KALLABI 4

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*<Babi Na Huɗu>*

_Soyayyar gaskiya tana faru ce a bisa wasu manyan ginshikai! Imma ƙaddara ta haɗa imma kuma lokaci ya haɗa sai dai mafi girman soyayyar gaskiya ita ce ƙaddarar da zata zo bazata_

A hankali rayuwa ya cigaba da tafiya tare da fatan samun daidaito akan Al’amarin Yar shi, har tsawon kwanakin da basu kirguwa. Kwanaki sun rikide zuwa makonnin,. Da tafiya ta mike makonnin sun rikide zuwa watanin. Watannin sun juya tare da curewa wuri guda inda suka haifar da shakaru.

A cikin wannan yanayin Fulani Aminatu tana da shekaru goma sha,, gefe guda kuma Kilishi ta sakota a gaba, inda take ganin kamar ai ita da take da Yarinya mace budurwa ta dace Mai Martaba yayi magana akan ta, amma ya karkata ga Aminatu dan hakan suka hade kan su kaf matan mai martaba idan ka cire Fulani Shatu itace kawai taki shirya al’amarin su domin ta fahimci wani abun da basu fahimta ba, na Mai Martaba yana kokarin fitar da ita ne dan halin da take fuskanta. Shi yasa bata takurawa kanta da azababben kishi akan Aminatu ba.

Sauran matan sun gama ajiye magana daya akan Fulani Aminatu, dan haka Fulani maimatu ta same Mai Martaba a babban zauren shi na hutawa. Cikin nutsuwa ya Kalle ta domin yasan matukar zata zo gaban shi da nata bukatar zata zo, dan haka ta zuba mata ido.
“Allah ya baka nasara, dama akan batun Fulani Aminatu ce,Mai Martaba kana ganin a dauki Yarinya karama a bada ita aure babu wani abu? Sannan wani masarautar ce za a bada aurenta ga Yayunta Mata Fulani Barirah da Fulani Saudatu, ga Fulani Sakinatu duk Yaran da suka fito cikin jinin sarauta ne ita kuma Yar yantacciyar baiwa ce fa”

Murmushi yayi tare da cewa.
“Bakar Saniya…
Mai fidda fararr Madara ta samar da ita taya zan iya juyawa ƙaddarar ta baya? Masarautan da za a kaita aure kiyi hakuri lokaci zai nuna mana ko ina ne” ba haka taso ba, taso taji ina ne za a kai Fulani Aminatu.

*
Tawagar Gobirawa.

Sun yi tafiyar tsawon mako uku zuwa hudu kafin suka isa garin Kano, inda suka samu kyakkyawar tarba daga Sarkin Kano, shi kuma yayi musu tanadi na musamman, inda ya bada wakilin shi tare da wasu manyan mutanen Fadar shi. Tare da rubuta wasika izuwa Sarkin Hadija, dan haka babu b’ata lokaci aka sake tadda dawakai da kayan Alfarmar tare da akwatin gwala-gwalai izuwa masarautan Gombe.

Tafiya ce wacce aka yi ta a cikin kwanaki biyu rak,Mai Martaba sarki hadeja ya basu wasu mahaya kasancewar tafiyar har da rakumai kusan guda saba’in shima kuma Mai Martaba Sarkin Hadeja ya bada wasu manyan munduwar zinari ga amarya sannan ya kuma kara wasu manyan dagatai da zasu yi rakiya har fadar Gombe.

Kafin su baro garin haɗeja, Sarki Abdullahi na Hadeja ya bada wasika ga amintattacen mahayin shi kamar yadda Sarki Muhammad na Kano yayi mishi. Ya bada wasikar a kai ga Sarkin Bauchi, tafiya ce ta tsawon kwana biyar.

Advertisements

Kuma a yadda aka san masarautun arewa suna da kyakkyawar hadin kai da taimakon juna, haka yasa suka marawa Masarautan Gobir bayan, domin a tarihi ya tabbatar da cewa babu masarautan da suke sa karfin jarunta da kuma yawan sadaukai. Ko yayya suka shiga yaki ba a kada su, sannan dayawan masarautun suna kokarin Niman taimakon su tare niman goyan bayan su a yaki, haka yasa dayawan mutane ke tsoron wanda zai bude baki ya ce yana da alaƙa da masarautar Gobir. Sabida karfin mulkin su. Da kuma iya sarrafa yaƙi.

Sannan sauran masarautar suna kokarin inganta zamanin lafiyar al’umma su,ba dan kome ba sai dan kar a fara yakin da za a yi asarar rayuka da duniyoyin alumma. Sannan babban abinda kunya ce ka shiga yaki baka da masu taimaka maka, masarautar Gobir ita ɗaya ke idda yaki babu mataimaki sai Allah wannan yasa kowacce masarautar ta shafawa kanta ruwan sanyi.

Baya haka haka kamar yadda sukewa Masarautar Gobir hidima itama masarautar da zasu shiga wani abu tabbas zasu iya taimakawa, wannan shine ake kira da karfin zumunci da dangantakar dake tsakanin masarautun.

