Lu’u Lu’u 50

Advertisement

*50*

 

Kiran da ya shigo wayarsa wacce ba k’ara take ba saidai vibration yasa shi duba wayar, duk da jininshi har gudu ya k’ara saboda son ya kai hannu ya d’auki kiran, amma dake jikin har ya fara sabawa da tsaiko da jan aji irin na sarakai, sai ya zura hannu a hankali ya d’auki wayar, hakan ma wai dan daga shi sai shugaban yan kasuwan ne, da yana tare da babban amintaccen bafadansa ne da shi zai d’auko ya mik’o masa.

Danna ok yayi ya kara a kunne yyi shiru, a k’asan zuciyarshi ya tambayeta “Me ki ke so sarauniyata?”

A zahiri kuma sai yayi shiru saida ta furta “Sarkina.”

Lumshe ido yayi sannan cikin nutsuwa ba tare da wanda ke kusanshi ya ji ba yace “Sarauniyata.”

A shagwab’e ta furta “Ka dawo dan Allah, bana jin dad’i.”

Tsai yayi da idonshi zuciyarshi na dokawa da k’arfi yace “Me kike ji? Cikin ne?”

Kamar za ta yi kuka tace “Bayana ke ciwo, ji nake kamar zai rabe biyu.”

Kallon shugaban yan kasuwan yayi ya taso daga cikin kujerar yana shirin mik’ewa yace “Ka gafarce ni, iyalina ce ba lafiya.”

Advertisements

Bai jira amsarshi ba kawai ya fice a falon na shi na karb’ar bak’i hannunshi rik’e da wayar bai kashe ba, ta k’ofar sirri da shi kad’ai ke bi ta nan ya shiga wanda yana bud’e k’ofar ta sadashi da k’aramin falonta, da sauri ya ratsa ta tsakiyar kujerun alfarmar dake zube ya bud’e wata k’ofar, turus ya tsaya sai kuma ya tafi a sukwane gareta yana jefar da wayar hannunshi.

Juyowa Ayam tayi ta kalleshi wacce ta sauko daga kan gado tana matse fuska, b’ata rai tayi tana mai rashin jin dad’in ganinshi saboda abinda ta ji a jikinta, ita dai tana baccinta kawai ta ji wani lema mai d’umi na fitowa a k’asanta, tana tashi zaune ta ji abun na dad’a k’aruwa, a k’ank’anin lokaci sai ga ta tayi jagaf a cikin wannan abu da ita take ganin fitsari ne.

Zagayowa yayi inda take ya rik’eta yana k’are mata kallo ganin sai tattare doguwar rigarta take marar nauyi, kallonshi tayi a marairaice tace “Sorry…na kasa rik’e kai na, tahowa kawai ya…”

Wani zul ta sake ji ruwan nan sun b’allo mata, hakan ya sa ta ja baki tayi gum ta damk’i hannunshi, k’asan data kalla shi ma ya bi da kallo, ganin ba zata iya da abun kunyar nan ba yasa ta durk’ushe tace “Dan Allah ka kira min Mah, ka ce ta zo da sauri wallahi fitowa yake.”

Zaro ido yayi yace “Yaron? Yaron ne ke fitowa ? Amma fa wata bakwai ne.”

Yarfa hannunta tayi tace “Ni ban sani ba, kawai ka kira min Mah ni dai.”

“To to.” Ya fad’a yana laluba wayarshi, dan tazara ce mai tsayi tsakaninsu da Mah d’in, hango wayar da yayi a k’asa ya hanzarta d’auka ya saka lambar Mah d’in ya kirata.

Ko da Kossam ta zo saida kunya ta kamata, dan matsayinta na babba wacce ta yi haihuwar nan ta san ko menene, hakan na nufin haihuwa ta matso saidai ba lallai yanzu yanzu ba, hakan yasa ta umarceta ta shiga ta gyara jikinta, saidai kafin ta fito daga ban d’aki har ta sake b’acewa, hakan yasa ta ma kanta dubara wajen yin k’unzugun data tabbatar zai tare mata wannan ruwan, ko da ta saka kaya sai ta ji tsaf yanzu, yana zuba saidai baya b’ata mata jiki, tana fitowa ta samu Umad ne a tsaye amma Kossam bata nan, rumgumota yayi jikinshi yace “Kin d’aga min hankali sarauniya ta, na d’auka zaki haifa min yaro bakwaini ne.”

Cikin fara’a tace “To ai hakan na nufin zan haifi bakwaini ne.”

