KALLABI 8

KALLABI
KALLABI

Advertisement

Babi Na Bakwai>*

*Godiya da fatan alkhairi son so daga Mai Daraja😍🔥*
Barka da Juma’a#

Masarautar Gobir.

Mai Martaba Sarki Bello, yana tsaye a saman masarautan, wurin an ware shi ne domin shan iskar sarki da iyalin shi ko kuma baiwar da ya yantatta da zama sad’akar shi. Wurin kamar tsarin gidan sama ne amma ba gidan sama bane anyi yar rumfa me ɗauke da wasu kyawawan mayafai, wanda ya kara kawata wurin. Asalin kasar wurin an shimfida mishi wasu irin kilisai tare da wasu irin dardumar yar gata. Sannan an saka wasu matasai tare da wasu abubuwan kamar katifa da ya sha adon sarakunan kasar Hausa.

Sarki Bello zaune cikin wani irin nishadi da nutsuwa, yana kallon tafin hannun shi. Sanye yake da shigar sarakunar dake ranar yau ya kasance juma’a. Murmushi yayi yana kallon tsuntsayen hasbiya da suke dan dandamalin da aka jera wasu kyawawan tukwanen shuka da furanni masu kamshi me dad’i.

A lissafin da aka yi dangane da daurin auren shi yau aka daura, daddin daddawa yanayin Nahiyar ya tabbatar da haka, duk da basu samu labarin daga can ba, dan tafiya ce ta tsawon kwanaki kafin a iso ga raƙumi kenan, ga hangarman doki zai iya kwashe satittka kafin ya iso masarautar. A hankali ya cire rawanin kansa yana kara sauraron tamburan da ake bugawa a masarautan baki ɗaya. Uwa Uba ga tashin algaitu da kakaki, haka kawai yake jin tsigar jikin shi yana mikewa wanda ya haifar da tashin gargasar jikin shi. A hankali ya mike yana me isa yar dandamalin yana kallon yadda ake shiga da fita a cikin harabar masarautan. Tsintar kan shi yayi da nad’e hannu a kirjin shi yana jin wani irin daidaiton nutsuwa na shigar shi. Yana jin wani irin kemawa da kamala na shigar shi na asalin igiyar aure da ya hau kan shi. A hankali ya juya cikin natsuwa ya zura kafar shi a saman kyakyawar takalmin fatar da yake kofar mashigar wurin shan iskar.

Juyawa yayi ya hango rawanin shi, murmushi ya sake sannan ya koma ya dauki rawanin ya daura akan shi, yana me juyawa a sanyayye cikin taku irin na asalin sadaukan maza, irin mazajen da suka san me ake kira da jarumta. Wanda galibi basu damu da nunawa duniya su din wasu bane , sai dai aikin su ya nuna haka.

Tunda ya fara saukowa Sarkin gida ya tare shi da bayanai.
“A bisa yakini da lissafi ana tabbatar da an daura auren mai martaba da Fulani Aminatu, sannan ana saka ran nan da makwani biyu sun iso cikin birnin nan. Sarakunan da suke karkashin jagorancin masarautan nan sun kawo maka ziyara. Akwai kyakkyawar liyafar da aka shirya domin tayaka murna.

Sannan manyan manyan Fadar ka sun baka hutun wata guda domin amarci.”
Ban san yadda zan muku bayanin irin yanayin da mai martaba sarki Bello yake ciki ba amma yana cikin yanayin nan ne da Bature ke kiran shi(romantic moment) shi kan shi murmushin da bai san yanayi ba yake sakewa. Idan da zaka kalli kwayar idanun shi zaka fahimci yana cikin wata mahaukaciyar yanayi ne me matukar daukar hankali. Sai da suka yi tafiya me tsawo har zuwa shashin sa sannan ya tsaya cak yana kallon kofar shashin da aka mallakawa Fulani Aminatu. Kallon Sarkin gida yayi ya nufi kofar, da sauri ya bude mishi ƙatuwar zauren da aka kawata shi da kome kalar zinari da ratsi-ratsin Ja. Sannan an kawata zaurenta (wato a can baya ana kiran Falo da suna Zaure zamu dauki haka a matsayin zauren kawai ba)

A cikin zauren kuwa shirya wasu irin mayafai masu matukar kyau da ɗaukar hankali, wasu shara-shara wanda zai zama hijabi ga mazan da zasu tawo ga Fulani ba sai sun isa cikin zauren ba, daga can zaka iya magana. Kuma zata baka amsa sarki Bello kawai yake da hurimin wuce mayafan kuma tsarin shine haka yace baya son Fulani tayi cuɗanya ga wasu mazan musamman bayi ma.

Advertisements

“Allah ya baka nasara,.tsarin yayi ta gabas maso arewa nan turakar Fulan…” Sarkin gida bai idda maganar shi ba, yaji sautin muryan Mai Martaba ya ce mishi.
“Shiiii!” Sannan ya cigaba da wuce mayafan, bayan ya dakatar da Sarkin Gida ga bin bayan shi.

