KALLABI 9

KALLABI
KALLABI

Advertisement

*GAISUWAR WANNAN SHAFIN NAKU NE YAN KALLABI LOVER FANS AKWAI KAUNA ME KARFI A TSAKANIN MU DA KU A CIGABA DA TAFIYA A HANKALI 🥰😍🤩😜*

“Baffa’m!!” Shima ya fada tare da kallon Innayoh a rude, dauke kai tayi dan kallon tuhumar da yake mata, tashi yayi a hankali ya kalli Fulani Aminatu da take kallon shi da Idanunta masu shirin kawo ruwa.

“Toh me yasa…?” Sai kuma yayi shiru, yana kallon ta, kafin yayi wani yake, ya juya ya bar zauren har zai rufe kofar ta ce mishi.
“Baffa’m!” Juyawa yayi yana kallon ta.
“Ka bar min dan dalago ya fita” tsintar kan shi yayi da yake, sannan ya ce mata.
“Za’a kawo miki shi” da sauri ya fita yana dafe kirjin shi.
*Haba Bello kai fa sarki, ita kuma yarinya ce*
Shashi na zuciyar shi ya bashi amsa, jinjina kai yayi yana kara yarda da abinda zuciyar shi ta gaya mishi.

**
“Auren shi ne karshen burin ku, ba zaku tab’a cimma shi ba.” Dan k’ank’anin mutum kamar yaro dan shekara uku ya gaya musu haka.

“Jarmai ya zamu yi?” Suka kuma tambayar shi a karo na biyu, zana kasa yayi tare da kallon su, sannan ya ce musu.
“Ku fita ku bar ni da wancan da wannan” ya nuna mutane biyu da kan su yake rufe da mayafi dariya yayi da yar muryar shi kamar na gyare ya ce musu.
“Kuna tsammanin zaku iya ne? Ko a tunanin ku Bello zai fadi ne kai tsaye? Hmm” ya faɗa yana watsa wasu kananan duwatsu saman kan yashi.

“Zaka yi mulki amma sai ka samo irin Aminatu, ko ka amshe ta da karfi ko kuma ka yi ta zaman jiran bayyanar ta” ya fada a karo na uku.
A matukar firgice suka kalli junan su, kafin suka kalle shi dan ya fato su yayi da kananun yatsun hannun shi ya ce musu.
“Kuna da zabi dama uku amma biyu zaku dauka.” Kasa yayi da murya sosai me kama da ta gyare yana magana baki daya jikin su rawa yake, kafin ya bude muryan shi.
“Wane kuka zab’a? Zaku jira amma kafin nan zaman taurari guda biyu wuri guda zai iya cika ya tumbatsa har ya fitar da wani irin haske, shi hasken zai kuma dakatar da ku dan haka a yanzu baku da hurumin dakatar da su, amma akwai shekaru masu zuwa”

“Kiru me yasa sai mun jira?” Matar ta fada ƙasa ƙasa.
“Idan kuka fito da burin ku zai iya kararr da ku, kuje bayan shekara biyar ku dawo ina nan ina jiran ku! Kuma kafin nan gyara muku kome sai dai damar haka, amma ku sani ku nisanta kan ku ga amayar da adawa ku musamma’n ma kai da baka da hakuri” gyada kai yayi har zasu mike, sai namijin ya ce mishi.
“Kace idan ba Fulani Aminatu sai dai na jira?” Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Idan ka kuskura ka tun kare ta, mutuwa yayi domin dalilin da ya saka aka had’a ta da Bello? Hmm ka kiyaye” ya fada yana dariya, a rude matar ta kalle shi.
“Kamar ya hmm?”
“Sabida akan ta zai fara? Akan ta zai fidda kan shi, idan har kuka fito da shi ba zai yi muku dadi ba, amma idan har kuka mishi kisar mun muke fa? Bana ce kuyi hakuri a jira lokaci ba”
Gyada mishi kai suka yi, sannan suka fita daga kokon ramin. Suna fita ya zubawa kasar gaban shi idanu yadda ya rine da jini, rintsa idanu yayi yana wasu yan surutai, jini ne ya cigaba da lullebe tiren, sautin karan takoba hadi da kukan mutane yasa shi buɗe idanun shi. Zanen hoton fuskar mace ce nan ya shiga zanawa sai da ya jima kafin sunan Fulani Aminatu ya bayyana a kan kasar.

