KALLABI 22

KALLABI
KALLABI

Advertisement

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

Zaro idanu Innayoh tayi, cikin tashin hankali tare da rufe bakin ta.
“Yakin cikin gida?” Ta kuma maimaita tambayar,
“Eh Innayoh, idan har muka basu goyan baya yanzun zasu iya ɓullo mana ta inda bamu zata ba, amma idan muka koma gefe dole shiri zamu yi na tsawon dawowar shi, dan haka kiyi kokarin ganin kin taushi Fulani Aminatu” inji Sarkin gida,
Wato al’amarin yana son kasancewa ne Sarkin Yawa ya fi Sarkin karfi, duk yadda zasu yi ba zasu iya ba, dole sai sun ninka karfin sarki Bello.

“Shi kenan, Insha Allah zan kiyayye kuma zan yi kokarin tausar zuciyar ta.” Inji Innayoh, sannan suka bar shashin, cikin gidan kuwa babu wanda ya kuma d’ago zancen Fulani Aminatu kowa ta kasan shi yake, dake abin ya hadu ta ko ina sai gashi kowa yakin yake da son samun damar da yake ganin shine mafi alkhairi a gare shi.
*
Ana ruwan saman amma zuciyar shi tayi nauyi, kallon shi sarkin yaki yayi.
“Allah ya baka nasara idan suka yi nasara akan mu fa?” Juyawa yayi ya kalli sarkin yaki sannan ya dauke kai, abin ya bashi mamaki.
“Idan ka dawo daga yaki kazo ka samu wani yana tarayya da me dakin ka ya zaka ji?”
Shiru yayi bai kuma magana ba, shima Sarkin yaki maganar ta dake shi sai ya ce.
“Tuba nake, Allah ya huci zuciyar ka” murmushi sarki bello yayi tare da cewa.
“Ba fushi nayi ba, ai bana fushi akan abinda na san zan dawo maka da abinka”

Tsayawa suka yi a kasar wani dutse na dan lokaci, kallon rundunar yayi sannan ya ce musu.
“Ban umarce kowa da shiga yakin ba, ku bar ni nayi yaki domin kimar mata ta. Dan haka ku naku yan kallo ne”

“Allah ya baka nasara, babu abinda zamu yi kenan?” Sarkin yaki ya tambaya.
“Babu abinda zaku min yakin nawa ne, ba na kowa ba. Idan kuka shiga bani da bakin da zan kare al’umma ta balle Mata ta, idan nayi kuwa har abada ina cikin kundin tarihin masarautar Gobir.”
Shiru suka yi na wani lokaci, kafin ruwa ya tsaya aka cigaba da tafiya, har zuwa filin da mutanen Sahil suke.
**
Masarautan Sahil
Kallon tursi yayi da take murmushi, sannan ta shafa kokon kan dan adam da wani irin ruwan dalma tana faɗin.
“Arkhan! Leka ka ga uwar Sarkin gobe duba kyakyawar surar da Allah ya mata”
Lekewa yayi, yana murmushin jin dadi, kallon Aminatu yayi da Innayoh take rike da ita.
“Amma ina ɗaya abokiyar tafiyar take?”
“Ba a san inda take ba, duk iya bincike na bamu ga inda take ba, amma nan da wasu shekaru zata bayyana abinda Uwa hil ta gaya min kenan”
“Dukkan su jini daya ne, bayyanar ta zai kuma haifar da wata tarzoma ne?”
“Idan muradin ka bai cika ba, dole sai bayyanar ta zai cika maka duk wani muradin ka”
“Bana fatar haka”
Dan d’ago kai tayi ta ce mishi.
“Sakon mu ya shiga cikin gidan, amma kalli yadda karfin abin jikin ta ya lalata shi” kurawa kokon kan yayi idanu.
Lokacin da Aminatu ta ture baiwar da tazo rike ta, wani irin siririn kifiya ne yayi wani irin fitar bazata daga hannun ta.
“Tabbas ita ce!”
“Dama na gaya maka tana nan”
Wani irin dariya yake fadar yana ɗauka, sannan ya ce mata.
“A shiga shirya min turaka na, yau akai min Yan mata masu tashen balaga, dasu zan gurje amarcina kafin zuwan ta ”
A duk lokacin da sarki yake cikin fara’a da farin ciki ana ware mishi yan mata masu tashen balaga, wadanda nonuwar kirjin su basu kai ga girma ainun ba, masu cikakken budurci wadanda zai kwanta da wannan zai sauka da wannan, haka tsarin shi yake, idan aka gama da su za a kai su can cikin gidan shi n bayan masarautar a iya yanzun ba ‘a san iya adadin matan shi ba, domin a labarin kunne ya girmi kaka, an ce sun kai dari da wani abu, kuma bai fasa kudirin shi ba.