Murmushi ya sakar mata yace “Ba zaki yarda ba kema, e yasa to?”

Kallonshi tayi tace “Saboda ni ce ke yi.”

Dariya yayi yace “Allah baki hak’uri Hajiata, tunda magana ce aka fad’a min.”

Advertisements

Tureshi tayi kad’an a jikinta tace “Ni dai ka tafi ka bani wuri.”

“Korata ki ke?” Ya fad’a yana k’ura mata ido, girgiza kai tayi tace “A’a, bana dai jin dad’in yanayi na kawai.”

Rumgume ta yayi sosai yace “Ni wannan bai dameni ba, ke kawai nake so Ayam, ke kawai.”

Cikin harshen Italy tace “To ai ni bana jin dad’i, salon ka min kishiya kuma ka fad’a mata ni k’azama ce ko?”

Yar dariya yayi yace “Dan Allah kar ki fara hassala ki fara canza min yare.”

A harshen Gallois tace “To idan baka so ka tafiyarka.”

Raba jikinshi da na ta yayi yace “Idan na k’i fa?”

A yaren fulatanci tace “Minkam miwala emi boya on (Sai na kwana ina kuka).”

Tsura mata ido yayi da mamaki, d’an shafa k’eyarshi yayi ya sake jawo kugunta tsam ya matse sannan yace “Matar sarki me kika fad’a ne haka?”

Matse bakinta tayi sosai ta d’aga kafad’a alamar “Uhum!”

Marairaicewa yayi yace “Na rok’eki ki fad’a min abinda kika fad’a?”

A harshen hausar da zuwa mata kawai yayi tace “Cewa na yi zan kwana ina kuka.”

Zaro ido yayi jin ta k’ara b’atar da shi, amma sai wata dubara ta zo masa, jayeta yayi daga jikinshi ya d’an had’e fuska yace “Yanzu ni kika aikawa wannan ashariyar?”

It ma kamar yanda ya zaro ido d’azun haka tayi tace “Lahhh! Wallahi ba haka na fad’a ba, cewa na yi fa zan kwana ina kuka.”

Murmusawa yayi ya jayeta daga jikinshi yace “To na tafi.”

Gimtse bkinta tayi ta bishi da kallo, tana so ya zauna kusa da ita saidai gaskiya ruwan nan da take ta bulbulowa sun saka ta jin tsantsenin kanta, bare har ta zauna da shi a irin wannan yanayin.

*Khazira*

Kamar yanda ya zaa sabonshi shiga wuraren da jama’a ke taruwa dan ya ji matsalolinsu da kuma ganin yanda abubuwa ke tafiya, yau ma a shirye yake cikin sassauk’an yadinshi an masa d’inkin riga yar shara, sai wata hula daya saka a kan shi ga bak’in gilashi da kuma face mask daya saka, hakan yasa kowa harkar gabansa yake babu wanda ya kula da shi.

Rab’ashi tayi ta wuce ba tare data kula da shi ba, hakan yasa shi juyawa ya bita da kallo, kallo irin na zuciya ta ga abinda take so, da sauri ya juya gaba d’ayansa sannan ya fara bin ta a nutse a nutse, alamu sun nuna masa ko dai ‘yar sarki, ko wacce ta shafi sarauta, duk da abaya ce a jikinga, amma hadiman dake take mata baya suna rik’e da ledojin ke nuni ta shafi masarauta kai tsaye.

Tunda ya bi bayanta shi ma escorts d’in shi suka bi shi a baya ba tare da yanda kowa ke ganewa ba, dan ba ma a layin da yake bi suke bi ba kasancewar kasuwa ce babba.

Daidai motocinsu biyu suka tsaya, da sauri wani bafaden ya bud’e mata k’ofa tunda ya ga ta taho, hadiman kuma suka k’arasa gaban d’aya motar, ganin duk sun shiga da hanzari an tayar da motocin yasa shi juyowa inda escot d’in na shi suke, suna had’a ido da wani ya masa alama da hannu ya d’auko mota, dan in da ido ya masa ba zai gane ba dukansu bak’ak’en gilashi ne a fuskarsu.

Cikin hanzari kam aka kawo motocin guda uku da babur biyu da matuk’ansu suka bi bayan motocinsu, doguwar tafiya sukayi har saida suka ga an dunfari shiga wani makeken gida, suna kallo mai gadi ya bud’e musu suka shiga su kuma suka tsaya, a hankali ya furta “Yar sabon sarki ce kenan?”

