A BAKIN WAWA 6

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

6

Sai 8pm suka isa, Ummusalma tayi bacci har tagaji ,gawata azababbiyar yunwa da takeji, babu abun da taci tun tea din da tahada ta sha bata Kara cin komai ba,a jirgin ma ba abinda taci kasa ci tayi,ita ba juriyar yunwa ba,ahaka de suka sauko daga jirgin ta kwasa kayan ta,sannan ta tsaida taxi ta Shiga bayan ta fada masa inda zai kaita, suna tafiya tana kallon garin,ga mutanen kamar yanzu ne gari ya waye a haka suka iso har bakin campus din ya kaita,Bayan ya fitar Mata da kayanta,ta Ciro kudi ta bashi(envelope din da Abba ya bata) canji taga ya miko mata,karba tayi tasa ajaka,tana nan tsaye tana kullawa tana kwancewa yanda zata fara daukan kayanta Allah ma yasa trolley guda biyu ne kawai, sai kuma yar luggage sai hand bag dinta shikenan,shahada tayi ta dauka luggage din sai ta afara Jan trolley din tana tafiya a hankali,kana ganinta kasan ta gaji,kawai tafiya take bama tasan room dinnasu ba bare yanda yake ,kawai de tafiya take abinta,wata baturiyar ce ta ganta, tasan ta gaji duba da irim tafiyar da take ga kuma Kaya,Jan trolley din ma kadai aiki ne, wurin ta taje tace” can I help??
Nodding Kai tamata alamar ehh, trolley din ta karba,suka cigaba da tafiya tambayar ta room din tayi tafada Mata room number din a sama yake don haka sama suka nufa, har suka iso,tare suka Shiga ta ajje mata kayan sannan ta wuce,dakin take kallo ya burgeta komai biyu ne a dakin gado biyu,da bedside drawer sai wurin karatu shima biyu, wardruppe ma haka sai kofa biyu da tagani,ajje kayan hannunta tayi taje ta bude kafa daya balcony dayan kuma toilet ne jakarta ta bude ta dauko abinda zatayi amfani dashi ta Shiga toilet,shima ba laifi ya Mata kyau kamar toilet din gida,kuma gashi a wanke tsab bako kura,wanka tayi da ruwa mai zafi don garin ba laifi akwai sanyi,kuma ga gajiya ta debo, alwala tayi sannan tayi brush ta fito mai kawai ta shafa ta saka wata doguwar Riga,ta shimfida dadduma tafara jera ramuwar sallah,har Isha tayi sannan tayi addu’ah daga nan ta ciro kayan da Mama ta hada mata taci ta koshi.
Kayan ta fara jerawa a cikin wardruppe tana cikin jerawa sai ga wannan dayan tazo taimaka Mata tayi suka gama gabadaya komai da komai,Zama tayi a bakin gadon itama dayar Zama tayi tare da Mika Mata hannu

tace’ I am Sahr
Mika Mata hannu tayi itama

tace’ Ummusalma,
Wani irin kwalalo ido tayi

tace’ umselm?

Not umselma Ummu then salma,

Ohhhh Salma?
Daga Mata Kai tayi sannan Sahr
Tace’ can I say umsalma?
Daga Mata Kai tayi kawai

Sahr tace’ am from Paris, am studying psychology, o level,and you?

