KALLABI 6

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*<Babi Na Shida>*

 

Wannan pagen gaisuwar taki ce Momyn noor Nagode kwarai da gaske 😍

A dan rude suka kalli kofar dakin, babban mayafi ta rufawa Fulani Aminatu. Jakadiya Jebu ce da wasu manyan bayi mata suka shigo cikin dakin, dauke da manyan manyan tasa na damamiyar lalle da yaji turare. Kallon su Innayoh tayi kafin ta sake murmushi ta ce musu.
“Daga ina haka?” Wani irin kallo Jakadiyar tayi mata sannan ta ce mata.
“Ana babbakun giwa wake na zomo, Malama bamu hanya mu wuce, Fulani Aminatu zo ki cire kayan ki za a miki wanka da..”

Bata kai aya ba Innayoh ta ce mata.
“Haba ai ko min saurain unguwar zoma ta jira haihu ko? Ki mai da shi an rigada an gama bamu bukatar na kowa sai na Allah” dariya takaici Jakadiya tayi kafin ta ce mata.
“Kina wasa da ni ko?”
“Jebu ke kudi tara ta ce da zan yi wasa da ke? Ko ke Kanwar kakata ta ce da zan dara dake? Ga hanya nan. Kika sake wani abu ya same ta toh wallahi da baikon Sarkin Gobir akan ta ki jinjina girman rundunar mayakan su mana” murmushi tai sannan ta koma gefe ta tsaya.

“Me furcin ki yake nufi?” Inji Jakadiya Jebu, murmushi Innayoh tayi sannan ta nuna mata hanya.

“Kowa ya ci tuwo dani hmm miya yasha. Ni jakar kaza ce sai na shiga sauran kajin suke shi Innayoh inda rai da rabo zaki biya bashin da kika ci” inji Jakadiya,
Dariya Innayoh tayi sannan ta ce mata.
“Haba? Gaske toh ai kafin ayi ɗaran akayi kwanɗi, dan haka ki ajiye a hannun ki wata rana ba mamaki Masha ruwa magirbi” a fusace suka fita da kayan. Murmushi Innayoh tayi sannan ta cigaba da shirya Fulani Aminatu..

**
Masarautar Gobir.

Ana cikin fadanci sunkuyar da kai Shamaki yayi sannan ya ce.
“Allah ya baka nasara, ya kuma taimaka dirken gobir” jinjina kai Sarki Bello yayi yana sauraron Shamaki dan yasan akwai magana a bakin shi.

“Sarki ya amsawa shamaki” inji Sarkin Fada, cikin wani irin shakka da abinda zai fito bakin shi Shamaki ya ce.
“Allah ya huci zuciyar Barden Gobir” “Sarki ya Amsawa Shamaki ya fadi abinda yake bakin shi” Sarkin Fada ya kuma faɗa, ganin Shamaki na gumi yasa Sarki Bello kara jinjina abinda yake son fada ba karamin abu ba ne. Caraf Sarkin Zagi ya fara magana.

Advertisements

“Allah ya baka nasara da nisan kwana, Shamaki ya kasa magana ai abinda yake son fada ba kome bane yaji rad’e rad’en da yake yawo a cikin masarautar nan ne akan Sarkin Gombe zai baka auren Yar shi ne dan ya fidda fulanin da suke cikin masarautan nan” ya fada yana muxurai. Dama shi sarkin Zagi an tanade shi domin sake kowacce irin magana da tayiwa kowa nauyi toh shi ko a gaban waye zai fade ta sai dai idan Sarkin ba adali bane yasaka a zage sarkin Zagi.

Shiru fadar yayi kowa yana jiran aji me Sarki Bello zai ce. Har ya mike ya zai bar fadar aka shiga cewa.
“Gyara kintsi mai martaba zai tashi” a hankali ya mike ya bar fadar, bin bayan shi da ido Shamaki yayi yana sauke ajiyar zuciya, domin abin da bai zata bane. Kallon Sarkin Zagi yayi tare da mai da hankalin shi kan kujerar da Sarki Bello ya mike.

