Zee Baby Book 2 Page 11

Advertisement

*Book 2 👉🏻11*

…”Ashe Zainab zaki iya kissan kai ashe ba kaunata kike ba gudan jinina zaki kashe mun wato shiyasa kika ce bari ki kawo mata lemo dan kirabani da abin da nafi so meyasa zaki mun haka dan kinsa ina sonki bazan iya rabu dake ba zaki sawa Aisha maganin zubar da ciki me ta miki ko ni me na miki.

Arikice zee ta dago ta kalleshi jikinta na rawa ta fashe da kuka ta nufo gunsa”Yayana wanene ya cema maka zan iya kashe ko da saurone bare dan mutum waye yake kokarin rabani da kai da kuma yar uwata Yayana kar ka manta nayi Alkawalin mutikar ka juyamun baya arayuwa wlh sai na kashe kaina dan bazan iya rayuwa babu kai, ta fada jikinta na tsuma ta nufi gunsa da gudu.

Sardauna hankalinsa ya rabu a biyu amma mugun haushin zee da yake ji bai bari ta isa gareshi ba ya fice da Nisha a hannunsa.

Zeey ta barke da kuka ta nufi gun Rabia cikin masifa da gudun bala’i take kiranta.
Akofar dakinta sukayi karo.

Ta sharara mata mari ta damki wuyanta tana wuci. Arikice Rabia tace”me namiki dan Allah karki ilatani.”zeey ranta ya gama bace
Tace”uban wanene ya sama Nisha maganin zubar da ciki mijina yake zargina ke daya ce agidan yar aiki kuma kinsan ita baza sha abinda zai mata ilaba ki fadamun ubanwa yasaki ta karasa maganar idanunta na fitar da jini dan ta gama zuwa karshan bacin rai.

Wasu irin bakaken kunamu ne ahannunta sunfi guda goma.
Rabia ta gama tsorata da, zee jikinta mugun kerrrma ya keyi bakinta na rawa tace”wlh Allah ban saniba ba ni bace ba Abu daya na sani jiya wata mata…daga wannan bata sake magana ba zeey taga ta fadi bata motsi jikin zeey ya dauki rawa da gudu ta shiga kitchen ta dauko ruwa ta zuba mata ta farka,tana zaro idanu.
Zeey tace”wata mata? ” wlh ban saniba kawai kame kame ne.
Shakuta zeey tayi suka fito ta hankadata parlo.
“Wlh yau sai kin fadi dalilinki na zuba mata maganin zubar da ciki kike neman rabani da rayuwata.

Ta haye saman bene da gudu ta, dauko hijabi ta fito amma sama da k’asa babu Rabia ba dalilinta.

Ciki ta koma ta dauko key daya acikin motocin Sardauna ta nufi rumfar ajiye motoci ta shiga daya ta fizgeta tin karfi take horn.
Megadi yazo ya bude mata kofa ta fice aguje tana rusar kuka ta nufi hospital.

Lokacin da ta isa hospital Sardauna ne da kansa yake ba Nisha temakon gagawa cikin ikon Allah ta farfado sai barci take cikin ya gama zubewa bayan ta zubar da jini dayawa saidai Sardauna ya kara mata jini cikin sa’a akwai irin nata Sardauna kuka yake yana jin ciwon zubewar cikin yana mugun jin haushin zeey dan yayi niyar sai ya bata mata rai fiye da tunaninta sai ya ajiye sonta gefe ya hukuntata.

Advertisements

Zeey tsaye take akofor tana bugawa yana rungume da Nisha ya janye jikinsa ya Mike ya nufo kofar ya bude, zeey yaga tsaye idanunta jajur.
Sardauna ya had’e face yace”lfy malama..?”fashe masa nayi da kuka na fada jikinsa na rungumeshi”Yayana ina sonka kar ka gujeni karka doramin laifin da ba nawa ba wlh bani bace ba mai aikin gidan muce na tsare ta yanzu wlh har dukanta nayi ta fadamun gaskiya yanzu haka ta gudu bata gidan My Sardauna ina sonka karka tsaneni.

Sardauna kasa magana yayi bai kuma tureta daga jakinsa ba idanunsa alumshe yana sauke ajiyar zuciya, wani Abu ya cizo sa ya hankade zeey “karya kikeyi kece baki sona, dan haka nima zanyi nesa dake zan fita rayuwarki tunda baki sona kika sakawa matata maganin zubar da ciki na auna lemon na gani Kenan ke bazaki haihu daniba zainab kinsan ina sonki bazan iya ilataki ba shiyasa kika zubar mun da cikina ya fada yana barin gurin ya koma gun Nisha ya zauna.

