KALLABI 68

KALLABI
KALLABI

Advertisements

_____

BABI NA SITTIN DA TAKWAS
*PLEASE KU ZIYARCI SHAFINA NA AREWABOOKS KU SAUKE MANHAJAR TA WANNAN LINK MASU APPLE PHONE ZASU IYA JOINING TA LINK KAFIN A SAUKE MUSU NASU MANHAJAR ƘARKU BARI A BARKU A BAYA*
https://arewabooks.com/book?id=62ad9f71e785d1df53cc25ec

_______________________
“Wallahi tun ban ganki ba naji ina da bukatar ganin ki, lokacin da na ganki naji kin dace da matar da nake so, sai gashi daga bakin ki naji baki sona, baki son dan matar da tayi abin kunya. Ban san me yasa nake gudun a tab’a min kimar Mahaifiyata ba, zan sallame ki idan lokacin haka ya samu amma a yanzun kiyi hakuri a matsayin kanwa na dauke ki”

Ya rigada ya fada mata gaskiya, bata ji kome ba sai bayan ta mike ta bar zauren ta tsaya ta fashe da kuka, ta sha kuka, a hanyar ta na komawa ne suka hadu da Mandiya.
“Ranki shi dade ko zaki iya zuwa wurin Fulani Bingel?” Kallon Mandiya tayi sannan ta ce mata.
“Kice mata Ni D’iya ce da aka haifa da d’igon jinin sarauta bana amsa kiran kwarkwarah mara daraja” ta wuce abinta. Koda sako ya isa kunnen Bingel murmushi tayi sannan ta zubawa Mandiya idanu.
“Na samu hanyar da zan yaki Amunatu da Yayanta”
“Indai a kaina ne na yafe, bana bukatar kome sai nutsuwa da zaman lafiya” ya fada yana shigowa cikin uwar d’ak’a.
“Baka da hankali ne? Akan waye nake wannan fadi tashin idan ta nine Gara na mutu akan nayi rayuwar kaskanci, Gara na mutu.”
Zama yayi yana cewa.
“Bana son kome bana bukatar kome, wallahi idan wani abu ya faru ba zan yafewa kowa ba, kuma matakin da zan ɗauka sai ya girgiza kowa,

Ki bar ni na huta, ki bar ni na samu sa’ada nima kamar kowa, matukar kika dame ni zan tafi nayi nisa daga inda kike” ya fada yana me mikewa tsaye, ji yake kamar bai cancanci farin ciki ba, bai zama dole yayi farin ciki ba idan da za a duba tarihin shi bai da kyakyawar makoma kamar kowa. Shi yasa yake jin babu dad’i.

Fita yayi yana kallon yadda garin yayi, kafin idanun shi ya sauka akan Lamido, takawa yayi ya je inda yake. Kallon juna suka yi kafin kowannen su ya juya yana kallon yanayin garin.
“Lokaci guda kazo ka ɗauke min Anum! Baka tab’a nazarin akwai wanda yake son ta bane?”
“Ina ganin girmanka a matsayin Yayana dan haka ka bar ambaton Anum anan”

Murmushi Barkindo yayi sannan ya haɗe hannun shi yana kallon can inda ya hango Waziri da Galadima.
“Ban san me yasa nake jin babu dad’i ba, sai dai ina da yakinin zuwan ku ya taka rawan gani a rayuwata, a Masarautar nan karka yarda da kowa idan da hali karka yarda d iyayen ka, matar ka kawai ce abin yarda a tare da kai, domin ita zata iya daukar kome domin ka, sauran kuwa zasu iya boye kome domin farin cikin ka ka huta lafiya” daga haka ya bar wurin, shiru yayi yana nazarin maganar shi, a hankali ya juya tare da nufar sashin sa, tun daga bakin kofar yake jiyo muryanta, tana dariya tsintar kan shi yayi da dariya, ya shiga ya samu tana shiryawa Innayoh tana mika mata wasu abubuwan a dakin ta, gyaran murya yayi Innayoh ta dan duka mishi.
“Barka da zuwa”
Juyawa tayi ta kalle shi.
“Innayoh shi kenan sai na shigo duba Ammyna”
“Toh Fulani Anum”
“Innayoh!!!”
“Toh gimbiya Anum”
“Hamma kace mata bana so” ta fada a shagwab’e,
“Innayoh Uwar Magajin Gobir tace a cigaba da kiranta sarauniyar Gobir”
“An gama ranka shi dade” ta fita da sauri.
Aikuwa ta shiga buga kafarta a kasa tana mishi bori.
“Yarinya tunda ba birgima zaki yi ba da sauki matar Barawon mutane”
“Hamma” ta kira sunan shi a sanyayye,. Tsigar jikin shi ne ya mike yana jin wani yummm. Fisgota yayi yana kallon yadda take tura mishi baki, a hankali ya kai bakin shi kan nata, k’amk’ame shi tayi, musamman yadda yake tsotsar bakin ta, kara mata jin wani irin kewar shi na tsawon kwanaki goma da tayi tana zibda jinin barin da tayi.
Sun jima a haka, kafin kuma suka sake juna.
“Anum! Gidado ya tafi bai min sallama ba, yau kusan wata biyu ina jin babu dadi” zama suka yi, ya kwanta tare daura kan shi a cinyar ta.
“Anum ban ji dadi ba, gani nake kamar akwai abinda yake kokarin boye min, Anum a duniyar nan zan iya barwa Gidado kome a cikin shi kuwa har..”
“Har da ni?” Kallon cikin idanun shi tayi, tana son jin amsar da zai bata, s hankali ta shafa kan shi.
Riko hannun ta yayi ya saka kan Kirjin shi.
Idanun shi yana cika da kwalla.
“Eh har dake” a hankali ta janye hannun ta a kirjin shi, mamaki yana kara kashe ta, ture kan shi ta fara yi ya k’amk’ame ta.
“Kiyi hakuri, dole ce ta sa na gaya miki. Ina son ki amma kaunar gidado a jinina yake da shi aka haife Ni”