Babban escot d’in shi ne ya juyo a ladabce yace “Ba masaniya yallab’ai, saidai idan kana so za’a bincika.”

Girgiza kai yayi sanda yake d’aure d’amarar wandonshi dan har ya canza kaya a cikin motar sannan yace “Ba buk’ata, zan sani da kai na.”

Yana fad’a ya bud’e k’ofar ya fito, duk fitowa sukayi sai ya dakatar da su yace “Yak’in neman aurena zan tafi, ba buk’atarku a nan.”

Da d’an sauri ya d’aga k’afarshi ya tunkari shiga, mai gadi na shirin rufe k’ofar ya ganshi, saidai yanda ya fito cikin shirinshi na wanda aka sani yasa shi kwasar gaisuwa a mutumce sannan ya bashi hanya ya wuce har yana lek’awa ya ga to ina jami’ai da masu tsaro, yana ganinsu a k’ofar gidan ya jinjina kai ya koma ya zauna.

Har hadiman sun kwashi kayan data siyo sun shige da su, ita ma bakin wata flower ta tsaya tana amsa waya, hakan yasa daga bayanta ta ji an ce “Barka da warhaka.”

Mamaki ne ya fara rufeta saboda yanda aka mata magana ta jima bata ji haka ba, a hankali ta juyo ta kalleshi, wata fad’uwa gabanta yayi saboda wanda ta gani tsaye a gabanta, wannan kyakyawan matashin mai jini a jika, wanda ya shiga sahun jerin mutane mafi d’aukaka a harkar mulki, matashin daya shiga sahun manyan mutanen da ake zana sunansu, matashin da ya shiga d’aya daga cikin matasan da sukayi mulki da k’ananan shekarunsu, *Abdul Basid’ Murphy* shugaban k’asar Texanda, wanda ya lashe k’uri’ar al’umma ba da kud’i ko kyautar cin hanci ba, sai dan cancantarshi da kuma zak’wak’urancinshi ga k’asarshi.

Ba tare data sani ba ta aje wayar tace “Yallab’ai?”

Murmushi ya sakar mata yace “Yallab’iya.”

Yar dariya ce ta nemi kubce mata sai kuma ta gimtse ta kawar da kanta, jim kad’an ta juyo ta kalleshi tace “Yallab’ai lafiya ko?”

Kafeta yayi da ido yace “Lafiya ba lafiya ba, na zo kama wata mai laifi ne.”

Da mamaki tace “A gidan nan ?”

Jinjina mata kai yayi alamar e, ita ma jinjina kan tayi tace “Bismillah to, wuce ciki.”

Gyara tsayuwa yayi ya kalleta da kyau yace “Yallab’iya, wajenki na zo.”

Nuna kanta tayi tace “Wajena kuma? Wani abu ne ya faru?”

A tsanake yace “Ba abinda ya faru a yanzu dai, amma gaba kad’an zamu gane da yiwuwar faruwar wani abun.”

Nuna masa hanyar shiga falon tayi tace “Bismillah to.”

” *Ina son ki*.” Kalmar daya fad’a kenan kamar saukar mari a kunci, da wani razanannen firgici ta kalleshi ta a zazzaro ido, a zuciyarta kuma tana maimaita kalmar ina son ki, me ya d’auketa to? Me ya gani a tare da ita? Wace manufa ce ta kawoshi gareta ? Yasan ma wacece ita?

A hassale ta juya da niyyar barin wurin yayi gaggawar tare gabanta yace “Baki ce komai ba?”

Kallonshi tayi fuskarta a had’e sosai tace “Me kake so na ce? Me zan fad’a maka? Kasan ko ni wacece? A budurwa ka d’auke ni? Da zaka tareni da wannan maganar kai tsaye.”

Wayar hannunta ta d’ago masa tare da danna madanni hoton Ayam ya bayyana akan screen d’in, nuna masa tayi tace “Ka ga wannan? To ‘yata ce, yanzu haka ita ma tsohon ciki ne da ita, dan haka ka ja jikinka malam, ina girmamaka sannan ina mutumta alak’ar dake tsakaninka da tsohon sarki *mijina* mai mutuwa.”

Tunda ta fara magana yake kallonta, tana dasa aya madadin ta ji yace” Dan Allah ki gafarce ni, wallahi na d’auka budurwa ce a yanda na ganki.”

Amma sai ya saki murmushi ya kuma furta” Ina son ki, kuma ina so na aureki, ba zan takuraki ba idan baki amince ba, aa dai zan tabbatar na shiga rayuwarki na addabeki har sai kin fad’a cewa kin amince zaki aureni.”

