Lu’u Lu’u 47

Advertisement

_Bismillahir rahamanir rahim_

*47*

 

 

Mi’kewa tayi da azama ta fita a d’akin, bafaden dake k’ofar shiga d’akinta ta kalla tace “A sanar da taron gaggawa ga duka masu ruwa da tsaki na masarautar nan, sannan a had’a min kan yan jarida.”

Da girmamawa ya sunkuya yana karb’ar umarnin na ta, wucewa yayi ita ma ta nufi masaukin sarki Abdallah, tana zuwa kai tsaye suka barta ta shiga, ta sameshi zaune a kishingid’e yana danna carbi, zaune tayi tana fad’in” Barka da hutawa yallab’ai.”.

Murmushi ya sakar mata yace” Gimbiyata, ke ce warhaka?”

Jinjina kai tayi ta kalleshi tace” Yallab’ai, mun yi magana da yallab’ai Umad yanzu, kuma ya sanar da ni wasu abubuwa, shi ne nake neman shawararka a kai?”

Wani k’ayataccen murmushi ya saki yace” Ki zartar kawai, nasan komai da ya fad’a miki, kiyi abinda ya fad’a ba matsala.”

Da mamaki tace” Yallab’ai, wai komai yana sanar da kai ne?”

Advertisements

Jinjina mata kai yayi a hankali yace” Ya kan sanar dani wani abun dan ya nemi shawarata, yaron kirki ne, shiyasa na fi kowa farin cikin kasancewarshi mijinki.”

Cikin zolaya ya d’an harareta yace” Duk da dai ma na fahimci kin fara son shi, amma dai ina kan bakana ni ma akan son ki.”

Dariya tayi ta mik’e tsye tana cewa” Ni ban ce ina son shi ba, haka kawai za’a lak’a min.”

Fita tayi a d’akin ya bita da kallo yana dariya, girgiza kai yayi yace” Allah ya daidaita tsakaninku, Allah wanzar da farin ciki a cikin rayuwarku.”

Tana fita wani bafaden ta sa ya nemo mata Adah wanda jimamin mutuwar sarki yasa ko fadar ya daina zuwa yana zaune gida, da girmamawa ya amsa kiranta ya zo, gaba tayi sannan tace” Ka jagoranci ne zuwa ga Dhurani.”

Da ladabi yace” An gama ranki shi dad’e.”

Da azama ya shiga gabanta fadawa biyu a bayanta suna take mata baya, a haka sukayi tafiya mai tazara zuwa kurkukun sabah, kallon wurin ta dinga yi saboda yanda ta ga wurin kuma dama bata tab’a zuwa ba sai yau d’in.

Har saida suka isa inda Dhurani yake, yana ganinsu shi ma ya taso daga zaunen da yake ya tsaya suna kallon juna, tabe baki tayi tace “Wasu mutanen ba sa da sa’a a rayuwarsu, kamar dai kai d’in nan, da kana da sa’a da kayi nadama aka abinda ka aikata, amma sam babu wannan har yanzu a tsarin rayuwarka, hakan yasa ni Ayam Musail na yanke maka hukuncin d’aurin rai da rai a gidan kurkukun sabah, zaka dawwama a nan ba mataimaki, ba abokin hira ga kuma aiki mai tsanani, sannan ba’a baka damar ganawa da iyalinka ba ko da k’arshen shekara ne.”

Juyawa tayi zata wuce sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace” Mutuwarka ba zata zama da sauk’i ba, zan iya sa wa a cire min kan ka a yanzun nan, amma hakan zai zama sauk’i da hutu a gareka, ni kuma ba haka nake da buk’ata ba.”

Wani malalacin murmushi tayi tace” Ka ji dad’in sabuwar rayuwarka.”

Cikin b’acin rai Dhurani yace” Ke shashasha dak’ik’iya, kin d’auka zan tabbata a nan ne kamar yanda kike zato? To ba zan jima a nan ba, idan na so gobe goben nan zan bar nan, kuma ki zuba ido ki gani, ke ma saina ga bayanki kamar yanda na ga na mahaifinki.”