Advertisements

_____

From Nigeria study gynecologist,but I will change the course,I want business and psychology ,I don’t know what to do,
Takarashe cike da tausayi, kallanta Sahr tayi ,amma bata tambaye ta ba tunda ba tasan gynecology amma dai tasan is a good course,
Hannunta ta kamo tace’ kada ki damu uncle Dina Yana aiki a school din za’a San yarda za’ayi idan zaka iya studying Duka biyun to idan kuma bazaka iya dole sai kiyi guda dayan.
Kallanta kawai Ummusalma keyi daga haduwa yau yau din nan Amma shine harda temako?
Sahr cigaba tayi kinga kar ki damu bakomai.
Nodding kai tamata, tace’su zo su kwana anan, tunda ita kadai ce,kafin dayar tazo,daman itama ita kadai take kwana dakin su satin ta guda da zuwa Amma dayar bata zo ba.
Haka suka kwanta tayi addu’ah sannan ta lula tunanin gida,bata taba barin gidansu daidai da na kwana daya ba,amma yau ta tafi tayi nesa dashi tasan ita da gida nan kuma sai a mafarki kuma don a lahira bata zatan Tama hadu da su Abba da Mama kuma,wani sashe na zuciyar ta kuma su Yusseer take tunani ko ya zasuji idan lokacin dawowar ta tayi basu ga ta dawo ba? Tasan tunda tace wa yaseer zata dawo to ya kudurta zata dawo din kuma sai yayi ta kirgen kwanaki,indai itace har yayi ya gama.Sahr kuwa video call takeyi da yan gidan su tana yi tana narka shagwaba,yayindda Ummusalma take kallanta don kuwa ta burgeta mutuka,tunuwa tayi lokacin da take ganiyar mulkinta itama, hawaye ne ya zubo mata tayi saurin gogewa,ahaka bacci yayi awan gaba da ita,daman kuma ta gaji saidai baccin da ta sha a jirgi.
***********
Asuba nayi ta tashi don ta Riga da ta saba, alwala tayi, dan lungu tagani a wurin gefen gadonta a nan ta shimfida daddumar ta tayi raka’atul fajr tana Azkhar har lokacin yayi tayi sallah,tana so tayi karatun Qurani kuma bata so ta tsahi Sahr, tasan bakowa ne yakesan haske ba idan Yana bacci,kamar ita duk baccin da take idan aka kunna haske to sai ta tashi,hakanne yasata kin kunna hasken,kuma babu duhu a dakin kasancewar street light dayake ko ina a wurin hasken yana shigowa dakin.wayarta ta janyo ta bude Qur’an app, kararu ta fara ahankali yarda sautin bazai dame wani ba,tana har gari ya fara haske sannan ta je zata koma gado,Sahr ta ga ta tashi,ta nufi toilet,ita dai kwanciya tayi kawai,Amma kuma ga mamakinta data fito daga toilet din wurin da tayi sallah ta nufa hijab sannan ta gyara sallayan daidai gabas sanna ta tayar da sallah,kawal kallanta take daman musulma ce?
Tana cikin wannan tunanin bacci ne ya dauketa.

Bata tashi ba sai tara,tana tashi toilet ta nufa ta wanke Shi tas sannan tayi wanka,koda ta fito Sahr ta tafi dakinsu,mai ta shafa ta fesa turare,tasa kayanta,gadon ta gyara Duka biyun,sai tayi rolling ta rataya jakarta tana Shirin fita sai ga Sahr tazo,tare suka fita suka je cafeteria,ita de dakyar taci abincin daga karshe ma sandwich da lemo kawai tasha, Sahr na Mata dariya,da haka de suka gama, school din suke zagaya wa Sahr ce ke nuna Mata ko ina sun sha yawo a cikin school din sai da lokacin Azahar yayi suka koma daki,Sahr ta kawo masu abinci ita dai kawai tsakura tayi ta barshi,suna hira dukda rabin da kwatan hiran Sahr ce keyinta,ita nata kawai daga Kai ne da girgiza kai, Sahr kuwa bata damu don yayarta ma haka take bata magana kodan sai ta kama shiyasa bata damuwa don ta saba da hali irinnasu,a ganinta magana ne be dameta ba,har lokacin la’asar yayi suka yi,sannan suka fita zagaya campus,namma de sun zagaya dagana kuma suka samu kujera sukayi zaman su suna kallan mutane kowa na harkarsa,ahaka de suka tashi sukayi magriba, Ummusalma ce tace Sahr ta rakata zatayi siyayya,haka kuwa ta rakata sukayi siyayya,itama Sahr din tayi ba laifi,sun jido Kaya harda na girki komai da komai suka siyo,sungaji iya gajiya,sai tara suka dawo da Kaya nikiniki,wanka ta Shiga,koda ta fito taga Sahr ta jera kayanta a wardrobe,kallanta kawai tayi kafin ma tayi magana Sahr din

