KALLABI 14

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*<Babi Na sha hudu>*

*Rundunar dakarun kasar Sahil*
Yada zango suka yi aka shiga kafa tanti masu fita farauta sun tafi har aka gama can sai gasu dauke da gadda da barewa, suka zuba a hankali tare da kallon shugaban su, a take aka hada itacce tare da ciyayi, aka feɗe dabbobin aka bankare su sannan aka saka gwaf, aka shiga gasu su.

“Shugaba akwai tafiya wata goma sha biyar a har yanzu fa” inji wani badakare da yake tsaye, a gefen shi.
Shiru yayi yana zane a kasa kafin ya d’ago kai yana kallon shi.
“Lati bana tsammanin zamu samu nasarar dauko Yarinyar”
Zaro idanu Lati yayi yana kallon Shugaban shi. Kafin yayi kasa da kan shi.
“Ya shugabana! Ka kuma nazari akwai wani abu ne?” Lati ta fada yana kallon shi.
“Duk abinda na saka a gabana ban tab’a jin shakka ko tsoro ba, amma wannan karon yakin kamar ba nasara, dan haka zan tafi ne domin biyayya ba wai dan na samu nasara ba”
Cikin gamsuwa Lati ya gyada mishi kai yayi yana kallon shi kafin ya ce mishi.
“Toh ya zamu yi da sauran dakarun!” Mikewa yayi yana me d’aga labulen ta tantin.
“Ba zan so su rasa rayuwar su ba, ni daya zan tunkari yanki idan yi nasara ba sai ku juya” ya fada yana kallon lati da yayi shiru shima yana sauraron shi. Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Karka damu lati zamu yi nasara amma ka sani tafiyar da zamu yi da komawar mu”
“Kawai ina tsoron abinda zai faru domin Sarkin Arkhan ba zai tab’a hakura da burin shi ba, kawai muje koda zamu mutu ne gara mutuwar mu ta isa gare shi da ace Mun koma babu yarinyar.”
Shiru yayi yana nazari abinda lati ya fada yana kallon Shugaban su.
“Lokaci ne zai nuna haka, idan yayi toh zabe yana gare mu ko mu juya ko mu tsaya a kashe mu amma tabbas masarautar da zamu tunkara ba karamar masarauta bace da zamu iya murkushe ta a lokaci guda, masarauta ce me cikin gashin kanta, idan har muna son galaba akan su dole sai mun tsaya ka’in da na’in mu yake su ba dare ba rana”
“Na gamsu da bayanin ka. Amma karka manta idan har muna son muci galaba akan masarautan sai mun samu hadin kan wasu babu wata alkaryar da za a ginata babu kalubale, imma na kishi ko na hasadda shine kawai zai bamu damar fahimtar haka.”
**
*Shashin Ajuji*
“Allah ya baki nasara uwar Sarkin goben, takawarki lafiya gaba salama baya salama. Na samu labarin Mai Martaba ya tafi kilisa da Fulani Aminatu” cak ta tsaya daga taunar soyayyen naman da take ta ajiye shi, sannan ta kalli Jakadiya Rama.
“Ki kawo min lantana da Zulai” ta fadawa Jakadiya.
“Allah ya baki nasara,an gama” ta fita tana fita ta harari kofar shashin Ajuji, tsabar jin Haushin sannan ta fita zuwa can wurin bayin ta sami Innayoh da Sarkin Gida.
“Sarkin gida ya gaya min yanayin da kuke ciki,sannan insha Allah zamu duba, kuma za a tura kome wurin mai Martaba ko za a gyara shashin ku baki daya”
