KALLABI 3

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*<Babi Na Uku>*

~Masu azancin harshe sukan ce dakan d’aka shikar d’aka….masana harshe kuwa suka karasa azancin da da tankad’en bakin gado…. Inji Masana harshen Hausa~

Wannan haka yake domin sarakunan baya suna daukar ษ—iyoyin su mata masu daraja su hawa wata masarautan, ba dan kome ba sai dan kulla alaka me kyau, sake raya zumuncin su.

Ko nace masarautan buba Yero! Masarautar ce da Fulani suka kafata,karkashin jagorancin Mujaddadi Shehu Usmanu danfodiyo, inda ya turo wakilin shi Muhammad Kwairanga. Ita kanta Gombe an samo ta ne daga wasu kabilun.

Tarihi ya nuna a karni na 13 aka fara sanin garin Gombe, sai dai kafin wannan lokaci an yi wadansu mutane masu karama da sarauta da ake kira โ€˜Soninke Mandigosโ€™, wadannan mutane su ne suka samar da tsatson garin Gombe, kuma littafin โ€˜Tarekh-el- Sudanโ€™ (Tarihin Kasar Bakake) na musu lakabi da โ€˜Fararen Shugabanniโ€™.Wadannan mutane ana kuma kiransu da โ€˜Kaya- Mangaโ€™. Sun mulki yammacin Sudan na wasu karnoni da dama. A cikin Kaya-Manga an samu wani mutum da ake kira Bin-Kaya Mob, wanda sarki ne a wata masarauta da ake kira Mande, a yammacin Sudan din, wanda kuma wannan sarki ya ci zamaninsa a cikin karni na 10.

Sarki Bin-Kaya Mob yana matukar ji da jikansa Bin-Abubakar, wanda har ta kai ko kuda ba ya so ya taba shi. Ya mayar da shi dan lelensa kuma shafaffe da mansa. Hakan ce ta sanya Kaya Mob ya bai wa jikansa wani bangare na masarautar tasa da ake kira Ukuba. Bin-Abubakar kaka ne ga Aliyu Ukuba, wanda shi kuma yake mahaifi ga Usman. Aliyu Ukuba shahararren malami ne, ya haddace Alkurโ€™ani, wanda daga baya aka hada shi aure da โ€™yar gidan wani attajiri a garin Tibati, inda kuma suka haifi Usman. Zuri’ar Usman ta rayu na wasu tsawon karnoni har zuwa lokacin da suka tashi daga yankin gombe.

A cikin shekarar 1913 Hedikwatar Gombe ta tashi daga garin
Gombe zuwa Nafada, wanda a cewar Nasarawa Nafada ta fi
saukin zuwa daga manyan garuruwan Arewa irin su Kano da
Bauci da Maiduguri da sauransu. Har ila yau a wannan shekarar
aka girke sojoji masu lura da shige-da- fice a kan iyaka. Sarkin
Gombe Umaru ya halarci wani hawan daba da aka yi a Kano,
lokacin da sarki Edward na III ya kawo ziyara Kano. Bayan sarki
Umaru ya dawo daga Kano ne, ya sake zabar wani
gari da ake kira Doma karkashin Akko. Inda a shekarar 1919 aka
sake rada wa garin suna Gombe-Doma.
A kuma wannan shekarar ce aka mayar da Gombe- Doma zuwa
masarautar Bauci, sannan aka rage mata dagatai zuwa 3, wanda
a da take da 13. Daga nan kuma sai aka dawo garin Gombe…. Takaitaccen tarihin masarautar Gombe.
__________________________________
Masarautan Gombe

Kallon Kanin shi jibril wanda suke kira Babayo, yayi cikin nutsuwa sanna ya ce mishi.
“Jibril ina ganin kamar ba zasu amshi tayin ba?” Shiru yayi kafin ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi da biyayya.
“Hamma Shehu, babu inda ba zasu so tayin ka ba, sabida Fulani Aminatu tana da nagarta, kuma kai ma nagartaccen mutum me, sannan idan yadda ka hango ne, Sarki Bello ya dace da Fulani Aminatu, kuma idan kayi nazari a da tarihin shi yana daga cikin sarakunar gobir da suke kin tashin hankali ba laifi bane idan aka bashi tunda har aka yi nad’in sarautar babu wanda yayi yunkurin bashi mace. Haka yana nufin cewa sun gaji da bawa mazan masarautar mata ne sabida..”

