KALLABI 15

KALLABI
KALLABI

Advertisement

BABI NA SHA BIYAR*
Wani jan numfashi take cikin tsananin tsoro da tashin hankali, idanun ta sun firfito waje, ta kuma damke damtsen shi ta fashe da wani irin kuka jikinta babu inda baya rawa, tsoron da take ji a bayyana a kan fuskar ta, ware idanu tayi tare da fashewa da kuka tana ture shi.
“Baffa’m don Allah kayi hakuri, Wayyo Allah Innayoh, Wayyo Baffana. Hamma na kazo ka ceci ni”
Baki daya sarki Ballo ya rasa nutsuwar shi yar Kwailar shi ta gama rikita shi, ji yake duniyar kamar shi tafi kowa dace da wannan yanayin, shi yasa bai ji ta ba, bai kuma ji me take cewa ba, ya rintsa idanun shi tare da toshe kunnen shi yayi ta kwasar baiwar da Allah yayi mata tare da cin alwashin babu abinda zai isa raba su. Bai tab’a sanin cewa haka aure yake ba, sai da ya nika yar mutane, yayi mata bulaliyar shi, bai san lokacin da ya dauka yana zungure ta ba, amma tabbas yayi fatan hakan ya kasance har gaban abada.

**
*Birnin Sahel*
Wani irin uban ihu bokanya Tursi tayi tare da kutufal da halwar tsafinta wanda a kala zai kai kimanin shekaru dari da casa’in domin gadar dashi tayi a wurin kakanin ta, halwar ta mirgina ta faɗi kafin ta kuma tashi zaune, kasancewar aiki da suke da manyan ifiritai.
“Uwar gijiyata ƙaddara ba ta karya, Ƙarki manta bai zama dole sarki arkan ya samu Magaji ba, kuma kema kin san da haka” d’ago kai tayi ta kurawa turwa Idanu, kwalla na zuba mata sili-sili.
“Na rantse da toshe zuri’ata ba zan dauki faduwa ba, maza mu wuce fadar sarki Arkhan!”
“Ya shugabata a wannan gabbar akwai son rai! Nasarar da ta zo har gidan ka itace nasarar ka, amma ƙaddarar da zata dauke ka har zuwa wuni wurin sunan shi son zuciya. Matukar aka farmaki mutanen da basu ji ba babu gani ba, tabbas an kawo karshen Sahel ne, kuma kin san da haka, kuma kin fahimci haka ba kaddaran Arkhan bane haihuwa.”

“Turwa ya zan yi da sarki Arkhan? Tunda na tabbatar mishi da cewa wiwar haihuwar shi a wurin yarinyar yake?” Ta tambaya tana me zama dabas akan shimfidar da yake dakin.
Sunkuyar da kai Turwa tayi tana kallon kasa.
“Daga lokacin da kika tabbatar zaki iya yaki toh ina ji a jikina zaki yi nasara, amma da zaran na fara jin kamshin faduwa jikina yake bani ki dakatar da zuwa ga Arkhan domin..”

“Babu nasara ko? Domin dakarun da muka tura su ma basu da kwarin gwiwa ko turwa?” Ta tambaye ta.
Gyada kai tayi, tana me had’e hannun ta wuri guda tana matse shi. Takawa tayi gaban ta tana kallon yadda take tsaye.
“Turwa baki daya na kasa gane wacce irin halitta kike da ita na sunshino kaddaran wasu?” D’ago kai tayi, kafin ta sunkuyar da kanta tana me jin wani irin kaduwa, na tsoro kafin ta zube a gaban Tursi tana cewa.
“Ya shugabata ki gafarce ni”
***
*Masarautar Gobir*
A hankali ya janye tare da rubda cikin shi yana goga kan shi a kadadar Fulani Aminatu, baki daya ya rasa kuzarin shi. Ji yake kamar bai da cikakken lafiya domin baki daya da zuciyar shi yake bin al’amarin ta, ya kai wani lokaci a wurin kwance, amma sama-sama yake jin shashekar kukan ta. A sanyayye ya juya yana kallon ta, yadda ta dunkule samun kan shi yayi da kasa tabuka kome, yadda take jan kukan ta cikin yarinta yana kara fisgar zuciyar shi da imanin shi. Wani irin kaunarta da begen ta, suna kara samun mafaka a ruhin shi, baya jin akwai wani abu da ya kaita tasirantuwa ruhin shi kamar yadda take shashekar kuka. Cikin tsananin gajiya ya matsa bayan ta, sannan ya sakala hannun shi a K’ugunta, ya juyo da ita suna fuskartar juna.
“Kiyi shiru Kinji” ya fada mata yana me daura yatsar hannun shi a saman bakinta, idanun ta a rufe ta shiga gyada mishi kai.
Bakin shi ya kai habb’arta, ya sumbaci wurin a hankali, kafin ya janyota kirjin shi yana shafa bayan ta, kamar dama jira take ya janyota, ta shiga mishi wasu kananun rikici wanda ya haifar mata da zazzafar zazzaɓi a daren, abin gwanin ban tausayi.
Dakyar ya samu ya mike ya tsaftace jikin shi, ko kafin ya fito ya samu har ta koma barcin ta. Hakura yayi da wurin kwanciyar ya koma kasa ya kwanta a Kilishi da matashin sa.