“Barka da arziki” Chiroma ya fadawa Shamaki, girgiza kai yayi.
“Kana tsammani da Iro ne tuni ba a sauke min rawani na ba” murmushi yayi shima ya bar fadar yana dariyar Shamaki.

Haka dayawan dattawan fadar suke mishi barka da arziki, domin kuwa ta tsallake rijiya da baya.


A can turakar Sarki Bello, zama tayi yana cire kayan shi, Sarkin gida yana bakin kofar shiga.
A yau yana jin tsohuwar al’adar shi tana kuma yawo a ranshi. Gyaran murya yayi Sarkin gida ya shigo tare da zubewa kasa.
“Tashi bana son kana min haka.” Tashi yayi ya zauna yana murmushi.
“Allah ya baka nasara.” Kallon juna suka yi kuma suka sake murmushi lokaci guda.
“Ina son shiga dawa” ya fada yana kishingida, a saman gadon shi. Gyara zama sarkin gida yayi yana faɗin.
” Ba dai da rana nan ba? Wani ya bata maka rai ne?” Yayi mishi tambaya biyu lokaci guda, sai kuma ya gyara zama sannan ya cigaba da ce mishi.
“Tsohuwar al’adar ka ko? Amma me zai hana kayi rubutu, ko kuma kayi barci yadda suka zama al’adar ka”

Murmushi yayi yana faɗin,
“Maza a shirya min baka” mikewa Sarkin gida yayi ya fara kokarin fita.
“Karka manta har da kai a tafiyar” juyawa yayi cikin girmamawa ya gyada kai.

Wato Sarki Bello yana da wasu al’adu guda uku, da kowa a cikin Masarautar yake kokarin kiyayye shi. Al’adar shi ta farko ita ce farauta, duk wani fatar dabba daji da aka kawa da ita a cikin masarautan Sarki Bello ya kamo ta, kuma shi daya, tun yana Yaro yake fita dawa. Al’ada ta biyu ba kome bane facce rubutu, Sarki Bello ya kasance hazikin marubuci da yayi shura a nahiyar da babu irin shi, idan wannan dabi’ar ta motsa mishi wanda jama’ar masarautar suke mishi lakabi da al’adun, toh kafin ya zama Sarkin rikon kwarya yana iya zama yayi kwanaki yana rubutu ko kukan tsuntsayen ba a son su gifta ta inda yake sabida yana bawa ƙwaƙwalwar shi damar nazari da rubutu, kuma yana rubutun ne da ajami.

Sai al’ada ta uku, duk ranar Laraba baya zuwa fada ba dan kome ba sai yana ware wannan kwana ɗaya yayi barci da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar shi, Allah ya zubawa Sarki Bello fasahar magana domin matukar zai bude baki yayi magana Insha Allah sai ya sauke hankalin mutane, wannan halin na shi yasa dayawa talakawa suka yi na’am da shi a matsayin sarkin rikon kwarya.

Yan mata dayawa suna kaunar Sarki Bello, tun kafin ya zama sarki Ubangiji ya saka mishi farin jinin yan mata, dan ma idan zai shiga cikin gari ko wani wurin yana yawan rufe fuska shi da rawani, sabida kambun idanu.

Shi da Sarkin Gida Aminai ne na kud da kud, tare suke samartakar su. Wanda sunan shi Jafar, duk da wannan yanayin Sarki Bello bai tab’a zuwa yaki ba, domin yasha fada shi matukar zai samu damar da kowa yake samu toh shi ba zai yi yaki ba, yakan fada cewa.
“Matukar takobi ba zata sauya al’umma ba toh tabbas alkalami zata iya sauya su” wannan maganar ta isa har kunnen mahaifin su tun yana raye, yayi baƙin ciki sosai da ya haifi dan da bai damu da yaki ko zubda jini ba. Koda mahaifin su ya kira shi a irin baiwar da Allah yayi mishi yayiwa mahaifin su magana irin ta hankali sarki Jatau ya kwana da maganar Bello toh ya za ayi su yaki kamar a jinin su yake gudan jinin su duk digon barandami ne. Yaki da nasara suka sani babu ruwan su akan kome zasu yi yaki.