Kallon Adah tayi wani kallo dake nuni da sak’o ta aika masa, da sauri Adah ya zaro ido yana mamakin yanda ta bashi umarni kamar yanda mahaifinta ke yi lokuta da dama, wanda hakan har ya zama zaurace tsakaninsu, lallai *jini ya fi ruwa kauri*, da sauri ya kalli mai tsaron k’ofar yace “A bud’e.”

Advertisements

Da sauri bafaden ya bud’e k’ofar hakan yasa Ayam sunkuyawa kad’an ta shiga ciki, saida ta tsaya gaban Dhurani suna kallon juna, siriri kuma dogon hannunta ta d’aga ta wanka masa marin daya saka shi jin d’ummm! Hadiman da suke tare da ita a lokacin da Adah duk saida mamaki ya kamasu da kuma tsoro, duk girman Dhurani amma ta mareshi har saida ya d’an rank’wafa, rai b’ace tace “Ka sani da ina tare da iyayena tun a waccen lokacin, da baka yi abinda ka yi ba, amma da kayi abinda kayi ina mai maka albishir cewa zan fara nuna baiwata a kan ka, da izinin Allah marin nan da na maka sai ka fara zab’a da ma kasheka na yi da marin nan, ina kuma jiran ganin matakin da zaka d’auka saboda hakan, wawa dadk’ik’i.”

Tana fad’a ta juyo a hassale ta fice a kurkukun su Adah suka bi bayanta da sauri, suna fitowa daga wurin ake shaida mata an taru ita kawai ake jira.

Tana shiga babban falon ta samu yan jarida zazzaune, masu micro da cam茅ra da k’aramin littafi da biro duk kowa jiran d’aukar labari yake, ga kuma dattawa kuma masu fad’a aji na Khazira zazzaune suma a kujeru na alfarma.

Shigowarta yasa kowa ya mik’e ya gaisheta kamar yanda ake ma sarakuna, duk da ta aje mulkin amma dai har yanzu a matsayin sarauniya suke kallonta, amsa musu tayi ita ma da martabawa ta d’an adam sannan ta zauna kan kujerar da aka ware dan ita, a bayanta Adah ya tsaya yana zazzare ido ga duk wani da zai iya kawo wargi gareta.

Cikin nutsuwa da k’warewa tace “Ba zan tsawaita abinda zan fad’a ba saboda nasan kowa na uzurin gabanshi na datse masa, abinda ya sa na taraku ba komai ba ne sai wata shawara dana yanke, ba kula ni kad’ai na yanketa ba, saida na shawarci magabata na, zan bar garin nan yau, shiyasa na ga bai dace na tafi ba tare dana bar sarki a bayana ba, dan haka zai iya haifar da wani tsurmutsutsun, abisa haka na yanke hukunci d’ora *Adah* a matsayin sarki *Khaizra*, sarkin da zai mulki gaba d’aya k’asar *Texanda*.”

Gyara zama tayi sannan ta had’e fuska tace” Idan kula akwai wanda bai amince ba ya d’aga hannunsa.”

Tuni yan jarida suka fara watsawa dan wasu kai tsaye suke fitar da labarin, Adah dake tsaye bayanta kallonta yayi ba ko k’yabtawa, sai kawai ya fashe da kuka ya durk’usa a bayanta tana kuka, dayawa daga cikin datawan Khazira hakan ya musu dad’i, dan haka mafi yawansu suka saki murmushin daya bayyanar da soyayyarsu ga Ayam abisa shawarar data yanke, wanda kula bai musu dad’i ba basu iya d’aga ko da idonsu ba bare su ce uffan, dan idonta na firgitasu kamar yanda suke firgita sauran marasa gaskiyar.

Haka ma a labarai duk wanda ya ga hakan dayawa ya musu dad’i, dayawa kuma bai musu ba wannan kuma abu ne da dama dole a same shi, ba kowa zai ce yana son ka ba, saidai iyalin Adah hakan ya musu dad’i fiye da kima, inda suke hango kansu a matsayin masu mulki Khazira a yau? Lallai duniya sabuwa.

Ayam dake shirin mik’ewa kan kujerar ta ji Adah yace “Alhamdulillah, Allah idan har mulkin nan alkairi a gareni Allah ka tabbatar, idan kuma sharri ne gareni ya Allah ka karb’i rayuwata yanzu yanzun nan kafin na zalinci wani saboda ikona.”

Hakan ya mata dad’i har ta sunkuya kusa da shi tace “Hakan na nufin ka musulunta kai ma?”

