A BAKIN WAWA 2

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

 

2

 

Bayan sallahn magriba kowa Yana gida amma banda Ummusalma tana dakinta tana assignment yaran Maza  gidanne suka shigo dakinnta game da sallama,amsa musu tayi Amma babu Wanda ya jita,a bakin gadon suka zauna suna kallanta kasancewar a tsakiyat gadon ta zauna,dago Kai tayi ta kalle su

 

tace’ Yusuf,Yaseer

Atare suka amsa mata duk da sun San cewa daga nan ba zata Kara masu magana ba Amma bedame suba sai ma Kara gyara zama da sukayi suna kallan zanen da takeyi na biology

Yusuf dinne

Advertisements

_____

 

yace’  yaya wai taya kika iya Zane haka?ke kowanne Zane kin iya ne?

Yaseer yace’ Yaya yanzu idan na maki kwatance mutum zaki iya zana sa ?

 

Akace maka a film ne da zata iya zanashi?kodon kaga a film anyi?

 

Ai yaya zaki iya ko?

Ya tambayeta Yana kallan fuskar ta da bazaka iya karantar taba,

Nodding Kai kawai tamasa batare da ta kalle  shiba,

Yusuf yace’ Yaya idan kika masa Nima sai kin zana min PJ mask daman kin dade Baki zana min ba. A shagwa e ya karashe maganar yana kwanciya Akan gadon.

Yaseer yace’ dalla can wai Kai don aji tausayinka a maka ai yaya baza ki masa ba ko? Yasan ba kulashi zatayi ba kuma yanzu don dazu ya samu ta daga masa kai

Cikin sauri Yusuf ya tashi yace’ dalla waye dalla din??

Nima waye dalla din??

Kan kace me sun fara kokawa kowa Yana cewa ai ance masa dalla. Ko dago Kai batayi ba bare su sa ran zata raba su kamar da,haka suka karaci kokawar su suka Gama suna mai da numfashi

Advertisement

_____

Mai aikin ce tayi knocking Yusuf yaje ya bude tace’ Hajiya tace ku fito kuci abinci,ta juya ta tafi, komawa yayi batare da ya kalli Yaseer ba

 

yace’ kazo abinci,wai Shi be yarda cika Yana batsewa,yajuya ya tafi,shima Yaseer din sauka yayi daga gadon

 

yace’ yaya sai da safe Tunde ke yanzu bakya cin abinci,be jira amsar taba ya sauka don yasan ko ya jira ba ji zaiyi ba.

Suna fita ta kalli kofar dakin kwalla taji ta cika Mata ido da sauri ta kawar da tunanin da ta Suma ta cigaba da zanen ta har ta Gama sannan ta dauko Qur’ani ta karanta har aka Kira Isha,bayan tayi sallah takwanta don tayi bacci duk da tasan ba bacci zatayi ba yanzu hira zatayi da abokin ta,mai bata shawara haka tayi, tayi har kusan Goma bata runtsa ba sai daji baccin tukun tayi addu’a.

Asuba tagari

 

 

🌼🌼🌼🌼🌼

A parlour kuwa da suka sauka yan gidan na dining har sun fara cin abinci su Abba da mama sai Sameera(yarinyar dazu) suka karaso kowa fuskar nan a murtuke take wai su a dole fushi sukaja kujera suka zauna suna kowa yaja plate ya fara cin kasancewar an  zuba masu.mamace ta kalle su

 

Tace’ yanzu haka fada kukayi ko??

Ta tambayesu tana kallan daya bayan daya.

Kamar daman jira suke a tare suka dago sukace

 

To bashi  ne ba?

Yusuf ne a ya aikawa Yaseer da harara

 

yace’ ai mama Shine yace min wai dalla

 

Nima ai ka fada min,kuma kai ka  fara cakumoni ai nagani.

 

Ya isa haka Abba ya tsawatar masu,shiru sukayi sai hare hare itama mama bata Kara cewa komai ba.

 

Sameera ce tace’yanzu akan Dan wannan abin shine kukayi fada, kukam bansan sai yaushe zakuyi hankali ba wallahi,

Ba Wanda ya tanka Mata haka suka Gama cin abinsu suka wuce sallah.

