KALLABI 19

KALLABI
KALLABI

Advertisement

BABI NA SHA TARA
*WANNAN PAGEN NA KUNE MUTANEN BAFFA’M DA YAR KWAILAR SHI MUSAMMAN AUNTY SA’A WAI AN SAUYA MATA NI 🤣😂🤌🏽 TOH A DAWO DA NI KAWAI*

Janyo ta yayi jikin shi, yana shafa bayan ta, yana jin wani sabon kaunarta yana huda duk wani kusurwa na jikin shi, sumbatar goshinta yayi yana faɗin.
“Ba kuka nake ma, ciwo na nafama” kifa kanta tayi a kirjin shi ta fara sauke ajiyar zuciya, samun kan shi yayi da kallonta musamman yadda zufa da gashin kanta ya lullube mata fuska.
“Kin gaji ko?” Ya tambaye ta, bayan ya mike daga kwanciyar, ya dauki mayafi ya rufa mata, a hankali yayi ta wasa da gashin ta, da sauri ya nufi dan makewayin da yake cikin tantin. Ya zuba ruwa yayi wanka da alola sannan ya fito ya taimaka mata itama tayi wanka da alola, shi ya jasu sallah. Suna idarwa ya fita jim kadan sai ga Innayoh da kayan abinci har da y’ay’an itacce, gaushi da ya’yan Audiga. A take ta saka ta yin tsuguno akan gaushin da ya’yan Audiga, yana gyara mace sosai, dan haka tana gamawa ta sata a gaba sai da ta ci abinci sosai. Sannan ta bar tantin, shima ya shigo ya zauna ya fara cikin abincin. Yana kallon yadda take ta zuba gyagyadi, dan haka ya gyara mata kwanciya ya shiga harkan gaban shi. A cikin yanayin da yake, kamar ya koma gida jikin shi na bashi wani abu na daban, dan haka ya tattaro duk wani abinda ya iya domin kare lafiyarta sai da yayi, sannan ya cigaba da wasa da gashin ta, kafin ya kwanta.

….
A hankali take ganin kamar ana wani sha’ani ko biki ne, sai dai kuma bai yi kama da bikin ba, domin dai wata mata ta gani lullube da mayafi, a gefen Baffa’m. Takawa tayi zata tab’a matar aka ture ta ta fadi.
D’ago kai tayi, ta ga Baffa’m. Kafin ta mike ya riko hannunta.
Bude idanun tayi ta gan ta cikin jikin shi, tura kanta tayi cikin murmushi zuciyar ta yana bugawa.
Ganin shi a tare da ita yasa taji wani irin nutsuwa da barci me dadi ya dauke ta.
*
Washi gari
Da wuri suka isa gombe, kuma Alhamdulillahi sun samu karba na musamman, domin a shashin Fulani Shatu aka sauke ta, anan suka zauna ana yi ta hada musu abinci kamar me,
Kiran Innayoh yasa aka yi. Cikin girmamawa ta zube a gaban shi.
“Innayoh ki bata wannan ta tabbatar ta ci a cikin abincin.”
“Toh Allah ya baka nasara” ta amshi kullin ta tafi da shi, ta bawa Fulani Aminatu ta gaya mata yadda zata yi amfani da shi.
Bata samu ganawa da mahaifin ta ba, sai washi gari. Tare da Baffanta, suka zauna a babban Zauren Mahaifinta.
“Alhamdulillahi Masha Allah, kin min abunda kowa ya kasa min, kin zauna da mijin ki lafiya. Haka ba ramin dadi yayi min ba, kiyi hakuri da halin da zaki shiga na rayuwa wata rana sai labari”
Gyada kai tayi. Haka suka yi ta mata nasiha. Har bayan wani lokaci sannan ta dawo shashin Fulani Shatu.
A wannan kwanakin, da kan shi Sarki Bello yayi ta bin wasu sha’ani na masarautan. Kafin ya gano asalin abinda yasa ake bibiyar matar shi. Da kan shi ya samu Surukin shi ya gaya mishi abinda ya ke hangowa. Ya kuma ce mishi.
“Idan Kilishi bata fita sabgar Aminatu ba, ba makawa zan dawo mata da kaidinta, kar ta kuma wannan yunkurin.”
“Insha Allah babu abinda zai faru”

A bangaren Kilishi kuwa tayi tayi aikin ta yayi nasara amma ina babu abinda ya faru, dan haka ta saka a ran ta sai tayi amfani da karfin ta, dake bata da imani, tana cikin wannan yanayin ta aka aiko mata yarta da za ayi bikin shekara me zuwa ta fad’o daga sama ta mutu, shi ne abinda ta shiryawa Aminatu.
Kuma dama Sarki Bello ya fada ta kiyayye shi, Mahaifin Aminatu bai gaya mata ba, sai gashi ana cikin kokarin sururar Yarinyar daya yar ta ma aka same ta ta mike kafin kace me sai gawa. Wannan tashin hankalin ba karamin haukatatta yayi ba domin bata tab’a tsammanin haka ba lokaci guda.

