KALLABI 23

Advertisement

BABI NA ASHIRIN DA UKU
Kaurewa wurin yayi da azababben yaki, me cike da kishi. Wato duk da bai cika shiga yaki ba. Amma yau sai da ya kure Sarkin Yakin sahil, domin baki daya sauya mishi salo yake.
“Duk akan Matarka kake yakin nan?”
“Toh dama akan ka zan yi yaƙin” ya fada a fusace, bayan ya kai wata gagarumar sara, Murad ya tare da sauri. Duk da yasan bakar magana ya gaya mishi bai hana shi takalar shi da wata maganar ba
“Idan na kashe ka ɗauke ta zan yi” ya gaya mishi haka,
“Sai dai idan bana numfashi matukar ina raye sai inda karfina ya kare.”

Haka suka yi ta yakin babu wanda ya samu nasarar koda lakatar jikin dan uwan shi, sai da rana ta fadi dai-dai lokacin sallah, Murad ya samu nasarar yankar Baffa’m a kirjin shi. Sai da ya durkusa,. Sake kawo mishi sara yayi ya kare da takobin shi. Dole aka buga tamburan a tsayar da yaki, lokacin ibada ya kusa, jinin da yake zuba ba na wasa bane.
“Idan ka sake ka dawo gawar ka za a dauka wannan shine gargadina da kai ka bani Aminatu” bai tanka mishi ba, ya koma wurin su, yana isa suka taso zasu rike shi ya d’aga musu hannu, sai ya shiga tantin ya cire kayan, yayi wanka sannan yayi alola ya gabatar da sallah, yana idarwa ya kira Sarkin yakin shi, ya dinke mishi ciwon, duk da zafin da yake ji bai kai zafin kishin da yake ji ba. Dan haka cikin karfin hali ya kalli sarkin yaki.
“Idan muka yi sallah Isha a gaya mishi za a cigaba”
Da sauri ya kalli Baffa’m.
“A cikin daren ka zubda jini fa?”
“Umarni na baka” da sauri ya fita ya isar da sakon Baffa’m, bayan sallah isha aka kewaye filin da wuta yadda ko ina zasu ga yadda ake yakin sosai.

Bayan ya idar ko abinci bai ci ba, sai niman nasara a wurin Ubangiji, sannan ya fito filin.
*
Ta dauki kofin kindirmo zata kai baki, kamar wacce aka mata wani abu, sake kofin tayi ta fita da gudu kafarta babu takalmi. Tare tare ake da ita. Dakyar Waziri Zakaria ya samu nasarar cafke ta. Wani irin ihu take tana dukar shi da yakushin sa. A lokacin Innayoh suka iso da hansiya. Suka rike ta,
“Fulani ina zaki da alumuru nan, yanzu aka shiga sallah fa.”
“Don Allah ku kyale ni, wani abu ya same shi.”
“Innayoh ki tafi da ita, insha Allah Baffa’m zai dawo” kuka ta saka tana kara kokarin kwacewa, amma haka Innayoh ta wuce da ita, dakyar aka samu ta nutse, amma burinta shine ta tafi wurin shi.
A masallaci Waziri yake labartawa Galadima, kallon shi galadima yayi.
“Ba mamaki taji hakan ne a jikin ta, son da sukewa juna ne ya haifar da ko ya dayan su, ya shiga wani hali zai ji a jikin shi.” Yana gama fadar haka, ya wuce, daga gidan shi ya bada sako aka kaiwa Innayoh, dakyar ta sha. Daga nan sai barci.
*
Tunda suka dawo yakin, Shugaban runduna yake samun galaba akan Baffa’m, amma Naci da taurin kai, a duk lokacin da ta tafi zai fadi, sautin kukan ta yake ji, sai ya koma ya tsaya, da wannan yanayin yake yaƙin tare da rokon Allah ya bashi sa’a. Har kusan goshin asuba, kafin Allah ya bashi sa’a,ya sari shugaba runduna a kirjin shi, faduwa yayi. Ya kuma kai mishi sara, duk da Baffa’m baya gani sai yayi amfani da sautin numfashin sa, da haka baffa’m yayi ta saran shi, har sai da ya daina numfashi.sannan ya fadi akan gwiwar shi yana aman jini.

Da gudu sarkin dakarun suka zo su dauke shi, daga nan shima shugaban rundunar Sahil aka dauke shi domin ya jikata, Baffa’m kan sai da ya share awa biyar kafin ya farka, sallah yayi saboda jikin shi akwai raunika.

Sannan ya saka kayan shi na sarauta ya nufi inda rundunar Sahil take, suna ganin shi suka fara ja da baya, tantin Murad ya shiga yana kwance magashiya wato rai kwai-kwai mutu kwai-, kwai, murmushi yayi sannan ya ce.
“Allah ne ya bani nasara akan ka, sannan na Barka ne a raye domin na nuna maka karfin Addinin Musulunci, ku tattara naku ya naku, ku bar min da’irar ta, na baku sa’a daya, idan kuka sake naji labarin kuna nan zan muku kisar wulakanci. Yanzun kan ku tafi ku rayu”
“Mutanen da suke kewaye da kai, ba masoyan ka bane. Makiya ne da suka bamu damar fuskantar ka. Kayi yakin neman su waye suke maka yankan baya?”
Gyada kai yayi tare da cewa.
“Ba zan yarda da kai ba, domin an hada kai da kai dan tozarta Ni, dan haka kai da wata tsiyar na rundunar ka ku tattara ku bar min Alkarya ta”

“Babu shakka, kai mutum ne me nagarta, na yarda da kai na roke ka da Allahn ku kar ka bari wani abu ya same ta, domin tana tsakiyar kaddaran ta ne”

Kura mishi ido yayi kafin ya saka kai zai fita Murad ya ce mishi.
“Tunda ka bani damar na rayu, ni kuma zan tabbatar ba biyaka halaccin da ka min.”