Galala tayi da baki sai ta rasa me zata fad’a masa kuma, tana kallo har ya kama hanya ya fita a gidan, nuna kanta tayi a hankali tace” Ni? Ni wai yake so? Ni Juman? Ina ! Da ‘yar tawa zan wani tsaya na yi aure, babba ma ba zan kula ba bare wannan da in ba tsarana bane a shekaru, to bai wuce shekaru d’aya ko biyu ne ya bani fa.”

Murgud’a baki tayi ta juya ta shige ciki tana bambami a zuciyarta da harare harare tana ji ya gama kunyata ta ai da wannan kalmar daya zo mata da ita.

**************

Irin tsangwamar da matan dake magark’amar suka d’ora mata shi yayi sanadiyar zubewar cikinta wanda saida ta jikkata sosai saboda cikin ya kai wata hud’u, ta jima kwance a asibiti k’ark’ashin kulawar jami’an tsaro, yanzu kuma data samu sauk’i ta koma magark’ama sai ta canza sosai, kullum tana d’akinta ita ka’dai, idan kuma an fito da su ne to zaka ganta a rakub’e, da haka take cike da takaicin rashin nasararta a rayuwa da kuma nadamar abinda tayi wanda take ji a yanzu daa batayi ba.

*************

Babbar magark’amar dake jahar Khazira aka kai shi, wacce ke tsakiyar babban tekun Gafil, saidai shi sab’anin Joyran ne dake nadama, shi kam kullum yana cikin kula duk wanda ya kulashi, yana cikin fad’a da mutane, wata rana ya doke wata rana kuma a dokeshi, Zafeera kuma ta k’i barin tunaninshi, har yanzu da ita yake kwana yake tashi, yayin da zuciyarshi ke k’ara k’ek’ashewa da tsanar Umad da farautar dama ko ya take ya kassara rayuwarshi, da haka shi ma yake tashi rayuwar a gidan da yake fad’in baya da iko a cikinshi, madadin rayuwa a matsayin sarki, yanzu yana rayuwa a matsayin mai laifi kuma duk ta dalilin Umad ne.

**************

Tunda ta mareshi a fuska ya rasa lafiyar sa, kumburi ga dinga yi tana kumewa, kunnenshi kuma ya fara masa azababben ciwo, idan dare yayi baya iya bacci ko kad’an, sannu sannu abun ya fara k’amari har saida aka fara dubashi a asibitin masarauta, da aka kasa a nan asibitin aka turashi babbar asibiti, da abun ya ci tura kawai sarki Adah yace a dawo da shi a aje a kurkuku ya k’arasa girbe abinda ya shuka, dan a jikinshi ya ji kawai ba zai warke ba saboda wacce ta mareshi da kuma abinda ta fada bayan tayi marin.

Izuwa yanzu kunnenshi ruwa yake fitarwa, ga kumburin nan da idan ka ga rabin fuskarshi zaka d’auka wani abun aka saka masa, duk ya gigice ya fita a hayyacinshi, a haka yake rayuwar wacce a kullum mutuwa yake fata ta zo ta d’aukeshi amma Allah bai kawo k’arshen kwanan na sa ba.

*Giobarh*

Adah da kanshi ya sanar da ita ai fa shugaban k’asa ne yake son mah d’in ta da aure, shi ma kuma yayi auren rasuwa matarsa tayi, d’ansu d’aya mai shekara uku a duniya, tana jin haka tace tasan me za ta yi, ai kam tsaf ta kwashe ta fad’awa su Bilkees, nan fa suka saka Juman gaba da umarninsu da shawawari, daga k’arshe dai ta amince amma fa ta rantse sai bayan Ayam ta haihu za’a d’aura mata aure, haka kawai ba zata tafi gidan miji ba ta bar yarta data haihu ba gyara, alhalin ranar da suka had’u da shi ma ta tafi siyo kayan gyaran da take tanadi ne ta ma ‘yarta.

馃槀Zo ka ga Ayam ta yi sabon uba, tun yanzu yake ganin tab’ara, gashi shi ma mutum ne mai barkwanci sosai da kuma son d’an wanda kake so, hakan yasa yake biye mata a waya su sha hira har da tsare tsaren bikinsu suke, wata rana kuma har ya dinga tsokanarta da cewa yaushe za ta haihu wai? Ko tana so tai ta ganinshi a tuzuru ne ? Haihuwarta ta masa shamaki d zama ango.