**
*Wayewar gari*
An tashi da wani sabon al’amari ne na farin ciki, wanda tun asubar farko ake buga tamburan masarautar wanda dama dabi’a ce ko ace al’adun masarauta ce, ana bugawa duk lokacin da Sarkin Gida ya samu labarin wani cigaba ya faru a masarautan, ko za’a tarbi mai Martaba daga dawowa a yaki,.ko an samu karuwa a cikin masarautan, ko sarki ya kwana da Amaryan shi da yake girmama al’amarin ta, toh tun asuban fari ya sanar da Sarkin gida a kira Innayoh, tana shiga turakar Mai Martaba, aka ji ta rangad’a gud’a tare da fitowa da sauri tayi ta rangad’a gud’a, wanda ya farka da wasu bayin sashin Fulani Aminatu, kafin kace me an shiga had’a gagarumin biki, kamar yau ake bikin Sarki Bello da Fulani Aminatu, biki me sunan buki, wanda Innayoh ita ta wanke Fulani Aminatu da madarar saniya da aka amso daga can gidan gonar masarautar

Tun Fulani Aminatu tana kuka da noke mata, har ta sake jiki tana me kallon abinda ake mata, an gasa ta kuwa babu iyaka, sannan ta wanke ta tass ta rikota suka dawo dakin Mai Martaba, haka aka kuma nad’e shimfidar su, aka fita da shi, aka fara terere da shi ana gayawa sauran Jama’a wannan shine dare mafi girma ga Mai Martaba Sarki Bello, daren da ya raya shi da Fulani Aminatu, wannan Al’adar ba karamin tasiri take da shi ba, a cikin masarautan kasar Hausa, domin da mace ta kasance ba budurwa ba, gara ta mutu tun kafin ta janyowa Zuri’ar ta kiyayya da tsanar masarautar domin zai fi sauki a tsinci gawar ta a yashe da ake ta shigo da wani abin kunya cikin masarautan.
Wunin ranar an yi shi ne cikin farin ciki da jin dadin domin shi kan sa sarki Bello a tarihi ba a tab’a samun Sarkin da ya yanta bayi babu adadi ba,.kamar shi duk da abin yayiwa wasu manyan fada ciwo, kuma da kan shi ya tafi har gidan kaso yayiwa wasu rifsinoni afuwa aka yafe musu laifin su, tare da musu gargadin kar su kuma.

Sannan an karawa wasu manyan bayin da suke tare da Innayoh matsayi wanda yasa kowa fahimtar cewa Fulani Aminatu mace ce ta musamman a rayuwar Sarki Bello. Kuma ta zama macen da babu biyun ta a cikin masarautan, wannan ya haifar da wani irin kishi da yawa me mugun ci rai, wanda har sauran uwaren gidan suka kasa boye damuwar su, kiri-kiri Ajuji ta fadi abinda yake ranta akan Fulani Aminatu, wanda haka yasa aka fara kananan magana, abin ka da gidan sarauta sai al’amarin ya zafaffa kamar dama jiran ake Sarki Bello yayi tarayya da Fulani Aminatu.

Zaune suke a babban turakar ta, Innayo ta saka mata abinci a gaba tana tsakura, kamar ba zata ci ba. Kamar zatayi kuka, idanun ta sun cika da kwalla tab. Jira kawai take su zubo,
“Kina nufin ba zaki ci abinci bane? Wai ma kina dauka al’amarin aure wasa ne? Maza ci ya kama miki jiki yadda zaki ji dadin daukar al’amarin mijinki da daraja.”