tace’Tace’na dawo nan da Zama idan dayar tazo sai muyi exchange da ita ko?
Kai kurum ta daga tama,itama daga nan shiru tayi,
Bayan sunyi sallah ta fito musu da snacks da dambu suka ci suka koshi,suka nemawa kayan su wuri,daga nan sai bacci.
✨✨✨✨✨
Washegari Monday da wuri suka shirya suka fita, direct wurin uncle din Sahr sukaje, Sahr ta masa bayanin komai,amsa takardun yayi yace” zai duba anjima su dawo su amsa, a haka suka tafi.
Dakyar dai yayi cuku-cuku aka samu suka bata course biyu physiology dà kuma business. Amma da sharadin idan batayi kokari zasu kwace daya su bar Mata daya,da haka aka barshi, clearance yayi Mata Duka komai da komai kawai sai lectures kuma ko yau ma zata iya fara Shiga. Sahr din ya Kira suka zo,

Yace’ sun bayar da duka biyun amma gaskiya da sharadin,idan suka ga bata yi kokari ba zasu ansa daya su bar Mata daya ne,don haka,ba ita kadai bama harke,kudage da karatu wannan makarantar tana San masu karatu sosai,kunji ko?
Godiya Sahr tamasa sosai da sosai,Yana tafiya Ummusalma ta rungume Sahr,sai hawaye,lallashinta tayi

tace’ ya isa haka ki dena kuka,yanzu mun Zama daya babu godiya a tsakanin mu ok?
Takarashe da goge Mata hawayen,tacigaba tace kinga muna da lectures yau kinsan yau Monday kuma kema kina ta business guda biyu,ga psychology yau har hudu muke da su ya za’ayi?
Kallanta tayi daga bisani

tace’ ai ba yanzu bane,muje kawai ta psycho din,haka suka tafi suna tafiya, sahr ta Mata hira har suka iso sahr ta zauna a gaba ita kuma Ummusalma ta zauna a bayanta don tafi son zaman seat na biyu,a haka Akayi masu lectures ba laifi don ta gane kusan gabadaya abinda aka masu,sai Azahar suka fito sukaje cafeteria sukaci abinci sannan sukayi dakin,bayan sunyi sallah,suka sake fitowa,wannan Karon tana da business saboda haka sai ta wuce sahr ma ta wuce, tana zuwa taji anacewa lecturer ba zai zoba,komawa tayi wurin sahr, lecturer har yazo Shiga kawai tayi ta zauna.
Washegari Basu da psycho sai ten ita kuma tana lectures 8 don haka ya riga sahr fitowa,koda taje ma ita kadai ce bakowa,abinda aka masu jiya ta fito tana karantawa,sai da kowa ya hallara akace ba zai zoba, direct ta wuce daya lectures.

Ahaka sukayi sati biyu suna suna ci gaba da zuwa lectures abinsu idan tayi Mata clashing sahr na koyamata yarda ya kamata,kuma balaifi tana ganewa sosai don a satin da suka fara lectures a satin ta afara karatu,kuma karatu sosai takeyi,tana googling abubuwan da ba’a musuba ma,sosai take karatu bakadan ba hada course is not easy amma kuma hausawa sunce _sa Kai ya fi bauta ciwo._

