A BAKIN WAWA 22

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

22

 

Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,

tace’ a hankali fa ake bi,

Yace’ Madam a hankali fa nayi,

Wanne hankali kasa duka karfin Ka kaja,sai kace Ka damu gashin doki,

Yace’ to naji sake min hannu, zanbi ki a hankali bazan yi da zafi,

Promise?

Advertisements

_____

Promise,

Sake masa hannun tayi,tana kallansa yarda ake kunshe dariya,aikuwa ta Kara hawa gashi yace Mata Madam, ahankali yake bin Kain yarda bazata ji zafi har ya taje Shi tsab,ya kawo mai ya shafa Mata,ya kuma tajewa,ya dauko ribbon,

yace’ to ki juyo mana a kulle kinsan bazai dauro ta haka ba,
Batayi musu ba ta juyo shikuma ya daure Mata kai,

yace’ kinma fi kyau haka,kyanta kitso aka min,a yarda suke haka sai sun fi kyau,

Tace’ ban taba kitso ba.

Yace’ to juya kiga yarda na iya gyaran gashi na tabbatar ko ke bazaki iya ba,
Juyawa tayi ta kalli kanta a jikin madubin ta kalle Shi yarda yake murmushi irin nayi abin arziki nan,

Tace’ sai kace wata yarinya zaka min three babies?
Ashe shiyasa yace da kitso ne sai yafi kyau, kallon Shi tayi,

tace’ wannan ai damuna zasuyi,

Shidai Yana tsaye Yana kallanta ta jikin mudubin, yarda take cuno baki tana kumbura Baki,shifa abin arziki yayi a ganinsa Ashe na yara ne, kuma fa tasan tayi kyau amma take kushewa shikam Allah ya hada Shi da Mata, a Dan zaman da sukayi da ita ya gane 70% a halayarta.
Sunkuyowa Yayi daidai fuskarta suna kallan juna ta cikin madubi,

yace’ kinyi kyau mi precioso,
Ya kaimata peck a kumatu ya fice, murmushi kwance a fuskar Shi,
Kallanta ta dawo dashi wurinsa har ya fice,ta dawo da kallanta ga madubin murmushi tagani a fuskar ta har dimple dinta duka biyu ya lotsa, shafa inda yayi mata peck din tayi tana mai kallan kanta a madubi, Idan aka ce Mata zatayi murmushi nan gaba to zata karya ta mutum,bare kuma ace tayi dariya? Ada tana tunanin yaushe zatayi Kara Jin farin ciki a tattare da ita, sabida damuwar da take ciki kuncin da bakin cikin da take ciki, shekara bakwai ta ta wuce,a tunaninta ma tayi bankwana da dashi, sai kuma yanzu rana daya kwatsam wani daban yasata dariya alokacin da bata shirya a lokacin da batayi zato ba, dukda shima Yana cikin damuwa ahaka yake danne damuwarsa don yaga annashwarta to ita Akan me bazata danne ta ta damuwar ba itama ta dawo kamar kowanne mutum??
Ajiyar zuciya ta sauke,ta cire hijabin da yafawa jikinta ta karasa shafa mai,tana shafawa tana tunano ranar da suka a London har yanzu ta manta inda suka fara haduwa amma Shi kamar ya tuna hakan,
Sai da tagama tsaf ta feshe jikinta da turare, har ta Kai hannu zata cire three babies din da ya mata ko me ta tuna kuma oho ta barshi, wurin trolley dinta ta nufa ta dauko kayan bacci masu laushi Riga da Wanda tasaka ta kuma fesa tureranta, sannan ta jera kayanta a dayan side din, ta jera komai da komai,ta zuke jakar ta sata a kasan wardrobe, kayan bakko ta dauko shima ta dau muhimman abubuwan ta, ta rufe ta ajje, ta fita

Suna zaune a parlour ta shigo kusa da Umma ta samu ta zauna da yake Umma a kasa take,
Umma tace’ ashe kun dawo ko? Ina sallah,

Tace’ eh,

Umma tace’ to ki tashi ki zuba maku abinci ni naci nawa tun dadewa,

Tace’ Umma sai anyi sallah zanci,

Advertisement

_____

Yana zaune Akan kujera Yana kallanta tun sanda ta fito,

Yace’ Sallah ai sai ta gobe yarinya,

Bata tanka masa ba shiyasa,

yace’ Madam yunwa fa nake ji, kinsan banci na Rana ba,tun abincin da naci na safe shima wani dan matsitsi aka min,

Umma tace’ wai ni audushakuru yaushe ne ka koyi surutu da Mita haka ne? Ni asanin da nayi maka kwata kwata baka da magana yarda kasan Babanka( danta Usman) haka kake amma yanzu gaba daya Ka canza? Kaine korafi,Kaine Mita,Kaine komai ma Ka hada,to ni bazan iya ba matar Ka zaka dauka kubar min gida,

Yana daga kwance ya tashi zaune
yace’ ai kuwa Umma da kin kyauta yaushe zamu tare ne ma wai?

