KALLABI 65

KALLABI
KALLABI

Advertisements

_____

BABI NA SITTIN DA BIYAR

Kamar yadda ake abisa al’ada ajiye sarauta yayi ya raka Gidado, duk da ya lura kamar shi Gidado yana dan jan jikinsa da shi, amma bai fasa shigewa gidado ba, haka ya raka shi har babban zauren Matan Gidado sannan ya fito zai koma sashin sa, shima Gidado ya biyo shi, rike kadadar Lamido yayi, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya rike hannun shi suka ci-gaba da tafiya, bangaren lamido jan hannun Gidado yayi suka shiga wani daki ya shiga dauko mishi wani wasu abubuwa yana mika mishi sannan ya zauna ya mishi bayani kafin ya ce mishi.
“Kasan ban san kome akan sarauta ba, amma zan yi kokari na fahimci wani ba, wannan yana da muhimmanci dan jiya Bana Galadima yake gaya min zaka koma nan da sati toh gashi nan Insha Allah idan ka dawo zamu sauya tsarin mulki tunda shine muradin ka,kayi hakuri ban cika alkawarin da na dauka maka ba, na idan ka zama sarki ni zan zauna a gefen ka domin tayaka zartas da hukuncin da ya dace, nasan kana jin babu dad’i ne Sabida haka ko? Kayi don Allah bani da kowa sama da kai” a hankali ya tako sannan ta rungume Lamido yana buga bayan shi. Sannan ya janye ya kama hannun Lamido ya ce mishi.
“Insha Allah zan zama me baka shawara na gari a kan mulkin ka, sai dai ba wato sati bane tafiya ta jibi ne” ya fada mishi haka da hannu, kamata yayi a ce sun koma wurin matan su, a’a sai suka bude shafin hira da juna, kamar na angwaye ba, ana hira ana dariya gwanin ban sha’awa, wannan daren shine suka dauke shi a matsayin daren su, su biyu dan haka suka baje hiran kiran sallah farko yasa su sake dariya suka fita tare zuwa masallacin, basu dawo ba sai da gari ya waye, sashin Fulani Aminatu suka nufa a rufe an ma hana su shiga wurin Innayoh suka nufa tana ganin su ta fara murmushi.
“Da fatan kun tashi lafiya? Ina matayen ku?”
Zama suka yi sannan Gidado ya Mata magana da hannu ya ce mata.
“Ai ba a wurin su muka kwana ba.”
Ware idanu tayi tana cewa.
“Uban ɗakina akan me haka ya faru? Maza ku wuce wurin matan ku” fata-fata ta kore su, suna dariya suka fita rike hannun Lamido yayi sannan ya ce mishi.
“Matar ka tana jiran ka, ka shiga a matsayin Jarumin soyayya, ka nuna mata duniyarta da duniyarka abu daya ne” murmushi yayi cike da kunya sannan ya daki kafadar shi.
“Nagode malamin soyayya” sannan suka rabu,
A can sashin Fulani Aminatu kuwa, wallahi tsofin nan babu ruwan su, durzan juna suke na yaushe gamo, kamar ba a sha ruwa ba, asalima ko kunya basu ji suke zabga kaunar su.d

**
A hankali ya shiga cikin gidan bayi ne ke ta zubewa daga ko ina na gidan, sashin Anum ya nufa, yana jin muryan ta tana wakar ayeee mama ayyye mama. Tsigar jikin shine ya mike yarrrrr, a karon farko da yaji zazzakar muryan ta tana waka, a hankali yake tafiya.

Har cikin katon turakar ta, tana rike da takobin shi, tana wakar.
_da aure yana raka aure! Da na bi ki mun tafi tare mama ayeee ye_
Ta madubin dakin ta hango shi, yana takowa a hankali. Bayan ta yazo ya tsaya, sannan ya kai hannun shi kan hannun da take rike da takobin, tafin dayan hannun shi ya daura akan shafaffen cikin ta, ya jinginata da kirjin shi, ya shiga juya mata hannun ta da takobin yake rike da shi, zanin da take daure da shi a kirjin ta sakamakon fitowa wankar da tayi bata saka kaya ba, ta shiga daukar takobin da yake makale a dakin, a hankali ya shiga juyata yana koya mata yadda ake aiki da takobin, ba koyarwar bace abin sakon da yake tafiya a tsakanin sarrafa takobin shine abin dubawa, domin a hankali maganar Gidado yake dawo mishi.
“Idan har zaka iya keta rigar mutum da takobin ka, ya kenan idan har ka yi amfani da hannun ka wurin sarrafa matar ka?”