Har dakaru zasu mike ya ce musu.
“A nima min har a can wurin dattijon nan domin matan su, sun fi sauran matan nan tsafta, wani irin kamshi yake fita a kasar su, jikin su kamar ana wanke su da ruwan madara” gyada mishi kai suka yi, duk da su matan wadancan kabilar idan ya kwanta dasu, bada jinin su ake ga hil, sauran dake nasu ne babu abinda yake faruwa.
Dan haka kafin Sa’a uku, an shirya yan matan an kai mishi turakar shi, sa nan aka zo aka gaya mishi.
Murmushi yayi sannan ya ce.
“Tursi me zaki bani, domin naji dadin juya kwankwasona.”
Rufe idanu tayi sannan ta bude da sauri.
“Ka kori yarinyar wurin dattijon nan babu alkhairi a tare da ita, kashe ka zata yi” sannan ta mika mishi wani kofin zinari, shanyewa yayi sannan ya kalle ta.
“Toh naji zan Kore ta” ya fada bayan ya mike, ran shi ya gama biyawa akan yarinyar tursi ta shigo da wani magana ba zai tab’a yarda ba, sai ya lashe kirjin ta zuwa kasar ta da yake fitar da kamshi nan.
*
Fulani Aminatu
Sai da rana ta fadi sannan ta bude idanunta, kanta yana sarawa a hankali ta mike tana kallon Innayoh.
“Baki tashe ni sallah ba?”
“Eh wai naga baki jin dadi ne” a hankali ta shiga ban daki, ta tsuguna zata yi fitsari jini ya sauko mata, sai da ta gama fitsarin ta wanke wurin sannan ya haɗa ruwa tayi wanka, sai da tayi wanka sosai, sannan ta shirya ta fito,
“Innayoh bani kayan wankina” ta fada tana neman wurin zama. Dauko kayan tayi ta mika mata, sai kamshin turaren suke, ta koma ban daki ra gyara jikinta, sannan ta fito saka wani riga tayi iya kwanjin ta, sannan ta kwanta tana kallon tagar dakinta.
“Ba zaki ci abinci ba?”
“Innayoh na koshi” ta fada tana kallon waje.
Yadda ta juya baya ba karamin damuwa ta saka Innayoh ba, dan haka ta zauna a wurin har aka kira sallah Isha sannan ta fita, sai lokacin ta fara kuka, kuka sosai take tana jin kamar ta mutu ta huta da wannan yanayin da take ciki. Har taji motsin Innayoh sannan tayi shiru kamar tana barci.
“Gashi inji Galadima wai a baki wannan kisha”
Tashi tayi zaune tana kallon ƙwaryan zuma ce me hadi,sai da ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta.
*
A can wurin kuwa har dare ruwa ake, dan haka sarki Bello da jama’ar shi, komawa ƙasar dutse suka yi aka kwana, bayan sun yi sallah asuba. Aka tura dan aike ya gaya musu ga sarki Bello da tawagar shi.
Aikuwa kamar jira suke suka fara maguzanci, ta hanyar bubuga abu ana ihu.
Sai da aka bari rana ta fara ketowa, sannan dukkan su runduna biyun suka bayyana a filin,
Shugaban rundunar sahil, ya fara magana da cewa.
“Zamu kyale alummarka idan ka bamu Aminatu, idan kuma ka ki zamu yake ka har zuwa masarautar ka”
Murmushi sarki Bello yayi sannan ya ce mishi.
“Toh Allah ya baka sa’a, amma da sharadi idan kayi nasara a kaina, ka ɗauki Aminatu. Domin Ni daya zan yi yaki da kai, sannan na baka damar kwace masarautar. Da yardan Allah idan ni nayi nasara akan ka, zan kashe ku baki daya kuma ba zaku kai labari ba”
Dariya suka saka mishi, musamman da suka lura da sarki Bello bai kai shugaban runduna wato Murad.
“Toh shikenan, Hil ta bani nasara” shugaban runduna ya ce.
“Alhamdulillahi Ubangiji ka bani nasara” inji Sarki Bello,

Komawa gefe lati yayi tare da shugaban runduna ya ce mishi.
“Ya shugaba shi daya zai yi yakin ba tare da yaji tsoron yawan rundunar mu ba, sannan kaga jama’ar shi basu da yawa, akwai abinda ya taka matukar bamu samu yadda muke so ba, zai karar damu dan haka ka wakilta wasu, yaki da shi muga yadda zamu shawo kan shi a yaƙin”

“Na gamsu da bayanin ka dan haka a ware mutane na musamman mutum goma su ji dashi”
Haka kuwa aka yi, ba wani dauki lokaci ba aka fara yaƙin, kamar zasu samu nasara akan shi, amma Allah ya bashi nasara, bai kashe su ba amma kuma ya nakasa su. Sannan ya koma gefe yana haki ya ce musu.
“Ka haɗa kan rundunar ka, ku bar min da’irar wankina” inji Sarki Bello.
“Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.”
“Toh Allah ya bamu nasara” aka sake turo mishi su.
Allah ya kuma bashi Sa’a kan su, haka yakin ya kasance babu sassauci sai lokacin sallah ne kaɗai ya sa sarki Bello hakura da yakin akan sai bayan la’asar, haka ce ta faru.