 

Yusuf yau bacci nake ji bazan tsaya kallo pi mask ba,kaji ko,

Ko kallan ba beyi ba yacigaba da kallansa,

 

Kaji ko,gobe Ka ban labari, na tafi?? Ya fada cike da zakuwa,

Namma shiru

 

Magana fa nake maka na tafi naje na kwanta zaka ban labarin na yau, kaga nima ina baka ehh na tafi?

A fusace ya juyo

 

Yace’nifah ka dameni,na hanaka tafiya ne? Tafi mana

Wata dariya yayi yace yesss kayi magana yau daman nace sai kayi magana ai indai munyi fada sai kayi tajin haushi ni banga abin Jin haushin ba tunda de ya wuce ai ko?

Besan sanda yayi dariya ba yace’ naji kasani magana sai me kuma?

 

Nifa yanzu kwata kwata kallan ma ba dadi daman yaya ce take sawa gidan ma Yana dadi Amma gashi yanzu ta koma wata shiru shiru da ita,

 

Nima fa kawai kallan nake amma badan dadi ba, da gidan ma nikam yafi min dadi,

Basuyi kallan ba har goma suka tashi suka tafi dakin su don kwanciya.

********Mama ta kalli Abba

 

tace’ me kake gani game da tura Ummusalma karatu kasar waje?

Dakatawa yayi da abinda yake

 

yace’ sabida me kikayi wannan tunanin? Kina nufin can zamu koma da zama har sai ta kammala karatunta ko kuwa ya kike nufi?

 

Tace’ba haka nake nufi ba kawai mu turata can don nikam gaskiya na gaji da zama da ita gaskiya wallahi kana gani de ta canja cikin shekara daya da kusan rabi,duk wani Abu da muka daurata akai ta ajje shi gefe,

Numfasawa yayi sannan

yace’ tou daman me mukeso ne dangane da ita komai ai abinda muke cewa tayi Shi takeyi walau mekyau walau marar kyau,to kin gani,

 

Ummmm Alhaji Kenan a gani na idan har taje can kaga ba ita ba karatu, kaga fa bata San kowa ba kuma ita kadai cezatayi rayuwar ta daga nan sai ta samu gurbataccin kawaye su daurata a hanyar su kaga shikenan mu rabu da ita,zuwa gidama sai taga dama,Amma idan tana nan kawayenta gabadayan su suna San karatu kuma makarantar da suke ita ma cewa zatayi nàn take so kaga daga nan sai sharawa da Shiga tsakanin har su ja ra’ayinta,

Tunda da tafara yake kallanta burinshi be wuce kar tayi karatu mai zurfi ba sannan tazo tace zata zama CEO na company dukka ba company daya bane Amma Shi kam gaskiya bazai iya bata koda guda daya bane balle kuma duka,duk dakanta take cewa ita Business zata karanta kuma ta zama CEO,Amma yanzu Jin wannan Idean na matar sà ya yarda dari bisa dari kuma daman yarinyar bata da wani kokari tunda daman  performance dinta tunda ta fara double number take dauka a tayi kokari tazo ta ashirin asu talatin.

Mamace ta katse Shi ganin shirun yayi yawa

 

Tace’Alhaji ya dai naji shirun yayi yawa ko baka amince bane?

Ajiyar zuciya ya sauke sannan

 

Yace’wato saratu bansan mezan ce bane ai tunda kika yanke shawarar nan to tayi kawai Allah ya shige mana gaba.Da ameen ta amsa

 

**********

Washegari kamar yarda ta saba tashi haka tashi,bayan tayi sallah tayi wanka tasa uniform dinta lokacin har 7 yayi sabida akwai ta da nawa komai yanzu a hankali take yinsa  sabanin da,

Time table ta duba ta dauko books dinta tasa ajaka,zama tayi ta sa socks dinta sannan ta jawo wayarta ta duba time gani tayi 7:25  yau har ta dan makara dukka ko Akan yarda take fita kullum,fitowa tayi ta shiga dakin baban su ta bude cikin safe ta dauki kudi kusan rabin rapern yan dari biyar tasa a jaka ta fito ta wuce.

