Lu’u Lu’u 49

Advertisement

*49*

Suna isa fadar ba ta iya gane komai ba, sai dai tana d’aukin ganin marik’inta Utais, amma sam bata samu damar ganinshi ba har saida suka sadata da damdamalin da Umad yake tsaye cikin wata shiga ta alfarma, kayan sun masa kyau sun kuma mayar da shi babban mutum, duk da dishi dishi take gani amma a haka ta iya gane shi ne tsaye a gabanta, har kuma ta hangi yana sakar mata lallausan murmushi.

Dattijon daya tsaya gabansu tare da kambu a hannunshi yasa suka kalleshi a tare, a hankali Umad ya rusuna gwiwarshi d’aya a k’asa hakan ya ba dattijon damar saka mishi kambun a kan shi, sannan ya mik’o hannunshi na hagu ya saka masa zoben azurfa mai kyau da girma, wata k’aramar takobi ya mik’a masa ya karb’a da hannu biyu, take wurin ya kaure da hayaniya da shewar shikenan ya zama sarki.

A hankali ya mik’e tsaye yana sunkuyar da kanshi, wasu zafafan k’walla ne suka d’aso masa a kumatu, a sanyaye a k’asan zuciyarshi ya furta “Shikenan, shikenan nauyi ya hau kaina, madadin matata k’waya da’aya tak, yanzu nauyin dubbanin al’umma ne a kai, Allah ka ga zuciyata, na rok’eka ka bani ikon rik’e nauyin nan da adalci a tsakanin mutane na, Allah ka jib’anci lamurana dana mutane na baki d’ayanmu, Allah ka dafa min komai ya zama mai sauk’i a gareni…”

Taffin da aka saka sanda aka saka ma Ayam wani kyakyawan zobe a hannunta da kuma kambun da bai kai girman na shi ba ya dawo dashi daga addu’ar da yake, kallonta yayi ita ma sai kallon zoben take tana jin wani nauyi na hawa kanta, fuskantarta yayi da kyau ya rik’o damatsunta ya juyota gareshi suna kallon juna.

A hankali yanda ko na kusa da su bai ji me ya fad’a ba yace “Ki yi hak’uri Ayam.”

Lumshe ido tayi tace “Me yasa baka fad’a min hakan ko da a waya ba?”

A raunane yace “Ban sani ba ni ma Ayam, sai yau d’in nan da kika zo gareni, kiyi hak’uri.”

D’an murmushi tayi tace “Ka daina bani hak’uri.”

Kallon zoben hannunta ta sake yi sannan ta kalleshi tace “Hakan na nufin na zama matar sarki yallab’ai Umad? Hakan ya tabbatar min da ni ma nauyi ya hau kai na kenan?”

Advertisements

Jinjina kai yayi a nutse yanda ba kowa ya fahimci hakan ba yace “Hakane, da fatan zaki tayani d’aukar nauyin nan Ayam? Ina rokonki da ki kasance a gefena, hakan zai k’aramin k’arfin gwiwar aiwatar da mulkina a tsanake, ki zama mai tausaya min, hakan zai sa na zama mai tausayawa al’ummata, ki agaje ni Ayam, hakan zai saka ni farin ciki har na zama mai fara’a ga mutane na, ki tattaleni ki zama mai sama min nutsuwa a sanda kaina ya d’au zafi saboda girman nauyin dake kai na, hakan zai sa na zama adalin sarki ga jama’ata, na rok’eki.”

Ya fad’a yana had’a hannayenshi biyu alamar rok’o, da sauri ta rik’e hannayentshi duka biyun tana fad’in” Zan yi, zan yi sarki na, shugabana, farin cikina, kima da darajata, duk kai ne silar dana samesu, zan yi maka komai daka buk’ata, In shaa Allah, fatana Allah ya bani ikon rik’e wannan nauye nauyen, sannan ka zama mai kawar da kai daga kuraraina, ka zama mai tausasa min yayin da na b’ata maka, ka zama mai jink’ai na a sanda na kasa, ka zama adalin sarki a gareni yayin yanke min hukunci, ka zama uba ga wannan marainiyar, ka zama mai sassauci ga laifukana, hakan zai bani azamar kyautata maka.”

