KALLABI 12

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*<Babi Na Sha Biyu>*

“Kayi hakuri amma ba yadda kake zata bane, kuma ba mayya bace” shiru yayi dunkule hannun shi yayi ya daki bango.
“Kenan duk kokarina sai da kome ya faru?”
“Ina ga da zamu iya dakatar da wasu abubuwan ba mamaki kome zai iya tafiya daidai” inji Galadima.
“Yanzu meye makasudin bayyanar abin wuyarta?”

“Baiwa ce da ita, da a ce zaka iya kusantar ta ne, haka zai ragu ko idan ta samu ciki zata samu lafiya, domin kaifin abu.” Wani Zubawa galadima idanu yayi kafin ya dauke daga kallon shi ya cigaba da abinda yake.

Tun lokacin ya saka idanu akan sannan shima da kan shi yake nima mata magani, duk da bata dauki kwanaki me tsawo tana hutun ta ba, amma kuma tayi kewar baffa’m. Har Innayoh ta mata magana.
“Ki rage yawan daukin da kike kar ya fahimci haka”
Shiru tayi sannan ta ce mata.
“Toh” a lokacin Innayoh ta shiga koya mata abubuwa da akanta, tana nuna mata yadda zata rike miji.

Ana cikin wannan yanayin watan azumi ya maka, har zuwa lokacin babu abinda ya nima daga Fulani Aminatu, a cikin gida kuwa kiri kiri Ajuji take jin daci akan Aminatu. Tun tana boyewa har ta fitar da kiyayyar ta.

Innayoh da wasu bayi da ita Fulani Aminatu, duk shirya abubuwan kyaututtuka suka shiga cikin gida da shi, dakin Gambo suka fara zuwa. Jakadiya na gaya mata ga Fulani Aminatu, ta mike da sauri ta faɗin.
“Lalle maraba da fara me farar Aniya” ajiye mata tiren bayi suka yi, sannan Fulani Aminatu ta zauna tana murmushi.
“Ayi hakuri ban samu zuwa da wuri ba, ga wannan na tarban azumi ne” ta fada tana Murmushi akan fuskar ta.
Murmushi Gambo tayi sannan ta ce mata.
“Idan akwai wata toh ba makawa taurarin da suke zagaye da shi masu haske ne.” Ta fada tana kallon Innayoh.

Bude baki Innayoh tayi zata yi magana suka ji muryan Fulani Aminatu.
“Hmm! Daidaiton hasken shi karfin kusancin shi, mun barki lafiya”

“Haka ne, sai dai kar kusancin hasken ya rage karfin wani shaashi. Koda yake kwanaki naji labarin Fulani Aminatu ta girma har yanzu bata yi daidai da tsarin mulkin Sarki Bello bane? Idan yau ban cire ba a gobe akwai masu cirewa!” Kallon Innayoh Fulani Aminatu tayi tana kuma kallon Gambo.

“Laa karki damu, da alamu baki tab’a haduwa da shi bane? Tambaya da kyau. Waye Sarki? Baffa’m da kike gani shine Sarkin” kallon Innayoh ta kuma sannan ta kalli Gambo, da take dariya.
“Ta Yaro kyau take bata karko, da alamu abinda nake ji ma da gaske haka ne, Fulani Aminatu bata san me ya kawo ta masarautar Gobir ba, auren sarki kike Innayoh wannan ba kauna bace boye abinda yake daidai,Kanwata Nagode ayi azumi lafiya sai dai ki sani baki dayan mu, mun auri sarakuna ne a shekaru irin naki, idan kika sake lokaci ya karu baki same shi ba, kwarkwarah itace zata hanaki rawan gaban hatsin kamar yadda Kwarkwarah Ajuji ta min.”

Idanun Fulani Aminatu ya cika da kwalla, amma sai ta mai da kwallar ta kwantar da hankalinta sannan ta kalli Gambo tace mata.
“Fulani Gambo, Nagode da tunatarwan ki. Ai na jima da sanin me nake a cikin masarautan, ni Mace ce kuma soyayyar sarki nake nima, ba baiwa bace ni, sannan ba karfin mulki nake nima ba, balle nayi tunanin bin shimfidar shi. Na barki lafiya”

Advertisements

Sannan suka fita tayi matukar kokarin boye tashin hankalin ta, har suka shiga shashin Ajuji.
“Ina ruwan maraba da gasashe, kura yaga bakin jaki, karku dauka da ku nake nufi.”

Cikin wani irin dakewa fuskar ta a had’e Fulani Aminatu ta ce.
“Innayoh ku ajiye kayan. Gashi nan na tarban azumi ne” tana me juyawa,
“Fulani Aminatu! Ana niman mazaunai ne ko ana niman kafa hujja ne?”

