Advertisement
BABI NA ASHIRIN
Da wani irin tashin hankali yake kwana yake tashi, bawai dan bai da karfin kwatar kome bane, ko ba zai iya tsayawa Aminatu bane sai dai kuma yadda suke had’e kai da matukar tashin hankali. Domin kiri kiri suka juya mishi baya. Kawai abinda suke so zai yi dab haka baki daya ya kuma rudewa.
Ga shi babu Galadima, shima an can galadima addu’a yake Allah yasa kar ya amince da bukatar su, domin akwai son rai a cikin shi. Ba sarki Bello suke son yaka ba, Tarayyar shi da Aminatu ne, ya jima da sanin haka tun tafiyar su Gombe suka nuna basu son shi da Aminatu domin baya fahimtar kome idan aka ce Aminatu tana nan gani yake kamar dan bata kasance daya a cikin su ba, amma bai ga abin tashin hankali akan ta ba..
*
Yau kwana bakwai kenan da ta sanya shi a idanun ta. Ya zabge sai tarin kasumba, da sallama ta shiga cikin dakin shi. Yana kwance kasancewar yau Laraba. Kallon fuskar shi tayi tana tafiya a hankali dan bata son ya farka, kallon shi tayi na wani lokaci sannan ta shiga ban daki ta dauko tasa, da ruwa sai sabulu, tana fitowa ta ja wani karamin adaka ta dauki aska. Kallon shi tayi ta zauna a gefen gadon, sannan ta goga mishi sabulun da ruwa ta fara mishi askin kasumabr da ya tara. Cikin kulawa da tattalin shi. Yana kallon yadda ta rame, wani karin kyau da ya ga ta mishi shine hancinta da ta saka aka huda mata, yayi mata mugun kyau, ya lura a yanzun take tashen yan matancin ta, a hankali take askin har ta kusan karewa, bata yi zato ba balle tsammanin kawai ta ji ya riko hannun ta. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana kallon shi.
“Na saka ki ne?” A hankali ta ajiye askar.
“Barka da hutawa” ta fada fuskarta tattare da damuwa.
“Yawwa yan mata” murmushi tayi me ciwo, sannan ta shanye tana kallon shi.
“Akwai wani abu ne?” Ya tambaye ta yana me tashi zaune, bayan ya dauki madubi.
“A’a” kallon yadda take wasa da kafaffunta ya yi. Murmushi yayi yana jin wani kalar tausayi take ba shi, wato tayi sabon lalle shine bari ta zo ya gani.
Tashi yayi daga gadon ya nufi ban daki ya jima, sannan ya fito daure da wani katon mayafi kamar amawali a kugun shi. D’ago kai tayi ta Kalle shi tana masifar kaunar shi hadi da kewar shi. Wani irin mahaukaciyar kewar shi take, a hankali yake tafiya ta kurawa surar mijinta idanu, yadda yake tafiya irin ta cikakkun maza masu tsannanin kuzari da lafiya. Mikewa tayi ta nufi wurin da kayan shi suke ta kuma dauko wani amawalin, ta nufe shi cikin nutsuwa hadi da wani taku, kamar ba zata yi tafiyar ba, kafatar ilahirin jikinta wasu mahaukatar motsawa suke, kura mata ido yayi har ta iso gaban shi, ta fara goge mishi kirjin shi me ɗauke da wasu tarin kwanji da gargasa, janyo ta yayi ya mannata da jikin shi. Yana tuna yadda kome ya faru har ya wuce shekarun baya. Yarinyar nan da aka kawo babu kome a kirjin ta yau ita ce a gaban shi cikakkiyar mace me nutsuwa da tarin Darajojinta. Mikewar da kafarta tai alamar zata kara tsawo domin goge mishi kan shi, aikuwa ba zato kawai taji ya dauke ta cak. Wani ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta cigaba da goge mishi, tana gamawa ta fara alamar zata sauka, bai dire ta ba sai saman lafiyayyen gadon shi. A hanya ya zauna da ita. Yana kallon yadda take kokarin boye damuwar ta.
“Nasan kin ji labarin abinda yake faruwa” damke amawalin tayi ta kura mishi Idanu kafin ta sake murmushi da ya boye kukan da take yi.
“Ba ga kamar sun fika gaskiya ne” bai zaci haka daga bakin ta ba, ya kura mata ido.