Koda mahayin ya isar da sakon Sarkin Bauchi, aka fara shirin tarban bakin masarautar Gombe,. Sannan aka musu kyakyawar tanadi, kasancewar masarautar Bauchi tana cikin manyan Masarautun da Shehu Usmanu danfodiyo ya kafa da kan shi inda ya turo wakilin shi yakubun farko haka ya haifar da wani irin daidaiton tsari a garin da masarautan baki daya.

Bayan kwana shida suka iso masarautan Bauchi, kuma Alhamdulillahi sun samu irin tarban da ya dace dan dama tun fil azal mutanen Bauchi akwai karamci da amsar bakon su,. A ranar Sarkin Bauchi ya tura sakon zuwa ga sarkin ga bakin shin nan zuwa. Kuma tafiyar kwana ɗaya ce da wuni. Dan haka ya gaya musu zasu taso nan da kwana biyu.

…..
Masarautan Gombe.

Tun daga yanayin gyaran masarautan tare da kula da wasu manyan bangarorin cikin masarautan yasa kowa ya sha jinin jikin shi. Tabbas duk inda ake tsammanin za a kai Aminatu babban masarauta ce me karfin iko da mulki. Kaf masarautan babu wanda yasa inda za a aurar da Fulani Aminatu, amma Innayo ta sani, .haka Jakadiya Jebu tayi ta bugun cikin Innayo amma bata taɓa bude bakinta domin magana ba. Baya kadan a cikin masarautan.

Ana tsakiyar fadanci Mahayin barci yazo, cikin girmamawa ya isa gaban mai Martaba. Ya zube.
“Sako daga masarautan Bauchi, domin isa da bayanin jibi insha Allah baki suna nan zuwa”

“Ku bashi sulallar zinari, sannan akara mishi dawakai uku, a bashi bayi mata biyu, tukwaici ne ga sakon da ka kawo”
“Allah ya kara girma da daukaka, Ubangiji ya jibanci al’amarin ka”
“Sarki Ya amsa” sannan Mai martaba ya kalli kanin shi Babayo ya matsa kusa da shi,.ya fada mishi bakin da suke zuwa.

“Masha Allah, surukan mu na wannan masarautan mai albarka zasu taso jibi talata, zasu huta Laraba da Alhamis, ranar Juma’a Insha Allah muna fatan daurin Auren a cikin masarautan nan” inji Babayo, kafin kace kwabo Sarkin gida da Sarkin Zagi sun isa cikin gidan sun sanar baki daya hankalin kowa ya tashi daga wata masarauta ce? A cikin gidan kuwa tun da aka yi sanarwar Innayoh ta saka Fulani Aminatu a daki ta hanata fita sabida tasan zuwa kowa ya wasa wukar shi da fitinar shi dole a shirya ta, dan ma an kawo mata jike-jike Baffanta Babayo idan ba haka ba ai da yarinyar ta kad’e har buzun ta.

Tun daga ranar da aka sanar bakin Gombe na zuwa aka kara yawan tsaro aka kara yawan kulawa ba musanman, sannan shi kan shi Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Shehu Usmanu, babban Addu’ar shi a fitar da Aminatu lafiya haka zai daka shi jin wata irin nutsuwa.

**
Rana bata karya kamar yadda aka sanar ranar Laraba talata da magariba, bakin Gobirawa suka iso. Sannan suka yadda zango a wajen garin gombe tare da tura bayi mata karkashin Jagorancin Jakadiya Rama. Tun kafin su iso aka shiga fadar da labarin ai bakin. Daga masarautar Gobir ne, kafin kace me labarin ya karade cikin gidan, take kowacce mace ya kama kanta da Yaran ta, tare da ganin adalcin da Mai Martaba yayi na aurar da Fulani Aminatu ga masarautan da kullum cikin shirin mutuwa yayi ya kyauta (shi fa Mahassadi kullum haka yake da zaran yaga can bai ci ba toh gaba zai ci kamar ba anan ake son sanin ina ne za a aurar da ita ba yau kuma ana ganin adalcin Mai Martaba)
_____________________________
*Hey gashi nan babu yawa. Amma da za a kara comments da Voting maybe na kara wani abu wannan labarin ba zance zai kai kwarkwarah ba amma ba mamaki suyi kunnen doki please share it*
#Mai_Dambu

Advertisements

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 33

Advertisement 33_* *_Arewabook@Mamuhgee_* Da zazzabin ta tashi da safe Dan haka sallah kawai ta iya Yi Takoma ta…
INAYAH
Read More

INAYAH 60

Advertisement 60_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Fatar wuyanta ya saka harshe ya lasa cikin sanyi da nutsuwa Yana sake Jan numfashi…
INAYAH
Read More

INAYAH 29

Advertisement _29_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Qarfe goma da minti arbain su Umma yaganah da Inayah suka fito tana shirye cikin…
KALLABI
Read More

KALLABI 18

Advertisement BABI NA SHA TAKWAS “Kai!!!” Ya fada da ƙarfi amma ina har zakin nan ya samu damar…