A BAKIN WAWA 4

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

4

Bata farka ba sai 4,da sauri ta tashi tunawa batayi sallah ba,ta shige toilet a gaban sink ta tsaya fuskar ta ta kalla taga yarda tayi wani iri da ita idanta ya kumbura sabida kuka, papern dake hannunta ta kalla ta warwareta ta kuma karantawa taji hawaye ya kuma zubo mata kallan kanta ta kumayi a jikin mirror

Tace’ a duk sanda nake tare dake inajin wani farin ciki da nishadi marar misultuwa,Amma yanzu nasan bazan kuma samun wannan farin cikin ba,kin kuma sani acikin rudani,meyasa zaki min haka ?dole kina da dalilin ki na boye min koke wacece amma meyasa? Duk Daren dadewa Zaki dawo.
Takarashe tana goge hawayen dake zubo mata, adana papern tayi gudun kar ta jike,zoben ta cire shima ta adana Shi a cikin cupboard, alwala tayi ta dauko papern har ta fito kuma ta koma ta hada papern da zoben ta tafito. Azahar tayi,tayi la’asar tagama azkhar sannan ta fito,bakowa a gidan kamar yarda tayi tsammani, kitchen ta wuce ta tsaya tana tunanin me zata ci, fridge ta bude dauko abarba ta yankata kanana,ta dauko madarar ruwa ta zuba tasa sugar,ta dau teaspoon ta fita garden,kujera tasamu ta zauna tana sha tana tunani,acikin zuciyarta tafara saka abubuwa,daga bisani

Tace’ yanzu mezanyi?
Wani murmushin takaici tayi ganin tasamu solution cikin sauki,tasan yanzu burunsu akanta ai, wuri dàya take kallo ta kai spoon bakinta tayi taji babu komai, bowl din ta kalla taga bakomai ta shanye, tashi tayi ta dawo parlour har yanzu Basu dawo ba ji, agogo ta kalla taga lokaci yaja.dakinta ta hau ta bude balcony ta zauna tana kallon harabar gidan,tana nàn har Akayi magriba ta tashi ta koma dakinta,bayan tayi magriba tana azkhar, idon ta ne ya kai kan hannunta,bata ankaraba taji hawaye na zuba da sauri tasa hannu tashare tacigaba da Azhar dinta,kamar kullum ta dauko Quran tayi karatu tayi komai da tasaba har aka kira Isha tayi, tasa kayan bacci ta dauko school bag,karatu tayi sosai wayarta ta jawo ta kalli agogo 11 Amma har yanzu basu dawo ba,kulle kofar tayi ta kwanta.

🌼🌼🌼🌼🌼

Basu dawoba sai 11:30 yusseer sunyi bacci,dakinsu ta kaisu ta rage masu kayan jikin su ta musu addu’a ta fita wanka tayi itama, coffee ta dafa ta kaiwa Abba Yana zaune Yana aiki da system,a gefenshi ta ajje,

Thanks yace
sannan ya daura dacewa banga kun dawo da sameera ba,
Kasancewar bada mota daya suka dawo dashi ba,

Tace’ ai sameera tun dazu tamin waya tadawo,
Gyada Kai yayi cike da gamsuwa sabida yasan Sameera nada hankalin uwa uba kuma ga ilimi.
Haka de sukayi tattauna,har sukayi bacci.

Advertisements

_____

Tashi tayi,ta zauna ta jawo wayar taga 1:30am gaban tane ya fadi

tace’kardai har yanzu Basu dawo ba,
Da sauri ta taso kofar ta bude ta ziro kanta waje ta leka, ahankali ta fito,don ba laifi akwai tsoro, a dakin Sameera ta Shiga dake opposite danata fitila ta kunna Amma bakowa,tsorone ya kamata ta fito, lokaci guda ta tuna sometimes tana kwana a gidan yayar mamansu da gudu ta Shiga dakin su yusseer ganin su da tayi sun dungule suna baccinsu hankali kwance,wata wawar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma dakinta ta kwanta,bata jima da kwanciya ba taji motsi, kasancewar dare kuma ko ina tsit, maimakon ta koma ta kwanta sai ta fito taga waye,a kasan parlour take Jin motsin sbd haka nan ta nufa Sameera tagani a kofar parlourn tana kullewa,mamaki tayi bakadan ba ita bata karasa sauka ba kuma bata komaba ganin zata hawo yasata cigaba da tafiya,maimakon ma ta Mata magana ko kallan ta batayi ba ta wuce kitchen.
Sameera kuwa gaban tane ya fadi Allah yasa bata ganta ba tana rufe kofa ba.Ruwa tasha ta koma dakinta,tana tunanin ko daga ina take Oho?