Juyawa tayi tana kallon Ajuji, sannan ta sake murmushi ta ce.
“Wasu lokutan ban cika gane banbancin me hankali da mara hankali ba, sunan su daya nake musu lakabi. Idan har akwai tafiyar Ƙaddara toh ba makawa sai ba fuskanci ire-iren ku masu tarawa da ragewa. Na barki lafiya”

“Ke Fulani Aminatu” bata juya ba har ta isa bakin kofa.
“Ajuji bana amsa kiran tababbu” sannan suka fita, sai da suka fara kokarin barin cikin gidan, kawai wasu daga cikin bayin cikin gidan. Suka fara dariya. Dama idanun ta ya gama rufewa da jin haushin kowa tsayawa tayi sannan ta kalli kande a cikin.
“Ki kira min Sarkin gida kuma ya tawo min da wadannan dabbobin” sannan ta wuce ta bar wurin. Aikuwa basu yarda hakan zai faru ba, dan haka suka kuma sake dariyar su. Tun da ta shiga shashinta, ta zauna idan akwai abinda ya tab’a mata ciwo bai kai yadda Baffa’m ya boye mata waye shi. Daga bakin kofar Sarkin gida ya ce mata.
“Allah ya taimaki Fulani Aminatu, gasu can a waje” shiru tayi bata yi magana ba, kallon ta Innayoh tayi.
“Koyi sarrafa fushinki kamar yadda kika yi a cikin gidan, wannan dalilin yasa nake nuna miki wasu abubuwan.”

“Ka cire musu hakoran dariya” zubewa Innayoh tayi tana me rarrafawa gaban Fulani Aminatu.
“Don Allah karki ce zaki yi haka baki yi kama da haka ba, ki musu afuwa”
“Sarkin gida nace ka cire musu hakoran su” ta fada da ƙarfi.

“Don Allah Fulani Aminatu hukuncin yayi tsauri” cikin fushi ta mike zata bar zauren ta yanki jiki ta faɗi.
“Sarkin gida maza ka kira Mai Martaba ka gaya mishi”

Yana barin wurin tana, gyara mata kwanciya ko daukar lokaci basu yi ba, sai gasu nan a tare, domin kai tsaye daga fada yake, kusan rabon shi da ita wata biyu kenan, sai dai ya aika mata da maganin ta, haka ya faru ne sakamakon kokarin kawo musu hari da ake. Yasa bai da lokacin kansa sai na amsar korafe-korafe, ga yan gudun hijira suna dawowa cikin masarautar da zama. Yana isa zauren ta ya dauke ta cak ya wuce shashin sa da ita, su kan su bayin bai bi ta kan su ba. Yana shiga da ita ya kwantar da ita. Sannan ta shiga shafa mata maganin yana kallon yadda take juyar da kanta.

Haka ya zauna tana ta fama da abu daya, har ya samu labarin zuwan galadima, cewa yayi ya shigo. Haka ba karamin al’amari bane da zai bari a shigo har cikin tukakar su, yana shiga ya mika mishi wani karamin kwarya, ya umarce shi da ya saka mata a tafin kafarta.
“Ka samu labarin abinda ya faru?” Galadima ya tambaye shi.
“A’a ya kamata ka girmama al’amarin ta, domin ta kai an fara mata dariya.”

“Su waye haka? Su waye masu bakin dariya? A kama min su a cire musu hakoran su” ya fada a fusace.
“Idan aka ce haka za ayi kiyayyar ba zata kare ba, amma idan aka rangad’a gud’a tare da fitar da shaidar ita din macen da sarki ya ke so ce me kake tunanin zai faru?kimar ta da mutuncin ta sai ya fi haka karuwa. Sai ya kai duk inda ta shiga kowa yana ja da baya ”

“Shekarun ta baki daya sha uku ne bata kai hudu ba, kawai bana jin haka ma mafita ne, kawai a bar abin a hukunta masu laifin.” Ya fada yana shafa fuskar ta.
Haka ce ta faru domin kuwa an hukunta su sosai, bayan ta farka bata mishi magana ba, sai dai bin shi da ido idan yayi mata magana sai ta fashe da kuka, ita a tunanin ta ya ci amanar ta. Har tsawon kwanaki uku, anan ne hankalin shi ya tashi yana kallon yadda take mishi kuka.

“Aminatu gaya min meye aka miki?” Ya tambaye ta, yana rarrashin ta. Wani sabon kukan ta saka mishi tana kallon shi kamar taga sabon halitta. Ya rasa yadda zai yi da ita kawai sai ya janyo ya ta rungume ta, tare da lallubar bakinta ya tushe da nashi, kamar yadda ya sabar mata haka yayi ta bin ta, sai gata tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.
“Gaya min meye aka miki?”
“Dama kai ne Sarki?” Ta tambaye shi. Goga hancin shi yayi a kafadar ta, yana kara jin wani irin nutsuwa akanta.
“Shine kike kuka? Eh ni sarki ne” janye jikin ta tayi daga na shi.
“Baffa’m” janyo fuskarta yayi a hankali kai hannun shi wuyarta, yana shafawa.
“Zamowana sarki ba wai na har na karshen rayuwa ta bane, akwai lokacin da zan rabu da shi. Kinji kwantar da hankalin ki ba zan jima ba zan rabu da shi”

