Advertisement
BABI NA SHA SHIDA
D’ago fararen idanun ta, tayi tana kallon shi cikin sanyin jiki, a hankali ta zare idanun ta cikin na shi, tana me wasa da mayafin da yake kare mata jikin ta.
A hankali ya zare mayafin albarkatun kirjinta suka bayyana, d’ago kai tayi tana son kallon shi amma yadda yake mata wasu abubuwan yasa kunyar shi kara turnike ta, cikin kulawa ya d’ago habb’atar ta ya ce mata.
“Ko baki son na fita fada ne?” Da sauri ta d’ago kanta tana kallon shi.
“Toh gaya min me kike so?” Ya fada yana sumbatar hannun ta, zuwa yatsun hannunta da suka sha lalle.
“Hmm” ta ce tana girgiza kai, a hankali ya kai kan shi wuyar ta ya sumbata, yarrr tsigar jikin ta ya mike, bata san lokacin da ta kai hannun ta wuyar shi ba.
“Kina son na cigaba ne?”
Da sauri ta dauke hannun ta, tana zare ido.
“Toh me kike so?” Ya kuma tambayar ta, bayan yayi mata rumfa da fadadden kirjin shi, yana me janye mayafin da take rike da shi, sumbatar goshinta ya fara har zuwa kirjinta, jan mayafin yayi ya rufa mata, sannan ya mike yana yar dariya, saka kayan shi yana kallon yadda ta rufe idanunta.
“Baffa’m!”
Bai kalle ta ba, amma hankalin shi yana kanta kacokan.
“Ina jin ki”
“Hmm dama yaushe zan je gombe?” Juyawa yayi ya kura mata ido, shekara kusan hudu bata tab’a tambyar shi ba, yau ta bude baki ta tambaye shi. Yayiwa kan shi adalci kuwa. Samun kan shi yayi da zama yana me kallon ta.
“Kunyi magana da Innayoh ce?” Ya tambaye ta,
Girgiza mishi kai tayi sannan ta ce mishi.
“Allah bamu yi magana da ita ba, nice dai na tambaya da kaina” ta fada mishi haka tana wasa da zanin ta.
“Toh zan duba” d’ago kai tayi tana kallon shi,
“Allah ya baka iko” yadda tai maganar shi kan shi sai da burge shi.
Haka ya gama shiri tsaf sannan ya kalle.
“Zan je na dawo nasame ki ne? Ko zaki koma wurin ki”
“Duk yadda kace haka xan yi”
Murmushin farin ciki yayi sannan ya shafa gefen fuskarta, yace mata.
“Toh ki jirani kin ji”
“Toh, Allah ya dawo da kai lafiya”
Ta fada tana me ƙoƙarin sauka a shimfidar su, cak yayi sama da ita sai da ta ja wani irin numfashi.
“Matsoraciyar yarinya” tura baki tayi tare da cewa.
“Baffa’m kullum daga kace min matsoraciya sai ka ce min raguwa kawai, ko sarauniyar raki me yasa kake gaya min haka?”
Murmushi yayi mata me sauti.
“Ina magana kana min dariya?” Ta fada cikin jin haushi.
Yana shigar da ita ban dakin ya ajiye ta akan wani dutse da ake zama a ban dakin, ya ce.
“Duk ranar da kika daina kuka a shimfidar mu ba zan kuma kiran ki raguwa matsoraciyar yarinya me raki ba” ya fada yana barin ta a ban dakin. Murmushi kwance akan kamilar fuskar shi.
Yana fita ta shiga tura baki gaba tana faɗin.
“Ba dole mutum yayi kuka ba. Abin kullum kamar abinci aka mai da mutum”
**
*Rugar bayan gidan gona*
Kallon Dabbobin Bingel tayi tana jin a ranta matukar ta cigaba da zama a nan rabon ta zai wuce ta, dan haka ta juya tana kallon rugar su, tasan abu me wuya ne wani ya ce zai je masarautar Gobir niman ta,amma a wurinta damar da yafi kowanne girma ta samu na tserewa izuwa ƙaddaran ta.
Tafi Fulani Aminatu kyau, tafi Fulani Aminatu sura me kyau, ta fita cikar halitta, sannan zata iya kome domin bawa Sarki Bello farin ciki, sai dai a lokacin da take wannan nazarin Allah ya gama na shi ikon, bayan ta gama zagaye da kiwon ta, ta koma gida anan ta samu labarin ai Jauro ya bada auren ta ga Dan kanin shi, Jabbu, da mugun gudu ta shiga ɗakinta ta rufe kofar, tana kuka baki daya ta rasa ina zata saka rayuwarta, dan haka sai da ta zauna a wurin har dare ya raba, sannan ta fito daga cikin dakin ta, ko tsoron daren bata yi, ta bar gidan tare da gudun ƙaddara.
