A BAKIN WAWA 5

Advertisements

_____

5

Kawai kallansu take yi,ba ko kiftawa, idan suka ce suna Santa wani irin bakin ciki takeji,wai suna Santa.
Abba ne ya mika Mata envelope

yace’ gashi takardunki ne da komai da komai mun ajiye copy a wurin mu,abinda nake so dake shine kiyi karatu,shine ya kaiki,banasan shirmen banza kina jina ai,
Batasan mezatace ba shiyasa ta zabi da tayi shiru,Amma har yanzu bata dauke idan ta akansu ba kallon su kawai take kallan irin kun tsaneni dinnan

Tafiyar kuma Nanda sati daya ce kinga saura kwana takwas kenan,sabida haka sai kifara shiri kinji ko,muryar Abba taji ya fadi haka,
Ganin sungama magana sun dauko wata yasa ta tashi ta fita,dakinta ta koma ta zauna a balcony, envelope din ta bude ta zaro takardun ciki ta dudduba komai, su biyu ne a dakin,don har sunan dayar akwai saidai ba musulma bace daga ganin sunan,maidawa tayi ciki,ta jingina da kujerar tana tunanin tafiyar kuma da dukkan alamu ita kadai zata tafi ina laifin ma su tafi tare sai su dawo Amma zata tafi ita akadai sai kace wani namiji,kuka takesonyi ko zata ji dadin abinda takeji amma yau taga bata da alamar yin kukan,tana zaune anan bata San iya adadin lokacin da ta dauka ba tana tunani, dakyar ta tashi ta rufe kofar, alwala ta dauro ta fara sallah tana rukan Allah yasa da alkhairi a cikin tafiyar ta kuma,tare da shiriya.
Tana kwanciya bata jimaba aka fara Kiran sallah dakyar ta tashi da aka shiga sallah,tana idarwa kuwa ta koma bacci.
Ba ita ta farka ba sai shadaya shima su yusseer ne suka zo suka tasheta zasu wuce tahfeez yau za,ayi hakan yasa akace suje goma Amma sai suka ce sai shadaya akace suje, zuwa sukayi suka tasheta suka Mata sallama sannan suka wuce,
Tashi tayi ta gyara dakin,yaukam sanyinta ta Kara karowa don Saida takusa awa daya da rabi Dana gyaran dakin tanayi tana tunani,ta wanke toilet tayi wanka,batajin zata iya wanki shiyasa ta hada takai laundry.
Lemo ta dauka da biscuit taci ta koshi, fitowa tayi ta Shiga parlourn Abba bakowa a parlourn sai tv dake aiki,dayan dakin ta shiga kudi ta dauko ta dawo dakinta kirga su tai sannan ta zuba su ajaka key din motar ta dauka guda daya Wanda yake wurinta ,sarkan gold dinta ta dauko da receipt dinsu ta hada ta dauko wani key din motar ta Wanda yake a wurinta guda daya shima ta hada.
Bayan tayi sallahn la’asar ta hada su Duka ta sa acikin jakarta, ta fito sameera kawai tagani a parlourn da’alama yau bata je islamiyya ba,wucewa tayi ta fita harabar gidan, drivern ta na ganinta ya taso da Dan gudunsa,yazo zai gaisheta saidai kafin ma karaso ta karasa wurin motar,budewa tayi ta Shiga, shima Shiga yayi sannan suka fita,inda zai kaita ta fada masa,sarkarta ta siyar,ta dawo kudin ta Mika masa,tace ranar Monday yasa Mata a account,daga nan ya kaita park,ta zauna sai dab da magriba suka dawo gida,har zata fita ta bude jakar ta Ciro mukullin motar

tace’ kasiyar da biyu ka samun kudin account,
Ta juya ta wuce.
Kallanta kawai yayi to wacce zai siyar tunda ya gane motar take nufi,Bari kawai ya siyar biyun a ajje Mata sabuwar Amma Allah yasa kar yayi laifi.