Sharr sai ga hawaye dama jiran hanyar sauka suke, kuma dama an ce me shirin kuka aka wurge shi da kashin awaki. Shine ya faru akan Fulani Aminatu.
Cikin mugu mugun shagwab’a Fulani Aminatu ta kalle ta.
“Innayoh na fasa auren!”
Daga waje suka ji sallama yana faɗin.
“Takawar ka lafiya, giwa me tafiyar kasaita, an gaishe ka alfadari me kashin kudi, Barde namijin zaki, gamji me tuhon alkhairi, Angon Fulani Aminatu, Namijin gaske namijin duniya”
Bayan shi kuwa fadawa ne ke take mishi baya, fuskar shi tana fitar da wata irin murmushi me daukar hankali, duk inda ya gifta murmushi kawai yake, yana kara jin wani irin shauki da mulki yana kwasar shi.
Kalaman Galadima ce ta dawo mishi rai dazun da suka kebe ya zuba mishi ido kafin ya ce mishi.
“Ka dan bita a hankali, yarinya ce matuƙar ka kuma Binta da zafi zata razana kuma ba xata iya sake jiki da kai ba, a yanzu kake da damar kafa soyayyar ka me gardi”
Shafa wuyar shi yayi ta cikin alkyabar shi yana kallon sama, kafin ya shiga yar karamar harabar sashin Fulani Aminatu, sannana aka bude mishi kofar. Manyan mayafan da aka saka a tsakar zauren yayi ta d’agewa har ya isa bakin kofar da take, ya fahimci tana wurin ne, Sabida bayin ta da ya gani a kofar dakin dan haka ya shiga cikin da sallama.
A wani irin sukwane ta d’ago kai tana kallon shi, kafin ta sauke da sauri. Hannun ta yana rawa. Kwalla ne ya cika mata Idanu,
“Barka da zuwa Mai Martaba.” Innayoh ta gaishe shi,.tana kowa gefen can.
D’aga mata hannu yayi, sannan ya zauna yana fuskar ta Fulani Aminatu, da take kallon Innayoh idanun ta yana cika da kwalla. Ko nace yana zuba, da sauri Innayoh ta fita, shi kuma ya zauna yana kallon ta, dan wauta sai ta fashe da kuka tana kiran Innayoh.
“Innayoh!!”
Kallon fuskar ta yayi, wanda suka bayyana tsoron ta ƙarara.
“Mmmm” ya sake murmushi me sauti yana kallon yadda take kara diriricewa hadi da shashekar kuka.
“Toh meye na kuka? Ni ne baki son gani na fita?”
Ya tambaye ta yana kallon yadda hannun ta yake rawa. Girgiza kai tayi.
“Toh me kike so?”
“Zan tafi wurin Innayoh, tsoro kake bani” a hankali ya cire alkyabbar shi, sannan ya zare rawanin ya kura mata ido, yana me ajiye kayan dukka a gefen shi, riko hannun ta yayi yana kallon yadda jikin ta ya dauki rawa, ba wai zai mata wani abu bane, amma baki daya yanzun ya rigada ya ji dadin ta, ba zai iya awa daya bai ji ta a jikin shi ba, dan haka ya dauke ta cak ya daura ya a saman cinyar shi, yana me sake wata irin ajiyar zuciya. Kuka ta saka tana me ƙoƙarin sauka a kan cinyar shi.
Kifa kan shi yayi a bayan ta, yayin da ya zura hannun shi cikin rigar ta, cikin kulawa da tattalin irin ta mazan da suka yarda da kan su, ya shiga latsa albarkan jikinta, yana hura mata iskar bakin shi a dokin wuyarta. Bata tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, namijin gaske, sai gashi lokaci guda ta b’ata shiru, da wannan damar ya shiga wasu shafuka na musamman a rayuwar su, ya shiga nuna mata shi din fa ba na yau bane yana son ta daga nan har karshen rayuwarsa. Bata tai shiru, malamin su kamar zai yi Hauka domin baki daya ta samu gyaran jiki na kwana biyu, dan haka da wayo da dabara, ya sake angwancewa a dakin ta, sai da yayi da gaske domin yadda take kuka da niman gayawa duniya yana tare da ita yasa shi toshe mata baki da na shi, haka yasa lokaci guda, ya shidar da ita sai da ya samu nutsuwa sosai kamar ba shi ba, sannan ya kyale ta, yana me daurata a saman kirjinn shi, kawai hakuri yayi dan wallahi da turakar shi ce take yau ba zai kyale ta ba, sai ya shan ye duk wani ruwan da yake jikin ta, amma ba damuwa zai reni soyayyar shi a hankali yadda duk duniya babu me ikon shiga birnin su.