Lokacin da Sarki Jatau ya tashi yaki, aka kashe shi kafin ya mutu sai da ya tuna da kalaman Bello.
“Baba karka manta yakin da za aka tafi bai zama dole ka dawo ba, idan kayi hakuri kuka janye yakin Alummomin da suke iyaka da masarautar mu zasu kwana cikin salama. Idan ka duba yakin nan bai sama dole ayi nasara ba ka duba lamarina” sai da ya gayawa Sarkin yaki abinda Bello ya gaya mishi. Haka lokacin da Ibrahim zai tafi sai da ya Bello ya nusar da shi illar yake yaƙen da suke amma ina su din wasu irin halitta ne masu matukar taurin kai da taurin zuciya, kuma duk abinda suka daka a gaba sai sun same shi.

Wannan kenan a cikin al’adar Sarki Bello,
Shiryawa yayi cikin kayan farauta, sannan ya dauki mayafi ya rufa, daidai shashin sa bayi ne mata da kunyagi suka taru, suna gud’a daidai fitowar shi, gud’a suke har ya fito ya haura saman doki, Sarkin gida ya kama dokin shi ya fara ja, amshi linzamin yayi ya kad’a kan dokin shima da sauri Sarkin gida ya haura na shi suka fita da gudu. Da sauri sarkin gida ya cimma shi. Sannan ya mika mishi jimammiyar fatar barewa. Wanda aka yi rubutu a ajami a cikin shi.
*Ka gaya mishi ya kula*
Kumshe Idanu yayi masu wani irin sheki kamar an diga musu mai a cikin su, ya kuma zaburar dokin shi suka nausa dawa. Tun daga nesa yake shakar kamshin ana bin su, dan haka ya kalli sarkin gida, yayi mishi alamar su kara gudu, haka suka kara gudu sosai wanda har suka b’acewa masu bibiyar su, ta wannan ɓangaren gare abokai guda biyu sun yi zarra domin sun iya sukwa akan dawakai.

Advertisements

Bayan sun shiga cikin dajin, suka daure dawakan su a kasar wata bushiyar loko, suka shiga cikin dajin sai da ya daure jejen sosai yadda babu wanda ya isa ya shiga musu. Tafiya suke amma babu wanda yayiwa dan uwan sa magana sai da suka isa gaban wata korama, wacce take bawa rafin masarautan ruwa.
“Allah ya baka nasara akwai abinda yake damun ka” murmushi yayi sannan ya kalli gaban su inda wata gada take shan ruwa.
“Kaga gada” sarkin gida ya kuma Magana, saka hannu yayi a bakin shi, har tasha ruwa zata wuce sai kuma ta kalle, dan haka ta rab’a gefen su zata wuce.
“Baka yi…” Dake hannun shi Sarki Bello yayi. Shiru yayi har ta wuce juyawa yayi ya ga ta b’ace.
“Ba gadar da kasaba gani ba bace.” Kallon shi yayi kafin ya ce mishi.
“Kamar ya? Ban gane ba?”
“Ita din yar aike ce, ta riga mu shigowa dajin rufe mata kofar da muka yi kasa ba zata iya isa waje har ta bada labari ba!” Inji Sarki Bello,
” Na razana!” Inji Sarkin gida,haka suka ci-gaba da farauta, har suka isa wani kurmi.
“Ranka ya dade ba a shigowa nan domin akwai wata zakanyar da take farautar.” Bai kai aya ba suka ji gurnanin zakin, kallon Sarkin gida yayi. A hankali ya zaro wani guru ( am so sorry da wasu abubuwan da zaku ji ko zaku yi karo da shi labarin it’s was about 200 yrs ago ne wato kamar a ce ancient ko? Toh akwai gurru akwai laya akwai baka, akwai maita akwai kambun idanu, akwai baiwa irin ta da kamar a ce supernatural ban san yadda zan muku bayani ba amma akwai tsohuwar al’adar can da jimawa ayi hakuri da abinda xa a gani kafin musulunci ta shiga cikin al’umma ne labarin amma zamu kiyayye abinda zai tab’a kimar al’adun Hausawa da ita kanta hausar Nagode)