Yau Friday Basu da psycho Amma ita tana da lectures,shiryawa tayi ta fita,da wuri tana so tayi karatun course din don bai taba zuwa ba amma tasamu abubuwan da zai koya masu kuma ta karanta sosai kamar an koya Mata,bakowa a class din samun wuri tayi ta zauna ta baje littafai tana karatunta hankali kwance abinta,tanayi har aka fara taruwa dahaka har kowa yazo,ita de karatunta kawai take dukda tana Jin hayaniya amma bata dena ba don bata hanata karatu,tana cikin karatu taji anyi shiru,ba’a surutu,a hankali ta dago taga meke faruwa,dagowar da zatayi taji zuciyar ta tayi wata irin buguwa,bata Jin komai sai sautin bugawa da kirjinta keyi,mezata gani BABA??(mutumin da ta zana)Amma kuma wannan yafi Baba haske kuma bashi da tsufan Shi,shikuma Baba a yarda taganshi bashi da wadata,duk bayanin da yake bata ji koda kalma dayace da yake fada ba bata ji komai ba,sai tsinkayo muryarsa da taji Yana fadar sunansa ABDALLAH ABDALLAH,daga nan bata karajin komai ba sai sautin bugawa da kirjinta keyi,tunda ya shigo take faman kallansa,bata kuma dauke kanta ba gashi ita ba sauraran komai take ba bayan sunansa saidai ta lura yayi shiru Yana sauraren wani abu sakamakon gyada kan da yake faman yi, bata Ankara a taji ta gabanta na fadin sunanta da garin da tazo dakuma meyasa take San karantar business, har an gama da kowanne row saura row dinsu,a halinda take ji batajin zata iya magana,bata gama tunaninta ba taji ta gabanta nacewa ta tashi, ita kadai tasan yatakeji a jikinta,gani take kamar kowa yasan halinda take ciki,a zahiri kuwa ba abinda ake gani,tattare da ita,
Ganin anyi shiru ba’a cigaba da maganaba yasa Shi dagowa karaf suka hada ido daman ita shitake kallo,yana dagowa suka hada ido,kallanta kawai yake,wani irin sanyi yaji yana ratsashi na musamman ,a take zuciyarsa tadena bugawa na wani lokaci,a hankali yasaki wata boyayyiyar ajiyar zuciya,sannan

yace’ am listening, your name?
Kallanshi kawai take,batare da tace komai ba,shima ita yake kallo,ganin bata da niyyar magana yasa ya tambayi daya daga cikin class members din, Wanda aka tambaya kuwa ca yace’ ai tunda ta zo babu Wanda ta tabayiwa magan haka take,su suna tunanin ma kurma ce tana ji Amma bazata iya amsawa ba,kallansa ya mayar kanta

yace’ haka ne,?
Batasan ma me akace ba kawai daga Kai tayi alamar ehh, yace ta zauna,Zama tayi akaci gaba da fada,har aka Gama daganan ya fara abinda zaiyi, Ummusalma da kyar tayi nasarar kwabar kanta ta fuskanci abinda ake masu dukda cewa tasan abinda ake Amma kuma rabi gwara ta Kara ganewa ai,sosai kuwa ta gane,suna gamawa ta dawo hostel kafin tadawo sahr ta dafa abinci ta fice,itama abincin taci Amma duk wani iri take ji,bacci tayi har lokacin sallah ya gota,ta tashi wanka tayi ta tayi sallah ta shirya kamar kullum cikin doguwar Riga tayi rolling ta fito,fita tayi tana zagaye gari,wani Dan shago ta gani na kayan pente pente taga kuma yarda mai shagon yake Zane,kayan zanen ta siya ta bada address din campus har dakin su,haka ta gama Dan zagayenta ta dawo,tana zuwa kuwa taga kayan da tasiyo a kofar daki bude dakin tayi ta Shigar da su ta ajje a balcony,ta dawo dàkin ta ,zauna sahr haryanzu batadawo ba,hutawa tayi tafa masu abinci,tayi sallah,Rasa abinda zatayi tayi Dan haka ta je balcony ta zauna tana kallan kasa yarda mutane ke hada hada abinsu, dauko kayan zanen tayi ta hada komai yarda yaka Mata sannan ta fara Zane batare da tasan metake zanawa ba,abinda tasani kawai tana tunanin AA ne(Abdallah Abdallah)koda ta Gama zanen Shi tagani ta zana sanye da bakaken suite yarda yake a tsaye haka ta zana Shi,zana wani ta kuma yi sannan ta zana Baba,a kusa dashi,kalla take tana so tagane menene bambamcin su saidai bataga wani bambanci ba,daukowa tayi ta dawo daki,cikin bedside drawer ta zuba su ciki.
Sai bayan magriba sannan sahr ta dawo, Kallanta tayi