“Hahhhhh” suka ji dariyar Jakadiya Rama tana faɗin.
“Ki tsaya daga inda kike nan mallakar matan tsohon sarki ne! Kuma masu fatan sake samun sabon Sarki nan gaba” murmushi Innayoh tayi sannan ta ce mata.
“Sarki goma zamani goma, duk sarkin da yazo da nashi tsarin mulkin wannan tsarin sarki Bello. Ki iya harshen ki kar bakin ki ta janyo miki magana”
“Innayoh meye nufin ki?” Inji Jakadiya Rama,
Murmushi Innayoh tayi sannan ta kalli bayin sannan ta ce musu.
“Daga yau za a gina babban madafin girki, a shashin Fulani Aminatu daga yau abincin ku na safe da na rana da na dare zai fito daga can. ”
“Godiya muke, a mika mana sakon godiya ga Fulani Aminatu”
Har ta juya zata tafi ta ce musu.
“Sarkin gida zai duba abinda kuke bukata, ka kawo min kome a rubuce yadda xan bawa Fulani Aminatu ta mika ga Mai Martaba kasan gobe laraba.”
“Insha Allah” ya fada yana me take mata baya. Shan gabanta Jakadiya Rama tayi tana faɗin.
“Ke kin zata zamu amshi wannan lamari ne? Baki isa ba, nice Jakadiyar masarautar Gobir tun iyaye da kakanni, sai na hana ki motsi” murmushi Innayoh tayi tana me nade hannun ta,tana faɗin.
“Karki damu, nasan darajar farin gashi bana son wata rana a min haka. Jakadiya ko Mai Martaba bai gaya miki ba ai ya kamata ki fahimta.” Wani irin zaro idanu tayi tana me kai hannun ta zata shake wuyar Innayoh. Da sauri sarkin gida ya shiga tsakanin.
“Jakadiya ki rike matsayin ki, ƙarki yi abinda zai saka mai Martaba ya Kore ki a masarautan nan domin kowa yasa kananun magana da yake yawo kece kike fitar da shi da taimakon wasu munafukan kusa dake” shiru tayi tana kallon Innayoh jikinta baki daya rawa yake.
“Na rantse da Allah ba zan bar matsayina ba, akan me nice haifaffiyar masarautar Gobir taya.”
“Muje Sarkin gida” suka wuce abin su, cikin tashin hankali Jakadiya ta nufi sashen Gambo ta zube a gaban ta.
“Uwar ɗakina ki min rai Mai Martaba ya nad’a Innayoh a sabuwar Jakadiyar shi, matsayin nan gadar shi nayi tun iyaye da kakanni yau daya a ture ni. Dariya duniya zata min” ta fada cikin matsanancin kuka da tashin hankali. Waziri Zakaria da yake zaune yana shan kindirmo, mara tsami domin zuwan Fulani Aminatu yasaka su koyan shan madara kindirmo da dai wasu abubuwan.
Ajiye ƙwaryan yayi sannan ya zuba mata ido.
“Jakadiya matsayin ki bai sauya ba, kina nan a Jakadiyar Ajuji da Yarimar Gobir, sai dai gamu da muka yi mubaya’a ga sarki Bello ba zamu dauke ki a matsayin Jakadiya ba, sai kiyi hakuri, abinda kike aikatawa kamata yayi a yanke miki hukuncin kisa, amma dake dattako yana jinin shi ya zab’i a barki ki rayu kawai bata shugaban bayi yayi kika firgita idan kuma ya bata Jakadiyar da? Wani lokaci muna son abu muke hakura da shi. Amma kin kasa gane haka shi yana wurin ne ba dan ran shi naso ba, ku kuma kun dauka yana zaune ne domin yana jin dadin rayuwar shi. Haka ya tsara mulkin shi bai san izza ds d’agawa. ” Daga haka ya mike ya fita a dakin.