“Tabbas ita ce! Ita ce!! Ita ce!” Ya fada yana zare idanun shi. Buga kasar ya kuma da sandar hannun shi, wani irin duhu ya mamaye yashin, rintsa idanun shi yayi na wani lokaci kafin ya bude sakamakon dumin da yaji a hancin shi na alamar ruwa, shafawa yayi ya ga jini ne, sake buga kasa yayi da yar ƙaramar jaririyar muryan shi ya ce.
“Idan ba ita ba ce waye?” Ya fada da ƙarfi. Sannan ya bude wani tunkuyar da yake gaban shi. Ya zuba idanun shi cikin tunkuyar kafin ya ya rufe, tashi yayi a hankali ya nufi wata ƙatuwar randa ya hau kai, sannan ya leka a hankali yana kallon cikin tukunyar. Wani irin farin hayaki yake, kafin ya kurawa hayakin idanu. Wani irin sauti yake fita a cikin tukunyar, can kuwa da ya matsa da kallon sai ga wani irin hayaki me sufar zaki ya wani irin yunkurowa kamar zai cafke shi, mugun razana yayi sai da ya tintsira da sauri ya tashi yana me kartawa a guje. Jikin shi yana rawa zunzurutun tsoro. Komawa yayi wurin kasar ya sake ganin kasar shi tana fitar da wannan sufar Zakin a jikin zanen hoton Fuskar Fulani Aminatu. Dafe wuyar shi yayi tare da zaro idanun shi. Kafin kace me jini ya fara zuba ta hanci shi da bakin shi, haka yayi ta shure-shure har ya mutu.

Jinin da ya fita ta hancin shi da bakin shi suka yi ta gaggarawa cikin yashin, ya shige ya b’ata tass a cikin shi.

**
Kaiwa da komowa yake, Galadima da waziri sun yi cirko cirko. Tsayawa yayi yana kallon su. Duk da yana dame amma bai hana shi tsayawa ya kalle su ba.
“Baffa’m!”
Ya furta, cikin jimamin sunan Waziri Zakaria ya kalle shi kafin ya ce mishi.
“Yanzun don Allah Fulani Aminatun ce ta kiraka da Baffa’m?” Zama yayi a kujeran shi, sannan ya kalli Zakaria ya ce mishi.
“Jeka”
“Toh Baffa’m!” Bude Idanu yayi, kafin ya mai da ya lumshe, yana jin kamar yadda ta kira shi. Sam sunan bai mishi ba Waziri yana fita ya tashi ya zauna yana kallon Galadima yadda ya tsare shi da idanun ya shi zubewa a gaban Sarki Bello.
“Takawar ka lafiya! Matashin Sarkin da babu irin shi, akwai wani abu da na gano jiya zuwa yau” a hankali yayi kasa da murya. D’ago kai yayi yana kallon sarki Bello. Mikewa suka yi, suka shiga takawa har saman wurin shan iskar shi. Anan Galadima ya shiga mishi bayanin abinda aka gaya mishi akan Fulani Aminatu. Baki daya sai da ya firgita sosai.
“Wannan shine dalilin aurar da ita kenan?”

Advertisements

Girgiza kai Galadima yayi tare da kallon shi, idanun shi ya cika da kwalla. Ya ce mishi,
“Wallahi ban sani ba, amma tabbas akwai hatsari masu yawan gaske a rayuwar ta, ba iya ita ɗaya ba hatta masarautan nan yana fuskar ta hatsarin matsalar bamu san ta inda zata fara fuskar ta rayuwar ta ba. Sai dai abinda nake hasashen indai zata kasance haka toh dole.”

“A’a! A’a!! a’a! Ba zan iya ba, ba kuma xan iya ba, ba zan bada ita ba. Idan na fahimta itace ƙaddara ta zab’a?” Ya fada yana jin wani irin yanayi kamar zai yi kukan tausayin ta.

“Galadima na yarda da kai, duk da ina tsoron cin amana. Galadima ka boye tauraron Aminatu. Idan ya kasance nawa tauraron zai mutu ka rufe nata, ina jin kaifin jinin ta a kaina.” Ya fada yana me juyar da bayan shi, dan baya son Galadima ya ga saukar kwallar da yake zuba daga idanun shi.
“Mai Martaba!”
“Jika kawai” ya fada bai juya ba, shi kan shi, yana jin wani irin abu a ran shi, domin jiya baki daya bai yi barci ba sakamakon mafarkin da yayi na yakin da ake. Dake shima kan shi Hatsabibin kan shi ne yana farkawa ya shiga bincike da dube dube, anan ya gano asalin abinda yake bibiyar Aminatu.

Sai dai har asuba bai iya barci ba, kuma bai rintsa ba, sai asuba bayan ya tafi masallaci ya dawo ya samu barci. Shi yasa ya kudiri Aniyar sanar da mai martaba gaskiyar abinda yake shirin faruwa.