Da fara’a a fuskarshi ya amsa da” Zan yi, zan yi sarauniyata, In shaa Allah.”

Da murmushi a fuskarta ita ma tace” Na ji dad’i, kuma In Shaa Allah kamar yanda na kasance mata ta farko a gareka, zan k’ok’arta wajen ganin na zama makarantar farko mai inganci a gareka.”

D’an girgiza mata kai yayi cikin rad’a sosai yace” Matata ta farko, kuma matata ta k’arshe In Shaa Allah.”

Girgiza kai tayi ita ma tace” Bayan Mah ta fad’a min addinin islam ya yarjewa maza musulmi auren mace biyu, uku, hud’u, idan ba zaku iya adalci bane aka umarce ku da d’aya ko kuma abinda damarku ta mallaka.”

Janye hannunshi d’aya yayi daga na ta ya lak’aci hancinta yace” To ai saboda ba zan iya adalcin bane nake son k’are rayuwata da ke, ba zan iya had’aki da wata ba sarauniyata, sarauniyar zuciyata.”

Kallonshi tayi tar tana gimtse dariyarta tace” Ba wani nan, bayan ma d’aukar fansa ce ta had’ani da kai.”

Dariya ce ta sub’uce masa bai yi zato ba, jawota yayi jikinshi suka rumgume juna cike da shauk’in juna, hakan yasa fadar d’aukar tafi da hayaniya ana mai jin dad’in ganin haka.

A wannan wunin basu samu tsagaitawa ba bare su huta, bak’i ta ko ina suka dinga halartar walimar da aka shirya ta zuwan sarauniya da kuma nad’in sarautar, sai gashi hatta da sarakunan wasu k’asar suna zuwa dan tayasu murna da addu’ar alkairi.

Ayam ta gaji iya gajiya, gashi duk abinda zata kai bakinta sai da taka tsantsan saboda komai za ta yi sai a ce ita fa yanzu sarauniya ce, bata ma bud’e fuskar ba saboda tsaro bare kuma ta samu damar cika cikinta, gashi tana da buk’atar ta ci ta k’oshi iya iyawarta, amma an k’i bata damar haka.

Ta galabaita sosai tana cikin jin haushin yanda aka kasa barinta shak’at jakadiyar sabon sarki ta shigo falon ta sanar da jakadiyarta mai martaba na son ganin sarauniya yanzu yanzu.

Advertisements

Da sauri ta mik’e ta bi bayan jakadiyar da tunanin tana shiga ta fashe da kuka tace yunwa zata kasheta, saidai suna shiga nan ma wasu bak’in ne, tawagar ma’aikatarsu ne suka yi tattaki dan tayashi murna da ita kanta, dan haka ya kirata dan su gaisa.

Ganinsu duk sai ya sage mata gwiwa ta k’arasa a nutse ta zauna, gaisawa sukayi sosai da girmamata saboda d’aukakar da Allah ya mata, dan in za’a bi salsala ne to gaba da baya ita d’in ba abar banzatarwa ba ce, ba dan tak’i karb’a ba da shi kanshi Umad zai zama k’asa da ita ne saboda kujerarta ke gaba da tashi.

Addu’o’i suka musu kafin su mik’e da niyyar zuwa wajen da sauran bak’in suke, da kallo ta bisu har suka fice ta ga an rufo k’ofar, mik’ewa tayi tsaye ta jaye rufin fuskarta hakan yasa kwalliyarta bayyana, kallonta yayi yana murmushi zai fad’a mata kalma mai dad’i, sai gani yayi ta zube k’asa tayi zaman yan bori ta fashe da kuka iya k’arfinta tana dafe cikinta da fad’in “Wayyo! Mah ke! Mahhh ! Shikenan mutuwa zan yi ni wallahi.”

