KALLABI 24

KALLABI
KALLABI

Advertisement

BABI NA ASHIRIN DA HUDU
A hankali yake isar mata da sakon isowar shi, a tunanin ta mafarki take, sai da ta bude idanunta tarr akan shi, sannan ta fahimci shine ba wani, rike hannun shi tayi tana girgiza mishi kai.
Dan sumbatar bakin ta yana jin kewarta na kara samun matsuguni a ranshi, zai kuma kai hannu ta mike zubur, kafin ya riko ta ta dira da sauri ta shige ban daki, wanka tayi sannan ta gyara jikin ta kasancewar har lokacin bata gama Al’adar ta ba, ta fito ta same shi kwance, sassanyar murmushi ya sakar mata,
“Yaushe kishiya na yazo?” Ya nuna mata gefen shi ta zauna.
Zama tayi, tana wasa da hannun ta, yau da ta gan shi sai ta nime duk wani damuwar ta, ta rasa. Riko hannun ta yayi yana wasa da shi.
“Fulani Aminatu” ai kamar jira take ta fashe da kuka.
Sosai bai hanata kukan ba, dan haka ya zuba mata ido, sai da tayi ta koshi sannan ta mike zata fita.
Riko hannun ta yayi.
“Dawo ki gaya Meye na Miki?”
Ya tambaye ta,
Cikin shashekar kuka ta ce.
“Babu kome” rungume ta yayi tare da cewa.
“Toh shine zaki tafi ki bar ni? Baki tunanin ciwo na ne?” Girgiza kai tayi sannan ya zauna a gefen shi tana shafa kan shi. Wani gyara kwanciyar shi yayi tare da narke mata kamar me jin zafin ciwon jikin shi. Ita kanta mantaewa tayi da kome, haka suka kasance a dakin yunwa ya fidda su, bayan sun karya, ya dawo dakin yayi wanka ita kuma ta koma bangaren ta, ta shirya amma bata kome ba, dan tasan dole za’a zo gaishe shi, dan haka ita da Innayoh suka shiga babban zauren girkin ta, suka fara abinci ana fita da shi bangaren mai Martaba, kuma kamar yadda tayi hasashe ne, an jama’ar da suke ta shigowa ba iyaka, sai dare ta samu damar zuwa wurin shi, a daddafe haka aka yi ta hidima a gidan kamar ana biki, na tsawon kwana takwas, kafin jama’a suka tsagaita.
Duk da ciwon shi akwai wasu a kirji da damtsen hannun shi, bai hana yau da yake ganin jama’a sun tsagaita ya janyo ta jikin shi ba, kura mata ido yayi, a hankali na tura hannun shi kan lallausar matashin audigar shi, wato kirjin ta, da dukiyar Fulanin ta da yake fisgar shi. A hankali ya daura hannun shi, ya ji sun cika mishi hannu sama da kullum, murmushi yayi yana kallon yadda ta lumshe idanun ta. Murmushi yayi domin yasan ba makawa zai buga shagali yau, aikuwa yadda ya saka a ranshi haka ya shiga lugwaigwaita yar mutane, tun daga sama har zuwa ƙasa, baki daya yasata mantaewa da sunanta sai sunan shi.(🤣🏃☹️😭 Wallahi mutumin nan ya isa da ciwon amma yake shirin buga isa) aikuwa bai kuma rikicewa ba, sai da ya d’aga buje, ya fahimci iya shi daya ne a wurin, sai gashi har da wata irin shashekar yaushe gamo, itama Yar banza shiru kuke ji, ta mika mishi rayuwar ta da kome nata, sai yadda yayi da ita. Aikuwa taga aya domin Baffa’m sai da ya juye mata ruwan jikin shi a kanta, sannan ya rungume ta, dan ma jikin shi da ciwo, haka ya hakura da sauran ya barta. Itama almura ko a jikin ta.
Haka zaman jinyar su ya kasance, domin gefe guda ba jinya ake ba, soyayya ake shanyewa. Sai da suka kwashe sati biyu, sai dai ta fita bada umarnin abinda za’a girka. Har ya warke sumul kamar ba shi ba, kafin ya kome fada. Ko hutawa bai yi ba, Chiroma ya gabatar mishi, da Kwarkwarah biyu. Shiru yayi kafin ya ce musu.
“Amma!”
“Ka amsa tunda ai yarjejeniya ce” hankalin shi idan yayi dubu sai da ya tashi. Yana cikin wannan yanayin Wanbai ya bashi wasu biyun, zasu kara mishi Galadima ya ce musu.