“Lati gaba dani zai kara na ga dai jikata min dakaru yake kuma yana yaƙin kamar wanda yake da karfin ifiritai” Murad ya fada cikin matsanancin bacin rai.
“Ai yaki yarda a yi yakin gamayya ce, dan haka ka shiga da shi muga karyan kare matar shi.”

Haka suka yi ta tattaunawa,
*
A can wurin su sarki Bello, bayan an yi sallah kallon shi, sarkin yaki yayi tare da cewa.
“Mai Martaba ban tab’a ganin yakin ka ba sai yau, a zaman da nayi da ahalin ku baki daya yakin su akan kasa ce da kara karfin mulki yau naga yaki akan mace da kare kimarta. Ya shugaba na, wacce irin kauna kake mata haka? Dukkan mu muna da mata da yara, matan mu har da sa’o’in yaran mu, ya shugaba bamu tab’a damuwa akan muna son su haka ba, kai kuwa a cikin Masarautan ka nuna Fulani Aminatu tafi kowa me yarinayr tafi sauran da shi”
Gyara zama yayi yana kallon Sarkin yaki gyatsa yayi a hankali, sannan ya kalle shi da kyau ya ce mishi.
“Ita din renon mashahurin marubuci ne, na san soyayya tun kafin na hadu da Aminatu, na karanta hikayoyin soyayya da kauna, sannan na rubuta labaru akan soyayya, yau da na samu matar da nake so idan ban mata soyayyar da na ke ji a raina ba me zan yi? Yarinya ce na same ta a lokacin, bata da hankali, bata da kome akan ta sai shirme duk abinda Aminatu zata yi koyarwa na ne, sannan bana jin koda xan mutu zata yarda ta zauna da wani namijin dan Ni daya nake gaban ta, nine murmushin ta nine dariyar ta, na mai da kaina sa’anta, sannan na zama abokin ta mijin ta, tana hira dani sama da yadda take da Jakadiyar ta Innayoh, na koya mata abubuwa da idan bana rayuwar ta zata iya kasa yin kome. Ba matan ku tafi ba a’a Tarbiyyar da na bata ne yake da bambanci da na kowa.”

“Ikon Allah, dama akwai wata soyayya ne da ta wuce ka auri mace ta haifa maka yara idan baiwa ce ka mai da ita sad’akar ka.” Inji Sarkin yaƙi.
“Kazo daidai kuwa. Toh duk ranar da ka ware macen da kake so, ba zaka tab’a farin cikin ganin ta cikin damuwa ba, Sarkin yaki kar dai kuna cikin.mazan da basu iya dauke Damuwar iyalin su sai ta kwanciyar aure?”
Sosa kai sarkin yaki yayi yana kame-kame.
“Kawai idan kuka ji bindin ku ta kumbura sai ku kai ta wurin abinda take bukata ba mamaki ma haka kuke hake musu” ya fada yana kallon sarkin yaki da yayi tsamo-tsamo kamar kazar da ruwa yayi mata duka.
Murmushi sarki Bello yayi tana cewa.
“Nasan yanzun tana can tana kuka. Insha Allah ina samun nasara zan tafi gare ta”
“Allah ya baka nasara”
“Amin Ya Allah”
Bayan la’asar suka fito, anan suka ga ikon Allah, domin shugaban rundunar ne da kan shi, dan haka suka shiga filin.
Kallon sarki Bello yayi cikin nutsuwa ya ce.
“Me yasa ba zaka bamu ita ba kawai akwai mata dayawa sai ka samu sauran” zaro takobi sarki Bello yayi cikin takaici ya ce mishi.
“Ban ji zan iya wannan kasadar ba”
“Toh zaka gani domin ba zan kashe ka ba, akan idanun ka zan tafi da ita waye yasan me zan mata a hanya kafin na isa da ita Sahil tunda naji ance yarinya ce qarama daidai tashen balaga take kome ya daidaita a tare da ita zata ji sabon kugun” cikin wani irin fusata sarki Bello yayi kan shi da azazzaben kishi….
____________________________
*Anya kuna tsoron Allah 😂🤣 wai page biyar a rana 🤔 yo ko dari na baku sai kun bukaci kari mu lallaba juna kawai a page ɗaya 🚶🏾♀️amma babu wasu dabarbarun da zan yi gaisuwar wannan shafin naku ne yan Fitilar hikayar Mai_Dambu🫶🏻*
🏃🤣 Nima nayi kan ku da azzababen sauri domin nayi posting kome zai faru oho….?

Advertisements

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 21

Advertisement *Page 21* ********************* Bayan su umma, sun Kare gani ne aka saka ranar da za’a Kai lefen,…