KALLABI 18

KALLABI
KALLABI

Advertisement

BABI NA SHA TAKWAS
“Kai!!!” Ya fada da ƙarfi amma ina har zakin nan ya samu damar bangaje keken dawakan da suka gan shi a fusace suka tsinke domin tsira da rayuwar su.
Kamar wani aikakke domin burin shi bai wuce yayi ta wasan tamola da keken ba, har ya kai ga ya fasa cikin ya zakulo bil adam din da yake cikin keken ba, sai dai kash! Ihun sarki Bello ya tsayar mishi da kome, a fusace ya juya ga sarki Bello da ya ke tunkarar shi gadan-gadan, ohoho faduwar gaba asarar ragon maza, cikin tsananin fushi da fusata, sarki Bello ya amshi wani ya tare da ambaton Allah ya wurgawa wannan zakin, amma ya kauce. Tabbas abin ba karamin al’amari bane dan haka kamar waɗanda aka tinxira su, suka fuskanci juna da mugun gudu, sarki Bello ya rungume zakin suka fada can kusan rafin dumduma, burin Zakin ya fasa kan sarki Bello. Shi kuma sarki Bello burin shi su fada cikin ruwan, gashi zakin ya jima shi ciwo da faratun shi, (wato kumbar shi) jini yake zuba Sosai, a can kuwa dakarun sun yi nasarar ciro Fulani Aminatu, amma ta jigata sosai, domin ta bugu ta ko ina gyara mayafinta tayi sannan ta ce musu.
“Ina Baffa’m?”
Gurnanin zakin da suka ji yasata, mikewa ta nufi wurin suna tare ta ina ta karta a guje, har bakin ruwan suma dakarun suka iso, lokacin baka ganin kome sai jini da ya bata saman ruwan, wani irin dafe kirjin ta,ta fasa wani irin kuka tare sa kiran shi.
“Baffa’m!!!” Zata shiga cikin ruwan.
Innayoh da suka samu damar isowa ta kamota,
“Don Allah ki sake ni, Wayyo Allah na Baffa’m Wayyo kar ka tafi ka bar ni, don Allah ka fito mu tafi” ta kuma fada da ƙarfi zata shiga cikin ruwan. Wani juyi suka yi a cikin ruwan. Zakin yana wani irin kuka na niman agaji. Suka kuma nutsewa, ba a kuma jin karar su ba, da gudu Fulani ta kwace, ta fada cikin ruwan tana niman shi, ihu take tana shawagi a cikin ruwan, kamar an ce ta juya ta hango gawan zakin, a saman ruwa.
“Baffa’m!!” Ta fada da ƙarfi tana kuka, a hankali ya sako a hannun shi ta cikin ruwan ya ja kafarta ta fada cikin ruwan ji kake tsudummmmm.
“Fulani Aminatu!!!” Suka fada da karfi, d’ago hannun yayi daga cikin ruwan yana musu alamar su tafi kawai.
Juyawa kowa yayi simi-simi. Koda ta nutse cikin ruwan kokarin tashi take ya sakalo hannun shi zuwa kugun ta, yana murmushi a hankali ya janyo ta har wurin da kafarta ba zai iya kaiwa ba, ya d’ago ta yana kallon yadda take shaƙar iska, sabida ya d’ago kanta saman ruwan.
“Kin zata na mutu ne?” Ai kuwa ta fashe da kuka tare da rungume shi.
“Baffa’m naji tsoro”
Sumbatar bakinta yayi yana cewa.
“Ni ma naji tsoro amma ban zata idan na gan shi zai miki wani abu xan daina jin tsoron shi ba, sai kawai naga Sabida yar kwailata nayi fada da zaki” tura baki tayi tana faɗin.
“Ni ba kwaila bace” ta fada tana kokarin kwace kanta.
“Toh Fulani karki manta nan ba zaki iya tafiya ba sai dai ki nutse dan haka a jira na fito dake ko?” Kwalla ne ya cika mata Idanu. Baki daya ya gama rena mata hankali, zata tambayi Innayoh taji me yasa yake kiranta da kwaila? Komawa tayi ta kifa kanta kirjin shi, sai yanzu ma take jin tsoron biyo shi cikin ruwan da tayi.
“Kayi hakuri ka fidda ni waje!” Ta fada kamar zata fasa kuka.
“Hmmmm” ya fada cikin jin radadi sannan ya ware idanu shi akan ta.