Yana zuwa ya bude kofar dakin da aka ware domin ita Fulanin. Murmushi yayi sannan ya fito izuwa wurin Sarkin gida. Suka fita har zuwa shashin sa, ya zauna kallon Sarkin gida yayi sannan ya shiga cire rawanin shi.
“Jafar kai da waye kuka yi aikin?” Cikin girmamawa Sarkin gida ya ce mishi.
“Allah ya baka nasara, da nisan kwana ni da wasu bayi biyar ne” saka hannu yayi a kunnen shi yana me kishingida a inda ya zauna. Jijjiga kunnen shi yayi.
“An gama ranka shi dade, an cika umarni.”

Mikewa Sarkin gida yayi da sauri ya fita daga cikin shashin Mai Martaba, ya nufi Bai wato gidan bayi. Yana shiga ya kira bayin nan maza da suka yi aiki ya musu magana, cikin matukar farin ciki suka zube a gaban shi suna masu godiya da sakawa auren albarka. Anan suka tattara iyalan su, suka bar masarautan bayan Sarkin gida ya basu dawakai da guziri masu yawa ya ce.
“Sarki Bello yayi muku afuwa, kuma ya baku damar ku tafi kuyi rawa inda kuke so, amma kar ya kuma ganin fuskar ku a cikin masarautan wannan shine daidaiton adalcin da ya muku”

“Mun gode kuma mun yi na’am da wannan halin girman da yayi mana, a isar mana da sakon godiya, Allah ya albarkaci rayuwar shi da Fulani Aminatu.” Sannan suka bar masarautan ta kofar Bai, wato kofar bayi nan.

Sarki Bello ya dauki matakin haka ne, domin wasu dalilai irin ta gidan sarautar su, amma idan da lokaci yayi haka zai bayyana kan shi.

**
Masarautan Gombe.

Tun kafin a daura auren, aka turo kiran Innayoh wacce ta farka tun karfe biyu na asuba tana shirya kayan Fulani Aminatu, da sauri ta fita bayan ta rufe kofar sosai ta nufi shashin Mai Martaba Sarkin Gombe. A bakin kofar shi ta same shi yana tsaye shi da Babayo.
“Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, barka da dare”
“Innayoh ba zan gaji da baki amanar Aminatu ba, idan wani abun farin ciki ya faru kece zan yi alfahari dake, kuma kamar muradin mahaifiyar ta ce, idan akasin haka ya faru kamar faduwar ki ce, ga Aminatu nan tarbiyyar ki ce nan da wasu sa’o’in za a daura auren ta da Sarkin Gobir, kuma an shirya kome na tafiyar ku, kayan ta ma sun yi gaba. Kar naji kar na gani, idan ƙaddara ta fado bata da inda ya wuce masarautar da yafi wannan.”

Wani irin kwalla ne ya cikawa Innayoh idanun ta, iya soyayyar da zai nunawa yar shi ita ce koda wani abu zai biyo baya bata da inda ya wuce nan lallai Fulani Aminatu tayi dacen Uba na gari.
“Insha Allah babu abinda zai faru da zai kawo ta ma sai alkhairi”

“Maza ki shirya ta akan lokaci ana daura auren zaku dauki hanya” ya fada tare da barin wurin, sai da ta daina hango hasken fitilar shi, sannan ta mike ta koma shashin Fulani Aminatu. Suka ci-gaba da shirin su.

Kamar yadda ka tsara haka ce ta faru, ana daura auren da manyan manyan akwatin gwala-gwalai da suturanta masu yawan gaske daga masarautan elkaname aka kawo mata, sannan aka akwai wanda aka Kawo mata daya masarautan gobir na auren tare da manyan akwatin nan zinarai. Na auren ta wanda lokacin da aka shigar da shi cikin gida abinda matan mai Martaba suka fada shine.
“Amma dai sayar da Fulani Aminatu mai Martaba yayi ko? Wannan in ba sayar da ita yayi ba ina za a kai wannan kayan me mugun yawan gaske sai kace ita ce tafi kowa.”

Sun manta akan ta aka ya fara aurar da Y’a, kuma ya fara bikin shi na farko a cikin masarautan, dan haka ya saka aka daura duk kayan a kai mata kayan ta tayi ta sakawa tana ado dashi. Sannan kafin su bar masarautan yayiwa Innayoh Alkhairi me tarin yawa, aka bata bayi kowa daki sai da suka bata bayi, lokacin da aka kawo na dakin Kilishi kiri kiri Innayoh taki amsar su, da sauri Jakadiya Jebu ta koma tana me gayawa Kilishi abinda Innayoh ta ce.
“Ki mai da su bama bukatar su, muna da wadatattun bayin da zasu mana kome.” Lumshe jajjayen idanunta Kilishi tayi ta mike tare da gyara mayafin ta, ta fito harabar masarautan. Tana fitowa bata tsaya ba ta tsinke Innayoh da mari wacce take rike da Fulani Aminatu zata shiga leken dokin da aka kawo mata daga masarautan Yola.
“Tasss” sautin marin ya karade harabar masarautan. Rike hannun Innayoh Aminatu tayi cikin tsananin tsoro tare da kifa kanta a kadadar Innayoh.