Rarrafawa ta yi gaban Gambo.
“Ki min rai, na cancanci kowani hukunci amma wofatar da ni akwai tashin hankali” ta fada tana kuka.
“Jakadiya babu wanda ya wofatar dake, kece kika bukaci haka
Jakadiya mun iya taku da salo ne dan a zauna lafiya ba wai dan mu zama masu tadda husama ba”
Daga haka itama ta bar zauren tana jin kamar ta saka baki a dawo da Jakadiya matsayin ta amma ai ba cire ta yayi ba kawai ya rage mata yawan damar da ta samu ne, kuma haka shine ya kamaci masu irin halin ta. Baki daya.
**
*Gidan gona*
Inda suke zaune babu kowa yana nazarin wasu abubuwan ne yake cikin gidan gonar, ita kuma tana kwance kanta akan cinyar shi, tana kallon yadda yake ta rubuce-rubuce, kallon shi tayi sannan ta mike zaune ta ce.
“Baffa’m! Ina son ganin gidan gonar” ta fada tana kallon yadda yake kokarin ajiye alkalamin shi.
“Baffa’m!”
“Hmm! Yar Kwailar Baffa’m!”
“Nace ina son” bakin shi ya kai kan nata, shiru tayi tana kallon ƙwayar idanun shi, kafin ta lumshe idanun ta. Tana jin yadda yake kokarin saka hannun shi cikin rigar ta da sauri ta mike.
“Baffa’m!”
“Zo nan” ya kira ta, matsawa tayi kusa da shi, ya janyota har kan cinyar shi ya matse ta yana shaƙar kamshin turaren ta, hannun shi yana murza kananun dukiyar Fulani da suke mishi iyaka da ita, b’ata suka yi a wurin.
Wato mai Martaba idan ya samu Yar Kwailar shi a gefe baka jin kome sai kawai yayi ta matse ta yana rage zafi.

