Zee Baby Book 1 Page 48

Advertisement

*👉🏻48*

….kallon mutumin da yake kusanta zaune tayi taga yana kama da ummi Raiyan sosai gemunsa ta kama tana dariya.shikuma idanunsa Akan kofar katafareran gidan da zainab ta fito yar kofar da ta fito irin tasu ta larabawa ce. mamaki yakeyi dama Faisal din masu arzikine haka. zee ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi Dan har sunyi nisa bai saniba yaji tana cewa “kaima D’an ummi Raiyan ne ko. kaima my babyna zai baka abunci abaki ni shine yake bani mahbeer mijina ya mutu amma har yanzu basu kaina naga mutuwar ba bare tabani mijina mahbeer mudawo ko zamu yanzu. ta kalli balaraban mai tuka motar tace” kai ka kamu gun mutuwa ta bamu mahbeer mijina sai mu bar mata wannan ta Nuna Fahad Abu Rahaman burki mutimun ya taka da karfi yana dariya Dan yasan abunda zainab ta fadi da Abu Rahman najin Hausa da tuni ya matsa kusanta “zainab ai bayajin Hausa kekuma yanzu bazaki gane Arabic ba sai kin dawo normal. da harshan larabci ya fadama Abu Rahman abinda zainab ta fadi idanu yazaro ya matsa gefe dariya tayi tace”meye kake matsawa muji to kaga babyna yanada kirki daddy yace shima mijinane fah kuma ni bansa ma inda zanga mijin ba. Abu Rahman yace”Turki metace ne.?duk abinda ta fadi ya zaiyane masa tun shigarta motar.gabaki daya tausayinta ya kamashi Sam bai taba tunanin abun haka tazama ba bai taba son zainaba ba kullum burinsa yaga karshanta Dan yasan itace kezuga

umminta ta bujire masa har tabaro k’asar haihuwarta amma tunda yaganta cikin wannan halin yaji ya fasa cutar da ita ya kalli Turk yace”abinda za’ayi yanzu muje muyi shirin tafiya nayi alkawalin kaita amata magani har
ta warke zan bawa mahaifiyarta farin ciki duk nasan yanzu sai sunshiga damuwa ina anfanin dukiyar da aka Tara babu temako gashi suna babban gidan an hada jin dadin duniya amma sun kasa fitar da ita k’asar waje Dan haka muje yanzu mu kama hanyar kano. “to shikenan Allah bata lfy shiyasa ai bayan nagama bincike na kiraka nasanar dakai komai kuma kaga ta yada nayi bincike na cikin sirri har muka gama babu Wanda yasanmu shima Najib din kaga bayan muntafi kano zai fadi ga yada akayi ko tsoro ya hanashi fadin gaskiya tunda kaga bazai taba tunanin daga gareka bane. “insha Allahu nagama cutar da yarinyata zan bata farin ciki sosai Allah yaba zainaba lafiya. “Amin zee baby da idanu take binsu da batasan me suke cewa ba sai dariya takeyi kai Abu Rahman ya girgiza cike da tausayinta yana mai nadamar abun da yama mahaifiyarta da mahaifinta tabbas yasan idan zainaba tasan shine yasa aka kashe mata mahaifinta kasheshi zatayi Dan yarinyar akwai bakar zuciya ahaka har suka isa masaukinsu hotel Turk ya shiga da motar ya yayi parking yana budewa zee ta fara kuka sai tabishi Abu Rahman ya riketa “tsaya yazo chocolate zai kawomiki. yo ita ba larabci ta saniba shiyasa bata ganeba dukansa ta fara harda cizo tana ihu