Da sauri ya zaburo ya zo gareta ya durk’usa yana rik’o hannunta yace “Me ya faru ne sarauniyata? Me ya sa ki kuka?”

Tsit tayi ta kalleshi ta turo baki kamar zata tsinkashi tace “To ba yunwa nake ji ba, tunda na zo ban ci na k’oshi ba, komai zai yi sai a wani ce sarauniya sarauniya, ni na gaji ba zan iya ba gaskiya, kawai ka ban abinci na ci na k’oshi.”

Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi, a sanyaye ya furta “Yunwa ce matsalar?”

D’aga kai tayi tace “E.”

Shafa kuncinta yayi yace “To kwantar da hankalinki, matar sarki ai ta fi k’arfin yunwa ta kasheta sai dai k’oshi.”

Hannunshi daya d’ora kan kuncinta ta kamo da hannu biyu, lumshe ido tayi ta saka yatsunshi biyu a cikin bakinta, wani d’ummmm ! Ya ji ni’imtaccen d’umi ba mai cutarwa ba, bai san sanda ya furta” Ahhhhhhhhh.”

Zaman dirshen yayi saboda kxantar da kanta tayi kan damtsenshi tana ci gaba da tsutsa ka rantse loli pop ce take tsutsa, da wani k’arfi k’arfi ya jawo hannunta d’aya ya d’ora kan kuncinshi yan shafawa, a hankali a hankali wasar dake tsakaninsu ta canza zuwa wani salo na daban, rana ta biyu kenan a garesu, had’uwarsu ta biyu kenan a rayuwa, hakan ya k’ara jigatasu musamman Ayam da tunda ta fahimci wani irin girma da mijinta ke d’auke da shi ta tsorata ta kuma zabura zata mik’e, amma haka ya danneta da hannu d’aya har saida yayi nasarar ida nufinshi a kan ta.

Sai ga Ayam mai kukan yunwa ta koma na wahala, dan abun ne ya mata yawa, ga rashin k’oshi ga kuma azabar daya gana mata, amma haka ta daure ta k’i nunawa a fuska sai dai ta yamutsa fuska kawai, har saida ya sa aka kawo masa abinci mai rai da lafiya ya kawo mata har d’akin baccinshi kan gado, da hannunshi ya dinga bata tana amsa a kunyace, shi kuma ya k’ura mata ido yana kallo k’aunarta na sake huda zuciyarshi, shi kad’ai yasa me yake ji akan baiwar Allahr nan, shi kad’ai yasan irin abun da yake ji idan yana tarawa da ita, shi kad’ai yasan irin gamsuwar da yake samu a tare da ita, idan har zai iya bud’a bakinshi yayi magana sai yace ” *Lallai abinda aka gani a hasashe kenan, shiyasa maza suke haukacewa a kan ta, watak’ila irin albarkar dake tattare a jikinta kenan, shiyasa kowa ke son ta zama tashi, sai kuma Allah ya wanke ya bani.*”

Ta so yin bacci da ta k’oshi amma ya hanata saboda yamma tayi sosai, dole ta hak’ura ta zauna a b’angaren na shi shi kuma yana tare da ita, duk masu son ganinshi dole suka hak’ura saboda da an fana musu yana tare da sarauniya dole ka yi shiru.

Sai bayan magriba kad’ai ta samu damar ganawa da Utais, tayi kukan rabuwa da sukayi kai tsaye, sannan ta nuna bata jin dad’in duk’a matan nan da suke, haka kuma ta k’uduri niyya a ranta zata nemi sarki alfarmar ya ware musu gidansu na daban ba kusa da ita ba, dan bata so tana ganinsu suna sunkuya mata, dan ita a uwayenta take kallonsu, su kuma har yanzu girmamata suke ba kuma zasu daina ba.