*Sati d’aya* cir ta kwashe tana zubar da wannan ruwan zak’i, a ranar da suka tsaya tana murna bata jin komai yanzu zata shirya ta tafi turakar mijinta, sai dai ina nak’uda ce gangariya ta sakota a gaba, da gaggawa Kossam da jakadiya da likitarsu mace suka rufu a kanta, cikin ikon Allaah saida ta kwashe awa uku tana nak’uda kafin Allah ya amince d’anta ya sanyo kai zuwa duniya.

Masha Allah masarautun biyu babu wanda bai shaida an yi sabon magaji ba, sai gashi hatta da gwamnati ta san da haihuwar Ayam saboda ita ake jira ta haihu dama sannan shugaban k’asar ya angwace, tunda aka dinga ganin hoton yaron akan bpnshi na WhatsApp da Instagram da sauransu yan jaridu suka bibiyi labarin, daga nan suka shiga yayatawa su ma suna fatan alkairi.

A satin nan d’aya da ya gabata haka Juman data zo take gyara yarta take mata wanka na musamman, saida Ayam ta ji a jikinta a iya hakama aka tsaya taji dad’in jikinta kuma zata birge mai gidanta.

Ranar suna an ci an sha an tara bak’i bila adadi, anyi murna sosai da shagalin wannan rana kafin daga bisani yaro ya ci sunan *Abdul Waheed*, yaro mai shiga rai wanda yayi kama da Musail, hakan yasa yayi kyau gashi b’ul bul kamar ba d’an wata bakwai ba.

*Bayan wata takwas*

Zaune take a kan kujerar dake d’akin tana wayarta, yar dariya tayi a nutse tace “Abba na, gaskiya idan Mah ta haihu sai na biku har can, kun wani tafiyarku Atlanta kunyi zamanku.”

Dariya yayi shi ma yace “Karki damu ‘yata ta kaina, ai jirgi na tanada da zai d’auko min ke da kuma abokina (Abdul Waheed).”

Dariyar jin dad’i tayi tace “Yawwa Abbana, kuma ka ga…”

Kafin ta kai k’arshe aka bud’o k’ofar d’akin na ta, sanin ko waye yasa tace “Abba zan sake kira ka bani Mah, yanzu gaba d’aya shareni take bata son muna magana.”

Dariya yayi shi ma yace “Kunya take ji saboda tana da ciki.”

Murmushi tayi tare da aje wayar ta juyo ta kalli mai shigowar, jallabiya ce jikinshi bak’a da hula a kan shi, sai Abdul Waheed dake d’auke a kafad’arshi cikin kayanshi na kanti masu kyau, tubarkallah ba zaka ce d’an wata bakwai ba ne, a haka ma dan sanda zai yi hak’ori yayi amai da zaho ne duk suka ramar da shi, amma yanzu har ya maido jikinshi gashi har ya fara tatata.

Yana zuwa d’oro mata shi yayi a k’afafu ya kai hannunshi cikin rigarta ya ciro nononta, yaron na gani kam yayi ram da shi ya fara tsutsa, rufe ido tayi tana jin zafin tsutsar da yake saboda nonuwan sun cika mak’il sai zuba suke.

Zaune yayi daf da ita a hannun kujerar ya k’urawa yaron ido dake tsutsar nonon idonshi rufe, kallonta yayi yace “Uwar yaron nan baki da tausayi wani lokacin, tun safe da kika kai min yaron nan ban kuma ganinki ba, ke wai ba kya tunaninshi ne?”

Turo baki tayi tace “To ai ina so ne ya ga yanda kake gudanar da mulkinka dan yayi koyi da kai.”

A hassale yace “Sai kuma na ce miki ina buk’atar haka ni? Ko ya koya ai kya bari har yayi wayo ko?”

Marairaicewa tayi tace “Shikenan ka yi ta min fad’a saboda na yi abinda ya dace, ai dai ranar da aka nad’aka mulkin nan kayi alk’awarin ba zaka hassala a kai na ba, amma shi ne…har da min tsawa yanzu.”

Hawayen k’arya ta fara sharewa hakan yasa ya jawo kanta a k’irjinshi yana fad’in” Shikenan to yi hak’uri, gani nayi yanzu ba kya kula wannan yaron, jiya ma fa Mah ta fad’a min wuni yayi wurinta bai sha nono ba, me yasa zaki k’i bashi abincinshi yasha ya k’oshi?”

D’aga kanta tayi ta kalleshi sai ta mak’ale masa ido d’aya, da alamar raha yace” Akwai magana kenan?”