🌼🌼🌼🌼🌼

Washegari da rana gaba daya gidan suka tafi rakata shopping banda Abba,duk wani Abu da zata bukata,kayan sawa kam an jide su ba laifi,ita kawai ido ne kawai nata, daga nan suka wuce yawo Basu suka dawo ba sai tara na dare, don haka kowa dakinsa yayi ya kwanta.
Haka mama tasa drivern gidan yake kaita gidan kawayenta acewarta tayi masu sallama,ita kuwa duk inda taje ko sallama bata masu bare kuma gaisuwar da daman can ba gaida su take ba,ko ruwa batasha bare aje ga abinci,haka zata karaci zamanta ba magana,idan kuwa zata tafi ba sallama take wucewa abinta,Haka kawayen mama zasuyi ta kiranta suna Mata complain akan Ummusalma,ko mama ta sameta ta mata fada,bazai hana gobe ma idan taje takuma yin shirun ba,tun mama nayi har tagaji tayi shiru.
Ya rage sauran kwana biyu ta tafi ta dena fita ko’ina tana gida abinta,mama kam ba laifi ta Mata snacks da dambun nama sai yaji dayawa, kasancewar tana San dambu da yaji,Sameera ce ta hada Mata kayanta ana gobe zata tafi,tana zaune tana kallanta tana shirya Mata kayan. Tunanin Sameeran take a zuciyar ta,yanzu iyayenta bama iya iyayenta ba kadai ba mutane dayawa kallan mai hankali suke mata ga nutsuwa da kokari, gata da biyayya dai daibgwargwado, yarinya mai Shiga Rai indai har kazauna da ita zaka fahimci hakan,Amma kuma anyi ba’ayi ba wai an raka bako ya dawo, iyayenta na bata tarbiya daidai gwargwadon su amma kuma batare da sun saniba suna tufka ana warwarewa ne,ko kawaye Basu bata taba to ta tabbata samari na bata ta.sameeran ce

tace’ yaya kuma yanzu zaki na dawowa gida?
Nodding Kai tamata alamar a,a

Advertisements

_____

Taaab har shekara shida ko?
Namma de daga Mata Kai tayi alamar ehh,
Cigabawa tayi

Nikam da nice gaskiya zan dawo,
Nama Gama hada maki kayan bari na tafi,
Tashi tayi ta fita,tabi bayanta da kallo,har ta fice, ajiyar zuciya ta sauke daga bisani taje tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga tayi rolling tasa takalmi ta rataya jaka ta dau key din mota fita.
Gidan su Neena ta nufa sai yarda ta ganshi ranar da suka zo haka yake babu abinda ya sauya,fita tayi ta Shiga gidan matar da suka Shiga, sallama tayi ahankali tasa Kai ta shiga,matar na zaune akan tabarma tana yanka alaiyyahu, lalle matar tamata tabata wurin zama,bayan ta zauna ta kalli matar

Tace’ ina yini
Da fara’arta matar

tace’ ahhh wallahi lafiya qalau ya mutanen gidan ?
Shiru ba amsa,ta kuma

cewa’ ince de kowa lafiya,
Namma de shiru,
Ta kuma
. cewa’ to madalla ya hanya kuma?
Girim ba amsa,ganin haka yasa matar

cewa’ni kamar Ummusalma?daga Mata Kai kawai tayi
Tace’ to ai yayi,
Kinga kinzo ban baki ko ruwa ba yi hakuri Bari na dauko,.tashi tayi taje ta dauko Mata ruwan,
Kallanta tayi a zuciyarta tace tafiye surutu ca duk amsar ta dayace amma ta damu mutane ya kaza kaza mtsw taja tsaki,ruwan ta kawo Mata ta ajje,
Kallanta Ummusalma tayi bayan ta harhado abin fada,

Tace’ Amina fa?shiru?
Matar kallanta ta danyi,yanzu fisabilillahi maimakon tace ya labarin su Amina ansamu ko kuma har yanzu shiru? Amma shine zata ce Amina fa? Shiru?
Numfasawa tayi tace’ wallahi har yanzu shiru,ba amo ba labari,kuma su ba wayaba, bare a Kira aji ko lafiya?
Kudi ta Ciro ta jakarta ta ajje sannan ta tashi ta fita,da ido matar ta bita

tace’ohhhh ni yau fatsimatu kekam wannan daman kurma ko bebeya akayi ki tunda Baki San magana.
Ta jima a cikin mota tana kallan bracelet din da Neena tabata,Neena ce mutum na farko data sota Sona tsakani da Allah,gashi yanzu ta tafi ta barta,goge hawayen da ya zubo Mata tayi sannan ta ja motar ta tafi,park ta nufa,Itakam a rayuwar ta tanasan zuwa park duda yanzu ba wasa takeyi ba Zama kawai take tasha ice cream,amma tana San zuwa,
Zama tayi tana Shan ice cream tana kallan yarda yara ke wasan su hankali kwance,sam Basu da damuwa.
Tana nan zaune ganin magriba ta gabato yasa ta tashi ta tafi.
Kamar kullum driving take a hankali,yau kam tunanin take kawai tana driving,da karfi ta ja wani irin wawan burki, sabida jan danjar da aka bayar amam kwata kwata bata luraba,don har ta kusa bige wani dittijon mutum Amma dukda haka sai da ta Dan bige Shi,da sauri ta fito,mutane har an taru anzo kallo,ganin bata wani bigeshi sosai ba kuma zai iya yasa ta koma cikin motar,namma mutane har sun fara magana akai saidai kuma ganinta da kudi yar Rafa guda yasa kowa yaja bakin Shi yayi tsit,kamo hannunshi tayi ta damka masa kudin,ta kalle she bata taba ganin mutum mai kwarjini irin wannan ba,bata taba kallan mutum taji gabanta ya fadi ba sai yau,yau takasa hada ido da mutum,yau itace take Jin zuciyarta na bugawa saboda wannan mutumin,cikin sauri tayi kasa da kanta,samun kanta tayi da magana cikin rauni da taushi gami da nutsuwa, ahankali kuma,