Sarakuna da Yaran su a wannan lokacin, suna shirya kan su ne musamman Gobirawa wanda kaf tarihi an san su da zallar jarumta da iya yaki, yana daukar gurrun ta saka a cikin Aljuhun rigar sarkin gida,. Cikin wani irin zafin nama, ya falla da gudu aikuwa zakanyar tana najin haka ta fito da gudu ta rufa mishi, sai da yayi gudun fitar hankali suna ratsa kwazazxabai, ya samu damar zaro kibiyar shi. Kafin ta cimma shi ya zabga mata harbin da ya ratsa cinyar ta ya maka ta sa kasa, bata iya tashi ba komawa tayi ta kwanta, zuwa yayi kanta ya tsaya, sannan ya ciro takunkumi ya daure ta da shi,. Sai lokacin ya lura da ashe namiji ne.

Shafa gurrun sa yayi tare da dafata, sai gashi a wurin da ya ajiye Sarkin gida.
“An gama farautar yau! Taya kasan da zakanyar?” Sarkin gida ya tambaye shi.
“Amma ranka shi dade kaji dalilin da yasa Sarkin Gombe baka Yar shi!” Da wutsiyar ido ya kalli sarkin gida, sannan ya saka hannu a bakin shi yana girgiza kai.
“A bakin mutane!”
**
Masarautan Gombe.

Shiru Kilishi tayi tana kallon Jakadiya Jebu, kafin ta ce mata.
“A nimo min amintattun bayin masarautan gobir, su zasu min wannan aikin”
“An gama uwa mabada mama koda uba nai sarki ne” inji Jakadiya, da sauri ta fita ta nime wasu bayin biyu suka tafi har inda aka saukar da baki mata aka tawo da wasu mata biyu. Suka isa dakin Kilishi.

A yau Alhamis aka saka Fulani Aminatu a lalle, cikin wani kyakkyawan shiga ta jajjayen karanmiski, wanda ya fidda hakikanin kyanta da kankantar shekarunta. Dake Fulani suma suna da al’adun aure, an yi mata babu iyaka.

Washi gari juma’a bayan sallah asuba aka daura auren Fulani Aminatu da Muhammad Bello Sarkin Gobir, inda aka bada sadaki mafi girma da daraja…

_________________________________
*Hi ya kuke! Alhamdulillahi na gama rabin aikina Insha Allah zaku na jina duk bayan kwana ɗaya! Yau nayi Insha Allah dai friday ku amshi wannan yanayin da farin ciki 😍🔥 ko ya haduwar Fulani da Sarki zai kasance 😍 Nagode sosai keep yourself in this journey ba zaku yi danasanin karantawa ba gaba kadan zaku fi kowa bukatar shi ma kamar yadda muka tafi a Bororoji 🔥*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 15

Advertisement pisode 15……………… Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya buɗe , sannan ya yaye lulluɓin da…
Read More

TARTSATSI 77

Advertisement *Page 77*   **********************   Hafsa tana sharar hawaye ta bud’a motar ta shiga, Sadauki ya bita…
Read More

TARTSATSI 90

Advertisement   *Page 90*   **********************   Hajiya zulai tana k’are sambatun nata, dannawa kulsum kira awaya, jiki…
IDON NAIRA
Read More

IDON NAIRA 17

Advertisement *_Arewabooks@Mamuhgee_* 17 Yamma nayi zuciyarta takasa nutsuwa saidai Kuma ahakan tanajin sassaucin zama anan idan har tana…
INAYAH
Read More

INAYAH 27

Advertisement [10/26, 8:44 PM] Sweet sis: *_27_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Kasa riqe hawayenta tayi suka gangaro Mata ta juya a…