Lu’u Lu’u 48

Advertisement

Bismillahir rahamanir rahim_

*48*

 

 

 

Awa biyu da rabi suka kwashe a sararin samaniya, babban filin jirgi suka sauka inda mutane mabambamta ke saukowa daga jirgin cikin nutsuwa, da k’yar take d’auke da jakarta tana saukowa a matakalar, yanda ta mata nauyi ji take kamar ta saketa ta fad’i, ta gaji matuk’a abu d’aya kawai take hangowa kanta, tayi wanka ta sha madara mai sanyi sai ta kwanta akan gado ta d’ora kanta a k’irjin yallab’ai tayi bacci isashe.

Haka ta sauko har suka fito daga zagayen da aka killace dan saukar jirgin, tana dosowa inda kowa ke jiran wanda ya zo d’auka suka had’a ido, ya hakimce gaban wata mahaukaciyar Ferrari jajir da ita ya had’e hannayenta, kamar yanda fuskarshi ke gimtse haka ita ma bata samu walwala ba da yanayin ganin fuskar ta shi, dan haka ta ci gaba da takowa sannu sannu tana jan akwati mai tayar har saida ta kusa k’arasowa kusanshi sannan ya gyara tsayuwarshi.

Ta k’asan ido ta k’are masa kallo cikin shigar k’ananan kayan, kamar dai kullum ya yi kyau sosai, hannun da ya kai ya d’auki akwatin ta bi da kallo, take kuma ta raka bayanshi da kallo dan juyawa kawai ya yi, matse baki tayi tana d’an aika masa sassauk’ar harara, cak ya tsaya a hankali ya juyo ya kalleta.

Da sauri ta kawar da idonta da tunanin ko ya ga sanda ta harareshi ne, cikin d’aurarriyar murya yace “Me ki ka saka a jakar nan ne haka? Ta yi nauyi dayawa.”

Kallonshi tayi sai kuma ta turo baki tace “Kayana ne fa kawai.”

Advertisements

Fuska a gimtse yace “Amma dai har da kayan masarufi a ciki ko? Dan na ga kin fiye taune taune yanzun.”

Kyab’e fuska tayi irin gaf take da fashewa da kuka tace “Amma ai ba haka na ke ci ba kawai, dalili ne ya kawo hakan.”

Da alamar tuhuma yace “Wane dalili ne zai saka ki cinyewa mutane abincinsu na shekara a kwana d’aya?”

Zaro ido tayi ta bud’e baki galala, sai kuma ta fara dira k’afafunta tana kukan shagwab’a tace “Da nasan abinda za ka min kenan da ban zo ba, da ma nasan ba wani kulawa dani za ka yi ba, amma Mah ta matsa sai na zo.”

Murmusawa yayi ta gefen labb’a yana girgiza kan shi, a hankali ya dawo daf da ita ya kama hannunta, hakan yasa kukanta tsayawa tsaf ta kalle shi, janta yayi har suka tsaya daf da motar, gidan gaba ya bud’e mata da hannunshi wanda ya aje jakar k’asa ta shiga sannan ya rufe, d’aukar jakar yayi ya zagaya baya ya saka a cikin boot sannan ya zagayo ya zauna mazauninshi.

Saida suka d’auki doguwar hanyar nan kafin ya kalleta yana rik’o hannunta a cikin na shi, kallonshi tayi sai kuma ta yi kasa da kanta, a tausashe ya furta “Ya hanya?”

Jinjina kai tayi sannan tace “Lafiya lau.”

Murmushi yayi yace “Kina lafiya ke ma?”

Cike daa kunya tace “Lafiya k’alau na ke.”

A hankali ya zame hannunshi a cikin na ta, kamar bazata sai kawai ya d’ora hannunshi kan cikinta, sannu sannu ya dinga saukar da hannu har ya kai shi k’asan cikinta ma’ana kan mararta dake shafe, zazzaro ido tayi sai dai bata kalleshi ba sai wani abu da take ji a gaba d’aya illahirin jikinta kamar yana amsawa.

Cikin sanyayyar murya yace “Yana cikin k’oshin lafiya?”

Rarraba ido ta shiga yi kamar wacce aka kama da kayan mutane, shiru tayi tana jiran ta ji ya d’auke hannunshi daga mararta, amma sai ta ji ma shafawa yake kuma kamar yana jin dad’in haka, dan tuk’i yake da hannu d’aya a nutse yana sakin murmushi, nefi jefi kuma sai ya dinga kallon hannun na shi yana sake shafa mararta yana kallon fuskarta.