Tace’ Baba kayi hakuri,wallahi ban lura bane,amma ga wannan Ka sai fruit ka sha kar Ka zauna haka Baba,
Kara damke hannunta yayi

yace’ Allah yayi maki albarka yata, Allah ya kareki, Allah ya biyaki duniya da lahira Allah kuma ya jikan magabatanmu,nagode sosai yata nagode nagode,
Sannan yasa Kai ya fice yabar ta a tsaye tana kallanshi, gani take kamar tasan mutumin Amma kuma a, INA????
Horn taji ana Mata tazo ta zanje motar ta,zuwa tayi ta Shiga,ta tafi,
Lokacin da taje gida an fito daga magriba, parking tayi tafito,so take takira drivern ta amma bazata iya daga murya takirashi ba kawai tadau waya ta kirashi,Yana ganin kiranta ya tashi Dan ma yaga zuwanta,durkusawa yayi

yace’ gani madam,
Mukullin motar ta Mika masa,
Karba yayi ganin zata wuce dasauri

yace’ madam amm daman naga gobe naji ance zaki tafi karatu kuma daman ke kadai nakewa tuki a gidannan,gashi kuma Alhaji ya sallameni,shine nace mezanyi da wannan din?
Tsaki taja a zuciyarta sannan

tace’ idan baka so Ka yar,
Tasa Kai ta wuce.
Ikon Allah ya furta Shida tunda yake beta tunanin zai samu motar nan ba shine ya bar sabuwar Ashe rabonsa ce Ikon Allah, Kenan cike da zumudi yadawo benchi sauran ma’aikatan ya fada masu,sun tayashi murna kam balaifi.

Sallah tayi sannan ta dauko Qurani ta karanta, taso ace tayi sauka kafin ta tafi,Amma kuma hakan ma ta godewa Allah da tasamu,kuma Insha Allah bazatayi sakaci ba,tana nan zaune har Akayi Isha tayi, sannan tayi Shirin bacci,ta kwanta Kenan mutumin dazu ya fado mata rai,babu abinda yafi mata dadi irin addu’ar Shi,batasan idan akayi kyauta haka akeji ba,to ita wama ta taba bawa Abu?Neenace kawai take sai mata chocolate kuma idan ta kaimata ma sai tace’ ban gode ba kuma bazan gode ba,amma hakan bayana nufin idan takuma bata takuma cewa hakan ba.ajiyar zuciya ta sauke tana Kara tuno inda tasan fuskar mutumin nan,ganin ba mafita yasata sauka a gadon ta kunna fitilan dakinta, dakin zanenta ta Shiga ta yaye abinda take rufe zanen dashi,zaninka kalakala duk abinda taga ni indai ya Mata kyau to sai ta zana shi,a da tana bawa zanen muhimmanci kusan shine yake cinye Mata lokutanta. Bin zanen take daya bayan daya don duk sunyi kura,Idonta ne ya tsaya kan zanen yaseer da ta masa daukowa ta kura masa ido,tabbas kamar su daya dashi,kayan drawing ta dauko ta zauna adakin tafara zane, mutumin ta zana sak sak Shi,sosai kamaninsu suk Yana tsaye cikin kayan data ganshi babbar riga ce a jikinshi Amma duk ta Kode,ta tsufa sai dai awanke take tas,kallan zanen takeyi wani iri Abu take ji mai kama da nishadi da nutsuwa,ganinta fara jin bacci yasa ta fito da zanen a hannunta ta daura akan mirror takashe fitila ta kwanta.
Da Asuba da ta tashi sai da tayi addu’ah sosai da sosai akan tafiyar ta,batakoma ba ta zauna tana harda har gari yayi haske sosai,komawa tayi ta kwanta,bacci ne ya kuma dauke ta batare data sani ba,jirgin 11 zatabi,bata sani ba tana bacci,mamace tazo ta tasheta tace ta tashi ta fara shiryawa,wanka tayi ta fito,zama tayi ta dau zanen ta kalla itakam har ga Allah wannan Baban ya birgeta kuma tana jinsa a ranta sosai,ajjewa tayi ta shirya,doguwar riga baka ta dauka tasa sai rolling ta fito lokacin har 10 tayi,ganinsu a dining yasata karasa parlourn zata zauna,ai da gudu Yaser