D’aga gira tayi alamar e, jinjina kai yayi yace” To gama bashi yasha sai muje ki ga wani abun mamaki, amma tukuici na shine ki fad’a min me ke faruwa.”

Jinjina kai tayi tace” Na yarda.”

 

*Bayan minti arba’in*

Hannayenta take ta lalubawa kamar makauniya saboda rufe mata ido da yayi da wani farin k’yalle, a hankali ya kwance mata d’aurin na fuska, a hankali ta fara bud’a idonta har ta saukesu fes a kan wani ni’iltaccen lambu, bayan korayen itatuwan data sauke idonta babbar zakanyar nan ce ta biyu ta zuba idonta a kan ta, wani farin ciki ne ya lullub’eta har ta furta “Wow!”

Bud’a ido tayi sosai tana kallon gurin, a b’angarenta ne ya killace wani gurin aka nomashi da shuke shuke irin na jeji, sannan aka zuba nau’in dabbobi, zakanya, biri, barewa, rak’umin daji, dorina, aku, d’awisu da sauransu, nau’in tsintsaye kala kala masu kyawun gaske.

Juyowa tayi ta kalleshi tace “Yallab’ai…”

Juyawa tayi ta kalli zakanyar nan tace “A ina ka samota?”

Dariya kawai yake saboda ganin farin cikin da take, rumgumeshi tayi sosai ta sumbaci wuyanshi tace “Nagode sosai mijina, ina alfahari da kai.”

Cikin kunne ya rad’a mata “A bani tukuicina.”

D’agowa tayi daga jkinshi suna kallon juna, hannunshi na dama ta kama a hankali har ta d’ora a kan mararta, sannan ta kalli k’wayar idonsa tace “Abdul Waheed, zai samu k’ane ko k’anwa.”

Da mamaki ya kalleta yace “Da gaske? Kina nufin ciki ne da ke? Amma…”

Dariya ce ta kubce masa ya kalli cikin na ta ya kuma kallonta yace “Amma kuma shi ne kike farin ciki? Duk da kinsan Abdul Waheed bai ko shekara ba, sannan kin sha wahala wajen haihuwarsa.”

Langab’e kai tayi tace “To me ye a ciki? Ba na ka bane? Wahalarka ce ? Zan iya mijina, zan iya da yardar Allah, ko da shi ma ina haihuwarsa zan sake d’aukar wani, na yi maka alk’awarin ba zan gaza ba ko da bautarka ce zata kasheni.”

Wata wawuyar rumguma ya mata tare da bata wani zazzafan sumba mai haukata k’walwa da gaggar jiki… 馃グ馃

 

*Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka nuna min k’arshen littafin nan lafiya, kamar jiya ne aka fara gashi yau an kawo k’arshen sa da amincewarka, Allah nagode maka, Allah ka k’ara mana lafiya da aron rai.*

_Hak’ik’a VIP grps kun nuna min k’auna, kun bi ni a novel d’ina na kyauta sannan kuka bi ni a novel d’ina na kud’i, kun min hallaci kuma kun nuna ku d’in masoya ne ba masoyan baka ba, hakan yasa a kullum nake kiranku da *yan amana*, ku d’in na daban ne a zuciyar Samira, Allah ya bar k’auna a tsakaninmu. Yanzu ma ga wani sabo nan na kud’i, na san zaku fara mamaki dalilin da yasa na ke son fara na kud’i? Dailin shi ne ina jin dad’in ganin wanda suke ikrarin suna tare da ni na kuma ga sun saka kud’insu sun siya saboda ni, hakan kuma na zama alkairi a gare ni, ina mai muku albishir da labarin *MALLAKINA CE* zai baku mamaki da sakaku nishad’i, dan na tabbatar zai fi *JIHADI* citta haka kuma zai fi *MATAR MUTUM* zak’i da saka walwala, abinda na ke so daku kawai shi ne ku biya kud’inku ku samu labarin, sannan alfarmar da zaku min ta biyu ita xe ku tayani tallata labarin dan k’ara samun masoyan asali._

*D’AND’ANO*

 

A nutse kamar yanda ma fi aksarin masu sunan *Abbakar Sadiq* suke kasancewa ya shigo falon da sallama, cikin haiba da k’asaita ya dunfareta, tunda ta ji bai jira an amsa sallamar ba, bai kuma kalli kowa dake falon ba sai ita ya tabbatar mata da wata a k’asa, amma sai ta nutsu tana kallon dogayen k’afafunshi masu d’auke da zara zaren yatsu har saida yayi daf da ita ya rage kad’an yayi saura k’afarshi ta tab’a k’afarta da ke mik’e.

