye dayan su domin samun wannan babban rabo”

 

Kallon boka zeela yayi kafin ya bude baki yayi magana bokanya Tursi ta bayyana.

“Zeela me yasa kake aiki da jahilci? Ina gaisuwa Mai Martaba. Babu macen da zata haifa maka da namiji a cikin su, dan ko an haifa zai koma. Ita wannan macen da zaka sadaukar ba a haife ta ba, sai dai taurari sun tabbatar tana cikin su. Kafin nan a cikin matan a duba mace da take da alamar wata a jikin ta idan aka samu sai a fara kawo maka ita sauran mutanen ayi sadaukarwa da su. Domin idan ba haka ba zasu yi tawaye kuma zasu iya daukar kasada domin baiwar su bata kanannun mutane be.”

 

**

“Shugaba akwai matsala anan” wani matashi ya faɗa.

Jinjina kai tsohon yayi tare da cewa.

“Amjad ka ɗauki ke su,  ƙaddaran tana tare da su, ku bar wannan nahiyar ku tafi.” Ya kalli wata karamar yarinya da take tsotsar hannu.

“Karka had’a su wuri guda, domin zasu iya bayyana baiwar su ka raba kan su. Idan ta kama bauta ce ma su. Ban shirya ganin tashin hankali”

 

Zana inda suke yayi sannan ya d’aga hannu yana addu’a, tare da yiwa Ubangiji kirari, wani irin duhu ne ya mamaye inda suke kafin ya shiga washewa.  Babu mutumin da Yan matan.

 

Suna barin wurin dakarun sarki na zuwa aka kwashe su da karfin tsiya aka kai su fada, anan aka shiga duba su babu yan matan.

“Kai me farin gashi ina sauran Yaranka”

“Babu su iya mune”

“Ku sake dubawa, ko ku kashe su baki daya.”

“Da haka kuka yi tabbas da yafi sauki akan mu bayyana muku inda sauran suke”

“Kenan kun san inda suke?”

“Bamu sani ba, amma mun san kana niman Kallabi.”

“Tursi babu wani mafita?” Zeela ya tambaye shi.

“A sadaukar da jinin su amma ba dukkan ba, domin ba mamaki yan matan su kuma haifar masu irin wancan baiwar”

 

Haka suka wuce da mutanen a take aka yanka tsohon sannan aka watsa jinin shi ga abin bautar su hil. Kafin nan kuwa garin ya dauki wata irin hadari da ruwa lokacin guda..

 

Bayan shekaru sha tara.

 

Bincike suke baki dayan su bokanya Tursi take kafin ta d’ago kai tana kallon Sarki Arkhan.

“Akwai yiwuwar akwai dayan su a raye sai dai sun yi wata irin nisa na ban mamaki.” Sake mai da kanta tayi tana cigaba da bincike jini ya shiga suka daga hancinta. D’ago kai tayi tare da cewa.

“Tafiyar shekara hudu zuwa biyar zai kai mutum inda suke, sai dai tauraro daya ne yake bayyana, daya yana boye. A cikin wannan yanayin cikar shekara biyar din nan wata da rana zasu samu kusfewa a cikin wannan yanayin Imma a kawo maka dayansu ta samu digon ruwan ka Imma ayi ra zubda jini domin nan da wani lokaci shekarun fuskarta rayuwa ce”

 

“A ina? Yaushe?” Sarki Arkhan ya tambaya a gaji burin shi magaji. Burin shi a haifa mishi da namiji,

 

“Idan har kayi hakuri hakan zai faru ne ta sanadin shekarun rayuwar macen da zata iya daukar haka”

 

Shiru yayi yana kallon su amma baya jin yana da rabon samun da namiji, kuma Sadauki wanda zai dauki mulkin kasar baki daya. Baya son ya rasa wanda zai gaje shi da karfin sihirin shi yana da y’aya mata babu adadin amma namijin yake nima.

 

“Kince daga nan zuwa Nahiyar shekaru huɗu zuwa biyar. A shirya yaki domin dauko ta” ya fada cikin izza.