Advertisement

_____

yace’ don Allah kizo muci abinci,kinga daga yau shikenan baza mukara ganinki ba inji mama wai har abada haka ne?
Maganar yaron tabbas ta daki zuciyar ta duk da tasan hakanne amma gudun wani Abu yasa ta ta girgiza masa Kai

tace’ zandawo,
Amma kar Ka fadawa kowa kaji ko?
Tsalle yayi

yace’ ehh bazan fada ba, Yusuf kawai Zan fadawa ko?
Daman tasan sai ya fada masa kuma kamar yarda ya fada bazai fada dinba,
Daga masa Kai tayi,yaja hannunta suka nufi dining,kujera ta ja kusa da yaseer ta zauna tea kawai Tasha shima bata shanyeba,
Masu aiki tasa suka fito mata da kayanta akasa a mota,gaba dayansu suka fita Mota biyu sukayi,daya Abba da Mama daya kuma su,kallan gidan take tana kassimawa a ranta ko zata dawo? Ko bazata dawo ba?wama yasani.sune suka fara fita sannan su Abba,idanta ne ya sauka Akan bracelet din hannunta bata san lokacin da tace’ tsaya,
Dakarfi ta fada sabida haka cikin sauri ya tsaya Allah yasa ma Basu fita daga layin ba ko nisa ma basuyi ba, ko gama tsayuwa baiyi ba ta fito a guje,tafara gudu har taje gidan, fara bugawa tayi mai gadi ta zo ya bude mata yayi mamakin ganinta su da suka fita yanzu me kuma ya kawo ta,saura kadan ta bangaje Shi yabata hanya Amma ya tsaya Yana kallanta,da gudu ta shiga,dakinta ta wuce ta Shiga toilet cupboard ta bude ta dauko zobe da papern nan sannan ta fito kallan mirrorn tayi da sauri ta dauko zanen sannan ta fito gudun kar ta bata lokaci,koda ta fito ma a kofar gida ta samesu,kawai Shiga tayi suka tafi.Ajiyar zuciyar tayi Allah ya taimake ta bata manta ba,har sukaje babu mai magana acikin su ,har su yusseer don yau ba kanta,suma bajin dadin suke ba,isowa sukayi kowa ya fito aka fitar mata da kayanta, suna nan aka fara Kiran su ganin su yusseer na kuka ne yasata itama Jin hawayen na zuba mata, amma Itakam ko fargaba bataji ba bare kuma taji faduwar zuciya,gainin irin kukan da suke, yasa Abba yazo kusa da ita

yace’ ya’isa haka,yi hakuri,ban tambayeki ba na manta ina motocin ki suke ne ban ga ko daya ba daga ciki?
Ko kallan Shi batayi ba

tace’ na bayar,haka kawai tace tasa Kai zata wuce ya riki hannunta, dawowa tayi da baya Amma bata kalleshiba ba envelop ya Ciro a aljihunsa ya damka mata sannan ya saki hannun.wucewa tayi ta tafi.sunanan har jirginsu ya daga sannan suka tafi cike da damuwa don hajiya mama ji tayi kamar an cire Mata wani gagarumin dutse akanta,bata da wata damuwa acikin zuciya amma a fuska kam akwaita,haka bangaren Abba shima hakanne.

Ummusalma kuwa a jirginma kuka tayi mai isarta kafin tayi shiru,bacci ya dauke ta….

Saidai muce _safe_ _trip_ Ummusalma πŸ‘‹πŸ‘‹πŸ₯³

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 45

Advertisements _____ BABI NA ARBA’IN DA BIYAR Yadda jikin ta yake rawa, yasa baki daya hankalin su ya…
KALLABI
Read More

KALLABI 49

Advertisements _____ BABI NA ARBA’IN DA TARA “Yazidu!” Ta daka mishi tsawa, juya fararren idanun shi yayi akan…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 34

Advertisements _____ Kallanta yakeyi bako kiftawa tunanin da yake ya tasheya ko a’a yama Rasa me zaiyi,sai yayi…