A BAKIN WAWA 16

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

16

Gefen takardun ya zauna sannan ya kalleta yace’ Mahmud or Muhammad,

Bata bashi amsa ba taci gaba,

tace’. Ummusalma Mahmud, na kasancewa yarinya mai farin jini,walwala,fara’a, surutu,tsiwa,masifa,duk wani kalan rashinji,to na dame kowa na shanye, bana Jin magana koda kuwa ta iyaye na ne, ina da shekara uku a ka haifi Sameera,sai dai tunda aka haifeta, duk wani Abu da zanyi a gida ba’a min magana a lokacin an sani a makaranta sai dai bana zuwa Islamiyya sai dai boko kawai, sai dai kuma bana san karatu kwatakwata wasa ya min yawa,ansha kawo karata daga makarata amma ko dan yatsa Abba baya daga min, bare kuma Mama, ahaka na taso a wani sangarce, ina da shekara shida aka haifi Yusuf tunda aka haifeshi kullum ina dakin,ina ganin yarda ake masa wanka, babu abinda nake so sama dashi,idan naga yana kuka to tsab zan masifen ce mai aiki ba ruwana daman Bana daga masu kafa,ahaka nake daukan sa tun ban iya ba har nazo na kwaya, makaranta kuwa daman sai naga dama, kuma Mama bata taba damuwa ba, ina da shekara bakwai ita kuma Sameera shekara hudu aka haifi yaseer sai yazamana bani da wani lokacin sai nasu,idan na dawo daga makarata ina tare da su a haka suka fara wayo tun ina karama nake masu wanka tun ina sa masu kumfa a ido a min magana na daina, amma da naci sai da na koya masu wanka, sai ya zamana da suka fara baki ni nake koya masu wakokin makaranta #children rhythms, babu abinda na tsana Sama da karatu sana San karatu,Amma saboda su ne yasa na dan fara maida hankali sai naga ashe duk abinda Akayi ma ina iyawa,daga nan kuma sai na dena maida hankalin,a haka na taso ga wani uban kudi da ake bani ina kashewa koda kuwa ban da bukata, ra’ayimmu ya sha bambam da Sameera we are parallel da ita, idan ni nayi gabas to ita tayi yamma, Sameera tana da mutunta mutane,bata da wulakanci gata da San karatu,duk kankantar laifi idan tayi za’ayi mata fada, sabanin ni da ba’amin fada ko me nayi. A haka na taso cikin so da kauna, har na zo js3, lokacin school dimmu boys and girls ce, ina da friends Maza da Mata banda mu ba,kowa ma ni nawa ne,ina da harka da kowa bana ware kowa, ga kuma uban kudin da ake bani ina kashewa hakan yasa ake min taken big girl, indai a school din kake to tabbas kasan big girl idan ma baka san ta ba to kana Jin labarinta. Ina js2 na matsa aka koya min mota, Abba beyi musu ba yasa driverna yake koya min har na kware, tsayi na baya kaiwa naga gaban mota to sai nayi ciko,ahaka na koya lokacin da na shigo js3 na kware abuna, duk weekend ko Thursday and Friday ina dibar su Yusuf mu tafi yawo,

Wata Rana za’ayi birthday din Dan class dimmu, kasancewar mazan class dimmu akwai sha’ani ba laifi, dukda cewan duk wani birthday idan za’ayi to a class ake yinsa, Amma shi sai yace ai baban sa ya yarda yayi a club, ni nafara cewa zanje, ganin ba Wanda yayi magana sai ni yasa nace” ya haka ku baza kuje bane?
Abinda sukace shine”‘ a gida za’a mana fada,
Nikuma nace” Naga sai da yamma basai muje har gidan naku ba kowa mu gayya to Shi ba?
Basu ce komai ba sukayi shiru,ana tashi daga school kuwa bayan na dauko su yusseer kasancewar haka nake ce masu banma Shiga da su gida ba,na fada bin gidajen kowannan mu ina fada,ba laifi kuwa duk an barsu.
Da yamma wasu suka biyo min muka tafi club,shine Karo na farko da na taba zuwa club wani wuri aka ware musamman saboda taron birthday dinshi, tun 5pm aka fara ba’a gama ba sai 12:30am a hakan ma bawai angama bane kawai gajiya nayi nace Zan tafi, tare da su sauran friends dimmu muka fito sosai munga abubuwa abinda bamu taba gani ba koda kuwa a film ne, bamu Kara tsinkewa da lamarin ba sai da muka fito waje ganin dahu yayi sosai kuma lokaci ya ja sosai muka tsorata idan anje gida me za’ayi mana ga goben zamu fara zana jarabawar mu ta BECE ni ce kadai kowa gida ban koma gida ba sai 2:30am, dukda na tsorata Amma na kasance mutum wacce bata nuna emotion dinta, a haka na Shiga gida,ina Shiga naga Abba da Mama a tunanina zasu min fada ko duka ma kamar yarda nake ji za’a zane wasu daga cikin mu daga bakin su, Mama

tace’ Ah ah salama sai yanzu? Ya birthday din?