ya saketa Turk bai jimaba sai tashi da akwatinsu ya bude bayan mota ya nasa ya shiga”ah yadai kuka taso dawo gaba yi shiru. tashi tayi ta tsalaka ta zauna ah gaba gun Turk yaja motar yabar cikin hotel d’in zee ta kalleshi tana goge hawayenta. “gun babyna zaka kaini ko.? eh can zamu amma sai kun hau jirgin saman keda kakanki. dariya tayi ta juyo tana kallon Abu Rahman yacema Turk “amma ina zamu samu abaya ta suturta jikinta.? “wannan ba matsala bace muje kano tunda jirgin sai gobe ma zaizo wlh abun yayi mutikar bani mamaki da Al’ajabi yada kace insha Allahu yau tsakanin Raiyan da zainaba sai kaci nasara samun daya acikinsu gobe dasu zaka saudiya wlh ban yarda ba amma sai gashi cikin hukuncin Allah kasamu daya kamu naji dadin yada kacanza shawara. ” ai nacema kafin nazo nasaka amun Addu’a Akan Allah yabani nasara akansu kuma Nima kwanana uku ina Addu’a nasan hakan araina jikina ne yabani zansamu daya daga cikinsu shiyasa tun shekaran jiya nacema muyi ta zurganiya har muyi masara. haka sukayi ta hira zee sai kallonsu takeyi sosai Turk yake sharara gudu na uban mamaki Ana kiran magarib lokacin sunyima katsina nisa sosai awani dan kauye suka tsaya sukayi sallah zee sai hiramin Abu Rahman ya bata ta nada akanta tayi sallah lokacin ta fara musu kuka tana kiran baby dinta daket Turk ya lallabata tayi shiru yaja motar suka dauki hanyar Kano.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

can gidan kuwa su ghaisha da su minata basu tashi dawowa ba saida aka fara kiran sallah magarib suka dawo kowa shiga yayi sallah ummi tana shigowa d’akin taga babu zainab ta duba bathroom batana Alwalla tayi ta fito tayi sallah zatonta tana dakin hafeeza bayan tayi sallah taje taga ko tayi sallah taga wayam batanan parlo ta fito ba kowa su nawwara ghaisha ta jasu suyi sallah dakin ghaisha ta nufa akofa, suka hadu. ” khadijah baby tana gunki.?” wlh batanan ina take. nawwara tace” momy ai mun turata gunku gidan daddah tunda yamma. idanu suka zaro hankalinsu atashe ghaisha ta wankawa nawwara Mari”Dan gidanku yaushe kika taba ganin anbarta ta fita ko hospital Sardauna idan zai kaita sai an rufe mata fuska duk Dan karta koyi fita waje. ummi da hankalinta yayi kololuwar tashi ta rike ghaisha” kiyi hakuri bari dukanta. ghaisha taja hannunta suka fita gidan daddah suka nufa. babu inda basu subaba lungu da Sako babu zee gabaki dayansu suka fito ghaisha ta kira dadday ta fada masa hankalinsa atashe yabaro masallacin ummi har ta fara kuka Sardauna daddy ya kira yana tambayarsa ko yana tare da momy ai basai lokacin da ya tsinke wayarba ya baro masallacin yazo ya shiga mota ya nufi gidan. lokacin da yazo kaf girman gidan babu inda ba’a nemi zee baby babu Sardauna hankalinsa atashe yace” yo duk kuna inane saboda Allah kuka barta ta fito ina anfani masu gadi da ma’aikatan gidan har zainab ta fita babu Wanda yaganta to wlh duk sai kunbar gidan kuma duk wani mai aiki

na gidanan wlh ya fita tun ban ilatakuba. Daddy ya rikeshi” haba Dr meye nasu aciki kaga mai aikinmu sabuwa ce ba wacce kasani bace tana kitchen batasan abunda ya faruba megadi yace wlh bata nan ta wuceba to me wanki ma bai ganta ba haka mai ba shifkoki ruwama bai gantaba su ghaisha suna gidan daddah. jikinsa ya janye ya nufi Swimming pool saida ya zagaye ko
ina suka biyoshi suna kara dubawa babu ita cikin ruwan ya fada yayi nema har yagaji babu zainab fitowa yayi hankalinsa atashe jikinsa sai rawa yakeyi ga ummi da ghaisha na kuka daddy na basu hakuri part d’insa yaje ya canza kaya ya fito ya shiga mota ya fizgeta ai tun kafin ya isu megadi ya bude masa, kofa ya fice aguje. Kai tsaye gidansu hayatu ya nufa gudu yake shararawa ikon Allah ne ya kaishi gidan akofar gidan yayi parking ya fito Kenan hayatu ya dawo daga masallaci aguje ya nufi gunsa ya harba masa Kafa saida ya fadi ya damkoshi ya rika wanka masa Mari kafin me ya hada masa jini da majina ya damki wuyansa ya wurgashi cikin mota yashiga ya fizgi motar