Advertisements

Jin ba za ta ce komai ba yasa shi fad’in “Ya su Mah da kuma matata?”

Da sauri ta kalleshi gabanta ya wani buga da k’arfin data rasa dalilin haka da kuma saurin da bata d’auka tana da shi ba tace “Matarka?”

Da sauri ya kalleta shi ma saboda yanda tayi ta kuma wani d’an zabura, da mamaki yace “Me ye?”

Wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta girgiza kai alamar ba komai, sannan ya maida hankalinshi ga tuk’i yace “Matata sarauniyar Egypt.”

Wata sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin kanta da abinda ta ji sanda ya ambaci matarshi, kasa amsa mishi tayi har suka isa gidan.

Tarba ta musamman ta samu daga hadimai da kuma yan uwan Kossam da shi kanshi Wudar wanda suka gama makoki, amma dakon jiran matar Umad wanda tsammaninsu ya raja’a kan shi zai zama sarki yasa suka tsaya dan tarbanta, sannan kuma ‘ya ga sarkin Khazira sannan sarauniyar Khazira ta kwana d’aya.

Yanda suka dinga nan nan da ita kuma kowa fuskarshi a sake sai ta ji dad’i matuk’a har take ji a zuciyarta lallai tayi sa’ar dangin miji.

Tunda ya mik’a ta hannunsu ya fita bata sake ganinshi ba, har lokacin da aka kira wata dattijuwa da aka gabatar mata da ita a matsayin k’anwar mahaifin Umad, ta jima a waje kafin ta dawo ta umarci kowa dake d’akin da su fita zata shirya Ayam.

Daga ita sai yayarsu Kossam da kuma jakadiyar sarki suka rage a d’akin, a tsanake suka fara tub’eta dan ta fara wanka, yayar Kossam ce ta rakata ban d’aki, ruwa ne na musamman da aka ma jik’e jik’e na musamman da kula had’i turaruka na musamman aka shiga zuba mata a jiki ba tare da an saka mata sabulu ba bare soso.

Saida ta tsane jikinta d sabon towel sannan yayar Kossam ta bata madarar turare ta shafe jikinta da shi, suna fitowa ta zauna kan kujera gaban madubi, a nutse suka shiga mata gyaran gashinta wanda yanzun ya taso sosai har yana sauka fiye da wuyanta, sannu sannu suka shiryata tsaf a cikin kaya irin wanda sarauniyar Giobarh kawai ke sakawa, ita kanta data ga kayan sai Kossam ta zo mata a lokacin dan ita ke saka irinsu.

*Umad* dake tsaye gaban madubi yana kallon kan shi bayan ya gala shiri, tunaninta yake a d’aid’aice, a hankali yake tambayar kan shi “Ko ta ci ta k’oshi? D’ana saka ta cin abinci yake.”

Sai kuma ya k’ank’ance ido yace “Ko ya za ta ji idan ta ji maganar nan? Ta gudu daga wani mulkin…”

Sai kuma ya yi shiru, sake k’urawa kansa ido yayi, lallai duniya ba ta da tabbas, kwanaki k’alilan mahaifinshi ne ke saka irin kayan nan, masu ado da kwalliya sannan masu zubi biyu, amma yau gashi an saka shi sakasu ba dan ranshi na so ba saidan tagomashin da aka hasasho mishi.

Dan Ayam na zuwa aka nemi ganinshi, yana isa fadar ya samu duka dattawan masarautar ne, zaunar da shi sukayi suka fad’a masa taka dokar garin ne barin kujerar nan na kwana uku babu mai mulkinta, dan haka shi ya cancanci hawa kujerar, nuna musu yayi sam ba wannan magana, bai da sha’awar mulki a tsarin shi, kasancewarshi mai aikin da yake so a cibiyar CBT ma ya da kuma kasantuwarshi d’an tsohon sarki ya isa, amma suka nuna su fa a shirye suke da su masa biyayya, sannan sun shirya karb’ar addininshi dan su samu alk’iblar data dace da duka wani mutum mai rai da numfashi, da ya ci gaba da tirjewa ne wazirin tsohon sarki kasantuwarshi mutumin kirki ya sa shi yi masa rad’a a kunne, nan ya tunatar da shi irin tagomashin da hakan zai haifar, sannan ya bashi tsoro da nusar da shi cewa idan fa wani ya hau kujerar ba lallai mutane su karb’i addinin musulunci ba, kenan ko dan wannan babbar falalar ya karb’a dan ya kawo gyara a k’asarshi.