Kamar yarda tayi tsammani hakan tagani su duka suna dining suna cin abincin su, dauke Kai tayi ta wuce taje kofa kenan Yusuf ya taso da gudu ya rungumeta ta baya shima yaseer zuwa yayi ya rungumeta,juyowa tayi ya hada su ta rungumesu yaseer

 

Yace’idan kin dawo zaki min zane na ko??

Da sauri Yusuf ma

 

yace’nima zaki min ko?

Kamar yarda suka sani nodding Kai kawai ta masu ta sunkuyo tayi pecking nasu tare da breaking hug din ta juya ta fice, suna tsaye suna kallon motar ta sun fita kasancewar bata rufe kofar ba,kallan juna sukayi sannan suka juya suka koma suka ci gaba da cin abincin su,

Hajiya mama tunda suka tashi take fama zabga masu harara ta tsani wannan shakuwar tasu, wani takaici ne yakamata,tayi ta antaya masu harara har suka gama,bama su San tana yiba,su surutun Suma sukeyi. Suka gama kowa ya watse suka fito aka kaisu makaranta,kowa ya kama gabansa.

 

 

🌼🌼🌼🌼🌼

Ummusalma zaune a  class a second seat  littafi a gabanta tana karatu Amma a zahiri ba karatun take ba tunani take  Neena har yanzu Bata zoba Anya kuwa lafiya?kodai batada lafiya? Ko kuma sunyi tafiya?

Bata ankaraba taji ana gaida teacher wato har ya shigo da sauri  ta tashi itama.bayan sun zauna taji yan bayanta suna cewa waifa oral test zaiyi mana

Dayar tace’ haka yace,ehh mana haka yace idan mun Kara haduwa zai mana test kuma oral, taaabbb.

Ita duk ba wannan bane damuwar ta damuwarta Neena bata zoba kuma tasan muddin bakayi test dinba bazaai maka make-up ba yazatayi?

Malamin beyi wani bayani ba ya fara daga farko

 

Yace’ you Stand up,

ya nuna ta farkon seat din ahankali ta tashi,

Yace’ explain Imagery or figure of speech, don’t waste my time if u don’t know,

In ina tafara tana fada tana in ina alamar be zauna ba ko kuma bata gane ba don dama ba meaning ya masu ba explanation ne kuma daman sai Wanda ya gane,

 

Is okay, your name yafada

Fada masa tayi ta zauna nan yayiwa ta gaba itama,akazo kan Ummusalma tun kafin ace ta tashi ta tashi ba ta kalle Shiba sabanin Shi daya kalleta,

 

Yace’ give me 6 Non African poetry and 6 African poetry,

Batare da ta kalleshiba ta fara fada masa tunda ta fara yan class din suka zuba Mata ido musamman new comers don wasu a tunanin su ma bebeyace bata magana Ashe tayi tanayi,shikuma direction din da take kalla ya kalla yaga idan ta a kofa kamar me jiran wani ya shigo,har ta gama sannan

 

yace’ your name

 

Amina Muhammad suraj tafada tare da zama ya kalleta yaga ita kaidai ce

 

yace’ your seatmate name,

Ummusalma Mahmud tafada,

Yan class da gulma nan kowa yafara kuskus da seatmate dinsa haka de Akayi har period din ta fita wani ya shigo ba Neena ba labarinta sai taji duk makarantar ta isheta daman ita kadai ce me debe Mata kewa a class din duk sauran ba kulata suke ba wai kurma wasu kuma suce Mata bebeya bata damu ba,amma Neena haka zata sata agaba tayi tayi kuma bata gajiya duk da bata taba tanka Mata ba,har Akayi break nan wasu daga cikin yan class din suka zo zasu Mata cikat karya akan rashin maganar ta tunda suka fara ko kallo Basu ishetaba balle ta daga ta kallesu gani take idan ta takelle Suma ai sun Sami wani matsayi ne babba makuwa,haka suka Gama suka tafi,yunwa take ji dole ta tashi ta fito taje cafeteria ta siya abin da zata siya ta dawo ta zauna tana ci a class,a takure de tajita duk ba Neena,har aka tashi tanan zaune  kowa ya fice sai ita,tashi tayi taje tayi alwala tazo tayi sallah ta fito lokacin har an watse tana cikin tafiyar ta mekama data hawainiya ta hango wata tana watering flowers,