Sai da aka yi addu’ar Bakwai sannan Sarki Bello ya dauki matar shi suka bar masarautan zasu koma gida.
**
*MAYAKAN SAHIL*
“Shugaban rundunar saura wata biyu mu isa masarautar”
“Tabbas Lati nasara bata gare mu dan haka zamu tura budadiyar wasika ga Sarkin su, idan ya amshi abinda ake bukata toh idan bai amsa ba, zamu shiga cikin masarautan mu dauko ta”
“Ya shugabana kana ganin haka babu matsala?”
“Babu dan haka a cigaba da tafiya” haka suka yi ta ratsa tsakanin manyan duwatsu har suka yi tafiya me nisan gaske.
**
*Bayan sati biyu*
“Baffa’m! Amma mun kusan isa gida ko?”
Ta tambaye shi.
“Insha Allah nan da mako guda zamu isa lafiya” ya bata amsa, haka tafiyar ta kasance wannan karon yada zango kawai ake a huta, qashin gari a wuce. Amma bai hana mutumin nan turmushe yar kwailar shi ba, har addu’oi tayi tayi Allah ya kawo mata bakon ta, ta huta da jarabar shi.
Bakon shima kamar yasan nufin ta yaki zuwa.
Bayan wasu kwanaki suka isa gida lafiya, tun daga bakin masarautan ya fahimci galadima ya kintsa kowani dan Banza, a ran shi ya ji haka ma yayi mishi. Bai saurari kowa ba, sai da ya huta gajiya na tsawon kwanaki biyar sannan ya koma fada, aka cigaba da mulki inda shima yayi ƙoƙarin kamanta halin Galadima, kuma Alhamdulillahi sun tattauna sosai akan abinda ya shafe su har akan Aminatu.
Kuma ta bashi kwarin gwiwa sosai akanta. Shi yasa yake mugun kaunar galadima domin ya mishi abinda bai zata ba, kuma yana cikin mutanen da yakeke girmamawa.
*
A duk lokacin da ƙaddara ta Kwankwaso maka kofa babu yadda zaka yi da ita dole ka bude mata, haka ce ga Aminatu domin ana cikin wannan yanayin musamman ita da sarki Bello aka fara tsiro da wani irin Gulma akan rashin haihuwar ta, wannan shine matsalar da dukkan su biyu suka fara fuskanta, maganar rashin haihuwa har cikin fada, kuma dake an shirya kome a nutse sai gashi sarki Bello ya fara fuskarta matsin lamba daga Wanbai, Sa’i, da sauran manyan fadar musamman da suka kasance kusan iyayen shi ne da baffannin shi, a lokacin Galadima ya tafi lardin sokoto. Mai Martaba sai da ta kai ya kasa barci balle ya samu natsuwa da Aminatu,.itama ta rasa kuzarin ta, musamman da ta ga halin da yake ciki, a wannan lokacin Innayoh ta amsa uwa domin taki yarda ta bar Aminatu ita ɗaya, a duk lokacin d ta zauna tana nazarin halin da take ciki zama take ta dauke mata tunani.
Ana cikin wannan lamari sai ga sako daga shugaban Rundunar Sahil ya turo da sakon lallai sarki Bello ya turo mishi da Fulani Aminatu zai kai ta ga Sarkin su.
Dama an gama fusata shi, da maganar haihuwa yana jin haka ya ce.
“Ka je ka gaya mishi ko baiwar masarautar Gobir ba zata isa gare su ba, balle Matar da nake tsannanin Kauna idan bai tattara haukar shi sun bar min kasata ba, idan na fito sai na sare kan shi na ajiyewa Ungulu suyi watanda da shi”
Da sauri dan aiken ya juya.
“Amma ina ga tunda haihuwa ce bata yi me zai hana ka bas….”
“Nasiru Chiroma!!! Sai na yanke harshen ka idan ka kuma furta wani kalma ga Minani!” Ya fada da ƙarfi sai da fadar ta amsa, wannan yanayin ya tsorata su. Baki daya aka rasa me magana dan haka suka taru a wuri guda. Cikin fushi ya koma cikin gidan. Yana shiga cikin gidan, ta samu labarin yana wurin shan iskar shi. A hankali ta nufi wurin da kayan marmari. Yana tsaye ta shiga da sallama.
Bai amsa ba, sai ma huci da yake ta faman yi, wani irin iska ake lokacin guda ya haɗa da wani irin bakin haɗari, da sauri ya juya zai sauka yayi karo da ita.
“Ina ga kamar akwai abinda kuke boye min ko?” Ta fada mishi.
“Kin ga ki tafi zan zo”
Murmushi me ciwo tayi tare da cewa.
“Yau kwana huɗu kenan, ina son ganin ka babu halin ganin ka, na tafi turakar ka kaucewa Sarkin gida na koma zaka zo, wai akan haihuwa ce ake min haka? Ni fa ba dabba bace. Sannan Ni ba yarinya bace, kai ka girma da tunanina haka. Ba zan hana ka yadda kake so ba, amma idan nice bana Haihuwa me zai hana ka kara wata matar….”