***********************

Washagari kamar yarda ta Saba duk asabar tana Riga su tashi kafin su tashi tayi wankinta,tayi gyaran dakinta wanke toilet ta gyara duk inda ya dace ta gyara tayi tagama,sai tagama tayi wanka wani sa’in ma sai taci abinci sannan suke tashi wani sa’in kuma ko wanka ma batayi suke tashi.
Tana kitchen taji motsin su yusseer suna fada Akan remote.
Chips da kwai tayi sai sauce mai kifi aciki, fitowa tayi taga yarda suke fadan wannan na fada dayan ma na fada girgiza Kai tayi baza su canja ba sukam,
Wucewa tazoyi

tace’ yusseer abinci,
Bada karfi tayi magana ba Amma sunjita,a Tare sukace Yaya
Wucewa tayi dagudu suka bita summa Rigatà Shiga dakin balcony suka bude suka zauna itama nan ta nufa, bayan ta dauko masu lemo, Yusuf ne ya dauko masu cup,suna ci suna Santin abinsu
Yaseer

yace’ Yusuf nifa yau bazani tahfeez ba gaskiya nagaji nidai.
Yusuf yace’ bawani ka gaji kawai kace baka iya hadda ba, kuma idan baka jeba amaka duka biyu Dana hadda nakin zuwa,

Islamiyya kawai zanke zuwa ta yamma ai itama ana hadda

Oho de nikuwa dole sai kaje ko nafadawa Abba,
Shiru Yaseer yayi bai Kara maganaba yasan halin Yusuf tsab zai fada,Amma kuma ya kudurta bazai jeba.
Ba Wanda ya Kara magana daman shine mai dauko maganar har suka gama suka kwashe kayan suka tafi dashi.
Bayan sun fita tunaninta ta fara har ko yaushe ta jima a wurin sannan ta tashi ta fita, tasan yanzu suna parlour su duka saboda haka dakin Abban su ta nufa,safe ta bude taga kudin ba yawa rufewa tayi ta fito har taje bakin kofar parlourn sai kuma ta dawo tunda take bata taba Shiga dakin ba kullum a rufe,yau kam sai ta Shiga tasan yau Yana gida maybe a bude yake , komawa tayi ta murda handle din aikuwa abude yake,Shiga tayi taga wardrobe ne mai kofa uku kawai a dakin sai bedside drawer guda daya, wardrobe din ta bude taga safe guda uku a jere,buder sauran kofar wardrobe din tayi sauran ma haka ne aciki,
Gwada bude daya tayi Amma be budu ba sunnanta tasa namma bai budeba,tasa sunnan kowa a gidan namma haka,kuma password ne ba pin ba,sunaye tayi tasawa be bude ba,gajiya tayi kawai zata rufe wata zuciyar tace kisa ummu,sawa tayi badan tasan zai bude ba,tasawa safe din ya nuna correct,dadine ya kamata,a hankali taga safe din Yana yin kasa Yana budewa kudine aciki dayawa,kudi Bana wasa ba,da sauri ta gwada sauran Suma duk kudi aciki guda daya ce kawai taga takardu rufe me takardar tayi, dankwalinta ta shimfida ta fara jidan kudin a cikin kowanne safe,ita kanta batasan yawan kudin datake jida ba kawai jida take,dayawa ta kwasa sannan ta rufe,ta kulle dankwalin ta fita daga dakin,Jin za,a shigo parlourn yasa ta buya a bayan labile,Abban ne yashigo,zama yayi ya ciro da wayar sa har ya Gama abinda zaiyi sannan ya tashi ya kulle dakin da tafito ya Shiga dakin sa,Yana shiga itakuma tana fita dakinta tashiga ta Adana kudin,ta kwanta.

