A BAKIN WAWA 19

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

19

 

Driving yake amma gaba daya jikinsa yayi sanyi hankalinsa kuma ba’a driving din yake ba, tunani yake akan wannan auran, yadai san Daddy be sanar Mata ba, akan me kuma zaiyi wannan abun, aure fa ba abin wasa bane haka kawai ‘ya ba tashi ba ba komai ba, “Ya ilahi Daddy why??
Abinda da ya furta lokacin da yayi parking a bakin gate dinsu, sai dai kuma ya kasa fita yana zaune kawai ya dafe kanshi da yafara ji yana sara masa, horn yayi aka bude masa ya shiga ko gama parking baiyi ba ya fito key din ma a jiki ya barshi, a parlour ya baje ya kwanta yana wani irin tunani na daban, shikadai yasan me yake sakawa yake kwancewa.
Ya jima a wurin ahaka har wurin 12 yana nan bai motsa ba jin wayarsa na ringing Allah yaso bai barta a mota ba ya tuna sanda Daddy ya kirashi da ita ya fito a mota,shi dai baisan sanda yasata a aljihunsa ba sai ji yayi tana ringing.
Daukowa yayi ganin number da har zai share sai kuma yayi tsuka ya daga, abinda aka sanar dashi yasashi saurin mekiwa,bayan ya kashe wayar shi yama manta da abinda ya fita yi badan an kirashi an tuna masa ba, daki ya Shiga yayi refreshing sannan ya fito key yafara nema sai kuma yayi tunanin ko ya barshi a mota ne .

 

✨✨✨✨✨

 

“Yanzu Adamu abinda kayi ka kyauta Kenan ko me? Uhm, yarinyar nan fa ba ‘yarka bace, sannan da kace min iyayenta sun rasu ita bata da me riketa ne ko me? sannan kuma wannan yaro ba mace bace da zakayi masa auren dole, Ka duba mana wannan lamarin, gashi kuma kace min yarinyar kurma ce,kawai don san a cuceta ko kuma me?

Kanshi a sunkuye yake bashi da daman tankawa yasan bai kyauta ba shi kawai abinda zuciyar sa ta Raya masa Shi yayi,

Advertisements

_____

” Ba magana nake ma ba, kana jina kayi shiru ka kyale ni ko? Wato yi ki gama ko?

Bude Baki yayi yace’ amm… amm.. umma ki..

” Rufe min baki wani amm amm umma,daka san zaka bani hakuri ka aikata ?

Wani mutum ne dake gefen Umma,

yace’ kiyi hakuri kuskure ne mun rigada munyi,kuma kinga bamu da ikon da zamu warware wannan aure, har sai mijinta ya saketa tukunna, Allah kuma baya san saki, umma kiyi hakuri kuma watakila ma dalilin aure nan sai kiga Allah ya shiryeshi,…

” aww da mai yake aikatawa? Ta kastse shi,

Daddy yace’ umma nema yake ya lalata masu yarinya fa a idona nasha ganin hakan tana faruwa shiyasa ma kikaga kawai na yanke wannan hukuncin.

Umma tace’ ehh lalle ne shi Audushakurun Kenan? To bari kaji ko duk jikina kunne ne bazan yarda ba,kawai dai ka cuci yarinya kawai shine magana. Kai kuma dan kaga inajin maganar ka shine aka dauko ka kana can wata uwa duniya amma kadawo saboda wannan auren ko? To shikenan ya zanyi kun dakeni kun hanani kuka bazanyi magana ba,kun nuna min ni ba abokiyar shawara bace shikenan ai aikin gama ya rigada ya gama.

Sai tayi shiru,Suma shiru sukayi babu wanda ya kara magana, sai can ta kalli Daddy,

tace’ kaje ka dauko min ita yarinyar,bazan laminta ba zamanta wannan gidan,kashe ta zasuyi daman ga aba kurma,

Daddy yace’ umma da kin barta acan din inaga hakan…

Zaifi ko? Yanzu ma ja zakayi dani ko? Baka sanar dani ba auren sannan kace zamanta a wannan firin din zaifi. Bana boka bana Mallam amma ko kaffara banayi na tabbata wallahi wannan shegun matan naka ne suka hada tuggunsu da munafinci suka fada maka,Kai kuma ka hau dokin zuciya ka dauka. To billahillazi bazan dauka ba,kai da kaina ma zani gidan bari gari yayi sanyi zanje na dauko ta,kuma yarda baka fada min kayi masa aure ba koda subutar Baki karka kuskura kafada masu tam.
Tashi tayi tana dingisa yar kafarta

tace’ idan kun tashi ku kashe min kallon kuma a tabbata an rufe min kofa. Ta wuce abinta ko waiwayowa batayi ba.