Fita Baffa’m yayi, ba’a yana jin dadi bane amma yau ya kudiri Aniyar ido hudu da Minanin shi. Har ya fara tafiya, jiri ya kwashe shi, kama sarkin yayi yayi, aka nufi Masarautan da shi.
**
Tana tsaye a saman wurin shan iska, ta hango kura na tashi daga nesa, haka ya kara tabbatar mata da shine ya dawo domin ta ga tutar Masarautar ce, dan haka ta sauko tare da murar waje, da gudu tana me ratsa kofofin cikin masarautan har ta iso wajen Masarautan, sama labari ya zo an yi nasara tun safe ita ce dai ba a gaya mata, ba, domin xata iya shiga kuncin son ganin shi.

Bata tsaya ba, duk da kuwa Innayoh tana biye da ita, haka ta wuce cikin kasuwar da yake wajen Masarautan tana kara tunkarar kofar garin da kafarta, tana isa ta tsaya daga bakin kofar bayan an bude mata, kurawa ƙurar da take kara tunkaro su tayi Idanu.
Yadda take sauke numfashi, zaka rantse da Allah mutuwa zata yi, sai lokacin Galadima da waziri suka iso, tana kallon inda dawakan suke kara zuwa a guje, a hankali ta d’aga kafarta, ta fara takawa cikin wani irin kaduwa sakamakon hango shi da a goye a bayan Sarkin yaki, ji take kowani numfashin ta da sunan shi take fita, lumshe idanun ta tayi ta fara kokarin isa wurin su, da suke gab da isowa kofar Masarautan.
Linzamin dokin shi yayi a gaban Fulani Aminatu, kama kama akayi tare da saukar da shi, keken dokin aka kawo aka shiga da shi, itama Aminatu ta shiga, har lokacin bata iya ko magana, daukar kan shi tayi ta daura akan cinyarta, ta fashe da wani irin kuka, wanda ba zaka iua fassara shi ba, domin ba kukan farin ciki ba kukan bakin ciki ba, rungume kan shi tayi har suka shiga da shi cikin turakar shi, yaga rigar jikin shi aka yi take aka fi aka kona bushashen ganyen kaba, aka kona shi tare da dutsen kwalin, aka shigar barbada mishi a ciwon. Sannan suka fita bayan sun gyara mishi kwanciyar shi. Tunda suka dawo aka yi ta bada labarin abinda ya faru, kowa jinjina mishi yake, ita kan tana makale da shi kamar zata koma jikin shi. Har qashin gari, tana barci a kasa hannun ta yana cikin hannun shi, ta jingina kan ta da shimfidar shi, bude ido yayi a hankali yana kallon dakin, kamshin turaren shi ya tabbatar mishi da cewa yana dakin shi ne, jin dumin yayi a hannun shi.
A hankali ya juya yana kallon ta, tana rike da hannun shi ga shi ta jingina bata jin dadi kwanciyar kawai babu yadda ta iya ne ma, haka ya saka shi mikewa a hankali ya zare hannun shi cikin nata, ya sannan ya sauka ya gyara mata kwanciya, yana zaune cikin so da kauna, Tausayin ta da yadda ta rame yasa zuciyar shi yayi sanyi.
Tashi yayi ya tafi ban daki ya gabatar da alola, sannan ya fito yayi sallah da ake bin shi, sannan ya gabatar da Wanda ya ce shi, sannan ya koma bakin gadon ya zauna yana kallon ta, yana jin wani irin sonta na kara fisgar zuciyar shi, a fisge yake jin tana kara samun matsuguni, hannun shi me lafiya ya kai yana shafa fuskar ta, kasancewar bata san ya farka ba.
A hankali ya koma ya gyara mata kwanciyar ta, sannan ya shigar ta ita jikin shi, shafa fuskar ta yayi yana mamakin ramar da tayi s cikin kwanaki biyu, gashi har nonuwar ta sun rame, ya gane haka ne da ya cusa hannun shi cikin rigarta, hadiye yawu, yayi yana kara jin kewar ta, kallon hancin ta yayi yana jin idan ta haifa mishi yarinya mace, zai yi fatar ta dauko siririn hancin ta, domin yafi kome daukar hankalin shi, sumbatar bakin yayi….
____________

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 16

Advertisement €pisode 16…………….. Da azama ya Nufo Naheela , yayinda ya ɗaga takobinshi sama, yana isowa ya rafka…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 4

Advertisement €pisode 4……………………. Cikin daƙiƙa uku ta sauka gaban tekun Zuwatu. Ware hannuwanta tayi tana fiffika su kamar…