Kamar Neena ta fada a zuciyarta

cigaba tayi ta tafiya taga de itadince,Kenan tazo takuma fada,

Neenan ce ta hangota ta gudu ta zo wurinta

 

tace’daman nasan kece ai kowa yafita sai ke,ke kullum sai kin tsaya kinyi sallah ko?kinga yau banshiga ba ko? Wallahi makara nayi fa shine aka bani wanan aikin nikuwa naki Shiga class,kinga nagama bari nazo nakai wannan Kaya sai mu tafi tayi sauri ta tafi, Ummusalma kawai kallanta take har taje ta dawo suka fara tafiya,kamar daga sama taji Ummusalma

 

Tace’ meke damunki???

Juyowa tayi ta kalli ta,bata taba zata wani zai iya gane damuwarta ba musamman ma Ummusalma datake ganin kamar batda damu da kowa ba amma kuma sai taji sabanin haka,bata kalleta takuma maimaita Mata tambayar

Wani hawaye ne ya zubo Mata da sauri ta goge kar tagani yake  tayi sannan

 

tace’ bakomai kawai de Babane beda lafiya shiyasa,

Ummusalma kallanta kawai take kallan nan  na ban yarda ba,Amma de bata furta komai ba,daidai nan drivern ta yazo,Jakarta ta bude ta Ciro kudi taba

 

tace’uhm

Kallanta Neena ta tsaya yi batareda ta amsa kudin ba, hannunta ta jawo tasa mata kudin ta Shiga mota ta tafi

Tana nan tsaye har motar ta bacewa ganinta hawaye ne ya  zubu kan kuncinta ta kalli kudin

 

tace’ Nasan zaki kewata dayawa Amma daga  yau bazaki sake ganin na ba am sorry Ummusalma,

Tana magana tana goge hawayenta,sannan ta kama hanya ta tafi..

 

🌼🌼🌼🌼🌼

Yunwa take ji yau bata biya ba eatry taci abinci ba kodan da wanne ma kudin zataci bacin duka tabawa Neena,

A zuciyar ta

 

tace’ komai yake damun ta?gashi bansan gidan suba danaje naji ko me ya faru da ita ko wannan Dan iskan saurayinta din nan  ne da yake takura mata?

Juyi kawai take tana tunanin Neena,har ta fara bacci sai ga Yusuf da yaseer sun shigo kasancewar yau ba islamiyya,suka tashe ta ta masu zanen su bayarda da iya haka ta tashi, taje ta bude wata kofa a cikin dakinta suka Shiga  kwaso kayan drawing din sannan ta bude musu balcony dinta na dakin suka zauna  ta kalli yaseer batare da tayi magana ba, da Shi Kenan zata fara don haka ya gyara zama ya fara zayya no Mata mutumin da zata zana masa,

Tunda yafara take ganin wannan zanen nasa hauka ne kawai Amma kuma ga mamakinta sai taga zanen  Yana making sense har taji interest Akan zanen sosai,har ta Gama bayan ta Gama ta kalli zanen sosai ta itama mutumin jiki ya Mata kyau bakan ba, tana kallan zanen taji yaseer Yana cewa yauwa na manta Yana irin wannan abinnaki(tusar jaki) asamar girarsa Saida ta diga taga yamafi kyau.

Yusuf ne ya matso

 

yace’ saura ni yaya,

Zana masa tayi sannan suka maida kayan drawing din suka ajje zanenna su daman a nan suke ajjewa sannan sukayi sallah a dakinnata

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 15

Advertisements _____ pisode 15……………… Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya buɗe , sannan ya yaye lulluɓin…
KALLABI
Read More

KALLABI 69

Advertisements _____ BABI NA SITTIN DA TARA *ALHAMDULILLAHI! RIJIYA TA BADA GUGA…. FATA NA GARI LAMIRI 🥰🤩* Tafiyar…
KALLABI
Read More

KALLABI 54

Advertisements _____ BABI NA HAMSIN DA HUƊU *Ina matan Alfarmar ga maman ZEEY me kayan mata tazo muku…
KALLABI
Read More

KALLABI 32

Advertisements _____ BABI NA TALATIN DA BIYU Duk yadda Aminatu taso kin shiga cikin gidan haka Innayoh ta…