Usaman Wanda yake gaba da Daddy kuma shine na farko a wurin Umma, ya matsa ya dafa Shi,

Advertisement

_____

yace’ Karka damu kasan halin Umma kuma kasan duk wannan zafin da ta dauka be wuce na yarda aka daura auren nan ba’a fada mata ba kayi hakuri,

Daddy yace’ umma baza ta taba saukowa ba, kaima fa kasan da wannan, kunyar kace fa yasa batayi min fada dayawa ba,nadauka laifina ne,gashi kuma tazo da maganar dauko ita waccan yarinyar,idan na kalli dana inajin dadi ganinsa nake tamkar mahaifiyar sa yaya yazanyi don Allah,

Har wata kwallace ta taru a idansa,ga muryan shi da ta fara rawa alamar neman yin kuka ganin haka yasa Shi yin shiru,ya sunkuyar da kansa,shikadai yasan me yakeji a zuciyar shi, zuciyar shi zafi take masa, amma baisan wazai fadawa ba yaji dadi, kuma baisan me za’a fada masa ba yaji dadi.

Shima Dan uwannsa shiru yayi ganin halin da kaninsa yake ciki,besan me zai fada masa ba shiyasa ya zabi da yayi shiru don shi magana bata dameshi ba tunda can ma. Sunjima a hakan hannunsa nakan kafadar shi alamar rarrashin,daga bisani kuma

yace’ ni Bari na koma idan umma ta fito kace na wuce sannan kuma kace mutan gidan na gaida ita

🌼🌼🌼🌼🌼

 

Zaune suke su uku suna tattauna yarda abin zai kasance daya daga cikin ma’aikatan ne,

yace’ yanzu Oga namu baya nan amma duk sanda yazo office zan sanar dashi,duk yarda mukayi dakai zakaji Insha Allah.
Murmushin dole ya kirkiro

yace’ thank you,yafada yana mika masa hannu,shima mika masa hannu yayi,haka ma dayan, daga nan kuma suka tashi don tafiya.

Koda ya dawo gida bai shiga wurinta ba,wanka kawai yayi yasa kaya marasa nauyi ya kwanta yunwa yake ji beci komai ba tunda safe gashi yanzu ana nema ayi la’asar,shafa kansa yayi Mai cike da suma sannan ya shafo cikinsa, ya lumshe ido yana tuno Anty ummi bata taba barinsa da yunwa bare kuma tabarshi da damuwa, a fili ya furta” Allah ya jikanki Antynah.
Jawo jakar da ya fita yayi,don yayi wani abu ganin ya fara tunani dukda kansa dake ciwo amma haka ya daure ya fito da takardun cikin jakar tashi yayi zaune dakyau takardun company din da ta bashi yasa shi dauka, dubawa yayi yaga yama fi na company daya ta dauko masa, sannan kamar harda ma takardun fili da gidaje, dubawa yakeyi daya bayan daya sai dai kuma kowanne yana ganin signing din Ummu da yake rubutawa a jiki,amma idan ba lura kayi ba bazaka taba gani ba, sosai ya nutsu yana kara nazarin takardun,Yana cikin dubawa wata karamar paper ta fado a ninke take sai dai kamar harda wani dan jajaja a jikinta, warwarewa yayi ya bude, ganinta da yayi tana da tsawo papern ashe nadinne aka yi karami sannan kuma rubutune a jikinta dayawa sai dai rubutun bawai a tsare akayi shiba, nadeta yayi yarda take ya mayarta inda ya gani. Jin sosai yunwa yake ji yasa shi tattarawa ya ajje a gefe guda ya fito, fridge ya buda ya ciro malt ya fito don nemawa kansa abinci, ta wurin dakinta ya zo wuce sai kuma ya dawo da baya azuciyar Shi yace”‘ kome take yi yanzu?,
Samun kansa yayi da bude windown ta kadan, tana kan katifa tana faman taje kanta, gashinta yana da cika dayawa don yama fi karfinta saidai yana da tsayi amma bawani can tsayi na’azo a gani ba, sai dai ace Masha Allah, tana sanye da t shirt sai zani da ta daura sai da yagama mata kallon tsab sannan kuma ya kawar da kansa,a zuciyar Shi yace'” haka kawai nayi ta kallanta ba muharrama taba ba komai ba” har yayi gaba yadawo yakuma lekata a fili yace’ ashe fa kedin halali nace, yafada yana yar karamar dariya,ganin bakinta na motsi yasa shi kara gyara tsayuwa ya zuba mata na mujiya Yana kallo,

Ita kuwa sai fama take da kanta tana mita ita fa a duniya shiyasa ta tsana zubawa kanta ruwa,kwata kwata bataso shiyasa idan ta kulle shi bama ta Kara kulashi sai wani lokacin kuma,ta tsani tajar Kai itakam,mitar ta take zubawa ba kakkautawa ita kadai,bakinta ne kawai yake motsi, haka ta bar kan badan ya taju ba sai don ta gaji, ribbon tasa ta daure kan shima dakyar sai kuma ta kama tufkar tayi mata kitso, kwanciya tayi ta lumshe ido tare da sauke a jiyar zuciya saidai kuma data kwanta sai taga kamar inuwar mutum a windown ta, kara bude ido tayi ganin bakowa yasata rufe idan ta, knocking din da taji a kofar dakinta yasa ta bude idanta ta zubawa kofar ido,ita fa tagaji wannan kwanciyar ta mata dadi bakadan ba,ji tayi ansake knocking tare da cewa “‘ko in shigo ne?