A tunanin ta farin cikin da Aminatu take ciki, ita ya dace da samun su ba Aminatu ba. Taya kamar Aminatu zata zama matar Sarki ita kuma da danginta suna bautawa masarautar Gobir. Zata tafi kodan ta samuwa ƙabilar ta abin dogaro ba zasu kare a bayi ba. Wannan shine dalilin da yasa ta ganin itace da damar da Fulani Aminatu ta ke ciki.
**
Da gayya taki motsi dan kar ya ce idanun ta biyu, shi kuwa babban abinda ya shigo da shi dakin daban, amma ganin yadda ta kwanta, kamar wata mage, sannan mayafin da ta rufe jikinta ya fitar mata da asalin kugunta zuwa mazaunin ta, dan ma baya barin ta. Ta huta amma Fulani Aminatu mace ce da ake kira mace, irin mata kalagun nan ne daga sama a cike yake sakamakon murzan da yake samu, haka ma K’ugunta shima yana bayyane da nashi kiran, doguwa ce me wata irin karuwar jiki, irin jikin nan nan da kome kankantar ado yana iya tafiyar da rayuwar wasu. Dan haka ya zauna tare da ɗaukar alkalamin shi da yake rubutun shi na ajami ya fara rubutun labarin su da yadda yake jin kome a kanta, bai tab’a ka manta yin zane ba sai gashi haka kawai yana kallon ta yana zana ta a jikin wani farin fata, ta shi yayi ya fita zuwa waje, yana goye da hannun shi a baya. Da sauri sarkin gida ya iso yana kallon shi ya ce.
“Allah ya baka nasara, dare ya fara rabawa!”
Shiru yayi na wani lokaci, kafin ya ce mishi.
“Ina jin wani abu a raina ne, ina son a niman min allin da ake zane da su daidai wanda zan iya zane a fatar bauna da fatar rakumi. Maza ina jiran ka”
“Allah ya baka nasara an gama” ya fada tare da juyawa da sauri ya bar wurin, har zai shiga sai ya hango wucewar wasu mata, bai wani damu ba. Ya ci-gaba da tsayuwa can sai yake jin babu dad’i kawai ya gwada haurawa saman wurin shan iskar shi, yana zagaye wurin, hango mutanen yayi suna hakka rami, ganin haka yasa shi, sauka da sauri tare da kiran masu tsaron kofar shi, suka nufi wurin. Jakadiya Rama ce da wasu bayi maza.
“Me kuke yi?”
“Shi kenan mun shiga uku” Jakadiya Rama ta fada da sauri tana kallon kasa.
“Me kuke yi a wurin nan?” Shugaban dakarun da suke tsaron kofar mai Martaba ya kuma daka musu tsawa.
“Me kuke yi anan? Ko baku ji ne?”
“Allah ya baka nasara, a yafe mu tsautsayi da asara ya kawo mu binne…” Sai kuma tayi shiru.
“Ku tafi da su” haka suka tisa keyar su, suna tafiya yasa aka tone ramin, aka ciro abinda aka binne, sannan ya koma shashinsa, da abinda aka tono yana mamakin yadda Jakadiya Rama ta zama haka ? Duk akan raba da matsayin da take ne ko kawai amfani aka yi da ita? Wannan ce tambayar da ya kasa amsawa, kuma yaji ran shi ya kuma b’aci dan haka ya wuce sashin Fulani Aminatu, yana isa aka bude mishi kofar, ya shiga da sallama Innayoh ta amsa kishi cikin girmamawa, tana me risina mishi, a sanin ta dai Fulani tana wurin shi, toh ko wani abu ya zo dauka? Ta tambayi kanta.
“Ko akwai wani abu ne a tsakanin ku da Jakadiya Rama ce?”
Ya tambaye ta, yana me kura mata ido, maganar ya zo mata bazata dan haka a dan rude ta ce mishi.
“Mu kuma? Toh me zai hada mu? Sai dai ko akan..”
“Akan me?”
Shiru tayi domin basu tab’a magana irin haka ba, dan haka tayi shiru, sai da ya kuma tambayar ta?
“Akan me?”
“Jakadanci ba!” Ta fada a matukar firgice,
“Toh” ya fada sannan ya juya ya bar sashin.
Koda ya koma, ya samu Sarkin gida da Galadima.
“Lafiya?”