A hankali yake juya ta har suka fuskanci juna, kallon ta yayi.
“Ina kayan ki?”
Ya tambaye ta kamar zuciyar shi zata fita Sabida girman bugawar da take, juya ta yayi bayan ta a kirjin shi, a hankali ya sauya rikon takobin, sannan ya saka daya hannun ya rike zanin sa karfi sai da ta juya ta kalle shi, sassanyar fatar bakin shi ya saka akan kumcin ta, wani irin kasala ya saukar mata wanda yasa ta Lumshe idanun babu shiri, a hankali ya cigaba da tab’a ta, sai da jikin ta ya mutu murus, sannan ya saka kan shi a kafadar ta, juyar da fuskar ta tayi tana shirin kallon shi, ba zata ya sauke bakin shi akan nata. Gabanta ne ya shiga bugawa a hankali ta sake takobin tayi tare da ware hannun ta, shi kuma ya sarkafe hannun shi sa nata, kamar wanda za a kwace mishi ita, wani fitinannen sumbata yake kaiwa bakin ta, kamar zai cinye har da harshen ta, a hankali ya juyo da ita, suna tafiya a hankali, janye zanin kirjin ya yayi, tare da ɗaukar ta kamar yarinya, maganar Gidado yana yawo akan shi.
“Ba wata babba bace da ba xaka iya sarrafa ta ba, a’a ka duba wannan labarin zaka fahimci yadda ake gudanar da rayuwar Aure a musulunci, duba labarin Ummu Salma kaji tambayar da dan ta ya mata akan soyayyar gidan Annabi, karka sake matar ka tayi kewar ka babu hujja baka ga Baffa’m ba ne, ko waziri bai gaya maka bane? Tambayi Innayoh kasha labari karka bari rashin maganar ka ya tauye rayuwar ka da ita. Allah da kan shi ya ce mana matan ku gonakin ku ne, amma karin armashin abin Manzon Allah ya ce kafin ayi nomar sai an fara da gyara yan ciyayin da suka lillibe gonar sannan a aika dan sako, ka aika mata da dan sako, ka koya mata yadda zata dauke ka a kowani lokaci”

Sauke hannun shi ne yayi akan kirjin ta, wani yarrr yaji daga shi har ita, sai da ta ware idanu cikin na shi, sannan ta Lumshe tare da sake mishi jiki baki,

Bai san lokacin da ya gigice yayi ta kaiwa na shanun ta daduma ba kamar xai cinye ta baki daya, kuka take son yi amma da ta tuna abinda Innayo ya fada musu shakaranjiya bata san lokacin da ta k’amk’ame shi ba. Jikin ta yana masifar rawa.
Abinda ta gaya mata yana yawo a kunnen ta.
“Karki sake kishiyar ki ta game kina tsoron mijin ku a shimfida kamar ba mace ba, dole ki zama. Zama Jaruma ki zama me ɗauke bukatar shi, dan haka kar na kuma ganin hawaye a kwance a fuskar ki, ki sake jikin ki babu abinda zai Miki da ya wuce aikin lada wanda zaa a kai har kabarin bakin ki ko baki son ya samu ladar ne”

K’amk’ame shi tayi idanun ta yana zubda kwalla, babu abinda yake D’aga mata hankali kamar yadda bakin ta wuyar ta da kirjin ta, kamar an watsa mata barkono. Sabida aikin sumbatar da suke sha kawai.

Advertisements

_____

Ganin yadda take shashekar yasa shi d’agowa yana kallon fuskar ta, gwanin ban sha’awa, ya sumbaci karamin bakin ta da yayi jajjur, sannan ya janye a hankali, ya bar ta, ya shige ban daki, wani irin yanayi ne ya shige shi yana jin shi kamar yafi kowa Sa’a, koda ya fito ya same ta a nan inda ya barta tana kwance a hankali ya kalli tudun kirjin ta da yadda bakin yayi wani irin, shafa laullausar gashin kan shi yayi ya fita, daga nan bai kuma bin ta kanta ba, amma Tabbas abin ya tsaya mishi a rai. Wani shauki yake ji na fisgar shi kamar zai tashi sama,wani sabon yanayi na kara ninka kan shi, dakin shi ya kwanta tare da jan mayafi.