Shiru yayi yana kallon kasa, gyara zama Mai martaba Sarkin Gombe ya ce.
“Babayo kana hidima da Aminatu domin Buba ne ko kawai dan ni ne?” Haษ—e hannun shi yayi cikin tsannanin tsoron da tashin hankali kan shi sunkuye ya ce.
“Ina yi ne dan Fulani Amrah” d’ago kai Mai Martaba Sarkin Gombe yayi ya kura mishi ido. Sannan Babayo ya cigaba da cewa.
“Nayi mata alkawarin tsayawa Aminatu, bakwai dan Abubakar yana son ta ba, sai dai muna duba Gombe mu ne kafin mu zartar da hukunci. Sannan idan na duba ita kanta kafin ta san Meye soyayyar ya dace a fitar da ita daga cikin masarautan yanzun take da shekaru goma sha biyu. Daidai ta tashi a hannun mijinta. Sannan haka zai saka ta taso da soyayyar mijin ta da kuma sanin sha’anin mulki.”

“Na yarda da kai, ku shirya kome yadda zai tafi” ya fada,
“Allah ya taimake ka, Ubangiji ya baka nasara Allah ya kare ka gaba salama baya salama”

Advertisements

Lumshe idanun shi yayi tare da jinjina kai, ba wai yana da zabin ba da auren Yar shi karama bane sai dai bai da yadda ya iya ne kawai, sannan tun lokacin da yaji ra’ayin Sarki Bello yaji a ran shi Aminatu ta dace da shi sabida tashin da tayi a cikin gidan sarautar a ware, kasancewar mahaifiyar ta kabila ce ba bafulatana bace kuma uwa Uba baiwa ce a cikin masarautar sarki ya yantatta. Sannan duk cikin masarautan tafi shiri da Babayo kasancewar shine mutum na farko da ya fara nunawa dan uwan shi dacewar ya shigo da ita cikin masarautar a matsayin kwarkwarah mana. Kuma Sarkin ya amince.

Mahaifiyar Aminatu ta kasance daga cikin bayin da aka kamo cikin ganimar yaki, kuma aka kai su shashin Fulani kilishi, maketaciyar mace mara imani, ga cin zarafin bayi kamar me.

Kasancewar Babayo yana yawan kai sako yake ganin yadda ake cikin zarafin bayin, yaso shi ya nemi Amrah, amma sai yaga koda ya nime ta, ba zata samu sauki ba a gidan shi domin shima lokacin matar shi tana da Masifar kishi. Amma idan a Kwarkwarah ne sarki zai d’aga darajar ta da kimarta. Da wannan ya bawa Dan uwan shi shawara kuma yayi na’am da shi.

Za a iya cewa table rabo ne ya tsaga bata jima da tarewa, sai ga ciki a lokacin sarki Shehu yana da mata hudu, kuma dukkansu yaran su manya.

Uwargidan Mai Martaba itace Fulani Shatu yar Sarkin Yola, sai Fulani Habibah daga masarautan kano,Hajiya kilishi daga nan yar wazirinsa ce.

(Ga masu bukatar Wata Alkaryar 300 uku me zasu iya tuntubar wannan number 08130269641)

Sai Fulani Maimuna daga daga nan cikin masarautan yar Kanwar mahaifin Sarki Shehu ce, sannan suna da yara kusan kowanni daki, babban abinda da yake faruwa su sauran matan basu kai Kilishi azababben kishi ba, domin ita baki daya gani take itace ta dace da Mai martaba ba su ba, haka yasa kowa take ganin zata taka, su kuma sauran suka ce basu iya ji ba, kalmar nan ne da ake cewa Haushin kaza huce kan dami, shine ana kawo Amrah ta sakata a gaba dama kuma tun can haka ne ta tsani Yarinyar tun farkon kawo ta. Amrah ta sha bakar wahala a hannun kilishi.

. Haka yasa koda tazo haihuwa ita da kanta ta haihu domin Kilishi ta hana kowa shiga cikin dakin ta, koda ta haihu an ji kukan jaririya, amma ba a ji motsin uwar ba. Dan haka baiwar da take tare da ita Innayoh itace ta shiga ta ga rai yayi halin shi. Ga jaririya a gabanta. Abin tausayi haka Innayoh ta dauke jaririyar ta kaita wurin Fulani Shatu. Babu laifi ta amshi yarinyar amma ranta bai so haka ba.

Lokacin da Mai Martaba yaji labarin mutuwar Amrah, da sakon da ta bawa Babayo, yayi kuka kamar zai yi yayya anan ya shiga bincikar dalilin da ya hana Jakadiya, kasa fadar gaskiya suka yi karshe Innayoh ce ta gayawa Babayo, wanda a lokacin shine mafi kusanci da mai martaba, amma yaki amsar mulki. Domin yace a bar shi lafiya da dan uwan shi. Shi ya gayawa mai Martaba abinda ya faru, shi kuma ya rantse ko za a bar shi a duniya shi da kilishi ne ya yafe ba zai kuma zama da ita ba, wannan dalilin ya kuma haifar da tsannar Aminatu a ran Kilishi.

A hankali yarinyar ta taso babu soyayyar kowa sai ta Innayoh, domin shi kan shi Mai Martaba ya tsani yaji sunanta ko ganin ta, wanda bayan rasuwar Mahaifiyar yake mugun kaunarta. A hankali aka wayi gari baya son ko ganinta, haka yarinyar ta zama kamar yar tsakar gida. Tana da Shekara biyar suka saba da Buba dan gidan Babayo, wanda shi yana da shekaru goma sha biyar a lokacin.