Jinjina mata kai yayi yace “Tare da yallab’ai sarki muka musulunta, kuma na musuluntar da iyalina ma.”

Murmushi tayi tace “Allah abun godiya, ka nemi taimakon Allah wajen tafiyar da mulkin nan abisa gaskiya da amana, sannan ka yi k’ok’arin sauke hakk’in talakawanka, sannan ka d’orasu akan turban data dace.”

Dafa kafad’arshi tayi tace “Allah ya tayaka rik’o, ina maka fatan alkairi.”

Jinjina kai yayi yace “Nagode ranki shi dad’e, kin min hallaci a rayuwa, duk da ina jin dad’in kasancewata sarkin yak’i na mahaifinki, amma dai kin d’aukaka darajata a cikin dubunnai, da yardar Allah ba zan manta da haka ba, kuma zaku ci gaba da kasancewa a cikin martabarku kamar yanda kuke a yanzu, zan nuna muku nima d’an halak ne.”

Fad’ad’a murmushinta tayi sannan ta mik’e da sauri ta d’agawa yan jaridu da dattawan hannu sannan ta fita a falon, kai tsaye d’akinta ta koma inda garin Khazira ya d’auki haramar sabon labarai.

Tunda abun nan ya faru basu had’u da Juman ba, har ta kwanta bacci cike da kewar mijinta.

*Tsaf* ta gama shirinta cikin sassauk’an rigar abaya bleue da kallabinta ta yane kanta, dake asuba ce ba hayaniya sosai a gidan, d’akin Juman ta shiga da sallama a bakinta, kan sallaya ta sameta ta rabka tagumi tana jan carbi, har k’asa ta duk’a ta gaisheta kafin tace “Mah ni zan tafi.”

D’auke tagumin tayi ta kalleta a nutse sannan tace “Allah ya tsare, Allah kiyaye hanya.”

A ladabce tace “Ameen Mah.”

Jim ya biyu baya na wasu sakanni sai kuma Ayam ta kalleta tace “Mah, dan Allah karki saka damuwa a ranki dayawa, kinga hakan fa zai iya haddasa miki hawan jini, Mah ! Kin ga dai ke kad’ai gareni yanzu, dan Allah kar ki dinga kuka kinji, ki dinga masa addu’a.”

Majina Juman ta ja sannan ta jinjina kai alamar to tace “Na ji, zan kiyaye.”

K’ura mata ido tayi tana kallo kamar bata gamsu ba, a hankali Juman ta kamo hannunta ta rik’e gam sannan tace “Ayam, ki bi mijinki sau da k’afa, ki zama mai ladabi da biyayya a gareshi, ki yi iya bakin ranki wajen kyautata masa, ki zama mace ta gari a wajen mijinki, ki zama yar aljanna a gun mijinki, ki daure sannan ki dage ki zama macen da duk sanda mijinta ya kalleta zai yi murmushi, shawarar da zan iya baki kenan a matsayina na uwa gareki, sannan abu mai mahimmanci da zaki kula da shi Ayam shi ne gyaran jikinki, tsaftar jikinki, kar kiyi wasa da haka, duk abinda kika ga na miki a kwanakin nan ba abun wasa bane, dan haka ki kula sosai sannan ki zama mai gyaran jikinki dan ki zama tauraruwa a wajen mijinki.”

K’wayar idonta ta kalla tace” Kin fahimta?”

Jinjina kai tayi tace” Na ji Mah, kuma In shaa Allah zan yi aiki da abinda kika fad’a min.”

Jinjina kai tayi ita ma tace” Tashi ki je, Allah ya tsare.”

Jinjina kai ta sake yi ta mik’e a sanyaye ta fita a d’akin, haka ta shiga har wajen Bilkees da Abdallah sukayi ban kwana sosai har da kukanta sannan suka tafi dreba ya jata zuwa filin jirgi.

 

*Alhamdulillah.*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 83

Advertisement *Page 83*   *********************   Tana k’uryar d’akin Umma taji sallamar shi, gabanta ya k’ara fad’uwa, haka…
KALLABI
Read More

KALLABI 64

Advertisement BABI NA SITTIN DA HUƊU Takawa yayi ya isa har inda aka ajiye wani kujerar da yaji…