“Sai kin yarda ke kwaila ce” ai kuwa sai gashi ta harxuka, halin Fulani ya motsa kawai ta kwace daga jikin shi ta fara kokarin fitowa waje, ai kuwa yana sane ya kyale ta, ganin zata nutsu yayi maza ya biyo ta, tare da ɗaukar ta a kadadar shi har waje, ya shimfida ta a yashi, sannan ya zauna yana saukd ajiyar zuciya.
Kallon rigar ta yayi yadda ya kwanta a jikin ta, sakamakon jikewar da tayi.
“Lallai kwaila ta fara girma naga kirjin ba laifi” da sauri ta juya mishi baya tana tura baki, dan haushi ma tashi tayi tana kokarin barin wurin ya kamo hannunta, ta koma kan shi. Rungume ta yayi sannan ya sumbaci hancin ta, zuwa bakin ta yana kallon yadda take matsar kwalla.
Mikewa yayi ya ce mata ” karki yarda ki fito a bayana har mu isa wurin keken mu”
“Toh” ta fada, a hankali suke tafiya tana bayan shi yana gabanta, har suka isa wurin keken su, tantin da aka kafa ya nufa tana bin bayan shi, suna shiga ta zube a saman Kilishin da aka shimfida.
“Na gaji”
“Sannun yar kwaila” tura baki tayi taki amsa mishi, yana sane ya fadi haka domin ya kara bata haushi, har ya sauya kayan shi, ya duba kayan ta da yake ajiye a wurin ya fita, sannan yasa aka tura mata Innayoh.
Ai kuwa Innayoh na shiga ta rushe da kuka, zaka rantse ya mata wani abu ne kafin ya fita nan kuwa kalmar kwaila ce take yakushinta.
“Kiyi hakuri tunda babu abinda ya faru da shi” cewar Innayoh sabida a tunanin ta ai sabida abinda ya faru ne, ai kuwa tura baki tayi ta fara jan dan hancin ta.
“Innayoh wai me yasa yake kirana kwaila? Don Allah gaya min kullum daga ya ce min kwaila sai ya ce min matsoraciyar yarinya ko ya ce min raguwa” aikuwa take Innayoh ta d’ago bakin zaren, dan haka ta toushe kanta tana murmushi.
“Idan ya kuma ce miki kwaila, toh da gaske ke Kwailar ce, karki kuma mishi kuka idan ya bukace ki kin ji ko?”
“Toh naji, amma Innayoh dole ne sai an yi wani abu, wallahi ni baya na ne ma yake min ciwo.” Ta fada tana juya mata baya, fita Innayoh tayi ta sa aka nimo hararabi, a take aka tafasa mata shi, sannan aka shiga da shi ta sakata dole ta sha, ita kuma ta shiga rarrashinta, tana gaya mata wasu manyan manyan sirrin mowar mace, tunda ya ce mata kwaila ta yarda a tafi a haka sai ta mishi irin aikin kwailayen. Aikuwa haka ce ta faru, bayan Innayoh ta fita tayi Sallah, ta ci abinci kaɗan. Sannan ta kwanta barci ya kwashe ta.
….
A waje kuwa kwashe gawarwakin mutane aka yi aka binne su, sannan aka shiga gyara keken dokin su.
“Allah ya baka nasara dole sai mun kwana asuban fari mu bar nan”
Mikewa yayi yana kallon su, sannan ya ce.
“Kuyi duk abinda ya dace” sannan ya juya zuwa tantin su, yana shiga ya same ta akwance tana barci.
Shafa wuyar ta yayi zuwa fuskar ta, aikuwa tayi wani munafikin mika, duk rabin cinyoyin ta suka bayyana, kura mata ido yayi yana kallon ikon Allah, yarinyar nan ta ci uwar kwaila sai dai uwar Kwaila. Garin ya gyara mata kwanciyar ta, ta wani juyi ta koma saman shi. Hàdiye yawu yayi cikin nutsuwa yana kallon ta, a hankali ya sauke ta, tare da kamo kafarta zai gyara mata zaman mayafin, ta wani bararraje kamar wacce ake gaya mata. Wani dauke wuta yayi kunamar shi da zuciyar shi suna wani irin bugawa lokaci guda. Gashi kamar dole an ce mishi ya gyara mata, sai kokarin ganin ya gyara mata kwanciya yake, aikuwa ya ɗan mike tare da mata rumfa zai ja mata bargo, kawai takai kyakyawar kafarta ta zungure mishi. Ya liman din shi, innalillahi wa’inna alaihil