“An gama”

 

**

Masarautar Gobir.

 

Yau kwana huɗu kenan ana niman dan dalago, sama da kasa babu labarin shi. Abin duniya ya taru ya dame Aminatu, tana zaune ta Zubawa kofar shigowa zauren ta ido, ga bayi mata sun yi jungum-jungum.

“Ayya Fulani ki saka wani abu a bakin ki mana”

“Taya zan yi hakuri bayan an nime shi an rasa” ta fada tana kuka.

 

Shigowar Mai Martaba da kwana uku kenan baya nan, ya shiga cikin zauren da Sallama. Mika mishi gaisuwa suka yi kafin kace me sun cika mishi gaban shi da abincin, sannan suka bar wurin. Mika mata hannu yayi ta taso, fashewa tayi da kuka.  A hankali ya janyo ta jikin shi, yana me kallon ta, turaren da Innayoh ta saka mata yana ratsa hancin shi. Saka kan shi yayi a dokin wuyarta, ya shiga goga hancin shi, yana tambayar ta.

“Ke da waye?”

“Dan dalago ya b’ata” ta fada tana zubda kwalla, dumin kwallar yana ratsa jikin shi sabida saukar da yake a hannun shi. Juyar da ita tayi yana kallon yadda fuskar nan tai jajjur. Lashe bakin shi yayi a hankali ya kai bakin shi kan nata. Ya sauke mata karamin sumbata, lumshe idanun ta tayi kwalla na zuba mata.

“Baffa’m!”  Ta kira sunan shi, tana me janye fuskar ta, a hankali ya mai da ita ya kwantar, yana kallon yadda take shirin bare mishi baki, juyawa yayi sannan ya mike. A shekarun shi yana bukatar abokiyar rayuwa, shi kuma matar da yake kallo tayi kankanta.

 

Fita yayi baki daya, sannan ya koma shashinsa.

“Ka kira min Galadima” ya fada a sanyayye,

“An gama”

Bayan wani lokaci sai gasu tare sun shigo.

“Allah ya baka nasara, gani nan”

Shiru yayi, kafin ya ce mishi.

“Ina bukatar wacce zata dauke min nauyin Aminatu.”

“Allah ya baka nasara, kayi hakuri mana. Akwai alkhari a tarayyar ka da ita idan ka sako wata cikin al’amarin ku zai lalace. Kayi hakuri”

“Toh ya zanyi?”

Mikewa Galadima yayi, sannan ya kalle shi.

“Kai namiji ne, janta jikinka sakata a jikin ka zai saka kaji sauƙin wasu abubuwan, ka koya mata zama a jikin ka yadda kome nata zai tsayar da kai amma matukar ka sake taraba shimfida da wata haka zai kasance mata tashin hankali. Zai haifar da kishi idan har wacce zata zo ka mai da ita abar biyan bukata Aminatu zata wahala. Don Allah kayi hakuri”

 

Shiru yayi bai ce kome ba, kafin Galadima ya cigaba da cewa.

“Kai ka gaya min baka son ayi kishi me zafi a gidan ka kuma kana niman baiwa dan nasan ba aure zaka yi ba sai dai Kwarkwarah” haka Galadima ya gama maganar shi bai ce uffan ba. Har ya tafi.

 

Wa shi gari

Tura sako yayi a kawo mishi Aminatu kasancewar ranar Laraba ne. Tunda aka fadawa Innayoh, ta sakata a gaba tayi mata wanka, a wurin wankar take kallon kirjinta da kan dukiyar fulanin ta yake dan turo kai. Kasancewar ta daura mata mayafi, a saman jikinta. Goge mata jikin tayi sannan ta ce mata.

“Fulani idan Baffa’m ya tab’a jikin ki karki gayawa kowa kin ji, mutuwa ake idan kika fada, karki ji tsoro kin ji amma kiyi shiru da bakin ki” gyada kai tayi tana kallon Innayoh, haka ta gama shirya ta, sannan aka raka ta har babban zauren shi suka dawo, yana zaune yana rubutu.  D’ago kai yayi ya mata murmushi. Ganin haka yasa ta nufe shi ta zauna. Haka ya cigaba da rubutun shi, sannan ya tura mata wani katon tire dauke da kayan ciye-ciye.