Hawaye ne ua zubo mata, muryanta yana rawa ta ce mishi.
“Ba zan tab’a sadaukar da kai ga kowa ba, amma kai tunani kake zaka bar ni domin wanin ka? Shin ni ba Y’a bace? Ko an ce maka bani da zabi ne? Ina son farin ciki kamar kowa me yasa kake tunanin cewa zaka barwa wanin ka ni?”
“Toh kiyi hakuri ba zan kuma ba”
“Ka daina”
“Naji” hannun shi ya tura cikin rigarta,amma fa buge tana hararan shi, dariya ya saka mata daga nan suka lulla wata Alkaryar.
**
Tun da ya dawo Sudan yake jinya, a zahiri lafiyar shi lau. Amma abadili bai da lafiya sosai, kirjin shi ciwo yake, zafin da yake ji tasa wani lokaci sai yayi tarin jini yaƙe iya samun sauki. A daddafe yake ta faffutukar karatun shi musamman da yake son kasancewa alkali, wanda yasan Shari’ar Muslunci, haka ya kara mishi wani zabari sosai, har yau ya kasa cire ta a ran shi, lokacin haduwar shi da ita, dukar kirjin shi yake a hankali jini na d’igowa ya hancin shi, wata biyu kenan ana shirin shiga na uku rabon shi da gida, shi ko irin sha’awan nan baya ji na wata Y’a mace, kawai ita daya ce a duniyar shi, shigowar wani abokin shi da suke daukar karatu ne ya ga yadda hancin shi yake zubda jini yayi maza ya ture littafin gaban shi, sannan ya dauko ruwa yana kwara mishi akan shi. Ajiyar zuciya yake saukewa a kai akai, a hankali ya shiga dukar kirjin shi, hawaye na zuba mishi, yana kuma kara kokarin cire ta, amma ina ji yake kamar kara kusantotta yake ga rayuwar shi, yasan son Anum itace ajalin shi. Son Anum itace ƙaddaran shi.
Dan haka yayi ta kuka tana buga kirjin shi, yana jin ina ma da zai iya da ya cire ta a rayuwar shi.
“Yarima zaka kashe kanka fa? Kadaina ajiye damuwa a ranka, wallahi idan baka da lafiya ka tafi gida mana, zai fi maka zaman nan babu me kula da kai, amma al’amarin ya tsannanta ya kamata ka je gida ka samu magani” girgiza kai yayi, domin kosu abokan karatun shi bai nuna musu ya samu lafiya ba, kawai ya a mu’amalar su da yadda ya saba, lokacin da suka tambaye shi Lamido ya basu labarin ya zama sarki sai da suka tausaya mishi, domin burin shi ne ya zama sarkin amma rashin magana yasa an bawa dan uwan shi.
Haka yayi ta tafiya da ciwo a tsaye, duk ya kare kamar kudin guzuri.
**
Yanayin da ake zaune lafiya da sauke hakkin kowa yasa Baffa’m ya gamsu lamido ya dace dama da mulkin, gashi ko ina aka zaga sai addu’oi da fatan Alkhairi, haka yasa duk zaman da zasu yi su hudun nan akan yadda zasu kara nunawa lamido yadda ake mulki da hukuncin sa, Baffa’m sarkin gida, Galadima, da Zakaria. Duk wani cigaba na masarautar suna kokarin kawo mishi. Sai dai abinda ba za a rasa ba.
Barcin la’asar take yau, cikin barcin kamar wata uku da suka wuce haka yau ma aka kuma mika mata ta’aziya, tare da bata hakuri, farkawa tayi taga ashe kuka take a barcin ta.
Gidado ne ya fado mata.
Mikewa tayi ta nufi wurin Innayoh.
“Lafiya?”
“Innayoh ina son ganin Gidado wallahi bai da lafiya ni dai Allah yasa ba mutuwa yayi ba!”
“Kai haba Amunatu wani mutuwa kuma? Kawai yana nan lafiya”
Bata labarin mafarkin da tayi tun maiduguri, shiru suka yi kafin kuma Innayoh tace mata.
“Wani lokaci mafarkin bayan la’asar ba gaskiya bane domin akwai shaidanu da suke amfani da haka, kuma ai babu kyau.”
Ta amince da abinda Innayoh ta fada ne kawai amma zuciyar ta bai mata ba, dan haka suna cikin tattaunawa Lamido ya shigo ya zauna yana kallon su.