“Baffa’m akwai mutane anan, kuma girman ka da Alkhairink yawa ce da Ita” ta fada a hankali, tana wasa da zaren alkyabbar shi.
“Idan na fahimci Fulani Aminatu tana bukatar a kame ko?”
“Shima yana cikin mutunttawa” ta fada tana wasa da zaren.
Mikewa yayi ya saka takalmin shi sannan ya mika mata hannu ta mike, suka shiga zaga gidan gonar, har suka isa inda ake kiwon tumakai, wani jaririn rago ta gani ta nufi wurin da sauri ta dauke shi tana kallon mai Martaba.
“Ina uwar shi take?” Ta tambayi fulani da suke kiwon cikin harshen fulatanci.
“Uwar ta kasa, gata can an kyafeta” dattijon ya fada yana sunkuyar da kai.
“Ayya Baffa’m kaji mamar shi ta kasa kamar n..” kura mata ido yayi dan ba abu me wuya bane ta fashe da kuka.
Kasa tayi da kanta tana wasa da dan ragon sannan ta ajiye shi.
Suna tafiya amma dukkan su shiru suka yi.
“Baffa’m! Ina ce ba zan mutu da wuri ba ko?” Ta tambaye shi.
“Insha Allah sai kin rike jikanki”
Rufe fuskar ta tayi da hannunta, cire hannun yayi yana kallon ta.
“Karki sake ki min kuka” ya fada yana jan kumatunta.
Haka suka yi ta yawo har zuwa dan wani karamin korama da yake cikin gidan gonar, suka zauna. Matso da ita yayi jikin shi, yana sauke numfashi, idan bai yi karya ba zai iya dogon rayuwa babu ita ba, kara matse ta yayi.
“Fulani na!”
“Hm!”
Ta ce mishi,
Saka bakin shi yayi a dokin wuyarta yana sumbatar ta.
“Kar ki kalubalenci hukuncina nayi miki alkawarin baki kariya muna tare ko bama tare fata na ki rayu cikin aminci da salama, bana son ko bayana kiyi maraici.”
“Baffa’m akwai wani abu ne? Sabida maganar ka yafi kama da wanda yake bada wasiyya! Ban san ya akayi ba kawai naji ina son na zauna da kai baki daya rayuwata, kawai ko dan yadda ka sake min ne? Ko dan yadda ka bani lokacin ka ne hala. Amma ina farin cikin zama a inuwar ka, bana fatan tafiyar da zata nisanta ni da kai!” Ta juya yana me tallafe fuskar shi da hannun ta.
“Kin damu da ni ne haka?” Ya tambaye ta, dan sunne kanta tayi tana murmushin jin kunya.
“Wacce hazikar mace ce zata same ka bata yi fatan nisan kwana da kai ba?”
“Yaushe Fulani na ta fahimci haka?” Murmushi tayi sannan ta ce.
“Tun ranar da baffa’m ya fara shigowa sassa na”
“Wato lokacin kika ga Jarumin maza ko?” Ya tambaye ta yana murmushi.
“Bana ce ba!”
“Ki ce ma”
“A’a mai Martaba.”
“A’a Fulani Aminatu” tana d’ago kai zata kalle shi ya sumbaci hancin.
“Wata rana labari zai shafe, tarihi zata manta da mu. Kowa zai manta da Fulani Aminatu. Amma nasan ni ba zan tab’a mantawa da kai ba, domin na samu farin cikin ne bayan zama da kai!”
Matse hannun ta yayi yana kallon yadda take kokarin boye murmushinta.
“Waye ya gaya miki za a manta dake a tarihin masarautar nan? Waye ta gaya miki zan manta dake? Bayan anan na rufe ki na ajiye!” Ya nuna mata kirjin shi daidai saitin zuciyar shi. Tana jin yadda yake bugawa kamar me..
“Laaa bugawa yake” ta fada a shirirince.
“Haka naki yake bugawa!”
“Baffa’m ina son daukar dan ragon nan, tausayi yake bani ina son na kai shi cikin gida ayi renon shi.”
Kura mata ido yayi ya ma rasa me zai mata yaji dadin rayuwar shi ya ce mata.
“A’a nima ina son kiyi reno na, kamar yadda kike renon dan dalago”
“Kai baffa’m! Kai yi kato da reno, taya ma xan iya renon ka?”
“Zaki iya mana, reno na da nasu da banbanci, kulawar da zaki bani tafi nasu, ni har da ɗaukar nauyi na”
“Baffa’m taya zan dauki nauyin ka? Don Allah kayi hakuri, ban san yadda zan yi da kai ba”
“Zaki sani Fulani Aminatu tunda gani nan a tare da ke sai ki san yadda zaki yi dani har daura ni a cinya zaki yi”