“A ka’ida hudu sun isa, idan kuma aka kara toh wallahi ba zamu amshi sauran ba ma balle ƙarin” dake yana cike da Galadima dauke kai yayi yana kallon ƙasa. Haka aka gama zaman fadar. A lokacin sarki Ibrahim kwarkwarah daya yayi sannan zamanin mahaifin su kwarkwarah daya yayi itace ya haifi Yara mata daya tana aure a kwantogora, daya tana aure a daura. Dan haka babu wasu yan uwa da suke cikin fadar sai galadima, koda ya dawo maganar kwarkwarah ya fada kunnen Aminatu, tana zaune a dakin shi. Ya shigo da sallama, kallon shi tayi sannan ta mike tana me cire Damuwar ta a gefe guda, ta taimaka mishi ya rage damuwa. Nasihat Innayoh yana dawo mata akan labarin da ya iso su.
_Karki sake ya fahimci baki girme tashin hankali ba, haka zai ajiye ki a ran shi. Ban hana ki jin kishin shi ba amma maganar ki mishi yaji bai taso ba, shima tilasta shi aka yi, sai ki nuna musu kina maraba da zuwan su, matukar kika rike mutunci mutanen banza ma mutumtaki zasu yi_
Da wannan ta shiga Taimaka masa, har ya shiga wanka, yana fitowa ya samu ta cire mishi wasu kayan sawa, zai da ya shirya ta rike hannun shi zuwa inda zai ci abinci. Zama yayi yana wasa da abincin.
“Allah ya baka nasara, kaci abinci” wani irin fisgota yayi tare da rungume ta, ita kuwa ta bashi wani irin lafiyayyen runguma, ba tare da sun fahimci kome ba, kawai suka fada wata irin duniya, sanin cewa bakin kofar akwai dogarai yasa shi daukar ta cak zuwa turakar shi. Daga shi har ita burin su,.shine amanta da damuwar su, bai san wani irin so da bukatar ta yake ba, sai dai wannan ita ce rana na farko da suka zama kamar basu ba, domin gata nan yar mitsitsiya, ta dauke nauyin shi da bukatar shi, tsabar jaraba tun daga gado saman Kilishi, wurin hutawa duk sai da suka yada zango a wuraren, kafin suka samu nutsuwa a lokacin suna kwance a tsakar dakin.
Juya mishi baya tayi tana murmushin jin kunya.
“Fulani Minani” ya kira sunanta yana shafa bayan ta, ita kuwa burin ta bai wuce ta dauko mayafin da zata rufe jikin ta ba, janyo ta yayi yana kara yaba halayyar ta, na kunya da kawaici. Tashi yayi ya dauke ta yana faɗin.
“Ni ba mijin ki ne kuma sirrin ki, idan har kika cigaba da kunya ta wacece zata min yadda kike min?” Boye fuskartar tayi a kirjin shi, haka suka yi wanka har aka gama, bata d’ago kai ta kalle shi ba, asalima yau ya lura wani irin yanayi yake ciki, domin taki saka kaya amawali ta daure a kirjinta, kuma har a dare sallah ne kaɗai yake bada damar saka kaya. Taki yarda su kuma magana akan kwarkwarah, asalima mantar da shi zancen tayi sai ma shagalin da take mishi, tsawon kwanaki suna kara kaunar juna, da ɗaukar bukatar juna.
Da fari burin magauta ita Fulani Aminatu tace ba ta amince ba, sai a goranta mata tare da tuna mata ai ita yar kwarkwarah ce, sai aka yi rashin dace bata nuna haka, musamman wani hidimar da aka yi a gidan galadima, suka hadu akayi ta jefa mata habaici yar batalikan nan bata d’ago kai ta lalle su ba, asalima nunawa tayi bata san suna yi ba. Kuma haka ya faru ne sakamakon kokarin Innayoh ta ce mata.
*Zasu nemi gaya Miki magana! Zasu takale ki da haibai ci. Zasu bakanta musu ki nuna musu ke mutum ce ba dabba irin su ba, don Allah kar ki nuna ko akan fuskar ki*
Shi yasa suna fara cusguna mata, suka ga fuskar ta sau murmushi take. Asalima tashi tayi ta koma wurin matar galadima, babu abinda yake kara bawa kowa haushi yadda shigar ta, nutsuwar ta kamalarta. Bata yi kama da mutanen da basu san ciwon kan su ba, har suka bar gidan bata d’aga ido ta kalle su ba, asalima sai suka fara kokarin dakatar da junan su, domin an ce shiru ma magana ce.
Tsakanin ta da mijin ta, kamar hanta da jini domin babu ruwan su, duk abinda za a yi sai ayi.

