A BAKIN WAWA 25

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

25

 

Washegari koda ya fita ya gansu a parlour babu Wanda yayiwa magana, sune da suka ganshi suka gaida Shi sai dai ko kallo Basu ishe Shi a bare ya su samu ya amsa ya wuce su yayi tafiyar sa,

Mas’ud yace’ Hajjaju wai ku mayar masa da matar sa mana kinga ni tunda nazo banga yaci abinci na kar ulcer ta kamashi,

Umma tace’ naci kwal uban gidan su baza’a mayar ba,olsar ta kamashi a haka zai kare shegiyar zuciyar Babansa(usman) ne duk zuciyar ubansa bekai ubansa Adamu ba sai kace shine ya haifo shi,

Mus’ab yace’ Allah sarki Umma wallahi ni tausayi ma yake Bani,da’alama Yana san matar Shi,

Umma tace’ kunga meye aciki Nanda sati uku mai kyau za’a bashi ita, ya cinyeta. Wannan da zaima iya ce Mata Yana sannata ne,

Mas’ud yace’ a,a fah ai irin wannan sun fi iya soyayy….

Advertisements

_____

Rufa min Baki marar kunya kawai,
Tafada tare da wurga masa ludayin hannunta da take Shan kunu,

Mas’ud yace’ haba Hajjaju da yanzu Bana roba bane da tuni kin min asarar Dan Baki nan nawa,kin rage min farashi,

Ummu tace’ na lura Kaine Ka koyawa waccan dinkimkim din rashin kunya idan Ka kuma magana wallahi rainka zai baci tam,
Shiru sukayi Basu Kara magana ba har suka gama cin abinsu.

Koda ya fita gidan Shi yaje yaga ankarasa gyaran da yakamata ayi komai angama daga nan kuma sai ya wuce company shima Wanda tuni an kusa gamawa befi kadan ba aiki sune bana wasa ba, duk inda ya kamata gyara an gyara hatta sunan companyn an canza ya koma UMMU LTD. Yafi so Nanda wani satin sun gama, anfara aikin da yakamata na sarrafa madara da sugar dayake da iya madara ce yanzu kuma harda sugar yake so ayi, da zai sai companyn harda gonar shanu ya hada ya saya. Sai da ya Gama zagaya ko ina ya dawo cikin office da yake Sama window ya bude dayake na glass ne kuma babba Yana ganin komai abinda ke faruwa a kasan office din na iya yankin wurin, dawowa yayi ya zauna, ya dauki waya ya Danna Kira,

yace’ nasan yanzu hankalin sa ya kwanta,kuyi duk abinda ya dace,
Bejira amsa ba ya kashe wayar sa, jakarsa ya dauko ya bude takardun Yana neman na company tunda company biyu ya gani sai gidaje da fili, Yana cikin dubawa ne wani rubutu yaja hankalinsa janyowa yayi yaga rubutun kadanne ajikin wata paper anyi stapling dinta da ta fili Zuwa ga Dana Umar Muhammad da date sai kuma signing date din daya gani yanzu shekaru talatin Kenan, numfashi yaja ya zaro takardar ya ajje ta a gefe cigaba da dubawa Yayi ganin Ummu yasa Shi dakatawa ya tuna da ya taba dubawa du haka yagani yawanci a takardar Kara Nemo na Company din da yake nema yayi sannan yayi copy guda daya yazo yaciga da dubawa Yana mai nazartar takardun wasu Basu Kai wasu tsufa ba dukda Duka sun tsufa sai dai kuma yanayi na ajjiya mai kyau yasa Basu ji jiki ba, biro ya dauko ya rubuta Umar, Ummusalma, mas’ud da mus’ab,