tace’ ina kikaje?
Sai da ta zauna

tace’ naje gidan uncle ne,shiyasa kuma wannan matar tashi tasani aiki wai sunyi Baki, takarashe tana ya tsine fuska, kallanta kawai Ummusalma keyi batayi magana ba, abinci ta kawo masu suna ci sahr na Mata Santi,duk sanda sahr tayi santin abincinta babu Wanda take tunawa kuma sai yusseer Allah sarki ko ya suke?

Haka rayuwa tayi ta tafiya cikin kwanciyar hankali ta jima da siyan simcard Amma bata ma sa numbern su mama ba bare ta kirasu,in fact bata da numbern ba kowa sai ta sahr ita kadai gareta.
Sahr kuwa a bangarenta tana mamakin umsalma tunda tazo bata nemi gida ba,abin na bata mamaki sosai,sai kuma abinda ta lura dashi duk dare tana karanta wata paper kafin tayi bacci haka idan tayi bacci ta tashi sai ta karanta ta,ko karatu zatayi tana karanta papern,ita kanta ta karanta papern ya kai sau ba adadi ita bataga amfanin karantawa ba,tunda indai haddacewa ne to ta tabbata ta haddace ta. Kuma tasan dole wata Rana zata bata labarin ta kamar yarda itama ta bata labarin ta ahaka.

 

Advertisement

_____

🌼🌼🌼🌼🌼

_~Nigeria~_

 

Tunda suka dawo daga raka Ummusalma su yusseer suke kuka,sunki suci abinci,sunki cin komai, suna ma dakin ta Akan gadanta sun rungume juna sun tukuikuye wuri daya suna razgar kuka,mama tayi fadan tayi fadan ta gaji,Basu taba rabuwa da ita koda na kwana daya bane, da can ma dakin ta suke kwana daga baya ne da tayi rashin lafiya suka dena kwana,har dare suna dakin ko sallah basuyi ba bare su tashi suci abinci ,haka har bacci ya dauke su,idan sun farka suyi kukan su suyi bacci,ga yunwa na cinsu Amma inaaa baza su iya ci ba.
Bayan anyi Isha Mama ta fadawa Abba abinda ke faruwa,idan ransa yayi dubu to yabaci sosai ya fusata ya dau charger ya fita da ita sai dakin Ummusalma Yana zuwa lokacin bacci ya dauke su gashi daman sun galabaita,baiyi wata wata ba ya zula musu,wata rin zabura sukayi suka Kara rungeme juna maimakon su gudu inaaa sai suka Kara tukuikuyewa wuri guda takaici ya Kara kama Abba baisan sanda yayi ya tafakar suba suna ihu suna kuka,Mama na gefe don itakam daman abin nasu ya isheta,ahaka yayi ya gaji ya fita,mama ma ta bishi, dakyar Yusuf daman shine mai Dan wayo ya tashi ya tashi ya zauna ya janyo yaseer Yana rarrashinsa lemo ya tashi ya dauko masu da cake da Chocolate,yanaci yana bashi ahaka suka ci dayawa idan suncinye sai ya Kara masu har suka koshi,tashi yayi ya daura kan yaseer a cinyarsa

yace’ Yaya bazata taba dawowa ba,
Kallansa yaseer yayi

yace’ a,ah zata dawo dazu ta fada min cewar kar na fadawa kowa zata dawo ai,

A,ah bazata dawo ba ta fada maka zata dawo ne Amma ba dawowa zatayi ba,
Cike da tausayi yake maganar kana ji kasan Yana cikin kunci ne,

Taya kasan bazata dawo ba ita ta fada maka ne???