A ranar wata juma’a, aka shigo da kwarkwarorin cikin masarauta. Sai da aka kawo mata su, tana kallon su daya bayan daya. Idanun ta ne ya sauka akan Bingel, cike da mamaki take kallon ta. Kafin ta cewa Innayoh.
“Innayoh na gan su, Allah ya basu Sa’a da iya daukar kome”
“Amin uwar ɗakina” sannan aka wuce da su,. Shiru tayi tana nazarin wannan al’amarin domin gudun kar ce zata hana shi zama da mace yasa bata yi wani abu ba.

Da daddare, tana turakar shi shi, kanta a sunkuye tana yanka mishi lemo ta ce mishi.
“An kawo yan matan fa”
“Sai aka yi Ya?”
Ya tambaye ta,
“Wai dama na tuna maka ne, daga gobe zasu fara amsar ragamar aikina.”
“Guduna kike Aminatu?”
“A’a ba haka bane” ta fada tana mika mishi lemon,
“Toh ki kyale su, a wurin”
“Amma”
“Amma me?”
“A’a babu kome” daga haka ya janyo ta jikin shi, sannan ya shiga bata labarin abinda ya faru, nan ta manta da batun kwarkwarah ta shiga dariya.

“Wai kuna ganin har sarki Bello zai nime mu?” Daya cikin kwarkwarah ta tambaye sauran,
“Me zai hana, mun fi matar shi kome fa me zata nuna mana da ya ce farin fata.”
Bingel na gefe bata ce musu kome ba, har suka gama hiran su.

Kamar yadda dai suka saba, haka ya shiga karatun d’aga buje, babu ruwan shi da wani abu wai da aka ajiye mishi, sosai ya gurje matar shi. Ai kuwa yana zuwa fada aka kawo korafin an kawo mishi mata amma Fulani Aminatu ta hana su isa gare su, zasu dauki mataki akan shi da Aminatu.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Idan kun dauki matakin iya kaci kuce na bar muku mulkin ku, kuma dama kamar kun san akan k’aya nake, idan kuka amsa sai na dauki mata na mu bar Masarautan babu wanda zai kuma ganin mu balle ya dame mu. Suma matan da kuka bani kazamai ne da suna da tsafta ba zan guje su ba,” daga haka ya kade alkyabbar shi ya bar su a wurin tunda sune suka zabi haka bai ji yayi danasanin maganar da ya gaya musu ba, tunda suka fahimci hanyar da zai balle mulkin ma yake sai suka shafawa kan su ruwan sanyi, domin haka ba karamin koma baya bane a cigaban su.

Bayan wata guda, lokacin Fulani Aminatu tana hutun Sallah, a lokacin Innayoh ta mata magana akan lallai a shirya daya daga cikin kwarkwarah ta tafi wurin mai Martaba, bata so ba domin shiru tayi taki magana, ita kuwa Innayoh bata kuma mata magana ba, amma tayi gaban kanta, domin kuwa bata jira abinda Fulani Aminatu zata ce ba, ta bada umarnin a shirya daya daya cikin yan matan nan, a kai wa Mai Martaba….
_________________________

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 8

Advertisement €pisode 8……………………. Cikin daƙiƙa uku Tsuntsu Bilbil ya sauka gabansu na Naheela. Cikin kakarin jini ta shiga…
Read More

TARTSATSI 53

Advertisement *Page 53* ********************* Aikuwa ganin sojoji a unguwar, ya sa yara da Manya, cincirindo a k’ofar gidan,…
Read More

TARTSATSI 74

Advertisement   *Page 74*   Yana nan azaune yana tunanin miye hakan kuma, wari Salma ina bazaiyiyu ba,…