Advertisement
<Babi Na Biyu>
Masu iya magana kan ce wanda ya riga ka kwana zai rigaka tashi haka.. inji Malam BAHAUSHE.
Abinda ya faru kuwa duk yadda Sarki Bello yaso had’a kan Yayan Wan shi abun ya ci tura musamman yadda Yakubu yake kara baudewa,yana kara fusata ga kuma yadda yake illa a cikin katangar bayi yasa Sarki Bello ya taka har wurin Ajuji.
Tunda ana gaya mata sarki yana iso gare ta, ta gyara zaman alkyabarta ta, sannan tayiwa Jakadiya Rama magana da cewa.
“Jakadiya zai iya shigowa”
Duk da bata sannan me ya kawo Mai Martaba sarki Bello ba, amma tayi imanin cewa ya kara mata daraja a cikin gidan duk da ba a bawa danta mukami ba, amma tabbas haka ya nunawa Mutanen cikin masarautan cewa ai tana da kima.
Cikin sallama ya shiga babban zauren ta, wanda yake dauke da bayi mata suke mata hidima. Zubewa duka yi tare da gaishe shi. Jakadiya ta amsa.
“Mai Martaba ya amsa, kuma yana son magana da uwar Dakin ku zaku iya fita”
Fita suka shiga yi daya bayan daya, dakin ya rage sai Jakadiya.
“Me ke tafe da Sarki Bello?”
Murmushi yayi cikin dattako, sannan ya ce mata.
“Nazo ne domin kece kika fi dacewa ki gargadi Yakubu. Barnan shi a cikin masarautar nan tayi yawa. Idan ya cigaba da haka abun ba zai mana dadi ba? Kin san da naga ake gane zurfin ruwa, kuma idan har akwai sa’a toh tafiyar ba zata zama mara amfani ba”
Ya cire mulki yayi mata magana ba fahimtar juna. Amma sai bata ce kome ba, asalima tayi na’am da yadda yazo mata domin tasan ba karamin al’amari bane a Kore Yakubu daga masarautar.
Dan haka bayan tafiyar shi, ta saka aka kira mata Yakubu da yake dakin shi yana masha’a da wasu bayi mata. Sai da ya gama abinda yake sannan ya saka aka fitar da baiwar. Yayi wanka ta shiga cikin gidan sarautar. Dakin Mahaifiyar shi ya nufa. Sannan ya zauna yana kallon kayan marmarin da aka ajiye mishi. Tab’awa yayi tare da cewa.
“Iya kiran me kika min?” Shiru tayi kafin ga fara cewa.
“A yayinda Duniya ta juyawa fatake baya, zai yi wuya ya fahimci inda ya dosa, ba zan tsawaita nusar da kai zafin da yake cinkushe cikin sahara ba, sai dalilin me matukar muhimmanci ya iske ka.”
“Kenan an samu baragurbin da ya fitar da tsumammiyar ma’ajiyata? Lallai dan Mutum mugu ne, yayinda yake take laihin shi ta hangi na wanin sa!”ya fada cikin matsanancin fushi,
“Ke Tallafi bani ruwan randan kasar nan ko zata sanyayya zuciyar Yarima na! Kome yayi tsannanin sauki yana tare da shi. Ba a kashe zafi cikin ruwan sanyi. Koda ciwo ne da zafi ake kashe zafi.” Mika mishi ruwan tayi tana cewa.
“Duk iyawar me iyawa matukar zai kai tufkar hanci dole a canza launin farautar… Kasan yadda ake farautar Zaki? Dan haka karka sake a kuma ɗibo gurbattani a kawo min domin ba zai mana dadi ba, kuma zasu zantar da duk hukuncin da yayi musu. Ka tausayawa Yayarka ta samu majingini a tare da kai”
Wannan abin yayi mishi tsauri amma babu yadda ya iya dan dole ya hakura da gargadin da ta mishi. Har zai fita ta Kalle shi ta ce mishi.
“Ban sani ba ko akwai wani darajar bayan haka a cikin fadar shi. Amma naji yana faɗin ba zai taba wanzar da zamanin shi ba tare da ku ba, shi din ma kamar wata damar ce da ta wanzu a gare ka. A koda yaushe zaman lafiya yafi zaman dan sarki idan ta kama da shi sarkin da kan shi. Haka ya ce nai”
Advertisements
Gyada kai yayi kafin ya fice daga zaurenta.
***
Kasurgumin daji ne mara kan gani me ɗauke da manyan kwazazxabai da kurmi. Hadi da manyan duwatsu, dan tafiya kadan zaka yi zaka taradda wata korama, sauka suka yi akan dawakan su. Sannan suka daure dawakan kafin suka isa bakin koramar wacce take fitar da wani sirrintacciyar zafi da dumi. Daukar wasu fararran duwatsu suka yi sannan suka watsa a cikin koramar.