“Ta ko ina sun fika gaskiya, shi mahaifina yasan da haka ai ya haɗa ni da kai. Sannan me yasa bai rike ni ba? Me yasa ya baka aurena bayan yasan akwai wannan yanayin a tare da Ni” fuskar shi ya kai daidai fuskar ta, ya ce mata.
“Ƙaddaran So shi ya sa shi tunanin idan ya haɗa mu, Allah zai bani ikon kare rayuwar ki da darajar ki” hawaye ne ya zubu mata tana kallon shi.
“A’a son zuciya ce” yatsar hannun shi ya kai bakin ta, yana gogawa sannan ya mike, amawalin kugun shi ya fadi ƙasa, bata iya d’ago kai ba sabida kunya.
“Sun bukaci ka bashi ni, shine ka ki?” Ta kuma tambayar shi.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Matar da nake so zan bawa wasu yan iska? Ke ki bawa ba zan basu daga masarautan nan ba, dan haka idan zaki kwanta ga amawali nan ki shiga ban daki kiyi wanka” ta fada yana cigaba da aikin shi.
“Amma kwarkwarah fa? Idan ka ajiye ta ba zan kuma samun damar kusantar inda kake ba.” Juyawa yayi yana kallon ta kan ta a sunkuye, takawa yayi gaban ta, ya zauna a gefen ta, sannan ya shiga cire mata mayafin kanta da duk wani abinda yake tare da ita. Bai tsaya wata ba. Ya kwantar da ita sannan ya ja mayafi ya rufe su. Tana gaban shi shi kuma yana bayan ta.
“Ba maganar wasa nake ba, wannan maganar na gaske nake rayuwar mu zaka duba.” Juyo da ita yayi da karfin tsiya yana kallon ta.
“Innayoh ce ta tsara miki abinda zaki gaya min?”
“Ina son ka fahimci.” Bakin shi ya kai habb’atar, cikin kwarewa gami da kewar ta, ya shiga bin ta. Baki daya sun yi kewar juna, sai ka rasa ita ce ko shi? Domin yadda suke gurzan juna, kamar sun shekara basu hadu bane, dan haka sosai yake murzata yana kuma hake ta lungu da sako na jikin ta. Sosai ya gauraya mata lissafi, sai da ya hanata sake furta kome sannan hankalin shi ya kwanta, ya bata kan shi da rayuwar shi. Baya jin zata kuma bukaci ya bata wani damu. Sai da ya gama sannan ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya.
“Na gaya miki bana son kina shiga harkan mulkin ko?” Buɗe idanun tayi tana kallon shi.
Sannan ta ture idanun ta. Tana sauke ajiyar zuciya.
“Kwarkwarah zaka yi fa! Ba kishiya ba balle ka ce min na amince a zauna lafiya! Baffa’m kawai ka tura ni wurin su zai fiyye min kwanciyar hankali da ina kallon ka bani da iko da kai sai na tambayi kwarkwarar ka” tana gama fadar haka ta fara kokarin mikewa.
“Ke” ya daka mata tsawa. A Matukar raxane ta zuba mishi ido.
“Ki dawo nan ki zauna sai kin maimaita abinda kika faɗa”
“Akan me zan maimaita? Ai nasan dukkanin kunnen ka sun ji abinda na ce maka. Ka mika ni gare su idan bana nan zaka iya auren ka, da dai ina kallon yadda zaka dauko min kwarkwarah bani da iko da kai laifi ne dan nayi magana akan ka?” Kura mata ido yayi yana mamakin yaushe Aminatu ta fara kokarin mishi tsaurin ido.
“Yayi kyau!” Ya fada bayan ya dauki amawalin shi ya daura ya nufi ban daki yayi wanka sannan ya fito.
“Ba zan basu ke ba, kuma akan idanun ki xan kawo kwarkwarah har turakata” bata san lokacin da ta fashe da dariya ba, ta ce mishi.
“Eh me zan yi? Ka zata xan yi wani abu ne? Amma tabbas ba zan kuma had’a shimfida da kai ba, ka tafi ka tara bayin gidan nan ka kwana dasu.”
Kura mata ido yayi yana mamakin yadda yarinyar ta Haukace mishi.