A hankali kome yake tafiya cikin wani irin taku, na kula da tattali, wanda shi kan shi bai san yana bata ba, sai dai ya tsinci shi a saman ta yake dawowa hankalin shi, tun tana jin tsoron shi, har ta fara sabawa idan yazo yana hada bakin shi dalibar zata dauki haske kamar daama yana ajiye akan ta.
A hankali shakuwa da zaman kurma itama take tare da shi, a cikin kwanaki biyar da suka yi babu abinda ya shiga tsakanin su wanda bai wuce tab’e tab’e ba, sannan yana matukar bata lokacin shi musamman yau da yake son su shiga wurin su Baffa’m, kallon yadda take kokarin daura abin wuya ta kasa,takawa yayi bayan ta ya amshi abin wuyar ya daura mata, sannan ya gyara mata zaman mayafin ta,kafin da dauki alkyabbar ya daura akan mayafin, durkusawa yayi ya ja takalmin alkyabar ya saka mata, tana dafe da kafadar shi, sannan ya mike yana karkade hannun shi. Kafin ya riko hannunta suka shiga takawa a hankali, yana yi yana satar kallon ta, fuskar ta tayi kyau kamar ba ita ba, sai kalle kalle take, gashi dai dare ne amma duk inda duka wuce sai an gaishe su, har suka shiga zauren Fulani da take zaune da sauran matan Bintu a damar ta, Dijah a hagun ta, sai Baffa’m a gefe can Gidado a kusa da shi, Haimah a kusa da gidado, zama yayi sannan Ya riko hannun ta zauna, cikin kunya ta zame hannun ta.
“Barka da isowa Zakin Gobir” gyara zama yayi tare da matso da Anum jikin shi. Yana me gyada kan shi, “barkan ku Ammynmu, barka dai BAFFA’M, Barka Hamma Gidado, Barka Bintu, Barka Dijah, Barka Haima”
Innayoh da kanta ta fara zuwa Abincin,
“Yawwa Barka dai Fulani Anum” inji Bintu.
“Fulani ai daga gidan sarauta ake samun su ba daga rugar Fulani ba”
Murmushi Anum tayi, Lamido ya d’ago kai zai yi.magana Ammyn ta mishi gargadi da idanu.
“Innayoh mu bani ba zubawa Saraki da kaina, shi sunan Fulani daga kabilar fulani aka same shi, na kalubalanci kabilar Hausa ta kira yan matan gidan sarautar su da sunan su, na Yaren Hausa a bar min yarena kar wata kadd’o tai amfani da kalmar Fulani”
Murmushi yayi cikin nutsuwa tabbas, ba gaba da gaba ba, ko ta baya sai an shirya, matse hannun ta yayi. Yana me kara jin wani sabon abun da bai tab’a fahimtar yayi zurfi a cikin shi ba sai yau.”

Haka suka gama cin abincin, ta koma jikin shi ta narke, hannun shi ya zura a cikin alkyabbar ta yana shafa cikin ta zuwa maranta, a hankali yayi kasa da murya yadda ita kawai zata ji shi.
“Kin shirya mai da ni Sarki?” A hankali ta kuma narkewa a jikin shi, tana k’amk’ame hannun shi da yake shafa saman maranta, har ya wuce iyakar. Idan baka san meye yake faruwa ba zaka tab’a kawowa Iskanci Lamido yake a wurin ba, sai da Innayoh ta lura da yadda Anum take kara narkewa a jikin shi, a hankali tayiwa Aminatu magana, ai babu shiri ta ce mishi.
“Lamido! Ka ɗauki matar ka don Allah ka bar mana zauren mu kaji sabon ango” kunya ce ta kama shi da sauri ya zare hannun shi, ba tare da ya ce uffan ba, ya mike ya dauke matar shi cak suka yi waje, suna fita tana haɗe bakin ta da na shi…..
Hmmm
#Mai_Dambu

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 5

Advertisements _____ €pisode 5……………………. Bobbo da har yanzu be gamsu ba, wata muguwar azaba yake ji, sandar girmanshi…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 15

Advertisements _____ pisode 15……………… Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya buɗe , sannan ya yaye lulluɓin…