Da wani irin sauri ta tank’washe k’afafunta ta ja baya sannan ta mik’e tare da sakin littafinta dake kan cinyarta tana karatu, rusunawa yayi tare da kai hannu da niyyar cakumar gashinta data bari a waje ba d’an kwali, sai muryar mahaifinshi wanda tun shigowarshi yana shirin amsa sallamarshi amma ya ga ba wannan ne a gabanshi ba sai ya dakata yana kallo ya ga me zai yi.

A razane yace “Kai! Lafiyarka k’alau kuwa?”

Da sauri ya janye hannunshi tare da d’agowa ya juya, sam bai yi tsammanin mahaifin na d’akin ba, ashe ba shi kad’ai ba ma har da mahaifiyarshi na zaune da kuma Goggon shi, cikin rashin jin dad’i ya dawo baya ya tsaya kusa da mahaifin na shi dake zaune kan kujera, kakkafeshi da ido Abba yayi yace “Da me ka yi niyyar yi Sadiq?”

Murmushi ya saki ya girgiza kai, tsaf Umma dake kallonshi ta fahimci da matsala, wato murmushin nan ne mai kama da kuka da yake yi idan ranshi ya b’ace, shi kuma gashi miskilin tsiya bai cika nuna damuwarshi ba, mutum ne mai koyi da fad’ar Manzon Allah (S.A.W), yana had’e fushinshi ko da kuwa zai iya d’aukar mataki, Abba kuma da bai fahimta ba d’orawa yayi da “Ban yarda da wannan girgiza kan ba, za ka fad’a min ko kuwa?”

D’aga kanshi yayi ya kalli mahaifin na shi, ba tare daya d’auke murmushin nan a fuskarshi ba yana kallon fuskarshi a ladabce yace “Abba, yarinyar can nake so na koyawa hankali, ina so na ji me ye tsakani na da ita da ke b’ata min suna? Me take nufi da ni da take min haka? Me kuma take nufi da abinda ta fad’a?”

Da sauri Abba ya kalli *Sajeeda* dake tsaye da rigarta t-chirt da zanen atamfa, ta d’auki littafinta ta ri’ke tana kallonsu ita ma sai zare ido take.

Mahaifiyarta da tun da ta ga ta wuntsila ta tashi tasan bata da gaskiya, harara ta cilla mata tace” Me kika masa?”

D’aga hannu tayi sama dake nuni tsakaninta da Allah sannan tace” Wallahi Mama ni ban sani ba, duk wunin yau ma fa ni ban gan shi ba.”

Wani kallo ya watso mata, a tausashe kallon yake kuma a nutse, sai dai daga k’wayar idon na shi zaka fahimci kakkausan kallon, yar k’wafa yayi sannan ya maida kallonshi ga Abba dake fad’in” Me tai maka kuma yanzu?”

Cikin sanyin murya yace” Abba har makaranta yarinyar nan ta samu *Zalika* ta fad’a mata wai ni da ita soyayya muke, kuma wai idan bata fita a harkata ba sai ta babbakata da ranta…”

Nunata yayi da hannu yace” Yanzu Abba sai da ita zan yi soyayya? Ta rasa abinda zata had’ani da shi sai da kanta? Abba…Abba, wallahi na rantse da Allah idan yarinyar nan bata fita a shirgi na ba zan sauke mata kafad’a, bana so ta daina daga yau.”

Wata k’wafar ya kuma yi a sanyaye sannan ya mik’e ya fita a d’akin, da kallo duk suka rakashi inda Bintu ta bi Sajeeda da kallo, kallo ne na takaici da jin haushin taurin kan yarinyar, ta sha nuna mata ta fita a harkarshi, amma bata san me yasa bata ji ba?

Umma kam ko kallon Sajeeda ma ba tayi ba sai mik’ewa da tayi ta bi bayan Sadiq, dan ita ta fi kowa sanin halin d’anta.

Abba ma juyowa yayi daga kallon daya bi shi da shi na mamakin yanda ya kora gargad’inshi amma a tsanake ba tare da hargagi ba, cikin taushin murya da ruwan sanyi ya aika mata sak’o mai razanarwa.

Kallon sauran yaran yayi dake karatunsu amma kunnuwansu da hankalinsu kaf yana ga abinda ke faruwa, inda Khausar sam bata ji dad’i ba, ta yi fatan ina ma Abba bayanan Yaya Sadiq d’in ya shak’i wuyan yarinyar can, tsawar da Abba ya daka musu cewa “Ku tashi ku koma ciki.”