Ai batasan sanda tayi saurin janyo hijabi ba ta bude kofar ta kalleshi sai kuma ta rasa me zatace,ta sunkuyar da kanta kasa kawai hannunta daya ta rike kofa dashi dayan kuma tana wasa dashi, murmushi yayi,

yace’ Azo aban abinci yunwa nake ji tun safe banci komai ba, amma baki damu dani ba,
Kumbura baki tayi,amma batayi magana ba don batasan me zatace ba,sai dai kuma azuciyar ta maganar take,ita kadai tasan metake fada,kamar ya San metake fada

yace’ aww zagina kike ? Allah ya sauwake ki zubo min ko? Kuma yazo ya dameki kina hutawa har da min Allah ya isa ko?

Zaro ido tayi Jin wannan lamari, batayi kuma magana ba kawai ido ta zuba masa,dafe Kai yayi

yace’ kuma tsorata ni dazakiyi da wannan idan naki Masha Allah dashi, don kinga ni bani da su ko? Shikenan bakomai nasan inda zani, shikenan wata rana zaki karasani shikenan ni daman babu mai dona babu mai kulada ni bari na tafi bakomai idan na mutu ki daure kyace Allah yaji kanshi ko sau daya kinji,
Yafada yana neman juyawa,

Itakam tasan idan tana tare dashi to komai nata kuncewa yakeyi,ganin ya juya zai tafi har ya sauka daga Kan barandar zai sha kwana yasa,

tace’ Ka tsaya,
Wani irin dadi yaji dabata tsaidashi ba dabai san sai yaushe zaici abinci,dukda yaji dadi kuma har kasan zuciyar shi yakeji,amma a zahira sai yayi kalan tausayi ya juyo, koda ya juyo ma bata nan hakan yasa shi dan yin tsalle ya dawo ya dauko kujera ya zauna, harda suyin tagumi ji yayi an Kira sallah, lokacin ta fito da abinci a plate tare da lemo sai anan ma ya tuna Ashe fa ya fito da malt a hannunsa ko ina take oho, mika masa tayi abinci yaki karba,kallansa tayi,

tace’ idan baka so na mayar,
Kar yayi biyun babu ukun zero yasa shi saurin karba ta mikasa lemun hannunta ya amsa,bata jira cewar sa ba ta wuce daki ta rufe sannan ta jingina da kofar tana sauke ajiyar zuciya saida ta dawo normal sannan ta tashi tayi alwala Jin za’a shiga sallah.

Shikuma Allah ya gani ba duka lemo yake sha ba don shi wannan ma basan shi yake ba,tashi yayi wai da zummar yaje ya dauko malt dinsa sai dai kuma ganin gwangwaninta yasa shi tsayawa irin yaushe na shanye, zuciyar shi ta bashi amsa da kana kallanta, shafa kanshi yayi ya koma ya fara zira abinci lemon ya bude ya fara sha sai kuma yaji lemon da dadi haka ya cinye tas ya mayar da plate din,sai dai kuma yana shiga kitchen yaga Hajiya ko kallanta baiyi ba ya ajiye plate din ya fito hana jinta tana tambayar wanda ya debo masa abinci a dining ko kallanta baiyi ba bare ya bata amsa,itama haka ta gama masifarta ta fita……

 

By: “`Hijjart Abdoul“`
Cwthrt😘
🍂 *A BAKIN WAWA* 🍂
_Akanji magana_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 3

Advertisements _____ €pisode 3…………….✍️ Kanshi ya ɗago yana kallon yanayinta, ya fuskanci akwai tashin hankali muraran shimfiɗe cikin…
KALLABI
Read More

KALLABI 13

Advertisements _____ *<Babi Na sha Uku>* Bayan shekara biyu. Wanke mata kai Innayoh take, tayi shiru zaka dauka…
KALLABI
Read More

KALLABI 45

Advertisements _____ BABI NA ARBA’IN DA BIYAR Yadda jikin ta yake rawa, yasa baki daya hankalin su ya…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 2

Advertisements _____   2   Bayan sallahn magriba kowa Yana gida amma banda Ummusalma tana dakinta tana assignment…