raji’un, kai idan bai yi karya ba har da yakuso mishi fatar limamiyar shi tayi, kura mata ido yayi yarinyar nan ta gama da shi saura lokaci kaɗan ayi sallah magariba, zata saka shi yayi wanka da almurin fari. Kasa hakuri yayi ya shiga lugwaigwaita yar mutane, tun yana kokarin yayi kaɗan bayan isha a sunkuya na gasken sai gashi, ya zurme baki daya ya shiga gurzanta kamar Allah ya aiko shi. Babu abinda ya bashi mamaki yadda ta lumshe idanun ta, tare da k’amk’ame shi babu kuka ko ture shi, haka ya cigaba da haketa, Allah ya gani bai tab’a marmarin mace tun samartakar shi, wallahi idan ya haye saman Aminatu gani yake kamar alfarma yake mata idan ya kyale ta, amma tabbas bai da juriyan kyale ta domin wallahi ji yake kamar ya dauke ta yayi ta yawo da ita. Yasan darajar ta, kuma yasan muhimmancin ta, baya jin akwai abinda zai fita daraja a rayuwar shi. Dan haka har aka yi sallah magariba da Isha yana daki yana bulale yar Kwailar shi, yarinyar bata da wayo sam ta haye keken beran Innayoh ta zauna yana gurje ta.
Kallon fuskar ta yayi da yake dab da fara kuka wiwi. Kai bakin shi yayi saman nata domin yana son lallai ya rabu da ita amma yan kukan da take yi da ture ture yau bata yi ba, kuma shine mafi girman a rayuwar auren shi, yana son yaga tana kukan domin jin shi.yake kuzarin shi na karuwa. Kallon fuskar ta yayi kamar zai zubda kwalla ya sake bakin ta ya ce mata.
“Minani ba zaki min kukan bane ina son kukan ki” a hankali ta bude idanun ta, ta kura mishi ido kafin ta kuma lumshe idanun ta.
Cikin wani irin yanayi yake tafiyar da ita, bai san lokacin da ya shiga sumbatar wuyar ta, yadda ya rikita mata lissafi yasa ta sake wani marayan kuka dan har lokacin ba zata ce ga yadda take ji akan rayuwar auren ta ba, sai dai yasan duk yadda yayi da ita tana jin kamar karta rabu da rayuwar shi. Kuma shine namijin da ya koya mata abubuwa dayawa, dan haka ta fara wani irin shashekar kuka, me mugun tafiya da hankali. Cikin salon da bata san ya zame mata jiki ba, sai gashi tana mishi kukan tare da wasu irin fisge-fisge..
Shi kan shi bai san cewa ya kunce mata ba, sai da yaji muryanta na shirin tashi sama, kawai ya tushe ta baki daya.
Bayan wani lokaci ya koma gefe yana kallon ta, yadda take sauke numfashi. Tausayi ta bashi wallahi bai san yadda aka yi ya haukace akan ta ba, kome nata zam-zam. Janyo ta tayi ta kara rungume ta, hawaye ba zuba daga idanun shi, ya sani soyayyar Aminatu daga Allah ne, bai san wacce irin ƙaddara ce a tsakanin su ba, amma yasan Galadima ba zai cutar da su ba. Kuma tunda ya gaya mishi kome akan ta yake kaf-kaf da ita, a yanzun yana jin matukar ya rasa Minani a rayuwar shi tabbas zai kasance mutum me matuƙar asarar mata amfani ita din rabin rayuwar shi ne, juyawa tayi tana kallon yadda kwalla yake zuba daga idanun shi.
“Baffa’m kuka kake ne?…
___________________”
End of page 18
Barka da warhaka ya hakuri da halina 😂🤣🚶🏾♀️free book kenan a amsa da hakuri 🤌🏽
#Mai_Dambu

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 22

Advertisement 22   Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 17

Advertisement 17 Washegarin da akayi hutu shine ranar birthday na, mun fito don na kai su yusseer islamiyya,daga…
KALLABI
Read More

KALLABI 14

Advertisement *<Babi Na sha hudu>* *Rundunar dakarun kasar Sahil* Yada zango suka yi aka shiga kafa tanti masu…