KALLABI 13

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*<Babi Na sha Uku>*

Bayan shekara biyu.

Wanke mata kai Innayoh take, tayi shiru zaka dauka kawai tayi shiru ne dan wanke kan, a’a a zahiri ba haka bane maganar da taji a bakin Balaraba ne yake dawowa ranta. Bude idanun ta tayi akan Innayoh kafin ta dan matsa kadan kasancewa kanta aka yi baya da shi, tana kwance an saka mata matashi a keyarta. Duk da ta fahimci kamar akwai abinda Innayoh take boyewa amma bata da wani damar da zata kasa magana.

“Innayoh da gaske za a bawa mai martaba auren Yar Sarkin sokoto” ta tambaye ta.
“Eh gara yayi tunda ita wacce yake tare da ita bata san yadda zata girma ba” inji Innayoh, shiru Fulani tayi bata kuma magana ba, domin Innayoh tana ganin a halin yanzu ya ci ace ta samu kan mai Martaba ba wai ayi ya ta kananun magana babu abinda ya kasance a tsakanin su, tun va a gane ba har an gano cewa babu kusancin aure a zaman su.

Babban amawali innayoh ta dauka ta nad’e mata gashin kanta, tana goge mata. Sannan ya tashi kwana lalle tai da danyen kwai ta shafa mata a fuskarta da wuyar ta, sai lalle da lemun tsamin da ta shafa mata a hammatarta, tana kuma komawa gwiwar ta tana shafa mata dankon zuma, tana fisgewa da dan ƙarfi tana cire gashin dake jikin Fulani Aminatu.

“Toh me zan yi?” Ta tambaya tana tura bakin ta.
“Me kuwa zaki yi? Bayan tun bara nake kokarin ki fahimci haka, Fulani kefa ba Yarinya karama bace, ke matar aure ce kuma a yanzun shekaru uku kenan da auren ki, idan lissafina yayi daidai kina da shekaru goma sha biyar a rayuwar ki. Ki zama mace mana”

Shiru tayi tana kallon ta, bata ce kome ba tana nazarin maganar ne, shiga cikin ban dakin Innayoh tayi tana fatar wannan gyaran da take mata karya tashi a iska, kasancewar gobe Laraba kuma zata shiga turakar shi, tana fatar idan ta shiga da kafar dama. Shi yasa take ta gyara mata jiki, yadda shi kansa mai Martaba sai ya gigice da Yar ficikar shi.

*
Kasancewar fada tana da wani daki na musamman wanda yake kawace da litattafai da sauran su, zaune yake shi da galadima.
“Kana min kama da sabon ango da yake shirin fara sabon rayuwa.” Inji galadima.
Murmushi yayi sannan ya cigaba da diban tawadar shi a jikin alkalamin shi yana me cigaba da aikin shi.
“Baka da aiki sai na maganar amarci” mai Martaba ya fada yana murmushi, kallon shi Galadima yayi dan ya fahimci mai Martaba yana son ayi mishi maganar kenan, gyara zama yayi ya duba wata kyakyawar kwarya da yake cike dam da fura da nono, man shanu ya kwanta a kai, ya mika hannu zai dauka, ya ce mishi.
“Ajiye min Fulani Aminatu ce ta dama min.”

Kasa Galadima yayi da murya yana faɗin.
“Kana iya shanye damunta amma ba zaka iya bata naka damun ba” ya fada yana wata shu’umar Murmushi, girgiza kai Mai Martaba yayi yana kallon Galadima, a hankali ya cire rawanin shi da alkyabbar ya ajiye a gefe sannan ya sauka kasa sosai ya zauna bayan ya tankwashe kafar shi ya zubawa Galadima idanu.
“Sam ka manta sarki ne ni guda” ya fada yana muzurai cikin zolaya.
“A’a karaga ne ba sarki ba, malam ga wannan Kyakkyawar hadi, amma gobe zaka yi amfani da shi.”

Ture hannun Galadima yayi yana daukar ƙwaryan fura da nono yana motsawa, sannan ya kalli galadima.
“Kana tsammanin sai nasha wani abu zan iya ratsa Fulani?”
“A’a shi yana kara kuzari ne” ya fada mishi yana murmushi.
“Ba sai nasha ba, ina da lafiyar da zan take bata hudu a dare daya ban gaji ba” ya fada yana kallon furan.
“Kai haba na zata irin mu ne da sai mun had’a da magani”
“Kai ma rashin godiyar Ubangiji ne irin naka amma bana tunanin sai ka haɗa da wani abu, maganin basir kawai xaka nima shima ya isa.”