Idanta a TV tace’ sai bayan sallah da sati biyu lokacin kowa yazo sallah Yana gida,ko kuma sai hutun da kuke yi hutun Nasara,

Yace’ haba de Umma azumin fa sai Nanda wata biyu, shikuma Wanda kike nufi fa nanda kusan shekara fa kenan,
Gaskiya bazai iyuba haka kika ji anayi ne?
Yafada Yana hade rai,

Ko kallanshi batayi ba,tayi banza dashi kamar bata jishi ba har ya fitar da rai zatayi magana don har ya koma ya kwanta yaji,

tace’ na yanke hukunci zata tafi gidan Safiya ko kuma gidan Babanka acan zata cigaba da Zama kira min ubanka,
Ta kareshe tana kallansa, shima be tanka mata amma kana ganinsa kasan Rainsa ya baci,waya ya daga ya Kira Daddy.

Ita kuwa Ummusalma suna fara magana ta tashi don dauko masa abinci taji yace Yana Jin yunwa da ta nufi dining ganin ba kulan abincin yasata nufar kitchen sai datayi warming din abincin shiyasa ma ta Dan jima, kawo masa tayi yana nan kwance a Kan kujera yarda ta barshi ganin Yana hade rai sai taji duk ba dadi amma ko a fuska bata nuna ba,

tace’ ga abincin

Ai nagani,ni ba makaho bani,
yace da ita tabe baki tayi itama taje ta samu wuri ta zauna a kusa da Umma ta daura kanta a Sama kujera ta rufe ido,

Umma tace’ ai ba ita takar zoman ba rataya bata ga an yiba bare a bata. Mata ce ni ZAINABU ABU mai tagwayen suna baza’a bayar ba,

Tashi yayi ya Shiga daki be jima ba ya fito hannunsa rike da leda a Kan cinyarta ya ajje karamar leda ita kuma Umma aka ajje mata sai da ya zauna a garo mata,

yace’ idan mutum ya gadama yayi zuciya na cinye abuna,
Janyo ledar tayi tace’ kuma wannan mutum din bazaiyi zuciyar ba bare asamu wani a Kara,

Ummusalma ita dariya ma fada nasu yabata,idan ta fahimta duk akanta ne yake cikar nan Yana batsewa, abinnasu sai burgeta sai taji daman itace da kakarta,bata taba ganin Inda ake wasan kaka da jika ba sai a wurinsu gashi de wai fada sukayi amma a wurinta a wasa ne,ledar ta ta bude taga dambu da ice cream Amma ice cream din ma ya narke ya koma ruwa sai sanyi kawai, budewa tayi ta fara ci abinta, itama Umma dambune sai yoghurt marar sanyi,kowa shiru yayi Yana ci a haka Daddy yazo ya same su,

yace’ Umma kice Daddy kike ci Kenan?

Tace’ to mene na tambaya kuma tunda Ka gani da Idanka ai sai kayi shiru kuma,

Shima mantawa yayi yayi magana da bazaiyi ba,har yanzu Kenan bata sauko ba,koda ya gaida ta ko kallansa batayi ba idan ta na TV tana kallo tana tauna dambu tare da korawa da yoghurt,

Ummusalma ta gaida Shi ya amsa daga nan ta tashi ta Shiga daki, ta cigaba da cin abinta sai da tagama tayi nakuma dauro alwala tayi sallah tare da shafa’i da wutri ta jima Akan daddumar daga bisani ta tashi tazuba robar abinda tack a dustbin sannan ta kashe wutar dakin ta dawo ta kwanta addu’ah tayi ta shafe jikinta, bata jima ba tayi bacci.

A parlour kuwa Binaif ne ya gaida Daddy ya cigaba da cin abincin sa sai da ya gama tsab Umma tace’ to ai sai Ka bamu wuri ko? Tashi yayi ya fita waje wurin mai gadi kawai yayi zamansa Yana tuna wani abu, Yana nan har Daddy ya fito ya tafi be tafi ba,Saida ta yagama tsare tsarensa sannan ya shigo gidan, bakowa a parlourn TV ma a kashe take,kulle kofar yayi ya Shiga daki, kunna hasken dakin yayi hangota yayi ta kudundune a wuri daya alamar sanyi, ac din dakin ya kalla alamar tayi yawa, toilet ya Shiga bejima ba yafito daure da towel ya Shirya goge ruwan jikinsa kawai yayi ya fesa turare shima bawani dayawa ba yasa Kayansa na bacci be rage acn ba Saima karata da yayi ya kashe masu hasken dakin sannan yaje ya kwanta a gefen ta, hasken da ya shigo na security light din da sai da nefa yake yi ko solar, Shi ya haska dakin, matsawa yayi ya cire Mata hijab ya gyara Mata kwanciya, sannan ya jawo blanket guda daya ya tura sauran kasa, ya ruf su.
Tayi nisa cikin baccinta Amma tunda ya kunna hasken dakin ta farka sai dai bata ko bude Ido ba bare kuma tayi motsi tana jinsa duk wani Abu da yake har rufar su da yayi,gashi kuma daf da ita ya kwanta saboda bargon da ya rufesu bame girma bane can sosai,bata iya komawa bacci kusancin su yayi kusa dayawa tana shakar kamshinsa, kamar yarda ta kasa bacci haka shima ya kasa bacci shakar kamshinta yake,yade rufe Ido ne kawai badan yayi bacci sai yarda kamshinta yake masa dadi ne yasa Shi yin hakan, juyi tayi don ta juya dayan barin ta gujewa abinda take ji sai batasan kusancin nsu yayi yawa haka ba,juyin da zatayi taji ta a jikinshi ta matsa sosai har babu gab ma, batason yasan idanta biyu,tunda bejima da kwanciya don ko addu’a batajin yayi hakura tayi kawai wai don kar yasan a farke take, jinta da yayi ta matso kusa dashi yasa Shi sakin ajiyar zuciya a boye ko batayi hakan ba Yana da niyyan janyota sai gashi kuma ta kawo kanta, hannu yasa ya rungume ta tsam Jin yarda kirjinta yake bugawa yasan ta farka,Kara motso da kansa yayi ya Dura a wuyanta cikin wata irin narkakkiyar murya yace’ relax,
Yarda yake Jin dukar da kirjinta yake shima haka take Jin yarda kirjinsa ke bugawa,bata ma iya motsi ba sai wani sauke lumfashi take yi a hankali shima hakan yake, Jin Yana bugun zuciyar Shi ya dawo normal alamar yayi bacci yasa sauke ajiyar zuciya sai dai bata iya kwayar kanta ba dukda yayi bacci hakan ya Mata dadi a yarda suke,batasan sanda bacci yayi gaba da ita ba.