Haka ya taimaka mata sosai har take jin kamar shi ne kome nata, ana cikin haka Mai Martaba suka tafi wani gari garin numan, bikin kamun kifi ana ya hadu da wani mutumin da yaga sarkin Gombe yayi ta bin tawagar shi har ya samu ganin shi.

“Allah ya taimaki mai martaba, hmm kana raye amma shukar ka tana bushewa, ko baka bukatar bishiyar tayi yabanya ne? Zanen ฦ™addara tayi tawo mugama da wasu manyan manyan alamura. Faruwar wasu abubuwan zasu biyo bayan kyakyawar yanayi me ษ—auke da manyan ginshikai. Masu biyu zasu kasance a danbar kowacce ฦ™addara, idan har zaka daka ta tawa, domin samun alaka me karfi ka gwada mika yasashen tsiron nan da yake gidan ka, amma bari na gaya maka bai zama dole haka ya zama karshen wasu abubuwan ba, kamar haka itace tushen wasu matsololin sannan karshen wasu matsalolin. Hawaye zai ta zuba, domin share duk wata cutar bayan kasa dole wannan tsiron na gidanka zata fitar da manyan manyan alamura. Kayi kokarin nan da shekaru bakwai masu zuwa ka gaggauta habaka yabanyar ka”

Advertisements

Daga haka yayi tafiyar shi, shiru suka yi daga shi har Babayo. Kafin suka kalli juna.
“Hamma kaina ya kulle” inji Babayo,
“Nima haka, Allah yayi mana jagora,amma abun da duba yanayin maganar shi domin yayi maganar cikin gaurariyar hausa ce.” Inji Sarkin Gombe, shiru Babayo yayi sannan suka wuce inda zasu zauna kafin a fara bikin.

Bayan sun dawo suka samu yarinyar bata da lafiya, abin tausayi haka Uban ya wuce, kasar zuciyar shi yana jin zafin wofatar da ita da yayi, tun daga lokacin. Babayo ya mai da hankalin shi kan yarinyar, har zuwa lokacin da suka fahimci shakuwar so Buba, hankalin su ya tashi, domin bayan nan sun kuma cin karo da wani mutum a lokacin wani bikin sallah, ana bikin sallah, shima ya gaya musu haka amma sai basu dauka da gaske Ba.

Sai da aka yi karo na uku zuwa wani yaki da aka yi da wasu maguzawan dutse, da suke gaban shi garin Gombe suka sake jin irin wannan maganar, tun daga nan hankalin shi ya tashi ya shiga niman masarautan suka kasance masu kwazo da rashin tsoro, a lokacin sarki Ibrahim ya tab’a zuwa da wannan batun sarki Ibrahim ya ce mishi.
“A kullum kabilar mu suna facaka ne cikin jini, sannan mu bamu kasance masu tsoro ba,kullum kwayar jinin mu barandami ne, bamu fita niman aure dan mun san ba bamu za ayi ha taya zaka kawo yarinya me daraja cikin mu? Shin kana ganin yin haka ba zai hanata fuskarta takaba bane? Duk wani namiji a masarautan nan an hore shi da yaki ne! Dan haka ba zan maida maka Y’a bazawara ba ka kai ta wani masarautan.”

“Naji abinda kace ko yaranka maza ai xaka iya nima musu auren tunda itama Yanxun take da shekara bakwai” domin lokacin shekarun ta bakwai ne, kuma Sarkin Gombe ya kagu ya dauke ta a cikin masarautan sabida yadda take Fuskar ta yawan rashin lafiya da yanayin takurawa.

Koda matan Sarki suka ji labarin ana nima mata babban gida a cikin gidajen sarautar kasar nan abin yayi musu zafi dan haka suka hasala…๐Ÿ”ฅ
____________________________________
Hi guys barka dai Wayyo kuka ta kira cigaba cigaba… TOH gashi nan thank you ๐Ÿ˜
#Mai_Dambu
[3/28, 11:48 AM] UmmuHabibah๐Ÿฅฐ๐ŸŒนโค๏ธ: ฦ˜ALLABI…..!
A tsakanin Rawuna.
EWF
Na
Mai_Dambu

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 11

Advertisement Page 11* ***************** Tayi wani bishi da wani kallon renin wayo, duk da jikinshi yayi sanyi, amma…
KALLABI
Read More

KALLABI 19

Advertisement BABI NA SHA TARA *WANNAN PAGEN NA KUNE MUTANEN BAFFA’M DA YAR KWAILAR SHI MUSAMMAN AUNTY SA’A…
Read More

TARTSATSI 102

Advertisement *Page 102*     ๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š     **********************   Lokacin aikin hajji yayi, Sadauki ya cika alk’awalin…