“Innayoh ce ta turo ki?” Yadda yayi maganar babu wasa a cikin shi yasa ta juyawa cikin fushi.
“Eh wani abu ne?” Ta fada bayan ta gama saka kayan ta.
“Babu shakka kin janyo mata masifa domin sai na saka a zane min ita” a tsorace ta juya tana yarfe hannu ta.
“Wallahi ba ita bane, kawai ni ce na kawo kai na, wallahi Innayoh bata san kome ba” tura ta ban daki yayi ya shiga shiryawa, yana mamakin kishi irin na Aminatu, domin babu abinda ya sakata wannan fadar sai zafin Kishi, yana gama shiryawa ya fita bai kuma, bin ta kanta ba ya nufi fada.
Suna kus-kus ne, amma ana ganin shi suka yi shiru.
“Sarkin yaki a shirya min tafiya yaki ni daya”
“Ya batun karin Mata”
“Bana bukata” kuma dama an gaya musu an ga Fulani Aminatu ta shiga shashin su.
“Akan me? ” Suka tambaye shi baki a hade.
“Akan babu wanda yake da iko da ni sai Allah, dan haka kar a kuma min maganar wata mace Aminatu ta wadatar dani”
Takaici yasa suka shiga mikewa zasu bar Fadar.
“Karka manta babu Sarkin da aka tab’a kaiwa wannan lokacin bai da Zuri’ar shi sai kai, idan har ka shiga yaki domin ta, toh abu na gaba dole ka nime macen da zata haihu domin matukar ka dawo a raye dole ka nime wacce zata haihu da kai”
“Haihuwar nan dole ne?” Ya tambaye su a tsawace.
“Dole ne domin ba zamu zauna da bakirariya ba, mun ji ka shiga yakin amma dole ka nimo wacce zata haifa mana magajin gobe idan ba haka ba, zamu yaki masarautan Gombe kamar yadda suka ci amanar aminci basu gaya mana Meke dabaibaye ga rayuwar Yar su ba.”
Shiru yayi yana fatar kafin ya sare Sarkin yakin Sahil Galadima ya iso, kusan haka aka rabu rai babu dad’i. Koda ya kome ya same ta kwance tana barci.
*Itama tana cikin damuwa kenan?* Ya tambaye ta, tana jin babu dad’i a ran shi. Har inda take ya tsaya sai kuma ya kyale ta, ya koma babban zaure, yana kallon abincin da aka shirya musu, na musamman.
Innayoh ce ta jagoranci kawo abincin,
Tana gama basu umarni ya ce mata.
“Innayoh meke damun Yar ki?” Shiru tayi sannan ta ce mishi.
“Ana tunzura ta ne da magana mara sa dadi.”
“Waye?”
“Ajuji”
“Yayi kyau, amma ki gaya mata borin ta da rigimar ta ba zasu sauya kome ba, don Allah bana son tana haka.” Ya fada yana daukar kofin da aka zuba mishi ruwa.
“Insha Allah zan mata fada ma” d’ago kai yayi.
“Karki mata fada domin ban shirya jin rigimar ta ba” ya fada yana cigaba da cin abincin.
“INSHA ALLAH”
Sannan ta fita daga Zauren.
*
Fada suke da wata mata, da ta shigo cikin gidan da tsohon cikin, a matukar tashin hankali, wasu mutane suka janyo ta waje, aka shiga rufe kofar Masarautan ga Baffa’m a tsaye kuka take da ihu tana kiran shi. Tun tana yin abin a cikin barci har Muryan ta ya fito ihu take, yana cikin cin abinci ya sake ya nufi cikin dakin da sauri ya same ta sai kuka take tana mika hannu,. Rike hannun yayi tare da sakawa a gefen fuskar shi. Sannan ya sumbaci hannun ta.
“Fulani na! Gani nan a gaban ki” bude ido tayi, tare da kallon shi bata san lokacin da ta rungume shi ba,.tana wani irin kuka me mugun ciwo.
“Baffa’m don Allah karka bari su raba ni da kai mutuwa xan yi” ta fada cikin matsanancin kuka. Rike hannun ta yayi yana kara jin wani irin kaunar ta, rungume shi tana kuka. Hannun shi ya kai bayan ta, yana bubugawa.