*Rayuwa* kenan, sai gashi komai na tafiya daidai, duk da anyi rashi amma dake hukuncin ubangiji ne manta abinda ya wuce, sai suma basu yarda mutuwar iyayensu ta hanasu rayuwa ba, Umad na tafiyar da mulkinsa yanda ya dace, da taimakon dattawan zaurenshi da kuma fasihar matarshi, wacce a zahirin gaskiya baiwarta ke dad’a fitowa fili a yanzun ana gani, indai har zata bashi shawarar yayi kaza, to In Shaa Allah za’a ga da kyau ko da wajen yanke hukunci ne a tsakanin talakawan gari.

Sannu sannu sai wani abun mamaki ya dinga bayyana, inda sunan Umad da masarautarshi ke bunk’asa a dalilinta, sai mulkinshi ya fara zama na al’ajabi da d’aukar misali ga sauran masu mulki da sarakuna, ta ko ina maganarsa ake ana bayar da misali da shi, hatta da harkar kasuwanci da Ayam ta bayar da shawara aka kuma rairaye matasa aka sama musu sana’oni, sai gashi Giobarh tafara karb’ar bak’in mutane suna zuwa ci rani a garin.

*Bayan wata bakwai*

Kallon shugaban yan kasuwan yake yana bayaninshi a tsanake da ladabi, saida ya kai aya kafin ya numfasa ya d’an muskuta, buk’atar da ya zo da ita yana son neman shawara dan yasan matakin da zai d’auka, saidai babban mai bashi shawarar ya barota ta koma bacci saboda sammakon da tayi ta je asibitin cikin gidan ta yi awo, idan ya tasheta yanzu rigima ce ta bugawa a jarida zata saka mishi, idan kuma ya yanke hukunci ba zai samu nutsuwa ba, dan shi kanshi yanzu yake yarda da abinda aka canfa a kanta, har wani lokacin ya kan takura zuciyarshi ta k’aryata abinda ake fad’a d’in, dan a matsayin shi na sarki baya so a ce ya yarda da irin wannan abun ta yanda zai kawo masa cikas a tafiyar mulkinsa, hakan zai sa wata rana ya ji lallai lallai sai da ita ne zai ciyar da mulkinsa gaba, kamar dai yanda mahaifinshi da Bukhatir suka canfa, amma da ya tuntub’i malaminshi sai ya nuna masa ba komai, indai har shawarar ta ta mai kyau ce kuma tana kawo ci gaba, saidai kar ya zama kullum zai shawarce ta kan lamuran mulki saboda wasu dalilai, dan haka yanzun ba kullum yake tuntub’arta kan abu ba.

Hohoho! Ina masoya kuma makaranta litattafan hausa novel? Yau ma ga jarumar ta ku ta dawo a cikin sabon littafin ta mai taken *MALLAKINA CE*, *MALLAKINA CE* littafine da ya k’unshi wata irin cakwakiyar soyayya, sark’ak’iya da kuma ban al’ajabi gami da barkwanci, zai fad’akar ya nishad’antar da masu karatu, albarkacin sabuwar shekara da za’a shiga, littafin zai fara zuwa muku *15/01/22*, domin samun na ki da wuri ki/ka hanzarta biya dan karatu cikin salama, ka da ki bari a baki labari maza hanzar ta ki nemi naki akan farashi mai rahusa. Ga mutanenmu na Niger zaku biya katin dala dari Cfa zaku tura akan lamba kamar haka *94-98-56-52*,
ga mtanen mu na Nigeria kuma zaku tura Naira 300 ta wannan account d’in 0594148516 lubabatu shehu Gt bank, bayan kun tura sai ku tura shaidar biyanku ta wannan lambar *94-98-56-52*
Mun gode sai kun zo.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 11

Advertisement Babi Na sha ɗaya>*   *Fatan Alkhairi gare ku Yan uwa da abokan arziki Nagode sosai 😍🥰🤩🔥*…
KALLABI
Read More

KALLABI 48

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA TAKWAS Tun bayan dawowar shi, baki daya ya kasa sukuni, asalima ko wurin…
KALLABI
Read More

KALLABI 65

Advertisement BABI NA SITTIN DA BIYAR Kamar yadda ake abisa al’ada ajiye sarauta yayi ya raka Gidado, duk…