🌼🌼🌼🌼🌼

Ranar Monday ta Gama shirinta tsab, dauko jakarta ta tayi zuba dubu dari dayake ta kirka dari dari ta ajje duka one million ne da duba dari biyu,wayarta ta dauka ta fita,bakowa a parlourn ta sa Kai ta wuce abinta
Banki tace ya kaita,bata fada masa wanne ba kawai taga sunyi parking a access,fitowa tayi ta Shiga kasancewar da wuri tazo yasa aka Mata da wuri account ta bude tabada dudu Dari amata transfer cikin account din,
Gobe kace tazo ta karbi atm card.
Daganan park tace ya kaita ko zata ji dadi don kwata kwata bata ra’ayin zuwa school yanzu sabida ba Neena,
Ahaka ta karashe ranar har yamma yadawo ya dauketa.
Washagari ma haka bataje ba daga karban atm park ta wuce,tayi zamanta har yamma.sai Wednesday ne taje amma badan tasan me ake cewa ba kawai tunani take ahaka de satin ya cinye kullum sai ta ba driver dubu dari ya kai banki an Mata transfer a account dinta.

 

🌼🌼🌼🌼🌼
Haka ruyuwa ta cigaba da tafiya a wurin Ummusalma kullum ba dadi,kullum cikin kadaici take duk da su yusseer na debe Mata kewa Amma ita kam bata gani haka,haka idan taje makaranta ji take kamar Neena zata dawo Amma kuma baita ba labarinta kuma bata Saba ba,yanzu abin kadan zata tuno sai tafara kuka, musamman idan Neena ta tuno,abin har mamaki yake bata,tayi bakin kokarinta ta daina kukan Amma inaaa bata iyawa sam.
Gashi har sun Gama waec da neco yau watan su 1 da gamawa saboda haka maganar tafiyarta kawai ake tayi.
A yanzu tunaninta ya karu kuma kwakwalwar ta takasu kusan uku da tunani na daya neman mafita nabiyu kuma abin da zata karanta na uku kuma Neena,wannan abin yabin yana damunta kwarai da gaske batasan ya zatayi ba.

Fitowa tayi kasancewar yau Friday bakowa a gidan sai ita, parlour ta sauko badan tasan me zatayi ba,idan ta Akan TV ta sauko tamanta yaushe rabon da tayi kallo hakan nan yau taji tana so,kunnawa tayi ta zanja Channel zuwa india,film din dake kallo ne ya fara Jan hankalinta,na shahid Kapoor mamanshi naso yayi police shikuma naso yayi film,wani tunani ne yazo Mata,da sauri ta tashi ta kashe kallon tasami mafita Kenan,
Da daddare yaseer ya kirata yace Abba na kiranta,bayan shi ta biyo har parlour inda Abba yake zaune
Zama tayi batare da ta kalle shiba,shima Bai damu ba

yace’ wato Ummusalma kinsan mu muka haifeki,kuma kunfi kowa sanki sabida haka badan bama sanki ba zamu tura ki wani guri mai nisa ba,sai dan muna sanki kiyi karatu mai zurfi,ki taimaki alumma gaba daya kinji ko.
Kallan Shi kawai take bako kiftawa tsayawa tayi kamar statue tana kallon shi,
Mama dake gefenshi tacigaba

Advertisement

_____

Tace’ muna matukar kaunarki kinji ko yata,abinda nake sodake Shine kiyi kokari ki maida hankalinki, kiyi rayuwar ki tamkar da kiyi hulda da jama’a sosai.
Sannan kuma zaki karanci gynecologist kinji ko Shi aka samu,don har babanki ya Gama komai da komai da ya kamata har hostel kinji ko?

 

By: “`Hijjart“` “`_Abdoul_“`

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 37

Advertisements _____ BABI NA TALATIN DA BAKWAI Kallon juna suka yi da Innayoh, kowacce fuskar ta dauke da…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 9

Advertisements _____ €pisode 9…………….✍️   Duka ƙarfinta take sakar ma Naheela amma ina, jikin Naheela ya rikiɗe ya…
KALLABI
Read More

KALLABI 28

Advertisements _____ BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS “Karya ne!” Rike hannun shi Waziri Zakaria yayi yana mishi alama…