Advertisements

“Kace mutumin nan kallon ka muke ashe kai, ba haka kake ba toh wallahi yar mutane.” Inji galadima yana dariya.
“Hmm” shima yayi dariya yana me cigaba da shan furan.
“Allah ya baka nasara, kayi kokarin ganin ka daidaita tsakanin ku bana son ka auri wata mace bayan Aminatu, sabida ita Aminatu renon kace, ba yau nake gaya maka ba Aminatu a hannun ka ta girma kai ka fara koya mata abubuwa dayawa, idan har zaka mata adalci toh tabbas bata bukatar zama da kowa sama da kai. Duk da nasan zai yi yiwa idan baka auri wata ba, ko a Kwarkwarah”

Ajiye furan yayi yana kallon Galadima.
“Ban san yadda zan maka bayani ba, amma ina tausayin Aminatu ne, shi yasa bana iya niman ta, amma insha Allah zan ga abinda ya dace” ya fada bayan ya mike, ya daura rawanin shi, sannan ya dauki alkyabar shi, yana me nufar hanyar waje.
“Yaushe zaka tafi daurin auren Yar Sarkin Rano?” Galadima ya tambaye shi.
“Kome yana hannun ka.”
“Amma zaka tafi da Fulani Aminatu ne?” Juyawa yayi yana kallon galadima.
“Tafiyar zata bada ma’ana. Ka duba zancen da idanun basira” Galadima ta fada bayan ya fita daga dakin karatun.

“Kuma!”
Tsayawa Galadima yayi, sannan ya juya yana faɗin.
“Kwarai da gaske, kwarai ka nunawa duniya ita din matar so ce, ba zaka iya tafiya me nisa babu ita ba”

“Toh Babu damuwa ka shirya haka ma” ya fada yana murmushin jin dadi, sannan ya nufi shashin Fulani Aminatu, tana zaune bayan ta fito wanka wata yar yaloluwar riga ce ba shan iska a jikinta, dan kirjin ta me ɗauke da dukiyar Fulani ya cika daidai na matashiyar budurwa. Fatar ta sai wani mugu sheki yake, rigar tana da tsantsi da wasu irin tsagu. Ya kwanta a jikin ta luff, ga ruwan gashin kanta da yake sauka a dokin wuyarta. saka mata lalle Innayoh tayi a hannu da kafa, shine take zaune a wurin duk da ranta a jagule yake bai hanata kallon kofar ba shigowa ba dan tasan yau zai shigo rabon ta da saka shi a idanun tun ranar Lahadi da daddare da ya rakota. har yau bata saka shi a idanun ba, taje shashin sa aka ce baya nan. Tabar sako bai biyo sawu ba. Ana cikin haka kuma Balaraba take bata labarin ai sarkin Sokoto zai bashi auren Yar shi. Wani irin kunci taji.
“Assalamu alaikum!” Ya mata sallama, d’ago kai yayi yana kallon ta, yadda tayi wani shar da ita, gwanin ban sha’awa sai wani fitanannen kamshi dakin yake badawa, kallon hannunta yayi da yake dauke da lalle sai kafarta shima yana dauke da lallen. Cire rawanin shi yayi ya ajiye, sannan ya cire alkyabbar shi ya ajiye ya gama sabawa kan shi da matseta, da ya ganta a wurin wani irin hàdiye yawu yake. A hankali ya taka har inda take, ya zauna yana kallon ta. Kafin ya kai hannun shi baki daya ya dauke ta cak ya daura akan cinyar shi. Tun can baya tana tsoron haka da yake mata, zuwa yanzun tasaba da shi sai dai kunyar da take da ita baya barin ta, tayi kome sai yadda yayi da ita. Rungume ta yayi yana me cusa kan shi tsakanin wuyar ta da kafadarta. Yana goga mata hancin shi.
“Ayi min kowani hukunci amma shiru da shariyar zata iya saka baffa’m ya sussuce”
D’ago kai yayi yaga har zuwa lokacin bata kalle shi ba.
Dan baya yayi da ita a hankali yake shafa cinyoyin ta zuwa saman cikin ta, wani zaro idanu tayi, tana jin yadda bugun zuciyar ta yake kara sauri-da- sauri kamar ana wasan tseren dawakai.