 

A hankali take ci tana mishi magana, sannan ta tura tiren komawa gefe tayi ta dangwali tawada ta manna mishi a gefen kumatun shi inda ya lubb’a. Lashe baki yayi yana ci-gaba da aikin shi dauke fatar raƙumin tayi da yake rubutu a cikin shi ya nade can ta ce mishi.

“Baffa’m har yau babu dan dalago”

*Ina zaki ga dan banza bayan ni da su waziri mun cinye dan banza*

Abinda ya faru, duk yadda yabi sai ya lura dan Zomo dai ya hana shi samun hankalin ta, shine yasa Innayoh ta kama dan banza aka bawa Sarkin gida ya yanke aka gasa musu, ya haɗa da guzirin shi.

 

Tunawa da yayi shima cikin jimamin ya rungume ta, yana bata hakuri. Gudun kar amishi kallon zallamamme amma babu abinda ya isa hana shi samun matar shi, yanayin da yake samun kan shi yasa baki daya. Cikin wani irin shiririta ta fara kokarin zamewa a jikin shi tana wani irin yauki da kiriniya, tana wani irin zamewa kamar karkashi. Baki daya kamshin ta da wani yanayi me dadin Bala’i yana ziyarta yanayin shi na lafiyayyen namiji cikakken jarumi. Wanda ya san me yake yi kuma yasan waye shi.

 

A hankali ta d’ago kai tana kallon yadda ya lumshe idanun shi, hannunta, ta kai kan tawadar ta shiga zana mishi akan fuskar shi. Bude Idanu yayi akan ta..

“Ah” had’a goshinsa yayi da nata,

“Zan miki bulala”

“Kayi hakuri” lallubar hannun ta yayi tare da jifa yatsarta a bakin shi yana tsotsa yana me lumshe idanun shi.

“Baffa’m!”

“Hmm”

“Karka cinye min hannu”

“Hmm” ya fada bayan ya bude idanun shi kanta, zare yatsar yayi yana me sumbatar tafin hannun ta.

“Baffa’m! Wata rana zaka yi fushi da ni?”

Sosai ya ware idanu shi akan ta, yana kallon cikin idanunta, itama shi take kallon.

*Fulani Aminatu ita zanen ƙaddara ba bawa keda ikon zata ba, ilahi yake zanata idan har akwai tafiyar Ƙaddara toh ba makawa sai na mai da ita sadaukarwar ƙaddara*

 

A zahiri kuma murmushi yayi mata,yana jan kumatunta ya ce mata.

“A’a”

Mai da kanta tayi ta kifa a kirjin shi, tana jan shashekar kuka.

“Baffa’m!”

“Hmm! Fulani”

“Karka zama kamar Baffana kaji. Karka manta dani kaji”

*Waye ya gaya miki marubuci yana rubuta labarin shi! Idan babu toh tabbas ba zan taba bada labarin mu ba*

“Ina tare dake” ya fada mata,

“Baffa’m! Karka zama sarki domin akwai dodanin da zasu shiga cikin mu”

*Ba halicci wani dabbar da zai shiga cikin mu ba*

 

Kukan da bata san dalilin shi ba, bata kuma san hujjar yin shi ba, take yi tana karawa, har da shiga jikin shi, ajiyar zuciya ya sauke. Sakamakon jin tayi shiru, yana leka fuskar ta yaga tana barci, gyara mata kwanciya yayi sannan ya dauki kayan rubutun shi ya ci-gaba yana yi yana kallonta.

 

A hankali lokaci ya cigaba da tafiya, ya kasance duk sati Fulani Aminatu tana kai ziyara shashin sa, idan ta shiga tun ranar Laraba baza a kuma jin duri’ar ta ba, sai ranar asabar da yamma zata dawo shashinta,  a lokacin idan ka gan yadda ta koma zaka yi tsammanin wani abu ake bata, sai kara kiriniya take, amma sabida sabo da tayi da zama a wurin shi dakyar Innayoh take lallabata, idan kuma taso sai ta tadda musu rigimar banza zata wurin shi.