“Allah ya baka hakuri” ta fada Idanunta yana cika da kwalla. Alamar baki daya ta rasa abinda yake mata dad’i.
“Toh Meye na shiga damuwa, bayan gani kwantar da hankalinki babu abinda zan miki” ya fada bayan ya ja hannun ta suka cigaba da yawo dan ya lura baki daya ya gama gigita mata hankali.
Haka suka gama yawon sai yamma likis, suka fara shirin dawowa masarautar. A lokacin aka shigo da manyan manyan shanun da ake kiwo.
” Baffa’m suma bayin masarautan da ne?”
“Eh bayin masarauta ne” ya bata amsa a takaice.
“Tsawon wani lokaci suka dauka anan?” Kallon mamaki yake mata.
“Gaskiya zasu kai kaman shekaru talatin.” Kallon shi tayi tare da cewa.
“Ina son naga gidajen su”
“Toh” ya ce mata, sannan ya tab’a kofar tsayawa aka yi, sannan aka bude keken.
“Ku Kai mu rugar Malam Jauro”
Juyar da keken dawakan aka yi ta wuce da su can gaba da gidan gonar.
Bukkar Fulani ne birjin sama da abinda idanun ka ya gani, gefe guda akwai wata fili babba da aka katange shi toka ne a tsakiyar shi. Alamar ana karatun Alkur’ani a wurin. Tun daga nesa aka gaya musu ga Mai Martaba nan zuwa, baki daya maza rugar har da shi Malam Jauro. A hankali ya fito daga cikin bukkar shi ya ratsa mutanen shi har gaban inda Keken mai Martaba yake.
“Allah yasa ba wani abu muka yi ba?” Mafi yawan mutanen wurin suka fada.
Fitowar Mai Martaba da Fulani yasa suka sauke ajiyar zuciya.
Zubewa suka yi baki dayan su, suna faɗin.
“Takawar ka lafiya sarki me daraja, Allah ya kare ka daga sharrin masu sharri gatan gobir!” Murmushi yayi sannan Sarkin fada ya ce.
“Mai Martaba ya amsa”
“Malam ka tashi yau. Yar kuce tazo ganin ku” ya nuna musu Fulani.
“Barka da zuwa Yar nan lalle maraba da zuwa cikin mu Barka da zuwa.”
Murmushi tayi iyaka farin cikin yau tayi shi.
“Baffa ka tashi” ta fada cikin harshen fulatanci. Wayyo Allah baki daya suka tsaya da mamaki kafin malam Jauro ya kalli Matar shi me suna Habi ya ce matar.
“Daadah maza ku shigo da Fulani Aminatu, maza a kira yan matan su gyara mata inda zata zauna. Mai Martaba zo ga bukka ka zauna” yana tafe mai Martaba yana bin bayan shi. Har cikin bukkar da yasha gyara kamar dakin mace. Ga kamshin turaren da yaƙe. Fitowa yayi yana me kiran Habi.
“Daadah maza ki gayawa Rabe da Ila maza su yanka kaji da a gasa shi kafin a fito magariba mai Martaba da Fulani su samu abincie”
“Toh Malam” ta fada,. Sannan ta wuce ta bada umarnin da ya bata, aikuwa kafin wani lokaci an gama yanke kajin.
A dakin da aka kai Fulani. Yan mata rugar da suke da aure sa’o’in ta, sai zuwa suke suna gaishe ta.
Wata ce me shegen kaudi a cikin su sunanta hari.
“Amma kece matar Mai Martaba ko? Amaryan da ya auro shekarun baya?” Cikin tsannanin kunya ta gyada kanta.
“Gaskiya labarin ya zo mana har nan, kuma muna cikin masu mishi fatan Alkhairi!”
“Ya gode” Fulani Aminatu ta fada tana kallon su. Shigowar Daadah da kayan abinci kala kala yasa yan mata nan amsa suka shiga jerawa.
“Idan kun gama ku bata wuri” kan Fulani Aminatu a sunkuye bata d’ago ba, har suka gama suka fita.
“Ayya Innayoh zata yi tsammanin ba zan dawo bane” kiran sallah magariba yasa ta fito waje, tayi alola kamar yadda sauran jama’ar rugar suke, sannan ta koma cikin dakin. Ta samu an shimfida mata abin sallah, a hankali ta gabatar da sallah, tare idarwa. Wata yar budurwa ta shigo dakin.
“Sannun Fulani” gyada mata kai tayi tana faɗin.
“Yawwa” zama tayi tana kallon ta.
“Mai Martaba yana wurin Baffa, shine nace bari na shigo muyi hira” yar murmushi Fulani tayi. Tana wasa da dafaffen madaran da aka kawo mata, bawai ba zata sha bane kawai, kallon Yarinyar tayi kafin ta ce mata.