“Ga bakin gida, ga irin mutanen karni ga masu bukatar biyan bukata.” Rabewa ruwan yayi suka wuce ta kan hanyar da ruwan yake, babban fili ne iyakar ganin ka idanun ka.
A hankali suke takawa har sun ka isa wani wawwakeken lambu, shiga cikin lambun suka yi tare da tsinkar ƴaƴan itacce, suka fara sha. Wani irin hadiri ne ya gangamo kafin kace me garin yayi matukar duhu.
Dariya wani dan tsabubburin mutum ya saka tare da durowa gaban su, kamar dan biri.
“Akan mulkin masarautan ku! Ai ku koma daga nan zuwa shekaru goma ku dawo. Amma ba makawa wasu shudadden al’amarin zai faru. Imma a mutu Imma ayi rai sakon daga kai da kai ne. Ƙwayoyin halittar bil’adama tana bisa ga muradin dan haka ga wutar can. Gutsira dan itaccen ka kashe kiyayyar ka… Amma ba zaka tab’a soyayyar da take cikin dinbun zukatan al’umma ba. Akwai Sa’a amma zama haka na tsawon shekaru goma akwai barazanar ko ta kwana wannan hangen dan tsinbura ne maza a tafi ayi ta aikin ba tare da kallon abinda zai dawo ba. Domin har yau taurarin ba zasu yi gamayyar halitta ba. Wannan a saka a cikin babban magudanar ruwan masarautan.. Sa’a tana gare mu”
Fitar da sulallar zinari yayi kafin ya zuba mishi.
“A cikin matan da suke cikin masarautan bayi ayi kokarin tara su a kara gine katangar masarautan da su… Kamar yadda muka yi bayanin karnin da ya gabata”
Godiya suka Mishi sannan suka juyawa tare da barin dokar dajin.
“Kana ganin idan har aka yi haka babu wata matsala?”
“Gaskiya babu domin na yarda da shi sama da kowa bani tab’a yarda da aikin kowa sai dan tsinbura”
Duk da kasancewar Muslunci tana wanzuwa a cikin masarautan amma kuma sha’anin bokanci yana kara samun damar wanzuwa a cikin masarautan.
**
Bayan kwanaki Yarima Yakubu ya cigaba da zuwa fadar ana zama dashi sai dai zaman babu wani alkhairi. Domin kiri kiri yake karta rashin arzikin shi. Idan ran Waziri Zakaria yayi dubu b’aci yake. Yau ma ana zaune ana fadanci ya shigo cikin fadar daidai magatakarda yana karanta sakon Sarkin Gombe.
Kallon Sarki Bello yayi kafin ya kalli magatakarda ya ce.
“Kai tafi can! Ka koma ka gayawa Sarkin Gombe cewa shi wannan baffan nawa kasancewar jimawa da yayi yana zama basir ta cinye mai kuzarin shi”
“Tir da halin ka wallahi.” Kallon Zakaria yayi tare da cewa.
“Gaya min uwanai ta min baki na? Ko ubanai ya min baki na? Kaga ba zan iya dundduke ina zaman jiran gawon shanu bayan nasan me bisa kai nai. Imma ka yarda an ci amanar mahaifin mu imma ka zauna zaman karen farauta sa” ya fada yana kwabe fuska.
“Hattara dai kasan me zaka fadi a gaban Mai Martaba sarki Bello.”
Wani makawa Sarkin Fada yayi harara.
“Kai kunshe min bakinka. An ce maka kowa maroki ne? Sai manyan suna zance a bisa sha’anin mulki ku da kuke karakad’anna karan kad’a miya kuna tsomma bakin ku acikin zancen mu”
Cikin fushi Waziri Zakaria zai magana , Mai Martaba ya d’aga mishi hannu.
“Da kabarni na gyara mishi zama, me bakin zuciya kawai. Allah kadai yasan Meye zai iya aikatawa dan fuskar shi ta nuna rashin amincin shi”
Wani irin kallon banza yayi tare ba mikewa yana kallon Sarkin Zagi ya ce mishi.
“Ka gayawa musu duk wata tafiya tana bisa hanya ce amma tashi tafiyar da ya hana kara faɗin kadada zata iya fadawa cikin hatsari dan haka a yi nazarin dakatar da yaki.”
Shiru fadar ya dauka, shi kan shi sarkin Zagi kasaka magana yayi dan yasan tabbas Mai Martaba yaji abinda ya faɗa Yarima Yakubu ya faɗa.
Advertisements
“Me yasa ba za a dakatar da shi ba!” Murmushi mai martaba yayi tare da kallon Galadima. Mikewa zai yi fadawan da suke tare da shi suka mike tare da kare shi da babban rugunar su, suna faɗin.
“Gyara kintsi mai martaba zai tashi” haka ya tashi suka buda mishi hanya ya wuce fadawa na take mishi baya, har shashinsa.