Bacci sukayi mai dadin gaske,baccin da suka manta yaushe rabon da suyi Shi,shine ya farkawa ganinta da yayi kwance shame shame a kirjinsa yashi da tunawa moment din su na jiya, murmushi kawai yayi ya kwantar da ita ya shige toilet sai da ya fito yazo zai yasheta har yasa hannu zai tada ita sai kuma ya tuna wani abu, Zama yayi a gefen gadan ya sunyo daidai fuskarta ya hura Mata iskar bakinsa,Yana ruwa Mata ta ya tsine fuska tacigaba da baccinta,Kara hura Mata yayi yaga idanta ya fara rawa,be Bari ta Gama ba ya kuma hura mata, ahankali ta fara bude idanta bata dire su a ko’ina ba sai acikin idansa,

yace’ ki tashi lokaci yayi,
Ya fada Yana mikewa ya kunna hasken dakin, sannan ya fice,juyi ta karayi ta cire bargon Jin sanyin da dakin ya dauka yasata Kara rufe jikinta,dakyar de ta tashi ta sai da ta kashe acn ta kunna fanka ta Shiga toilet tayi alwala har an yada sallah shiyasa ma bata samun daman yin araka’atul fajr ba, u sallahnta tayi Azkhar duba Qur’an ta dauko nata Wanda tasa a ciki, ya fara karantawa.
Tana cikin karantawa ya shigo
A gefenta ya zauna Yana yarda take fitar da kowanne harafi dai dai iyawarta sai abinda ba’a Rasa ba tunda ba tahafiz tayi bazai iyu ba kuma a hada karatu da na tahfiz, sai da tsaya inda zata tsaya ta ajje ta juyo ta kalleshi, shima ita yake kallo,

yace’ izunki nawa?
Ashirin,tabashi amsa tana cire hijabi,sai da nade Shi ta zauna itama a gefen gadan,

Yace’ arba’in Kenan?
Daga masa Kai tayi,

yace’ ni daga maki Kai nayi ne?

Tace’ arba’in

Yace’ yayi kyau,
Sai kuma yayi shiru,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da bracelet din hannunta,

yace’ yau ma sai na tuna maki?
Dagowa tayi ganin ita yake kallo yasa ta mayar da kanta tacigaba da wasa da bracelet dinta,
Tashi yayi ya dauko system din shi ya koma kan kujera ya jona yana aiki,ta gefen ido take kallan sa, tashi tayi itama taje ta kashe wutar dakin, dukda haske ya dan fara yi,sai da tadawo ta kwanta
Kamar jira yake ta kwanta

yace’ kunna min haske,

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 8

Advertisements _____ Babi Na Bakwai>* *Godiya da fatan alkhairi son so daga Mai Daraja😍🔥* Barka da Juma’a# Masarautar…
KALLABI
Read More

KALLABI 17

Advertisements _____ BABI NA SHA BAKWAI *GAISUWARKU CE A WANNAN SHAFIN MASOYAN KALLABI NAGODE SOSAI* “Fita aka ce…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 4

Advertisements _____ €pisode 4……………………. Cikin daƙiƙa uku ta sauka gaban tekun Zuwatu. Ware hannuwanta tayi tana fiffika su…
KALLABI
Read More

KALLABI 35

Advertisements _____ BABI NA TALATIN DA BIYAR Barkindo Yazidu, Allah bai daura mishi kaunar wani hidima na mulki…
KALLABI
Read More

KALLABI 68

Advertisements _____ BABI NA SITTIN DA TAKWAS *PLEASE KU ZIYARCI SHAFINA NA AREWABOOKS KU SAUKE MANHAJAR TA WANNAN…