Haka yanayin ya cigaba da tafiya, har tsawon kwanaki. Kafin Galadima ya kuma samun shi da maganar.
“Allah ya baka nasara an rufe tauraron ta, sannan” shiru yayi ya rasa yadda zai iya gaya mishi.
“Ina jin ka Kawu, kome ka gaya min zan dauka”
“Na mai da kome nata na rufe, sai dai ban sani ba zaren ku zata yi tsawo da ita amma ba makawa cikin gidan nan za a iya samu wani labari domin ina da yakinin akwai wanda yasan wacece Ita”

Kurawa Galadima ido yayi, kafin ta ce mishi.
“Sai na datse makoshin kowaye! Tunda ka rufe shi kenan” daga haka ya juya ya cigaba da rubutun shi.
“Toh Baffa’m” d’ago kai yayi, wani irin yake yayi sannan ya cigaba aikin shi bai kuma magana ba.

**
Bayan kwana biyu.

Yau ya kasance laraba, fitowa tayi tana kallon gidan tun zuwan su bata tab’a fitowa ba, dake lokacin rana yayi zafi tsakanin sha biyu zuwa daya ne, baka ka ganin motsin kowa. Gyara zaman mayafin ta tayi tana rike da zomon ta, tsalle yayi garin sauka ya ja mata tsagiyarta.(beads ne ko nace jigida, amma a can an fi kiran shi da tsagiya sabida suna kara kamar duwatsun ruwa suke) aikuwa sai ga zaren ya tsinke ita kanta bata sani ba, shi kuwa dan dalago shashin Sarki Bello ya nufa, dake ta bayan gidan suke ba ta gaban gidan ba, dan haka babu wanda ya sani, wurin shan iskar karamar lambun ce, me kyan gaske wurin ya nufa ita kuma bata lura ba ta wuce ta wata yar karamar kofa ta shige shashin Sarki Bello.

Tafiya take har ta fito da kofar da masu tsaro suke.
“Baku ga dan dalago ba?” Da sauri suka juya suna kallon ta, cikin girmamawa suka gaishe ta.
“Yana ciki amma yana barci baya son hayaniya” gyada musu kai tayi, suka nuna mata kofar Mai Martaba, su a tunanin su shi take nima. Tattara mayafinta tayi ta shiga tana kiran shi a hankali.
Yana kwance akan wani farin buzu, yayi matashi da wani matashi me ɗauke fatar zaki. A hankali ta kara tana kallon shi, hango tawada tayi ta zauna a dauki alkalami, kallon shi tayi kuma sai ta fasa kawai ta dangwala da yatsar ta, ta nufi goshinsa domin ta dangwala mishi, ya rike hannun ta. Wani zaro idanu tayi tare da toshe bakin ta.

“Tashi ki koma can ki zauna!” Girgiza kai tayi ta rarrafe, tsagiyarta yana sauka yana wani irin kara, bude idanun shi yayi ya zuba mata idanu ganin yadda take rarrafen sai da murmushin ya so subuce mishi. Can kamar an ce ta juyo, lumshe idanun yayi kamar me barcin gaske.

Juyawa tayi ya bude idanu, jinjina Yaranta ta kawai, kuma da bai ji shigowar ta ba, haka zata zana mishi fuska da tawada. Gyara kwanciyar shi yayi, ya cigaba da barcin shi duk da barci rabi da rabi ne, domin yana jin yadda take barna, sai ya bude Idanu ya ganta zaune. Kamar ba ita ba tsabar rashin jin magana.

Tana zaune a wurin har itama barci ya dauke ta, tashi yayi yana kallon ta, kwashe tsagiyr yayi ya saka a cikin wata yar akwati ya ajiye, sannan ya karasa inda yake ya dauke ta cak, ya wuce da ita turakar shi (😏fassaru ba wani abu zai mata ba kawai ya kai ta ne domin tai barci yawwan dan nasan halin ku da ririta al’amari)

Advertisements

Sannan ya fita ya shirya, ya nufi masallaci, bai dawo ba sai yamma ya manta da ita ma baki daya sai da ya shigo ya samu taci Uban turakar domin hatta shimfidar turakar a kasa yake, litattafan da yake rubutawa ya samu an yi ɗai-ɗai da su, kamar ya kurma Uban ihu yake ji sabida barna kuwa tawadar shi ta rubutu, anyi wasa da da ita. Bata ci kome ba a dakin amma kuma tayi mishi barnar da ko a tarihi bai tab’a jin wanda yayi irin shi ba, kallon Sarkin gida yayi yana kallon gidan.
“Ka kirawo min Innayoh”
“Allah ya baka nasara, wannan ne karo na farko ayi hakuri idan tayi karo na biyu sai a kira ta.” Kwafa yayi, domin a cikin litattafan shi akwai wani labarin da yake masifar kauna me sunan Soyayyar kusurwa daya, labarin Sarkin dodonin da Zainatu. Wannan labarin kaf labarun sarki Bello babu kamar shi domin ita ce bakandamiyar shi. Amma yarinyar nan ta zo ta wargaza mishi kome, dam haka shi da Sarkin Gida suka gyara ko ina tsaf, sannan ya zauna yana mai da numfashi.