Kallon Sarkin gida yayi sannan ya ce mishi.
“Ka min magana da Waziri da Galadima da waibai da Chiroma”
“Allah ya baka nasara an gama” ya juya ya fita, bayan kamar minti talatin sai gasu, basu shiga ba sai da Jakadiya ta musu iso. Yana zaune a jikin tuntun, ya ɗan yi kwanciyar hutawa.
Zama suka yi sannan suka kuma gaisawa. Shiru suka yi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
“Me kuka gani da sakon Sarkin Gombe? Sai batun wancan sakaran nasan ya bakanta muku, amma akwai gaskiya a maganar shi. Irin su ba a hana su fadar albarkacin bakinsu. Domin akwai gaskiyar da gyaran da suke sun a cimma.”
Ya fada yana wasa da wukar hannun shi. Gyara zama Waziri Zakaria yayi tare da cewa.
“Duk da na kasance yaro ma kananun shekaru ina ga Baffa ka amshi auren ta ko Baba Chiroma ba Galadima”
“Kwarai kuwa Zakaria nima nayi na’am da wannan sakon Sarkin Gombe. Wanbai baka ce kome ba kai da Chiroma” inji Galadima, ajiyar zuciya suka sauke.
“Mun amince, sai dai kasan cikin gidan dama akwai kishin da ake na kujeran da kake kai,ka nusar da ita gaskiyar kujeran domin akan ta Yarima yake wannan shaguben” inji Wanbai.
“Tun fil azal bana jin zan iya zama dindindin akan karagar domin ga me ita nan. Idan al’umma suka bukaci a bashi duk daya ne, sannan ita matar da zata zauna a kasata bana jin zata samu karfin shiga cikin hayaniyar masarautan nan”
“Allah ya baka nasara, batun ka dawo da mulkin ba zai yiwu ba, domin ko al’umma sun bukata. Ba zan taba iya rike wannan muƙamin ba bayan dan uwana Yakubu Yana bukatar shine ɗan haka kai din nan dai kai ne zaka rike mana shi” shiru zauren ha dauka domin dukkan su, sun yarda fa Abinda Waziri ya fada koda an bashi mulkin Yarima Yakubu ba zai taba yarda ba, gwara mulkin ta cigaba da zama a hannun Baffan su domin haka ne zai saka a zauna lafiya.
Sannan ya gyara zaman shi ya ce musu.
“Batun fadada kadada fa?”
“Gaskiya akwai maganar ba zamu yi yaki ba, idan zamu fadadda kadada kuwa dole sai mun gina zaratan mayakan mu sannan mu tafi da’awa idan ba amshi mulkin ba muna da ikon fadadda kadadar mu, a gani na ko da zamu fadadda kadada dole zamu tura yankunan da suke jikin mune domin su cure a cikin mu yadda babu wanda zai mana tawaye. Sannan kuma akwai damar da mai martaba yake dashi bayan an daura auren shi da Fulani Aminatu yana da damar niman kwarkwara daga wadannan yankunnan da zasu shiga cikin masarautar mu.”
Girgiza kai yai kafin ya ce musu.
“Bana sha’awan kwarkwarah, mace daya nake bukata sai dai idan halin haka ya taso zan kara aure”
“Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi, haka yayi Wallhi” anan sai suka ajiye maganar ba za ayi yaki ba, kuma maganar aure, an shirya manyan daga masarautan suka tafi har Gombe da kome da kome, suka tafi dan har da mata da har da Jakadiya, idan aka ce sai an tafi an dawo ba zai yiwu ba sabida nisar tafiyar.
Duk da haka sai da Yarima Yakubu ya sake ce wani abu.
“Duk matan da suke cikin masarautan nan babu mace sai an tafi har zuwa wata nahiyar an dauko mace gaskiya wannan shine kwaba”
Babu wanda kula da zancen shi domin sun fahimci, lamirin shi babu ta arziki sai ta tsiya kuma da za a bashi damar haka ba zai iya ba, zunzurutun ya kular da kowa ne, shi din gashi nan dai,kamar me almatsutsai, kuma babu abinda yake damun shi.
Ko shi kan shi sarki Bello yana jinjina rashin mutuncin Yarima Yakubu, sannan batun bin yan matan bayin kuwa bai fasa ba, domin har yau yana bin su, kuma idan yayi abinda yake so dasu yai musu barazanar zai kashe su haka yasa musu matukar firgice da mugun tsoron shi….
_________________________________
*Ban sani ba gaskiya uzuri sun dan sakoni a gaba idan na kammala maybe Saturday Insha Allah zamu sake hadu amma babu Alhamis……*
#Freestorie
#Mai_Dambu
[3/28, 11:47 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: ƘALLABI…!
A tsakanin Rawuna
GIPHY App Key not set. Please check settings