Yabar gun aguje iya tashin hankali hayatu ya shiga tambayar Sardauna meye yayi ko kala baice ba. har ya iso gidansu lokacin daddy da nuhu da kawu saminu da Najib sun tafi gidajan Radio da Tv da gun yan Sanda sanar da hoto nanta duk an baza iya tashin hankali sun shiga daddah sai kuka takeyi haka ummi da ghaisha hankalinsu ba karamin tashi yayi ba. Sardauna ya fito da hayatu ya makoreshi har parlo sai su ghaisha tashi tayi” haba Dr sakeshi Kara shakeshi yayi” momy Dan ubanshi ya fitomun da matata ko nakasheshi. Amshe hayatun tayi tace”don Allah hayatu idan kasan inda zainab take ka fada mana.?” Narantse da Allah ban saniba ta yaya zan dauki matar aure na farkoma tsautsayine wlh bansan inda take ba. daddah ta rike Sardauna tana bashi hakuri. Su daddy suka dawo ya kama hannun Sardauna suka zauna” Faisal kayi hakuri insha Allah duk inda momy take Allah zai kareta kuma zata fito lafiya rungume daddy yayi jikinsa na kerrrma yama rasa meke yimasa dadi aduniya mairan karfe gun ummi yaje Dan tafi bashi tausayi ya zauna yana mata nasiya da jadadda mata zata fito haka suka zauna har shabiyun dare sun kurawa Tv idanu suna jiran ko sa samu wani labari amma shiru iya tashin hankali sun shiga daket daddy ya lallaba Sardauna ya tafi gida. suko kowa ya tafi gidansa alwalla kowa ya dauro aka kama Allah.

Lokacin da Sardauna ya isa gidansa karfe daya na dare nisha na zaune hankalinta a tashe Sardauna bai dawo ba yana shigowa ta nufi gunsa amma ganin yanayin da yake ciki ta tsorata ta fashe da kuka ta rungumeshi tana tambarsa nan ya fada mata zainab ta bace tayi mutikar tsorata da lamarin. Alwalla yayi ya fara sallah Nisha dakinsa ta bishi ganin yana sallah itama tayi alwalla take tadako abaya ta bishi sunayi. Bangaran zee baby kuwa karfe takwas bata yiba su isa Kano gidan Turk suka nufa masha Allah kallo daya zakama gidan kasan balarabene ya hadu sosai. saide zee ta Kafa musu rigima akaita gun baby daket suka shawo kanta taci abunci suka bata maganin bacci matar Turk nada kirki ita tayi ta kula da ita har tayi bacci Turk ya zaboma zee abaya mai kyau da tsada wacce zatasa gobe sun gama shirya tafiyar gobe karfe shabiyu na rana jirginsu zai tashi dama passport biyu yasa aka masa da na ummi da na zainab yazo dasu cikin farin ciki ya kwanta shima Dan yasan maganin baccin da tashi bazata farka ba sai washe gari burinsa ya kaita babbar hospital ta saudiya tasamu sauki ta dalilinsa yasan zata daina fushi dashi zai janyo diyarsa jikinsa ya zabama zee miji ya kashe auran da dangin ubanta suka mata Dan yanzu yana bukatar jikokinsa ahaka har bacci ya dauke sa. Family su Sardauna yanda sukaga rana haka sukaga dare babu Wanda yayi bacci sun dage da sallah suna rokon Allah ya baiyana zainab yasa tana cikin koshin lafiya aduk inda take har asubah tayi ba Wanda ya rumtsa wlh kallo daya zakama ummi Raiyan taba ka tausayi.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Advertisements

