KALLABI 17

KALLABI
KALLABI

Advertisement

BABI NA SHA BAKWAI
*GAISUWARKU CE A WANNAN SHAFIN MASOYAN KALLABI NAGODE SOSAI*

“Fita aka ce maka, me yasa baka da mutunci ne? Maza fita mara hankali daga yau an dakatar da kai shiga harkokin fada!” Inji Waziri Zakaria, shigowar sanda da dogarai, yasa Sarki Bello kura mishi Idanu.
Masu iya magana sun ce mara gaskiya ko a cikin ruwa yake gumi yaƙe, abinda ya faru kenan ga Sanda domin yana ganin shi a gaban sarki Bello ya fashe da kuka.
“Kai yi min rai ja gafarce ni, na tuba wallahi ni na kashe su” lumshe idanu sarki Bello yayi sam bai gamsu da Hujjar Sanda ba, dan haka ya kura mishi Idanu, kafin ya janye daga kallon shi, lashe bakin shi yayi yana kallon yadda yake gumi.
“Kana da iyali?” Ya tambaye shi, kafin ya cigaba da cewa.
“Ku mai da shi, bakin aikin shi a tabbatar da an yi suturar Jakadiya Rama”

Daga haka ya mike tare da barin fadar.
“Ban gane abinda Bello yake nufi ba, shin ya bar Sanda ne?”
Mikawa Galadima yayi sannan ya ce.
“Duk diya nai da ya hana uwatai kwance ai shima ba zai kwana ba” yq kad’e alkyabar shi yayi gaba.
“Shawara ta rage ga me shiga rijiya Imma ya hwada da kai Imma ya dira bisa sawaye nai”

Shiru fadar ya dauka domin maganar gaskiya magana suka gaya musu, amma toh duk wanda zai ji haushin wannan abin toh tabbas yana da hannun cikin abinda ya faru, dan haka sai gashi sun sani shiru babu wanda ya kuma tankawa.
Haka aka tafi Jana’izar Jakadiya Rama. Bayan an gama aka dawo fada, inda aka yi ta kanannun magana aka. Sarki Bello ne yasa a kashe Jakadiya, wanda ba haka bane tsabar sharri ne irin ta mutane.

*
Shiru wurin ya dauka, kafin Galadima ya ce.
“Ina ga an rufe daki da barawo fa, domin duk wanda ya kashe Jakadiya Rama akwai wani abinda ya boye ne, haka kawai ba zai kashe ta ba, dan haka ina da yakinin anyi haka ne dan rufe.”
Murmushin gefen baki Mai Martaba yayi yana kallon littafin hannun shi.
“Eh toh kana da hujja?” Ya tambaye shi.
“Bani da ita, amma yadda aka kashe Jakadiya ya isa ya tabbatar da hujjar da nake da ita, sannan idan ka dubi yadda ake gararanba da zancen dole ya tab’a kowa naka” inji Galadima,
“Bana jin haka kuwa kawai ina nazarin rayuwar al’umma ta ce”
Daga haka ya mike tare da nufar inda tukwanen shuka suke yana me tsayuwa wurin.
“Bana jin akwai wani kwanciyar hankali a cikin gidan nan. Ina son na dauki Aminatu zuwa Gombe tafiyar makwanin ne”
“Allah ya nuna mana” galadima ya fada yana me mikewa yana cewa.

“Amma ba zaka bar masarautar nan yanzun ba sai ka gyara wasu al’amarin, domin”
Juyawa yayi yana kallon shi, hango Fulani Aminatu yayi tana tsaye a bakin kofar shigowa ganin Galadima ya sata mai da takalmin ta zata juya.
“Shigo” ya ce mata, yana kallon ta.
Girgiza kai tayi zata juya tana kara jan mayafinta, dokin rufe fuskar ta.
Juyawa Galadima yayi wanda yayi dai-dai da juyawa ya itama, bisa tsautsayi kawai ta tafi baki daya.
“Aminatuuuuuuu” ya kira sunan ta da karfi wanda idan ba wani ikon Allah ba, kaf masarautan babu wanda bai ji kiran ba.
Da mugun gudu, ya nufi kofar ya samu ta gungura can sai kokarin tashi take amma ta kasa, da sauri ya isa tare da d’aga ta yana kallon yadda goshinta da hancin ta da suke zubda jini.
“Baffa’m! Ba wani ciwo bane fa” ta fada a wahale, saka farar alkyabbar shi yayi yana goge mata hanci, kafin ya dauke ta, dan har dakaru sun fara zuwa, ya nufi tarakar shi da ita. Wannan dalilin ya sa kowa ya kama gaban shi.
Ajiye ta yayi a bakin gado yana kallon yadda take lumshe idanun ta, tabbas yasan tana da hakuri da juriya, bai zata na yau zai zarce na kullum ba, dan haka ya shafa gefen fuskar ta yana kallon yadda take ajiyar zuciya.
“Sannun kin ji”
“Naji tsoro sosai” mikewa yayi ya nufi ban daki ya dauko ruwa a wani tassa, sannan ya zo ya wanke mata fuska da hanci, kafin ya zuba mata ido.