Ita ta dawo da ita daga tunanin da take, da sauri duk suka mik’e suna kwasar litattafansu, saida suka shige Sajeeda ma ta juya zata shiga na ta d’akin yace “Zo nan.”

A hankali ta shiga takowa har ta zo kusa da shi, tsugunawa tayi a raunane kamar za tayi kuka tace “Abba gani.”

Gyara zamanshi yayi sosai ya matsa kusanta yana kallon fuskarta yace “Sajeeda ‘yata, kinsan dai ni mahaifinki ne ko?”

Jinjina kai tayi alamar e tare da amsawa cikin shagwab’ a tace “E Abba.”

Jinjina kai yayi shi ma sannan yace “Ina so ki fad’a min me yasa kika samu budurwar yayanki kika fad’a mata cewa kuna soyayya? Me yasa kika yi haka?”

D’agowa tayi ta kalleshi, sai kuma ta sunkuyar da kanta k’asa ta fashe da kuka marar sauti, dafa kanta yayi yace “Na d’auka ni da ke abokai ne, na d’auka bama b’oyewa juna komai? Yaushe muka fara haka da ke?”

Girgiza kai ta dinga yi amma ba tayi magana ba saboda kukan dake tik’ak’arta, a sanyaye ya sake fad’in “Kinga Sajeeda, ki daure ki fad’a min abinda ya faru, kinga dai bana so ya tab’a lafiyarki a gidan nan, kin san fa bana so hakk’in maraya ya kamani.”

Cikin matsanancin kuka da shashek’a ta k’arasa yin zaune ta fara fad’in “Abba…ka ga dai ban tab’a fad’a ma kowa ba sai kai, bana so ka fad’a ma kowa kai ma, ya zama sirri a tsakaninmu.”

Jinjina kai yayi yace “In shaa Allah babu wanda zai ji, fad’a min ina jinki?”

Saida ta ja majina ta fara fad’in “Abba ni ma bansan me yasa ba, ban san ko yaushe hakan ya fara faruwa dani ba, haka kawai dai na ke jin na tsani Yaya Sadiq ya dinga danganta kansa da wata ‘ya mace, haka kawai nake jin ba dad’i idan yana firar wata ya mace a gabana, raina ya kan b’aci matuk’a idan yana alak’anta kansa da wata mace, wani irin abu nake ji a zuciyata a game da shi, Abba sai na ke ji idan zai nemi aure sai dubu, to zan lalata auren sau dubu saidai ni da shi duk mu zauna a haka ba tare da aure…”

Da sauri Abba yace” Shiiiiiiii!”

Girgiza mata kaibya dinga yi yana fad’in” Ko kusa kar na k’ara jin kin fad’i haka da bakinki, kar ki sake fad’in haka kin ji ko, me yasa kike tunanin zaku mutu babu aure?”

Kallonshi tayi tana share hawaye tace” Saboda baya so na, ya tsane ni Abba, ban san me na masa ba? Ban kuma san hikimar dake cikin abinda nake ji a game da shi ba?”

Kafad’arta ya dinga bubbugawa yace” Daina kuka haka ya isa, share hawayeki kin ji, In Shaa Allah indai Sadiq ne matsalar, to ni nan uban Sadiq *Aminu* na miki alk’awarin d’aura miki aure da shi.”

_____________

Sadiq dake ta fafutukar bud’e d’akinshi ya shiga rai b’ace yake fad’in” Na tsaneta, na tsaneki, me yasa ba zaki fahimci haka ba? Mayya kawai aljana bai bak’in hali.”

Umma dake sauraronsa girgiza kai tayi a tausashe tace”…

 

*Kun ji salon labarin ? Me kuka fahimta game da d’an tsakuren nan?*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 11

Advertisement Babi Na sha ɗaya>*   *Fatan Alkhairi gare ku Yan uwa da abokan arziki Nagode sosai 😍🥰🤩🔥*…
INAYAH
Read More

INAYAH 10

Advertisement 10_* *_Arewabook@Mamuhgee_* Tana isowa gidan tun a compound tasan Abbi yadawo gida sbd ganin sabuwar motarsa da…
KALLABI
Read More

KALLABI 33

Advertisement BABI NA TALATIN DA UKU. M. GOBIR Bayan shekara daya, masarautan ta zama masarautan mafi karfi a…