Suka tambaye shi,
“Hmm! Ga shi can ban san me ke damun mutanen gidan nan ba, Rama tana tadda min husuma kuma ina kokarin dauke kai daga gare ta, amma bata lura da haka, shekarun ta da kuma Surikin ta sarkin Yaki nake dubawa, ba wai ban san me nake yi ba, matukar aka samu sunan Fulani Aminatu a cikin wannan abin da suka binne tabbas sai na hukuntatta mafi girma da daukaka a cikin masarautan nan” yana gama fadar haka ya shige abin shi, bai kuma magana ba. Koda ya shiga cikin tsayawa yayi yana kallon Fulani Aminatu da take kwance mayafin rufuwar da yake yana da tsantsi, ya salube daga jikinta ya sauko har kan cikin ta, dukiyar Fulaninta suna tsaye cur-cur, lumshe idanun shi yayi kafin ya kauda kan shi, ya nufi ban daki yayi wanka, ya jima zaune kamar bai da abinda yi, a hankali ya fito ya haura gadon ya kwanta.
Yana sauke ajiyar zuciya, bayan ya janyo ta jikin shi. A hankali ruwan da yake jikin shi ya shiga gangara jikin ta, a matukar sanyayye ya juya yana fuskar ta shi.
“Baffa’m! Meke damun ka naji kirjin ka yana bugawa da sauri da sauri.” Tana maganar ne amma idanun ta a lumshe kamar me magagi. Shafa fuskar ta yayi zuwa wuyar ta, sannan ya saka bakin shi a habb’atar yana tsotsa, shigewa jikin shi tayi sosai tana sauke ajiyar zuciya a kan fuskar shi.
“Baffa’m!”
“Aminatu! Ina jin kamar zan rasa ki ne shi yasa yake bugawa da sauri da sauri” ya fada yana me sumbatar goshinta.
Gyara kwanciyarta tai a jikin shi.
“Babu abinda zai faru” ta fada tana sauke ajiyar zuciya a karo na biyu.
Gyara mata kwanciya yayi a jikin shi, sannan ya lullube ta.
*
Tunda ya shiga ya bar su, suka yi shiru sannan suka nufi wurin Dakarun suka tambaye su, keken faruwa, nan suka gaya musu sannan suka nufi wurin da aka ajiye shirgin, basu yi gangamin tabawa ba, sai dai kuma suna barin cikin gidan sarautar aka samu wani bakin labari. Na mutuwa Jakadiya Rama da bayin nan, kiran sallah farko ya d’aga shi, kan shi na sarawa a hankali ya janye ta a jikin shi ya shiga ban daki yayi wanka da alola. Sannan ya nufi hanyar masallaci. Kus-kus din da dogarai suke yi ne ya ja hankalin shi bayan an idar da sallah ne yake jin labarin mutuwar Jakadiya, idan ran shi yayi dubu sai da ya b’aci. A fusace ya nufi fada cikin abinda bai wuce rabin sa’a ba sai ga dattawan fadar sun Bayyana baki dayan su, basu tab’a ganin b’acin ran shi ba.
“A kira min sankira” shine me tsaron kofar gidan yari.
“Allah ya huci zuciyar zaki, Allah ya baka hakuri da afuwa” ya mike bayan ya gama fada, sannan ya nufi can gidan yarin da yake cikin masarautan.
Bayan kamar minti goma sai gasu, irin manyan mutane nan ne jibgege kamar kututturen bushiyar loko (wato bishiyar kuka🤫) zuwa yayi ya zube.
“Taya aka yi Jakadiya Rama da mutanen da aka kama suka mutu?” Waziri Zakaria ya wurga mishi tambaya?
“Allah ya baka nasara, wallahi jiya bana kofa. Sakamakon mai dakina tana bisa gwiwa” a zafaffe sarki Bello ya kura mishi Idanu,
Sankira waye a kofar jiy” Galadima ya wurga mishi tambaya.
“Allah ya taimaki Galadima, Sanda ne a bakin kofar jiya”
“Toh maza a tawo da shi” inji Waziri,
“Allah ya huci zuciyar ka”
“Hmm! Maraba gasashe kura taga bakin jaki!” Inji Yarima Yakubu.
A yadda Sarki Bello yake ji zai iya sakawa A bawa Yarima Yakubu kashi dan haka ya nuna shi da yatsa, sannan ya mishi alama da ya bar fadan.
Cikin rashin mutunci da ya saba ya bude baki zai magana.
“Kai!!!” Ya daka mishi tsawa, take dogaran fadar masu fushi da fushin wani suka harxuka, kuma daman haka suke jira suke kawai sarki ya d’aga murya su kaddamar maka, an hore su ne da hakan koda dadi ko ba dadi kullum cikin fushi da fushin wani suke….
__________________________________
End of page 16
_Ga bikin zuwa babu zanin daurawa. Eh TOH ina goron sallah na🙄🤔😒😏 idan babu tabbas Ƙarku saka rai da posting gobe sai kun bani happy sallah na_
GIPHY App Key not set. Please check settings