Abba kuma yace’ ya kika tsaya gobe ma ki dawo duk lokacin da kike so, soyayyar mu a gareki ita ce komai kiyi duk abinda kike so koda kuwa zaki kwana ne bai dame mu ba kinji?

Wani dadi naji kasan ance kuruciya dangin hauka, jinayi duk duniya babu masu sona sama da iyaye na, da gudu na zo na rungume su nace” nagode Abba na,
Yace’ ai bakomai salama komai munayi ne saboda ke farin cikin ki shine namu farin cikin, ina kaunarki yata,

Advertisements

_____

Washegari danaje school friends dimmu wayanci an Zane su, musamman mata kowa yana fadar abinda aka masa suna cewa bazasu kara ba har abada,ganin irin kukan da suke sha da danasani yasa ni jan bakina nayi shiru bance uffan ba koda suka tambaye nace ni ba amun komai ba,daya daga cikin kawayen na tace’ gaskiya iyayenki basa sanki,kikai wannan lokacin a waje kuma ko fada ba’a Miki ba? Anya su suka haifeki ?
Sosai mukayi fada da ita kaca kaca akan furucinta akan iyayena gani nake duk duniya babu wacce iyayenta suke so sama dani, dakyar aka raba mu da ita,
Tundaga ranar duk wani birthday da za’ayi ko a’ina ina zuwa bakuma na dawowa sai sanda naga dama,sai dai idan naje bana shan ko lemu ko cake din bana ci kawai rawa nake zuwa yi abuna.

Abba Yana da company,idan na zauna nida shi na riga cewa kenan idan nagama makaranta zai bani company daya Nima nake aiki aciki,burina Kenan kawai na zauna a kujera nake juyawa,abinda nake so kenan tun ina karama, a lokacin yakan bani labarin wani abokinsa mai suna Muhammad dashi da Mama suna yawan bani labarin mutumin nan shine ya cucesu ya sace masu yar su sannan ya kashe masu ‘ya’yan su,kafin ni sun haifi ‘ya’ya uku amma duk Shi ke kashe su, tun daga nan naji na tsane shi, idan muka zauna basu da labarin da ya wuce nashi da irin muguntar da yayiwa Abba, koda na tambaye Shi nace yanzu yana ina ca

yace’ Yana Abuja, gidan sa ne ya kama da wuta,
Ban wani tambaya ba sosai,a lokacin na tsani ma Jin labarin,na tsana yaudara da cin amana,karya gabadaya na tsane su.
Ahaka na cigaba da zuwa makaranta ta da islamiyyan da ake min a gida dukda malamin yana hakuri dani idan yazo tun four to sai five ko six zan fito ina fitowa zance aya daya zai Kara min, lokacin banfi hizbi biyu ba da aya daya daya din da yake karamin, dukda malami na ne amma madam yake cemin bama shikadai ba kaf masu aikin gidan nan madam suke cemin idan kuwa basu fada ba to kayiwa aikinka korarka zanyi ba ruwana,ina da tausayi amma kuma Mama takance ba’ajin tausayin talaka,talaka bashi da mutunci,idan kayi masa rana to Shi dare zaiyi maka, sai ta kawo min misalin Wannan mutum mai suna Muhammad shima talakane, ya cuci Abba,da haka tayi tasiri akaina, na dena Jin tausayin wasu, amma ba duka ba idan na fita indai naga kana neman taimako to Zan baka shi.
Akwai watarana nakai yusseer park lokacin ina ss2 munje da su,suna fada da wani yaro suka tarar mai suka masa dukan tsiya sannan suka ji mai ciwo a gefen idan sa, ashe yaran dan dpo ne aikuwa babansa yazo yana zuwa kuwa yace sune suka ji masa dan zuwana kenan daga siyo ice cream bansan me yafaru ba kawai gani nayi za’a tafi da su yusseer aikuwa nace nice, aikuwa aka tafi damu har su,aka rufe ni aka Kira Abba sai ca yace’ baya gari,Mama aka kirata itama tace’ bata gari tare suka tafi da Abba kuma zasuyi sati ne a can,sai suka ce a mayar da su yusseer gida ni kuma a barni a cell, sai da nayi sati biyu a cell sannan Abba yazo yayi bailing dina, yana ta ban hakuri,ko kallansa banyi ba, sai da ya fada min uzurin sa sosai sannan na yarda na hakura.Tun ina ss1 aka dawo dani makarantar nata kawai ni nace inaso saboda frienda dina wasu sun dawo ta, zamushiga ss3 aka min repeating Amma bandamu ba na bisu na cigaba da karatuna tare su har akayi hutun Frist term………..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 26

Advertisements _____ BABI NA ASHIRIN DA SHIDA Muryan shi na rawa ya rike hannun ta. “Zai fi kyau…
Read More

Zee Baby Book 1 Page 50

Advertisements _____ πŸ‘‰πŸ»50* ….”inajin wani irin farin ciki mara musaltuwa. Yayana kaima kanaji.?sansanyan Murmushi yayi ya sakarmun kiss…