“Me kika zo yi a wurin?” Hawayen da take dannewa ne, ya shiga saukowa bakinta yana rawa ta ce mishi.
“Me yasa aka kashe Jakadiya?” D’ago kai yayi ya kura mata ido, kafin ya mike tare da nufar ban daki ya zubda ruwan sannan ya fito ya nime wuri ya zauna. Kallonta yayi na wani lokaci kafin ya ce Mata.
“Waye ya turo ki?”
Yadda yayi maganar babu wasa ko sassauci, yasa ta d’ago kai ta ce mishi.
“Babu”

“Toh daga yau kar na kuma jin kin shiga harkokin masarautar nan kin ji?” Hawaye sharrr yake sauka ta ce mishi.
“Naji” kallon kofar dakin yayi tare da cewa.
“Nasan Innayoh tana jiran ki je ki” mikewa tayi, zata fara tafiya amma ina ta koma ta zauna, tare da rike kafarta. Kuka ne ya kwace mata tana yarfe hannu.
Kai hannun shi yayi samar kafarta, yaga yadda wuyar kafar tayi fushi.
A hankali ya tashi ya fara dauko kayan aiki da kan shi ya dauko wani abu ya saka mata a bakin ta, sannan ya koma wurin kafar ya ja, wani irin ihu ta sake amma sabida abin bakinta ya hana a ji ihun, tana kuka tana kome ya ja kafar sai da ya cire gocewar, sannan ya mike yana me daukar ta cak ya nufi sashin ta da ita, akan idanun Ajuji da ta zo wucewa ta hango su, kura musu ido tayi babu laifi sai dai cutar Hassada ta hanata hango iyakar su, gani take kamar shigowar Fulani Aminatu gidan zata iya yaɗuwa tayi yabanyya.
Kwafa tayi tare da barin wurin da bayin ta.
**
Bayan wasu makwanin kamar biyar Sarki Bello ya shirya tafiya zuwa garin gombe, tare da Innayoh.
Yadda Fulani Aminatu take murna ba zaka taba tsammanin zata yi shi ba,ko ya aka yi dai dole tayi daukin zuwa ganin gida, dan haka aka shirya dakarun na musamman tun daga masarautan har zuwa wasu manyan masarautu kama daga na kano, Sokoto, Hadeja, Bauchi har zuwa gombe. An shirya tsaf ranar Laraba suka bar masarautan inda ya barwa Galadima ajiyar garin shi baki daya, suna barin masarautan Bingel tana shiga masarautan. Dan haka aka samu saba’ni a tsakanin su basu ga juna ba ma,

**
Tun daga lokacin da ta shiga masarautan ta fahimci ashe kuskuren ƙaddara ce ta barota da gida, domin masarautan cike yake da mugunta da zalince, musamman da aka fahimci sarki Bello baya kasar, sannan shi kan shi Galadima bai san meke tafiya ba, wani abinda yasa aka kasa cimma Galadima sabida shima takadarirran mutum ne, Hatsabibi ne na gayawa mutanen gari, jan wuya ne da ya kware a rashin mutunci, kuma abinda ya sa yake biye halayyar shi amincin da ke tsakanin shi da sarki Bello, shi yasa bai cika shiga damuwan kowa ba, da kuma Allah ya sa aka wurge shi da rikon kwarya, sai ya fidda hakikanin gaskiyar shi, d’aga musu kafa da Sarki Bello yake yi shi ya ce bai iya ji ba, koda Yarima Yakubu yaso mishi iskanci rufe idanu yayi yasa aka bashi kashi, ya kuma tabbatar mishi an haramta mishi shiga harkokin masarautar Gobir har abada, idan kuma ya sake ya shiga toh ya kwana da sanin sai ya sheka lahira.

A inda Bingel take, shashin Ajuji aka kaita a nan kuwa ganima Yakubu yake diban mata da yan mata babu ruwan shi, koda Galadima yaji labarin haka ran shi ya b’aci dan haka ya saka aka kamo mishi ya kubu yasa Sarkin bulala ya zane shi, kuma ya saka aka raba bayin a cikin wadanda aka raba har da Bingel inda aka kai ta gidan Chiroma.
**
A cikin kwanaki biyar da suka bar masarautan yana cikin kwanakin da Aminatu ba zata tab’a mantawa ba, domin ya ajiye sarauta bawan Allah nan ya shiga bayyana kaunar shi, kamar zai cinye ta, haka kawai ma a ranar na shida da barin su masarautan ya ce a yada zango, bawan Allah nan tunda ya fito yayi Sallah ya koma dakin ya shiga turmushe yar mutane, Dakyar ya fito sallah magariba da isha, ai kuwa yana komawa ya shiga dasa bama-baman kaunar shi, itama mara kunya ta saba da halin shi, haka take amsar shi a duk lokacin da ya bukaci haka, wani irin mahaukaciyar kauna sukewa juna kamar zasu cinye kan su, har suka isa masarautan kano, a nan ma sai da Sarkin Kano yayi ta Mishi hannun ka me sanda, kafin ya kyale yar mutane.

Advertisements

Haka suka yi ta sauka a masarautu daban-daban har Suka iso masarautan Bauchi. Kwanan su biyar a Bauchi, sannan suka nufi masarautan gombe, sun bar bauchi sosai har sun isa dumduma, suka yi karo da gawarwakin mutane, kuma da alamu fatake ne, dan haka basu yi yunkurin wani abu ba, sai da suka gaya mishi, da kan shi ya fito yana kallon su, daya bayan daya. Kafin ya shiga juya da sauri dake tsakanin keken dokin su da inda suke akwai tazara, hango wani gawurtaccen zaki yayi ya nufi keken dokin su….
________________________________
End of page 17

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 41

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA DAYA. A wannan harin sai da yayi dogon jinya ganin haka yasa bingel…
Read More

TARTSATSI 86

Advertisement *Page 86*   **********************   Umma da Su Umaima, suna sashen Aunty amarya tareda su Gwaggo, da…
KALLABI
Read More

KALLABI 3

Advertisement *<Babi Na Uku>* ~Masu azancin harshe sukan ce dakan d’aka shikar d’aka….masana harshe kuwa suka karasa azancin…