“Fulani kilishi a iya yanzun baki da iko dani ko Aminatu, sabida muna ƙarƙashin mulkin masarautan Gobir ce, yin haka kamar lakatar rigima ce, dan haka ki mai da bayin ki bama bukata. Idan wani abu ya faru ba iya su zai tab’a ba, hatta ke da kike da mafarkin goben ki. Idan kuma aka samu akasin haka matar sarki ce fa” ta fada maganar cikin wani irin dakiya. Sauke hannu Kilishi tayi tana kallon ta.

Advertisements

Tabbas tsoro ya danne kashin bayanta, ba zata iya aikata wani abu ba, dan haka ta juya ta bar harabar da bayin ta. Juyawa tai tana kallon Innayoh da itama ta juya tana kallon ta. Juyawa Innayoh tayi ta shiga cikin keken sabida yadda Aminatu take kara riko hannun ta. Suna shiga aka fara busa algaitu tare da barin masarautar.

Riko hannun Aminatu tai tana faɗin.
“Daga yau babu tsoro babu shakkar kowa Insha Allah kina inda za a baki kariya da kulawa. Ba zaki kuma kuka ba sai dai ki ga wasu nayi amma ke, Ya kare a wurin ki”

Yadda Innayoh take mata magana da yadda take kara nuna mata wasu abubuwan har barci ya dauke.


Kasa zama Kilishi tayi tana kallon bayinta, kafin ta juya tana me fita daga cikin zauren ta, ta nufi katangar da yayi iyaka ga masarautar. Zuwa waje tana hango yadda ake tafiya da Fulani Aminatu. Wani irin bakin cikin ne ya cika mata rai tana tuna abinda hare ta gaya mata.

“Matukar ta shiga masarautar Gobir ba zaki iya mata kome ba, karshe sai dai ki rasa duk wani damarki. Tauraron ta yana haduwa da na Sarkin Gobir babu wanda ya isa ya iya samun gallaba akan su sai ƙaddara ita kuma wannan ƙaddaran zata zo ne kamar yadda guguwar yashi take tawowa daga tsakiyar sahara. Karki sake amon ki ya cigaba da kewaye ga Fulani Aminatu. Idan kuma haka ya faru tabbas da walakin goro… Domin Ubanta zai iya shirin yaki domin d’igar kwayar hawayen ta d’aya tal”

Dunkule hannun tayi tana jin wasu irin kwalla na zuba mata, tabbas ta so daukar fansa akan Yarinyar sannan abin da ya kuma d’aga mata hankali yadda hare ya ce.
“Yarinyar zata rayu cikin aminci da salama, zata yi farin ciki a farko a tsakiyar zata fuskanci rayuwarta na tsawon lokacin da ban san adadin shi ba. Kuka da kukan wasu zubda jini zai yawaita bayan shekarun rayuwar ta. Amma zata dawwama cikin farin ciki, kin ga yanayin da yake cikin ƙwaryan jinin! Kinga bakin duhun da ya ratsa hasken nan guguwar ƙaddara kenan, wannan hasken ita ce zata biyo bayan kome a wannan gefen matukar ka tunkaro ta domin cutarwa ba mamaki kanka ya sauka daga gangan jikin ka domin”

“Hare nayi farin cikin fuskar ta shekarun rayuwar ta, kuma zan yi farin ciki mara misaltawa domin wannan abin farin ciki ne ya same ni bana fatar Aminatu ta rayu cikin salama.” Ta fada tana dariya.
“Tana da uwa a gefenta, ba zata yi kunci a fili ba, amma a cikin ta zata yi bakin ciki kowani mutum yana tafiya ne bisa jagorancin ƙaddaran sa, amma ba makawa zata isa inda baki zata ba akwai tafiya me nisa da zai cimma kafin wannan lokacin karki sake a samar da fitilar da zata isar da ita ga ƙaddaran ta. Yawan adawar ki yawwan nasarar ta.”

___________________________

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 85

Advertisement   *Page 85*   **********************   Aikam Hajiya tayita sababi, bakinta yana kunfa, saboda tsabar masifa, dak’yar…
Read More

TARTSATSI 99

Advertisement *Page 99* ********************** Acikin farin ciki ta shige gida, Kai tsaye ta shige d’akin su, ta dannawa…
INAYAH
Read More

INAYAH 44

Advertisement _44_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Inayah da kafafuwanta suka kasa riqeta sbd kukan datake Mai tsanani Mara sauti ahankali ta…