zeey ta zube nan k’asa tana rusar kuka mai taba zuciya.
“Yayana zan mutu wlh zan mutu bazan iya jure rashin ka ba, wlh bani bace ba don Allah kamun rai karka rabu dani wlh zan kashe kaina mutikar ka juyamun baya Yayana meyasa kasaka mun dafin sonka azuciyata Wanda yakai matakin karshe kasan bazan iya rayuwa babu kaiba an fadama banajin ciwon mutuwar my Ahkhuya na ne wlh inajin zafin mutuwar sa fiye da tunanin ka kawai mugun sonka ne yake ragemun zafin mutuwarsa tun ranar da ka kusanceni a Saudiya Allah ya jarabeni da tsananin kaunarka amma saboda ka manta meye so har kake tunanin zan iya kashema gudan jinin ka kuma gudan jinin yar uwata Yayana shikenan na barma Allah komai kayi yanda ya dace na amashi kaddara ta fadi tana fitar da wani irin numfashi da sauri sauri idanunta na lumshewa dif numfashinta ya tsaya bata motsi.

arikice Sardauna ya taso”Ya Allah wai wannan wace irin masiface nake gani zainab babu damar kiyi Abu ba daidai ba atsawatar miki sai suma.
Ciccibarta yayi ya bude kofar ya fice ya nufi wani special room da ita ya kwantar da ita saman gado ya dauko ruwa a fridge ya kurbi kadan ya hau gadon ya shigar da ita jikinsa sosai ya tallabo kanta ya dora bakinsa, ahancinta ya fesa mata ruwan da karfi.

ajiyar zuciya ta sauke ta bude idanunta ta ganta kirjin Sardauna ta kura masa idanu kallon da ya matane yasa ta sada kanta k’asa ta cusa kanta kirjinsa tana zubar da hawaye ga wani irin sanyi da takeji zazzabi ya rufeta.

matseta yayi sosai yanajin hucin zafin zazzabi jikinta na ratsashi, ajiyar zuciya yake ya kankameta sosai yana shafa laulausan gashin kanta da ya zubo ya rufe mata fuskarta yana tatara mata gefe daya,ya janyeta jikinsa makaleshi tayi tana rawar sanyi.
Rankwafa wa yayi bakinsa saman kunnanta yana shafa fuskarta “ki sakeni zan hada miki magani bana son zazzabin jikinki ya kara fadar maganar cikin wani yanayi na shauki.
Sakinsa tayi tana nishi.
Ya mike ya sabka ya hada alluran ya shigar da ita jikinsa cikin mugunta ya tsira mata.

hadiye kukan ta tayi ta shige jikinsa sosai ahankali ta furta”Yayana ina sonka bazan iya rayuwa babu kaiba kamun adalci kar ka rabu dani pls Sardauna.”
Makaleta yayi yana wani irin numfashi jiyake kamar ana kara masa sonta da kaunarta sam bazai iya rayuwa babu zainab ba.
k’asan makoshi yayi magana yada bazata jiba ya tura kansa k’asan wuyanta yana jujuya kansa”My Abulena kin gama da rayuwata sonki yamun mugun kamu bazan iya cutar dake ba gashi kin kashe rai amma na,saka miki idanu na kasa fadawa kowa saboda banaso amuzanta mun ke sorry amma dole zan hukun taki.

Zeey kuwa jinta jikin Sardauna ga, Alluran da ya, mata bacci ya dauketa,
sai saukar numfashinta Sardauna yaji.

Janyeta yayi ya sabka ya dauki waya ya kira ghaisha, ya fada mata komai amma baice zeey ba ce ta zubar yace itama bata da lfy zazzabi take ghaisha tazo ta kwana da ita shi jinyar Nisha yake.

Bajimawa kuwa su ghaisha sukazo duk dare yayi har ummi gani zeey ba wani buguwa tayi ba suka koma ghaisha kade ta tsaya gurin zeey sai daddah tace ita zata kula da Nisha amma Sardauna ya tsaya su kwana tare.

Sai can tsakiyar dare Nisha ta farka,Sardauna ya kaita toilet ya mata wanka da ruwan gumi ya canza mata kayan da yaje gida ya kawo, ya bata abunci taci da maguguna ya fada mata gaskiya cikin ya zube haka tayi ta kuka tana cewe zeey ta cuceta amma ta yafe mata dan Allah Sardauna karda ya taba zee ko ya mata wani Abun sai daket ya samu ta koma bacci shima ya kwanta.
Ashe abinda basu saniba Daddah ba bacci take ba idanunta biyu ta jisu tayi mamakin ya akayi zeey ta zubarwa da Aisha cikinta, ahaka har bacci ya dauketa.

Washe gari bayan Sardauna yaje gidansa ya dawo lokacin zeey taji sauki zazzabin Sardauna ya sallamesu amma basu tafi ba ita da ghaisha suna gurin Nisha wacce ta sake da zeey ta nuna babu wani Abu itace ke Jan zeey da hira tana nuna mata karta bari yan gida su sani taji dadin hakan damuwarta daya Sardauna baya kulata.