… Ita kuwa Fulani Aminatu da ta ga irin barnar da tayi da sauri ta fita daga shashin ta nufi shashin ta, tana zare ido, bata ga dan dalago ba haka ta d’aga musu hankali. Aka fita niman dan dalago,can aka samu shi a cikin lambu yana fidda jini ta hanci ta baki. Wani irin ihu tayi tana faduwa a kasa ta dauke shi.
“Wayyo Allah na,Wayyo Allah na,Wayyo dan dalago Wayyo Allah na”. Ta fada da wani irin kuka tana rungume shi, sosai ji take kamar wani dan uwanta ne.
“Me ya same shi?” Inji Innayoh da ta ji kukan ta fito a razane, tana zaune ta saka shi akan cinyarta tana kuka kamar me.
“Lafiya?” Sarkin gida ya iso wurin su.
“Zomon Fulani ne wani abu ya same shi” d’aga zomon yayi ya kalla da kyau.
“Ku matsa akwai mugun dabba a wurin shi ya tab’a shi” ya fada ja bada kowa yayi, kamar sarkin gida ya san me zai faru ya sa kowa ya matsa, aikuwa sai ga wani irin bakin maciji yana tuttukowa kamar ana turo shi, ihun bayi mata ne ya saka Fulani Aminatu d’ago kai tana kallon bakin macijiin nan da ya fasa kan shi kamar faranti babba. Yana zaro harshen shi jajjur da shi.
“Fu…la…ni!!!” Inji Innayoh, da tsabar kidima da tsoro, ya saka bata iya magana ba, sai kiran sunan Fulani da tayi a rarrabe.

Kasa motsi ita kanta Fulani Aminatu tayi domin baki daya ta suma. Ihun da ake ya saka shi fara kokarin kai fashen yawu, yadda ya fesa yawun babu wanda ya ga zuwan shi sai dai sun gan shi durkushe da rigar saki a gaban Fulani Aminatu, yana kallon yadda ta kafe a wurin. Ciro wukar da yake kugun shi yayi a fusace ya saka wuyar macijin, sannan ta juya ga Fulani da take kamar an dasata zaune.

Ya saka hannu ya dauke ta, sannan ya mike.
“Ka kai gidan Galadima kace ina niman shi” sannan ya shiga ta shashin Fulani Aminatu ya kwantar da ita akan Kilishin da yake zauren ta.
“Ki saka idanu akan ta.”
“TOH ranka shi dade!” Shiru yayi yana kallon hawayen da ya bushe a saman fuskar ta. Tashi yayi ya nufi wurin shan iskar shi, nan ya samu Galadima. Zama yayi tare da kallon kasa.
“Allah ya huci zuciyar ka. Insha Allah babu abinda zai faru ga Fulani Aminatu!”
“Sakon daga ina ne?” Ya kalli Galadima bayan ya tambaye shi.
“Daga wajen masarautan ne, amma a cikin masarautan aka idda aikin.” Ya bashi amsa.
“Ita yarinayar meye na farmakarta?” Ya tambaya da ƙarfi.
“Sabida yanayin da aka tabbatar akan ta.”
Wani irin dariyar takaici ya kama yi kafin ya ce.
” Kafin gobe a fidda min me aikin ko na dauki salon da bana son dauka….
__________________________

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 26

Advertisement 26_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Ku jirani a motar Bara na sauya Kaya muje Nima zan gaisa da iyayen na…
KALLABI
Read More

KALLABI 47

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA BAKWAI Haɗe hannun shi yayi yana kallon ta, cikin murmushi ya saka hannun…
KALLABI
Read More

KALLABI 35

Advertisement BABI NA TALATIN DA BIYAR Barkindo Yazidu, Allah bai daura mishi kaunar wani hidima na mulki ba,…
Read More

TARTSATSI 86

Advertisement *Page 86*   **********************   Umma da Su Umaima, suna sashen Aunty amarya tareda su Gwaggo, da…
IDON NAIRA
Read More

IDON NAIRA 35

Advertisement *_Arewabook@Mamuhgee_* 35 Umma dake Jan numfashi ta qurawa Amal idanuwa tana sake shiga tashin hankali idan har…