Da gudu Anum ta shigo tana haki.
“Ammyn kice ya barni don Allah zan tafi rugar gona ce”
Kallon shi Ammyn tayi sannan ta ce.
“Ka amince ta tafi”
“Toh na Amince” ya mike yana dariya,
Fita suka yi yayi kasa kasa da murya.
“Sai kin bani ladan amincewa”
“Kai Hamma na lura baka kome domin Allah ba, wannan ba halin mutanen kirki bane”
“Toh ko na fasa?”
“A’a indai ba zaka ji ma ba, don Allah kar ka sani barci”
Dariya yayi kasa kasa, tun a zauren shi suka fara jaraba, itama Yar duniya ta zama sai yadda yayi da ita, dan haka suka kashe kan su akan jaraba, har cikin dakin su, sai da suka yi fatali da kome, cikin wani yanayi mara misaltawa, yau ce ranar farko da zai ce yaji dadin ya rabu da abinda yake ji, yanzu san yayi aure. Da ashe da zai rage maran shi ba ba auren yayi ba, wani irin rungume ta yayi yana sauke ajiyar zuciya, domin iya nutsuwa ya samu bai kuma san me zai ce ba.
“Anum!” Ya kira sunan ta.
“Na’am Saraki”
“Ina son ki”
“Toh yau na jiyar da saraki dadi ne?” Ta fada tana rufe fuskar ta a kirjin shi.
“Hmm” ya fada yana kara matso na shanun shi, ai kuwa ya sake mishi wani sauti da ya kuma kashe mishi jiki, ya janyo ta sosai yana wasa da ita,
“Muje kiyi alola” tunda taji haka tasan komawa zai yi, dan haka suka yi alola suka sake komawa kamar zai cinye ta haka suke ta gurzan juna,
Ya rasa inda zai saka kan shi domin jin yake kamar ya boye ta a cikin jikin shi, sai da ya nutsa sosai, sannan ya janye tare da komawa gefe ya zuba mata ido tayi laushi, sanin ta gaji barci take bukata yasa shi daukar ta suka shiga wanka, ya wanke ta tass sannan ya dawo da ita ya gyara mata kwanciya, tuni batun fita unguwa ya kare, ita kenan duk lokacin da taji kayan aikin inshallah bata kuma motsawa, domin wani kasala da gajiya yake saukar mata, kuma haka ce ta faru, dan haka ta cigaba da barci ta. Murmushi yayi yana kara jin soyayyar ta, yana kara samun daraja da matsuguni a ran shi. Kaunar ta kamar ya huda zuciyar shi, ji yake kamar shi ya dace da ita ba kowa ba a wannan duniyar, rike hannun ta yayi yana jin babban al’amari akanta wanda zai.iya cewa ya wuce babban karni, hannunta ya saka a kumatun shi yana murmushi lokaci zuwa lokaci.
**
Bayan wata shida da barin shi gida, ciwo ya mishi rubdugu. Tabbas baya jin zai kai labari, ciwon tayi mishi kamun kazar kuka, babu shiri ya nufi Gobir domin idan dai mutu ya mutu a can….🤣😂💪

*Hmm! Nan kuka addabe ni da Lamido yanzun kiri kiri zaku.juya mishi baya*
#Mai_Dambu
KALLABI..!

Advertisements

_____

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KALLABI 23

Advertisements _____ BABI NA ASHIRIN DA UKU Kaurewa wurin yayi da azababben yaki, me cike da kishi. Wato…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 20

Advertisements _____ €pisode 20…………….. Yau bobbo ya tashi da matsanancin zazzaɓi sabon mafarkin Nahad da yayi , Mamma…
KALLABI
Read More

KALLABI 37

Advertisements _____ BABI NA TALATIN DA BAKWAI Kallon juna suka yi da Innayoh, kowacce fuskar ta dauke da…
KALLABI
Read More

KALLABI 57

Advertisements _____ BABI NA HAMSIN DA BAKWAI _Wannan shafin naku ne Yan GRP din Queen Bee ku more…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 14

Advertisements _____ €pisode 14…………… Bayan ya gama shiri tsaf ya dawo ya zauna gefen gado tare da jawo…