Ba ita bace mama naji tanan fada.

Yaushe?? Ya tambaya cike da zakuwa

Dazu ta shigo kana bacci lokacin ta shigo tace’ indai Ummusalma ce bazata taba dawowa garemu ba har abada kuma sai mun manta da ita a kwakwalwar mu,
Ya karashe da kwalla na zuba daga idonsa, yaseer ma kukan yake,

yace’ shikenan yanzu bazata dawo ba?? Kana ganin zamu manta da ita ne?

Zamu manta da ita idan ta mana wani abun.

Mezata mana to?
Kallanshi yayi yace’ ina abokin mu da ya manta da mamanshi? Ka tuna Shi?
Daga masa Kai yayi yaci gaba yace’ to da ya fada min abinda yasa ya manta da shima lokacin da ta tafi ta barshi kuka yayi tayi shine antyn Shi(matar babanshi) taba Shi wani abu yasha tace inji mamanshi tace a bashi yace tunda yasha shikenan be Kara tunawa da ita ba sai da ya gan maman tasa. To itama mama Shi zata bamu bazamu Kara tunawa da yaya ba,
Kuka yaseer yasa don ya tuna wahalar da abokin su yasha kafin yaga mamanshi kulluma idan suka biya islamiyya zasuga Yana aiki idan suka tambayeshi ina mamanshi sai yace’ Shi baida mama.kuka sosai suka Kara sakawa daga karshe, Yusuf

yace’ idan mama ta bamu Abu kar mu karba kuma kar musha,idan ta bamu muce munsha,kuma mudena Zan can Yaya a gabansu ko???
Daga masa Kai yaseer yayi ya rungume Shi,shima rungume Shi yayi

yace’ kanina yau bamuyi sallah ba,
Dago yayi ya kalle Shi kawai sai yayi dariya

yace’ Yayanah ehh haka nefah
Dariya suka tuntsire da ita, yaseer

yace’ taabbb wai Kaine yaya taaab ko a mafarki bazance ma ba,
Yusuf shima dariyan yake yace’ Ka tuna sanda Yaya tace kana cemun yaya ??

Ai naga baka girmen ba da zance maka wani yaya,tsayinmu daya dai,

Amma ai na girmeka a shekaru ko ?

Laaaaaa shekara dayan? Dayace fa kuma Zan biya Ka kadena cewa Ka girmen,daga haka suka tashi sukayi sallah tun Azahar har la’asar kayansu suka je suka cire sannan suka dawo suka kwanta sunayi auna hiran yayar su,
Washegari kamar ba abinda ya damesu suka tashi sukayi wanka,wai su yanzu andena masu wanka,suka sa Kaya iri daya abinsu sunyi kyau kallo suka kunna yaseer yaje ya karbo masu abinci sukaci suka koshi,suka fita wasa,koda mama tace masu abinci fa, sukace sun koshi,
Washegari Monday ma zuwa sukayi suka ci abincin su sukace sun wuce,
Haka rayuwar su tacigaba da tafiya ko mama ta tambayesu yaya cewa suke babu wata yaya agidan idan ba sameera ba a tunaninta abinta yaci saidai kuma ba haka bane Sam don Basu manta da yayar suba…….

 

 

By: “`Hijjart“` “`Abdoul“`
Cwthrt😘

🍂 *A BAKIN WAWA* 🍂
_Akanji magana_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 33

Advertisements _____ BABI NA TALATIN DA UKU. M. GOBIR Bayan shekara daya, masarautan ta zama masarautan mafi karfi…