“Ya sunanki?”
“Bingel” ta bata amsa.
Daga haka bata kuma magana ba,.kawai jikinta da ranta bai mata ba akan Yarinyar.
“Fulani ko zan dawo wurin ki ne a cikin masarautan na zauna a matsayin baiwar ki” wani irin faduwar gaba take ji, kafin ta d’ago kai tana kallon ta.
“A’a ina da bayi sosai, kuma bana son Innayoh tayi min faɗa. Sannan kina da yanci ba zaki yi bauta ba. Ki zauna anan zai fi miki kwanciyar hankali, da a ce masarauta ka kare rayuwar ka a bautawa wani”
“Wacece Innayoh?” Ta tambaye ta.
“Mama ta ce” ta bata amsa,
“Mamarki ta biyo ki?” Gundura tayi da maganar domin ban da Mai Martaba da Innayoh bata iya dogon magana da kowa. Sai ta ja bakinta tayi shiru bata kuma magana ba, kuma bata kuma d’ago kai ta kalli Yarinyar ba.
Wani lokaci ƙaddaran mu tana shirye tsaf, amma bata riske mu ba, sai a ta wani sanadi na daban. Mikewa Bingel tayi sannan ta nufi dakin Baffan ta, da sallama dan tasan yana wurin karatu bayan anyi sallah. Shiga cikin dakin tayi da sallama.
Ta zube a gaban Mai Martaba. Kwarjinin da yayi mata yasa baki daya ta kasa ko furta kalma daya daga bakin ta, yana kallon ta bai ce mata kome ba.
A can dakin kuwa kasa sukuni Fulani Aminatu tayi da sauri ta mike ta fito, tare da nufar dakin da Baffa’m yake. Ta shiga kamar an wurgota domin taga lokacin da ya shiga cikin dakin, tana shiga ko kallon Bingel bata yi ba. Ta nufi Mai Martaba.
“Baffa’m muje gida” tashi yayi zaune yana kallon fuskar ta.
“Dare yayi Fulani Aminatu”
Wani irin gigitacen kuka ta saka mishi har tana jan numfashi sama sama. Baki daya ya rikice ya ma rasa me zai ce mata.
“Shi kenan zamu tafi yanzun” ya fada bayan ya gyara mata zama a jikin shi yana shafa bayan ta.
Baiwar Allah sake baki tayi tana kallon ikon Allah, burin ta burin Rayuwar ta. Babban burin ta ta sami namiji me riritatta. Yau sai gata tana ganin burin nan yana samuwa ta Yarinyar da bata fita kyau ba, bata fita kome. A hankali ta mike tana kallon su. Murmushi tayi sannan ta fita daga cikin dakin.
“Ko da za’a raba kaina da gangan jikina sai na tawo ko a kwarkwarah ce!”
A daren babu shiri suka bar rugar bayan an musu shatara na arziki. Sannan suka dawo masarautan tun a hanya tayi barci, suna isa ya dauke ta ya wuce da ita sassan shi ya shimfida ta. Sannan ya gyara mata kwanciya kasancewar sunyi sallah Isha a can. Dan haka ban daki ta shiga yayi wanka ya gyara jikin shi ya fito ya gabatar da shafa’i da wutiri, sannan ya kwanta a bayan ta. A hankali ya shiga cire mata kayan jikinta, sannan ya juyata gare shi yana kallon yadda take barci, a hankali ya shiga sarrafa kowani sassa na jikin ta, bude idanu tayi tana kallon yadda yake kome, sannan ta lumshe idanun ta, tana me sadakar da kome a gare shi da irin kallon da yarinyar can tayi mishi, gwara tabar shi yayi yadda yake bukata da ita tana jin shi har ya…
_____________________________
End of page 14

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 8

Advertisement Babi Na Bakwai>* *Godiya da fatan alkhairi son so daga Mai Daraja😍🔥* Barka da Juma’a# Masarautar Gobir.…
KALLABI
Read More

KALLABI 36

Advertisement BABI NA TALATIN DA SHIDA _DA KAKKAUSAR MARTINI DA HADE FUSKA NA FUSATA NAYO KAN YAN GRP…
INAYAH
Read More

INAYAH 21

Advertisement *_21_* *_Arewabook@Mamuhgee_* Tana isowa gidan tun a compound tasan Abbi yadawo gida sbd ganin sabuwar motarsa da…
KALLABI
Read More

KALLABI 44

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA HUƊU Cikin wani irin yanayi ya ke kallon ta, a hankali take kallon…