Ana sallah Asubah Sardauna yayi shirin tafiya gida Nisha ta fara kuka ya tafi da ita Dole ya tafi da ita Dan Sam shi maganar ma bayason yi sai Dole. aparlo duk suka samesu ana jimami Nisha ta nufi gun ummi ta rungumeta tana kuka. ” Aisha kiyi hakuri Allah zai biyanata insha Allah Sardauna ya gaishesu yaje ya rungume dadinsa ya lumshe idanunsa bayansa yake bugawa tuwusai da minata sai kuka sukeyi kawu Saminu na basu hakuri daddy yana shafa bayan Sardauna yana lallashinsa shiru yayi baiyi magana ba daddah tace”don Allah Sardauna kayi hakuri kar ciwo ya kamaka zainab zata fito insha Allahu. Aisha kema kiyi shiru ba ason mai ciki tana damuwa sosai ya kamata ku karfafawa Raiyan kwarin gwiwa ba kusata tana yawan kuka ba. haka sukayi jigum jigum har rana ta fara babu Wanda yayi yinkurin sakama cikinsa wani abu.

***
Da misalin karfe 11:50.am su zee suna Airport sanye take cikin abaya mai masifar kyau tayane kanta da mayafi sai murna takeyi saboda sun mata wayo sunce babyna na cikin jirgi yana jiransu zasu tafi gun mahbeer Turk na tare dasu sun bata waya wai ta babynta ce yana ciki da sun shiga ta bashi sai dariya take. Shabiyu daidai aka fara sanarwa matafiya su shiga jirgi Abu Rahman ya kama hannun zee suka nufi gun jirgi tana waiwayar Turk da Sauri yabar gun Dan yarinyar tabashi tausayi kuma yaji sonta ya kamashi zee baby tunda suka hau matatakalar jirgi kanta ya fara juyawa har suka shige ma’aikatan jirgi suka nuna musu kujerasu Dan alayin manya Abu Rahman ya saya zama sukayi zee tana ta zaro idanu inda zataga babynta ganin haka ya kalli wayarsa ya karanta abunda Turk ya rubuta masa yace” yana toilet bari zai fito kai ta daga tana hawaye ahaka har jama’a suka gama shigowa jirgi ya fara shirye shiryen tashi. Bayan minti goma jirgi ya fara tafi asannu sannun har yakai gunda zai cira da karfi yayi sama aikuwa yana cirawa zee wata irin hajijiya ta dauketa ta rinka ganin jiri tana ganin motar da ta bugesu da mahbeer Abu ya rikota wani irin gigitaccen ihu tayi da karfin gaske Wanda jama’a suka fara lekensu. tace” wayyo Mahbeer mota zata kashemu…nan take numfashinta ya dauke cak ta zube jikin Abu Rahman Asume Wanda yayi mugun tsorata zufa sai keto masa takeyi Dan zatonsa zainaba mutuwa tayi ma’aikatan jirgin ne sukayo kanta da gudu………… ✍🏻🤦🏻♀

 

 

*ZEE BABY*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 12

Advertisement 12_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Dad din zaid yasan Sarai waye A MAJEED Dan hakan Bai tsaya nemansa a wayaba…
INAYAH
Read More

INAYAH 35

Advertisement _35_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* *_’YAR ZURU Maman ZEE ZEE Best kayan mata_* Shin ko kunada labarin Yar Zuru mamar…
INAYAH
Read More

INAYAH 45

Advertisement 45_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Kofa ya dafa da kyau sbd ba zato yaji ta jikin nasa…. Yaune Karo na…
Read More

Lu’u Lu’u 45

Advertisement _Bismillahir rahamanir rahim_ *45*   Tattausan kayan bacci ya d’auko mata dogon wando da rigarshi mai k’ananan…
Read More

Lu’u Lu’u 20

Advertisement *20*   Mik’ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace “Kwantar da hankalinki gimbiya, ki ban lokaci…