“Keeee” ya daka mata tsawa, wanda ya firgita da ita, murmushin takaici tayi sannan ta ce mishi.
“Idan ba haihuwa kake so ba me yasa kake korata daga ganin ka?” Takaici yasa shi rab’a gefen ta ya nime wucewa. Rike hannun shi tayi.
“Yau ce rana ta farko da ka min haka, amma na maka uzuri domin nasan baka kome sai da dalili. Karka manta ka koyar min da kome ne da kanka ni dalibar ka ce, sannan wannan shine yanayi na farko da na fara fuskarta rayuwa ta a haka. Duk laifin da xan yi maka Karka juya min baya domin shine abu mafi raunin da zai kashe ni” wani irin juyawa yayi ya shiga sumbatar bakin ta. Ya Allah Ya zai yi da kaunar Yarinyar nan. Abinda ake shirin ya aikata shine katangar farko da xa a mishi da ita. Wani irin kaunarta yake ji me tattare da damuwa. Aikuwa iskar da ake ya sauko da ruwa me karfi. Yana zuba akan su. Domin iska ya yaye rumfar da yake wurin. A hankali ya janye bakin shi daga nata, sannan ya rungume ta.
“Kiyi hakuri da duk abinda zan miki” girgiza kai tayi tana Murmushi hawaye na zuba mata.
“Ba zan tab’a mantawa da haka ba” rungume ta yayi. Ita tana kuka shi kuma yana na zuci.
*
Lokacin da me sako ya dawo da labarin abinda sarki Bello ya ce ran shi ya B’aci dan haka ya tura sako kuma Masarautan ya basu wa’adin kwanaki uku su turo Fulani Aminatu ko kuma ya shigo ya sare kan sarki Bello ya tafi da ita.

Haka aka kuma kai sakon, sarki Bello bai ce uffan ba, domin yana bukatar Galadima. Abin sai ya hadu mishi kome yayi tsanani, dan haka ya tura Sarkin gida cikin sirri ya lardin sokoto, domin ya taso Galadima. Abu goma da ashirin shi a can bai da sukuni domin mutanen fadar sun Bayyana mishi bukatar su, ba zai cigaba da zama mace babu albarka ba, tunda ba zai yi aure ba dole ya nime kunyaga ko kwarkwarah, kuma yadda suka kawo hujjar su, sai ya kasa magana.
“Matukar aka baka auren mace ba zaka mata adalci ba, amma idan aka baka kunyaga ko kwarkwarah dole zaka sauke nauyin ta domin zata fi Fulani Aminatu baka lokacin ta, dan haka a matsayin mu na manyan fada mun yanke shawarar baka kwarkwarori daga kowacce gida, idan kuma kana ganin abinda muka yi ba daidai bane toh ka basu Aminatu domin kowa yasan kasar Sahil matsafiyar kasa ce da suka yi imani da tsafi yaki da su kamar yaki ne da rundunar bakaken ifiritai, dan haka ka basu ita ai shima Sarki Shehu Usmanu yasan cewa Yar shi tana da abinda Arkhan yake nima suka baka auren ta me yasa bai rike yar shi ba? Me yasa bai bata tsaro ba, matukar zaka shiga kasada saboda ita dole ka amshi batun mu ko ka janye daga shiga yakin ka bashi ita su tafi….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 46

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA SHIDA BARKA DA WUNIN JUMMA’A 🕌🕋 “Allah ya baka nasara ana kallon ka…
Read More

TARTSATSI 15

Advertisement Page 15* ******************** Asam’u tace “To sarakan hankali, ku sakeni inje ingaida umma” Salma tace “Abu dole…
Read More

TARTSATSI 66

Advertisement   *Page 66*   *********************   Basma Amarya da angonta Dr Sadik kam sunyi kwanan farinciki da…