A hankali mai Martaba yake samun kafa gwamnatin shi, ta yadda sai da ya budewa Fulani Aminatu idanun ta, ta zama cikakkiyar mace me hankali da nutsuwa, wanda baki daya masarautan ana mamakin sauyin ta, domin a da can an santa da wasu abubuwan kamar shjga cikin bayi ayi ta hira, toh yanzun babu sai dai su shigo shashinsa su mata hira, a da can an san ta da yawan fara’a toh yanzu babu fara’ar kamar da, sai wani irin kamewa wanda ya haɗa da girman aure da ya shige ta, wannan yana cikin dalilan da yasa Innayoh take kara samun daraja a wurin Mai Martaba Sarki Bello, domin duk wani girma da daraja yana samuwa ne ta sanadin Innayoh, hatta sauran matan gidan sun san da haka kuma ba karamin faduwa bane a gare su, da farko basu zata Innayoh zata iya zamewa Fulani kariya haka yasa duk sharrin su, da fitinar su baya isa gare ta, sai dai ya tsaya a kansu, hatta manyan mata bayi suna matukar shakkar innayoh, kuma ba kome bane dabi’ar mutanen kirki ne matukar zasu rike gaskiya kowa tsoron su yaƙe, ana shakkar su.

Advertisements

A hankali kwanaki yana tafiya, Mai Martaba Sarki Bello ya makalewa Yar Kwailar shi, wato Sarki Bello irin mazan nan ne da ake kira a turance (lover boy) domin a cikin lokaci ƙalilan ya nuna ko a fada Fulani Aminatu ce rabin rayuwar shi.

Ta kai ta kawo ko zaman fada sai da ya wargaza tsarin zaman shi, a madadin ya fito tun safe sai gashi ya dawo da zaman maraici, wannan abun ba karamin dadi yayiwa Galadima ba, sannan yana tashi ba zai kuma sauraron kowa ba sai gobe, daga cikin manyan fadar da haka ya basu haushi, akwai Chiroma, akwai Wanbai, akwai Yarimar Gobir, amma daga Waziri har Galadima garin su gabar domin babu abinda yake basu haushi sai farin ciki.

**
*Masarautar Gombe*
Fulani Kilishi.
“Jakadiya me yake shirin faruwa ne? Jiya na kai ziyara wurin boko ya nuna min Aminatu tana cikin da nutsuwa abinda bana fatan haka ya faru!” Ta fada cikin matsanancin b’acin rai.
Cikin kaskantar da kai Jakadiya Jebu ta ce mata.
“Aikin da aka yi sarki Bello ya karya, abinda nake jin kar muyi wani abu” Jakadiya Jebu ta faɗa.
Shiru Fulani kilishi tayi kafin ta ce mata.
“Ya bani wannan aikin bana son yarinyar ta rayu cikin aminci da salama”
Murmushin mugunta da kaguwa domin jin wani irin tuggu aka shiryawa Fulani Aminatu.
“Uwargijiya ta bani umarni zan cika miki”
“Ki nimo min, budurwa sa’ar Aminatu ki kawo min ita, amma dole ya zama a siritacce.”
“An gama uwargijiya ta, duk abinda kike bukata haka za ayi,” Jakadiya Jebu ta faɗa cikin farin cikin da jin dadi, sannan ta mike ta fita da sauri, bin bayan ta Fulani kilishi tayi da muguwar murmushi, wanda ya kara munana fuskar ta, kasance duhun zuciyar ta ya kara tsammari.

**
*Masarautar Gobir*
Zaune take a takure, kunyar yadda yake shiryawa a gaban ta, yasa ta sunkuyar da kai, takowa yayi cikin wani irin salo, ya dan zauna a saman gadon, sai tattare mayafin da suka rufa da shi yake, taki yarda ta kalle shi.
Zama yayi a gaban ta, ya riko hannunta yana murmushi ya saka a tarin kwanjin da yake kirjin shi, yana murmushi.
“Idan baki kalle ni ba wacece zata kalle ni da soyayya….
End of page 15

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 59

Advertisement BABI NA HAMSIN DA TARA “Sakarai dalla matsa min, kasan waye shi? Idan ya dawo masarautar nan…
KALLABI
Read More

KALLABI 22

Advertisement BABI NA ASHIRIN DA BIYU Zaro idanu Innayoh tayi, cikin tashin hankali tare da rufe bakin ta.…
NAWA BANGAREN
Read More

TARTSATSI 95

Advertisement Page 95*   **********************   Satin Hajiya biyu ta murje sumul k’alau, tamkar bata tab’a ciyo ba,…