“Ki bar kuka idan Allah ya ƙaddara abu babu me iya kauce mishi kin ji Minani”
“Baffa’m tsoro nake ji, kullum tsoro nake ji kar ka rabu dani don Allah kar kar ka bari su raba ni da kai, don Allah Baffa’m.” Yadda take kuka ba karamin al’amari bane a gare shi.
“Toh Insha Allah babu abinda zai faru” ya fada, yana wasa da sumar kanta. Tun ranar bata kuma samun nutsuwa ba, sai ranar Juma’a da ta bar dakin shi domin zuwan bakon ta, a ranar Allah ya nufa galadima shima ya dawo. Gwanin ban tausayi idan ka ga yadda suka damu, kallon Galadima yayi sannan ya ce.
“Na yarda haihuwa na Allah ne amma yadda suke kokarin ganin sun rabu da ita shine zuciyata ta gaza dauka. Galadima kayi wani abu.”
Shiru yayi kafin ya ce mishi.
“Kayi hakuri tunda Sarkin gida ya kai min batun na shiga damuwa, wannan shine adadin lissafin kaddaran ta, Babu wani abinda xan iya yi domin kare ta, ko hanawa sannan kamar yadda kake son haihuwar ba zai zo cikin sauki ba, dan haka ka amshi bukatar su, tunda dole ka kare rayuwar ta.”
“Kana nufin” ya tambayi Galadima tare da rike hannun shi idanun shi na cika da kwalla.
Gyada mishi kai yayi shima hawaye na zuba daga idanun su baki daya.
“Me yasa sai ita?” Ya tambaya cikin wani irin tashin hankali. Galadima shima zama yayi tare da sunkuyar da kan shi.
“Na tafi lardin sokoto ne domin dakatar da wani abun, Alhamdulillahi abu na gaba shine ba zan iya kome a tsakanin ku ba, kai ne kake da wuka da nama. Imma ayi nasara akan ka Imma kuma ayi akan ta.”
“Ni kuma?”
“Eh kai! Kai ne na gaba”
“Galadima wai me yasa kake min magana a dunkule? Ka gaya min meye zai faru.”
“Ba magana nake maka a dunkule ba, wallahi ban san dalilin ba amma ba makawa zasu iya bin ta kan ka”
Nuna kan shi yayi da dan yatsar shi.
“Kuma ni”
“Hmm! Kowani mutum yana bincike kafin ya aiwatar da kudirin shi, dan haka kayi kokarin ganin ka shirya.” Mikewa Sarki Bello yayi tare da cewa.
“Wannan zancen banza ne, tunda ba zaka min bayani yadda zan fahimta ba, sai kayi.” Baki daya dawowan Galadima bata mishi amfani ba, domin duk yadda yaso kare Aminatu sai ya samu Galadima yaki ba shi goyan bayan da ya dace karshe ma, sai ya kara fahimtar kamar ai da hannun Galadima a cikin abin da ake musu dan haka a zuciye ya shirya domin tunkarar makiyan Aminatu idan ya gama da su, zai dawo kan mutanen fadar.
Ana gobe zai tafi yakin bayan sallah isha.
Tana zaune a gaban shi.
“Baffa’m ka min alkawarin zaka dawo a raye!” Ta fada bayan ta kifa kanta a kirjin shi.
“Insha Allah zan dawo zan dawo miki da yardan Allah zan dawo kamar yadda na tafi”
“Baffa’m” ta kira sunan shi cikin shashekar kuka, hannun shi ya kai fuskar ta.
“Ba zan bari a ci mutuncin ki ba, kuma ba zan tab’a amince domin keta alfarmarki ba, ina son ki.”
“Baffa’m Insha Allah zan haifa maka Yarinya Kyakyawa kamar ka, ayi mata irin wannan tsagon naka, ina son ta kasance mace Jaruma kamar kai.”
“Ta zama me hakuri kamar ke” ya fada yana sumbatar goshinta, yau ne ranar farko da ta kalli cikin idanun shi tana son gaya mishi abinda take ji a kan shi. Amma kuka da shashekar da take ta kasa magana sai kallon cikin idanu juna suke, kamar ba zai dawo ba, hannun shi ya kai wuyar ta, ya janyo ta a hankali ya shiga sumbatar bakin ta, kamar ya had’a da ita ya cinye…
___________________
End of page 20
GIPHY App Key not set. Please check settings