Hancin shi ya kai bakinta ya sumbata sannan ya ce mata.
“Naga sakon ki a wurin Sarkin kofa” har lokacin bata amsa mishi ba.
“Fulani” ya kira sunan ta,
“Baffa’m! Aure zaka yi?”
“Waye ya gaya miki?” Ya tambaye ta yana kallon yadda take kokarin kauda kanta rike fuskar ta yayi yana faɗin.
“Waye ya gaya miki labari mara daɗi?”
“Taya za ayi abu a cikin gidan nan ta boya? Ka manta ina kake ne. A gafarce ni idan nayi shirme” ta fada tana kokarin tashi daga jikin shi.
“Nasani mantawa nayi, tayi aka min ba auren xan yi ba. Kuma ba gaya musu ina da yar kwailata wace kirjinnta bai gama budewa ba” sumkuyar dai kai tayi tana kallon lallen hannunta da yake kokarin burbushewa a jikin shi.
“Ina b’ata maka jiki da lalle” ta fada tana lumshe idanun ta.
“Toh ai nasan domina aka yi ko?” Goga hancin shi yayi a kumatun ta, yana shaƙar kamshin jikinta.
” Ki cewa Innayoh, na kara mata matsayi zuwa uwar bayin cikin gidan nan baki daya” a matukar mamaki ta kalle shi kafin kuma ta sake murmushi tana kara rungume shi.
“Nagode sosai” ta fada, ai kuwa mutumin ku ganin yadda take farin cikin nan shima ya shiga shagalin shi ina ga ya manta a inda suke baki daya sai kokarin (🚶🏃🤣 Ni dai yar hisba ce me amana) sosai ya so gwangwaje matar shi amma yadda ta birkice mishi tana zare idanun yasa shi hakura da ita. Dan haka da ya gama ya mike zai fita mikar da ita yayi yana faɗin.
“An jima ki shirya zamu tafi unguwa.” Gyada mishi kai tayi, tana kallon kasa, sumbatar bakinta yayi a sama sama sannan ya saka kayan shi ya kuma daure fuska kamar ba shi bane ( ya gama bitar d’aga buje ba 🤣😂) haka ya fito ya yana wani shan kamshi kai ba zaka rantse wani abu yayi a nutson da yayi a turakar Fulani ba. Kallon Balaraba Uwani tayi ta ce mata.
“Ai Fulani tana shan soyayya irin wannan jimawar da mai martaba yayi , shi yasa take kara girma”

“Sannun ku da gulma idan na kara jin wani abu dai na saka an zane ku” zubewa suka yi a gaban Innayoh suna bata hakuri.
“Kiyi hakuri ba zamu sake ba, ayi mana afuwa.” Wuce su tayi ta shiga wurin Fulani, kallon ta tayi cikin murmushi ta ce mata.
“Mai martaba ya kara miki matsayi zuwa uwar bayin gidan nan baki daya, sannan ya ce na shirya zamu fita shan iska” kallon ta Innayoh take ta ma rasa me xata ce mata, sai zubewa tayi a gaban Fulani Aminatu tana me rike kafarta.
“Alhamdulillahi Ubangiji ka jikan Amrah Nagode sosai” ta fada tana kara rungume Aminatu.
“Kai Innayoh meye a cikin wannan ba kome bane, tashi ya isa haka”

Mai Martaba yana fita ya gayawa Sarkin gida matsayin da aka karawa Innayoh, ai kuwa take aka sake maganar a cikin gidan kamar yadda ake wuta ke yaɗuwa, take tsofin bayin gidan abin yayi musu ciwo da zafi, taya Innayoh da tazo bayan su. Yaushe tazo gidan wato me ruwa a gindin murhu ba zai ci tuwon shi gaya ba.

Dan haka al’amarin ya zafaffa, yayinda wasu bayin suka kulla aniyar su sun ga bayan Innayoh. Domin ta hana su abubuwa dayawa musamman yadda ta hana su shiga jikin Fulani Aminatu, suna jin ciwon haka sai gashi an kuma wani an bawa Innayoh uwar bayin gidan, wato duk wani bawan cikin gidan ita ce shugabar shi baki daya.

Ina tasan suna yi balle ya dame ta. Kowa yaga zai iya yayi, Fulani Aminatu ne dai babu wanda zai shiga jikin ta a cutar da ita. Domin ta lura ana niman yadda za a cutar da Fulani Aminatu kota wani irin hali ne.