Da wannan ne yanzu haka yake tsaye kan k’afafunshi ya yi shiri irin na sarki inda zai je ya gurfana a gaban wani tsoho sannan ya saka mishi kambun da zai tabbatar lallai ya zama sarki, sannan a bashi sandar dake nuni lallai sarkin k’asaita ne.

Su hud’u suka shigo d’auke da wani kwando a hannunsu mai d’auke da furanni a ciki farare, mik’ar da ita sukayi suka sakata a tsakiya, biyu na gabanta biyu a bayan ga kuma sauran dangin dake gefe da gefenta, hannu k’anwar mahaifin Wudar ta kai a saman kanta ta jawo wani sange shara shara ta rufe mata fuskarta, hakan yasa ko k’ure mata kallo kaya ba zaka ganeta ba, ita kanta dishi dishi take gani ba dan suna mata jagora ba ga kuma furannin da suke zubawa a wuraren da take d’ora k’afarta.

Suna fita a d’akin suka tsaya, a tausashe ta ji an ce “Barka da fitowa ranki shi dad’e.”

Da sauri ta d’ago kanta saboda ta fahimci muryar da ta ji, muryar da ita ta fara ji a duniya a kunnenta kafin ta mahaifiyarta, muryar da ta jima tana d’aukin ganin mai dauke da muryar, hannu ta kai da sauri zata yaye labulen yayar Kossam ta rik’e hannunta tace “Ba gimbiya kike ba yanzu, ke sarauniyar Giobarh ce.”

D’auke hannayenta tayi ta saukesu k’asa, a sanyaye ta kalli matar tace “Wannan fa uwata ce, ta ya za’a hanani ganinta saboda Allah ya bani wani matsayi? Ba zan iya ba, zan d’aga na ga fuskarta dana jima ina mararin gani ko da hakan sab’awa dokarku ne.”

Da sauri ta d’aga mayafin fuskarta ta fito suka had’a ido da Habbee, wani murmushi ta saki mai kama da kuka wanda yasa Habbee sunkuyar da kanta kamar zata durk’ushe tace” Ki gafarceni uwar gijiyata, ka da ki zubar da hawaye ta dalili na.”

Da k’arfi Ayam ta jawota jikinta suka rumgume juna, kuka ta saki sosai tana fad’in” Na sha wahala tun bayan rabuwarmu da ku, an caza min kai na sosai Mah, an wujijjigani da labaran gaskiya wanda a gareni k’arya ne da farko kafin na yarda da su, Mah ! Me yasa ko sau d’aya baku fad’a min ba? Me yasa ba ku sake zuwa gareni ba? Me yasa Mah? Ina Aba?”

Habbee dai a d’arare take neman yakicewa daga jikinta, a sanyaye tace” Ki yi hak’uri sarauniyata, idan kina da buk’ata zan sanar da ke komai daya fara tun daga haihuwarki.”

Jinjina kai tayi ta d’ago ta kalleta tace” Ina Aba?”

Nuna mata hanya tayi tace” Yana fada wajen nad’in sarauta.”

Yayar Kossam ce tace” Mu je sarauniya Ayam, can muka nufa yanzu.”

Jinjina kai tayi da zumud’i ta sauko da mayafinta wanda ke nuni da matar sarki ta fi k’arfin ganin idon kowane mutan gari suka nufi fadar data cika tamk’am da dattawa da masu ruwa da tsaki.

 

*A yi hak’uri ba yawa, saboda hidima ne.*

 

*Alhamdulillah.*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 9

Advertisement 9_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* _A.A MAJEED’s_ _659 Melrose victoria mosmon,_ _SYDNEY,AUSTRALIA._ A hankali ta qarasa zare navy blue turkian…
INAYAH
Read More

INAYAH 40

Advertisement _40_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Babban tashin hankalinsa shine a yanayinda babyn Nan take ciki bazai iya bada ita ga…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 19

Advertisement €pisode 19…………….. “Naheela Ummanki tana inda kika fi tsana ” Sarki Zawatunduma ya faɗa , numfashi Naheela…
KALLABI
Read More

KALLABI 34

Advertisement BABI NA TALATIN DA HUDU Sannan ya saka kai ya bar dakin, ta kuma fashewa da kuka.…