 

A cikin wannan yanayin aka samu shekara daya da auren su, cika shekara daya yayi daidai da fara wani irin rashin lafiyar da ta fara, inda ta fara da wani irin abu a gefen wuyar ta, ya fito kamar bakin tabo…. Ba a lura da wuri ba sai da ciwon ya kwantar da ita,  ana cikin haka wata Jumma’a aka wayi gari da mutuwar dabbobi cikin masarautar. ba a taba samun irin wannan annoban ba. Galadima ne ya nufi wurin shan iskar Mai Martaba.

“Allah ya baka nasara, ina ganin a fitar da Fulani Aminatu zuwa Sokoto ko za’a dace”

“Toh amma ina ganin kamar haka bai da alaka da mutuwar dabbobi nan?”

“Bana fatar haka”

“Allah ya baka nasara kazo” inji Sarkin gida.

“Lafiya?” Galadima ya tambaye shi,

“Fulani Aminatu ce”

Bai rufe baki ba, Mai Martaba har ya isa matakalar wurin shan iskar, kafin su zo tuni ya isa shashin ta. Tana kwance wuyar ta yayi jajjur, tabon bakin ya washe yayi ja.

“Baffa’m! Zan sha ruwa” ta fada a sanyayye, karban ruwan yayi ya bata tasha.

“Baffa’m akwai ciwo, cikina yana ciwo wuyana kamar wuta” ta fada hawaye na zuba a idanunta, d’ago yayi ya rungume ta, yana jin yadda jikinta yake firfitar da wani irin zafi.  Janye kayan jikinta yayi bayan yayiwa Innayoh alamar ta fita, ya kwantar da ita ta shiga mata fifita. Dawowa wurin tafin kafarta yayi ya saka mata hannun shi yaji sanyi.

 

Tashi yayi ya lullube ta sannan ya bar shashin ta.

 

Fita yayi wurin Galadima, sun jima kafin zuwa dare suka fita daji, suka nimo saiwowi na bishiyoyi babu iyaka, aka kai cikin gida aka dake shi akan idanun Sarkin gida, aka dawo da shi nan aka hada mata magani kafin gari  ya waye an yi mata wanka da shi. Sannan an bata wani tasha. Zuwa la’asar jini ya fara zuba bata, domin tana barci taji kamar tayi fitsari.

“Innayoh” ta kira ta.

“Na’am ranki shi dade,”

“Innayoh nayi fitsari”

Dubawa Innayoh tayi, taga kamar jinin haila ce,  rangad’a gud’a tayi tana me fadin.

“Fulanina ta girma” kafin kace me labari ya karade cikin gidan, ana bada labarin girman Fulani, gyara ta Innayoh tayi sannan aka kwashe kayan aka kai wurin wanki. Innayoh da kanta ta wanke kayan.

 

Innayoh na fita ta kwanta, ko jimawa bata yi ba.

**

“Ban gane ba! Tsawon wani lokaci ka dauka da sanin haka?”  Mai Martaba ya tambaye shi a fusace….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 4

Advertisement *page 3* ******************* Salma kyakkyawa ce ajin farko, fara ce jajir Mai doguwar fuska Mai dauke da…
INAYAH
Read More

INAYAH 5

Advertisement 5 Daqyar ta iya furta “Hadiza Allah zai zama gatanki, Allah zai raya Miki ‘yarki cikin Aminci…
Read More

TARTSATSI 37

Advertisement *page 37* ******************* Salma cikin farin ciki, taje ta adana kud’inta, zuciyarta fal farinciki, don ganin takeyi…
Read More

TARTSATSI 67

Advertisement   *Page 67*   ****************   Daga Salma har Aliyu koda suka tashi da safe, dukansu ba…
Read More

TARTSATSI 68

Advertisement *Page 68*   **********************   Sadauki kam saida ya tabbatar ya karkare, duk wata tsatsa da ta…