…. Da la’asar likis, aka fitar da keken doki. Mai Martaba da ita Fulanin da tasha adon jajjayen karanmiski, sai kayan ado na kawa da aka shirya mata a jikin ta tayi mugun kyau. Yana tsaye a jikin keken ta fito, mika mata hannu yayi ya rike tana murmushi, ya tsaya mata yana kallon yadda fadawa suka juya musu baya daukar ta yayi cak ya sakata a cikin keken. Sannan Innayoh ta mikawa Sarkin gida kwando me cike da ya’yan itacce, da sauran abubuwan aka mikawa badawa suka rike dai Balaraba da uwani, suka jeru bayan mai Martaba ya shiga cikin keken suka shiga takawa su da kafa, kasancewar keken a hankali ake tafiya da dawakan.

Duk inda suka wuce mutane ke jinjina masu, suna kara Mishi kirari. Har suka bar masarautan.

“Baffa’m!” Hannun shi ya saka cikin nata.
“Na’am” ya fada yana kara rike hannun ta da kyau.
“Allah ya sa yadda kake da kirki Allah yasa haka kakewa talakawan ka”

Advertisements

A hankali ya juya ya kalle ta sannan ya sumbaci hannunta,
“Me yasa kike tunanin zan yi rashin kirki ga al’umma ta”

Juyawa tayi tana tuna abinda Innayoh ta fada mata.
“Talakawan da suke kasan ka, da ni da nake kasar ka, duk abinda tambaya ne a gaban Ubangiji. Baffa’m ina son talakawa su kasance suna alfahari da kai a koda yaushe, amma dole sai yanayin ya fara daga kaina” ta fada tana sunkuyar da kanta, sabida matsanancin kunya da take da ita, kan shi ya kai wuyar ta ya sumbata, sannan ya ce mata.
“Ke zaki fara alfahari da samun jarumi irina” ya fada yana sauke mata wani narkakken sumbata..

“Baffa’m!” Ya d’ago kai yana kallon ta,
“Kana sani jin kunyar ka, da abinda kake min” ta fada tana rufe fuskarta.
“Da gaske ina sani jin kunyar abinda nake miki” ya kai bakin shi kan yatsan hannunta da suka yi wani kalar ja na lallen da aka mata.
“Hmm”
“Bude baki zaki, Kice Baffa’m ina son abinda kake min nan”
“Wayyo” ta wani furta a hankali tana zare ido. Cafke bakin yayi yana wani irin tsotsar shi. Rintsa idanun tayi taki budewa tana sauke ajiyar zuciya a kai akai. A hankali ya sake bakin, yana me zura hannun shi cikin rigar ta.
“Baffa’m ana ganin mu” ta fada murya ta yana rawa.
“Kiyi shiru” ya fada yana daura hannun shi a kan shafaffen cikin ta.
“Ina rokon Rahamar Allah ya azurta mu da kyakyawar Ya mace irin ki”
Dariya tayi tana kallon shi kafin ta ce.
“Baffa’m! Ka daina irin wannan maganar” ta fada tana boye fuskar ta, a kirjin shi.
“Ba wani nan bude ido ki gaya min gaskiya ni dai mace nake so”
“Duk abinda kake so shi nake so” ya fada tana kara jan numfashi.
“Toh lallai gobe ki shirya karba na a matsayin sabon ango.” D’ago kai tayi tana kallon shi zuciyarta tana bugawa, a hankali ta sunkuyar da kanta. Tana boye tsoron abinda ya ce mata.
“Kin ji tsoro ne?” Ya tambaye ta,
“Hm” tace mishi.
Janyota yayi jikin shi yana shafa bayan ta.
“Sannun kin ji karki damu babu abinda zan miki” haka ya cigaba da latsata har suka tafi can gidan gonar masarautar.

Tun kafin su sauka an gyara ko ina, wasu Fulani ne ke zama a wurin suna kula da dabbobin masarautan, sai da aka gama kome sannan Sarkin gida ya musu magana.
“Allah ya baka nasara an shirya wurin”

Sun dauki lokaci kafin Sarkin gida ya bude kofar keken dokin, shi a hankali ya fito daga cikin keken, sannan ya mika mata hannu, itama ta fito, tana kallon wurin cikin wani irin jin dadi. Yau ta shaki isar wajen masarautan…

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 22

Advertisement Page 22* ********************** Ashe ba salma kad’ai ba mata da mazan dake wurin, ya tafi da tunaninsu,…
Read More

TARTSATSI 85

Advertisement   *Page 85*   **********************   Aikam Hajiya tayita sababi, bakinta yana kunfa, saboda tsabar masifa, dak’yar…
Read More

TARTSATSI 35

Advertisement *page 35* ******************** Umma da gwaggo haja da aunty amarya, sun k’ule falon na umma, sai hirar…