Advertisements

Da misalin karfe goma shadaya na safe dakin cike yake da yan uwa suna ta zuwa dubiyar Nisha kowa yaji zafin fitar cikin dan sunyi mutikar mamaki cikin wata biyar ya zube kai tsaye batare da tayi doguwar jin yaba ko ya nemi kasheta.
Zeey baby ce zauna kusan Nisha tana rike da hannunta zeey “my dear wlh inajin ciwon wannan zubewar cikin fiye da tunaninki.
Sardauna ne ya shigo da sallama karaf akunnensa idanu suka hada da zeey ya zafga mata harara.
kanta ta kauda zuciyara na mata daci kamar daga sama sukaji murya daddah tace”tsaninku da Allah acikin ku biyu waye ya zuba maganin zubar da ciki alemo da gangan.
Arikice suke kallonta gabaki dayan dakin suka hada baki wajan furta”innalillahi wainnahilahir Rajiun!!
Daddah tace”wlh dole mutum ya zuba maganin tsakanin Aisha da Zainab.

Zeey barkewa tayi da kuka ta, tashi tazo gaban Daddah tana raraba idanu”Sardauna zuface take keto masa hankalinsa amugun tashe idan yana kaunar abin da, zai batawa, zainab suna to yana kaunar mutuwarsa.
Ghaisha tace”nifa bana gane me kuke nufi..kamar daga sama suka tsinto muryar Rabia ta shigo tana cewa”yo dama ta yaya zaku gane ni Nice na keda shedar kumai.
Zeey ta nufi gunta yauwa munafuka yar iska ai dama nasan hakkin rai bazai barki ba dole jini zai tambayeki ki kawo kanki.
Hannu Rabia ta dagawa zeey”dakata malama ke Nisha tsakaninki da Allah ki fadi gaskiya kawai kice Zainab ta zubar miki da ciki dan me zaki boye.
Gabaka dayan dakin ya dauki salati.
Nisha ta fashe da kuka tana girgiza kai” dan Allah Rabia meyasa zaki tonawa yar uwata asiri wlh na yafe mata.
Jikin zeey ko ina rawa yake taji ta tozarta ta kasa koda motsa dan ya tsanta.

Sardauna ya isa gaban Rabia yana karantar wasu yanayi ga me da ita cikin daka tsawa yace”dan ubanki waye shedarki na cewa zeena itace ta zubar mun da cikina.
“Wlh itace amshi waya ka kalla idan baka yarda ba.”Wayar Sardauna ya amsa ya kurama idanu zeey tsaye a kitchen tana waige waige ta ciro magani arigarta ta bude fridge ta dauki drinks irin Wanda Nisha ta sha ta ballo maganin ta bude ta zuba ta girgiza sosai ta maida dan hancin ta rufe ta maida fridge tana tsalle da ihu tana juyi da rawa tana cewa”Sardauna na tsaneka ban taba sonka ba sai na dauki fansa bana yafiya bana Afuwa kuma bani manta ranar daukan fansa dole cikin Aisha zai zube zan kasance cikin farin ciki.

gabaki dayan ilahirin jikin Sardauna rawa yake.
yan dakin dikira suke da salalami.
Zeey ta barke da kuka ta fada saman Sardauna”Yayana ka yarda, dani dan Allah karka bari na tozarta wlh ba ni bace saidai idan wani sharri ne za’a dauramun don Allah kayi wani Abu akai.
Sardauna idanu kawai ya kurama zeey idanunsa jajur.
ghaisha tace”Rabia zo nan.”Sardauna yace”ghaisha wata shedar kike nema bayan wannan.
Rabia ta juya zata gurin ghaisha Zeey ta saki Sardauna tayi wani irin uban ihu tayi kukan kura ta damki wuyan Rabia ta mata muguwar shaka, amma sai kawai ta yanke jiki ta zube k’asa sumammiya.
Aguje Sardauna yayo kanta yana kiranta gabanta ya zube ya dagota ya rungumeta yana shafa fuskarta”Zainab tashi kallon Rabia yayi yana mata wani mugun kallon tsana yace”kinsan Allah Yau zakici durin Uwaki huncin ki sai yafi na zainab…………………….✍🏻

*8/February/2020*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 16

Advertisement 16 Gefen takardun ya zauna sannan ya kalleta yace’ Mahmud or Muhammad, Bata bashi amsa ba taci…
Read More

TARTSATSI 40

Advertisement *page 40* ********************* Mai napep yana ajiyeta, kudinta da tafita dasu dama bata bada ba, aikuwa cikinsu…
INAYAH
Read More

INAYAH 38

Advertisement 38_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Tana fitowa gidansu rungume da jaririyar tata dake lafe kirjinta tana bacci taji qafafuwanta na…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 6

Advertisement _*Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka*_.…
INAYAH
Read More

INAYAH 43

Advertisement   43_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Daga gidan Dr iklimat Hadiza sake komawa tayi gidansu hajiyar MAJEED wannan karon tana…