Shigewa jikin shi tayi tana faɗin.
“Baffa’m karka rabu da ni, don Allah kar ka min abinda Baffana yayi min”

Advertisements

Murmushi yayi yana kara matse ta a kirjin shi,
A cikin wannan yanayin aka yi azumi bayan an sha ruwa, ya tafi har garuruwan da ake kawo hari, ya duba su sannan ya kai musu agaji. A kan hanyar shi ta dawowa ne haka kawo musu hari. Bai tab’a yaki ba sai a lokacin dan haka duk yadda yaso kare kan shi, haka ya shiga yakinin sannan aka kama maharan, kallon su yayi sannan ya ce musu.
“Waye ya turo ku?”
“Ba zamu fada ba koda zaka kashe ku ne.” Lumshe idanu yayi sannan ya kalli Yarimar Gobir ya ce mishi.
“A matsayin ka na yarima ya zamu da su?”
“Me zamu yi kuwa wanda ya wuce a tafi da su masarautar ayi ta gana musu azaba sai sun fadi waye ya turo su.”
“Toh a daure su” duk da ba wani jin ciwo yayi ba, sai a damtsen shi. Tun kafin su isa labari ya karade gari an farmaki Mai martaba a hanyar shi ra dawowa gida. Fulani Aminatu tana shiri taji wasu bayi suna faɗa. A bayan tagar dakin ta, da gudu ta fito ta haura katangar shashinsa, tana kallon hanyar waje. Tun da ta fito bata koma ba, tana tsaye a wurin har garin ya dauki wani masifaffen hadiri bakikirin. Daga nesa ta hango keken dokin shi dan haka bata yi wani yunkuri ba, sai da ya kusan shigowa ta sauka da gudu, ta nufi hanyar da zai sadasu, ruwa na zuba a kanta. Tsayawa tayi a bakin kofar da xai shigo tana jiran shi. Fitowa yayi hannun rigar shi a yanke ga inda ya daure. Da gudu ta nufe shi tare da fadawa a kirjin shi. Rungume ta yayi yana jin kamar kar ya rabu da ita. Shashekar kuka take tana kallon raunin. Har cikin turakar shi suka shiga ko nace ya dauke ta. Sai da ya cire kayan shi ya wuce ban daki, dan ta juya mishi baya. Yana gama abinda zai yi ya fito ya saka wasu kayan sannan aka gaya mishi ga me maganin masarautan yazo.

“Sarkin gida kace ya je raunin bata da muni, zan kula da shi” yana fita ya koma dakin ya same ta saka wani mayafin shi zata fita. Tsayawa yayi a gaban ta.
“Ina zaki” kallon farfadan kirjin shi tai sannan ta sunkuyar da kai tana faɗin.
“Zamu kawo abinci ne”
Tallafo hannun ta yayi ya saka a kirjin shi yayi.
“Kin ji yadda yake bugawa”
“Eh”
“Kece sanadi” ya fada bayan ya sumbaci goshinta, sannan ya gangaro wuyarta. Zuwa habb’atar lumshe idanun ta tayi tana jin shi. Kafaffuwar ta ne ya fara rawa, murmushi yayi ya zungure goshinta.
“Raguwa kawai” da sauri ta fita, basu dauki lokaci ba sai gasu da manyan tire na abinci da ruwan zafi, ita dasu kande da yahanasu. Haka suka jera sannan suka fita. Yar karamar wasika ya rubuta ya tura ga fadar shi zai yi Hutu na kwanaki sabida ciwon shi. Aikuwa ganin haka ta barwa Innayoh kome itama ta tare a shashinsa, basu da wani aiki sai na soyayyar da yake koya mata, idan suna daukin baka jin kome sai muryan shi yana bata labarin da ya rubuta. Itama kuma bude kunne take tana jin labarai.

A gefen Innayoh itama bata bar su a baya ba wurin basu abincin da zai kara musu lafiya cikin yan kwanakin dakyar yake dakatar da kan shi, amma tabbas yana gab da amsar hakkin auren shi..
**
Bayan shekara biyu……

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 10

Advertisement *<Babi Na Goma>* _Gaisuwar wannan shafin naki ne Mrs Sadauki Mom Nasmah sakon ki ya iso Nagode…
KALLABI
Read More

KALLABI 37

Advertisement BABI NA TALATIN DA BAKWAI Kallon juna suka yi da Innayoh, kowacce fuskar ta dauke da murmushi.…
Read More

TARTSATSI 97

Advertisement *Page 97* ********************** A siyasance Abba ya dinga yiwa hajiya nasiha, tareda lurar da ita akan hak’uri…