Azuciyarsa yake tunanin,Umar Shi aka fara Haifa sai Mas’ud da Mus’ab sai Ummusalma kenan, numafashi yaja a fili ya furta yace’ Tabbas haka yake amma mene dalilin rubuta wannan abun? Yana nan Yana tunanin bashi ya tashi ba sai yamma sai da ya Kara lekawa ya tabbatar da komai normal sannan ya dau hanyar gida babu abinda yaci sai malt da yasha guda biyu restaurant yaje yaci abinci ya dau hanyar gida gabadaya kewanya yake kwana daya kacal be taba tsammanin hakan zaiji ba,Ashe jiya kadanne,Akan yarda yake ji a yanzu da zai koma gida ya tarar bata nan,yana zuwa kuwa ya gansu sun sata a tsakiya suna zuba,ko kallan inda suke beyi don haushin su yake ji,sune suka masa sannu da zuwa wuce su yayi ya Shiga ruwa ya watsa sannan ya fito ya tafi masallaci be dawo ba sai da aka idar da sallahn Isha sun Riga Shi dawowa don har sun zuba abinci suna ci,
Suna kallon film din da Umma ke kallo karangiya ta kalli film din saj tari ba adadi amma duk sanda sukeyi sai ta kalla tana cin dariya abinta, Yana shigowa ya dauki remote ya canza zuwa tashar labarai kallanshi ta budi Baki zatayi magana taji anacewa
Ayau ne mukayi hira da wannan sharar mai companyn wato M & M Wanda ya aka masa tambayoyi game da sace ‘ya’yansa da ‘yar sa wacce ya tura karatu tsawon shekaru har yau babu ita babu labarin ta ance de waka a bakin mai ita yafi dadi,

A safiyar yau ne mukayi hira da Alhaji Mahmud Isah wato mai company nan na M & M da kuma U & U Wanda muka tambaya sai dai kuma be bamu amsa gamshashiya ba,

Abba aka nuna sanda ya fito daga company ranar da ya saidashi,suna masa tambayoyi,

Dan jaridar ya Kara dacewa sa’an nan kuma munji jita jita cewan yaransa Basu mutu ba yayin da wasu suke cewa yaransa sun mutu,wasu kuwa suka Kara dacewa har gawarsu sungani, ‘yar sa kuma wacce ya tura karatu yace beda wata ‘ya yaransa uku ne kawai a yarda kukaji yace sai dai kuma Wanda suka je karatu dasu nan gida Nigeria sun tabbatar da tare sukayi karatu da ita kuma tare ya kamata ace sun dawo, tambayar da mutane suke yi anan shine shin tayi aure me acan? Ko kuma de dagaske ba ‘yarsa bace? Ko kuma ‘yar Dan uwace da ta tafi kuma sai ta koma wajen iyayenta? Wannan tambaya mutenan suke ta yadawa muma baza muce a gaskiyar lamarin ba, ni Bilal Abdullah nake cewa mu hadu a shiri na gaba,

To kunji de yarda wannan abu ya kasance sai dai muce Allah ya kyauta,
A jiya kuma aka nemi yaran minister aka rasa acikin garin Kaduna sunzo ne ziyara wurin ‘yan uwa sai dai kuma ba’a gansu an neme su ko Sama ko kasa anrasa sun bace bat kamar allura, Allah de ya kyaut.

Umma da ta bude zatayi magana sai sakinsa tayi tana kallo ganin ikon Allah, Suma kansu sunji mamaki sai dai basuyi gigin tambaya ba tunda basuga fuska ba, ko da suka dau wayar su duk zancen ake tun Basu fahimta har suka gane inda zancen ya dosa sai dai kuma Basu San gaskiyar lamarin ba,
Shima be tashi ba sai goma idan wannan tashar labarain sun Gama sai ya Kai wata kuma duk sai anyi labarin Abba kowanne kuma da irin abinda zai fada ahaka ya tashi ya koma daki, don ya kwanta sai dai Yana kwanciya baccin yaki zuwa tunanin ta kawai yake, ganin baccin yaki zuwa yasa Shi tashi ya bude wardrobe dinta ya janyo akwatinta ya bude takardu ya kwaso Duka ya daura Akan gado, ya baje su Yana bi Yana gani ya kwashe tsawon lokaci Yana ganin wannan takardun wasu gabadaya ya mallakawa ‘ya’yansa harda Wanda Bana kasar ba kalilan ne nashi Dana matar,na matar sa ma yafi nashi yawa, ya jima sosai daga nan ya tashi ya dauki paper yayi rubutu a ciki ya dauki takardan da zai dauka ya maida sauran papers na sketching yagani a jakar yace'” ita kuma me takeyi da wannan? Kamar ya bude sai kuma ya Maida yayi ya rufe,Yana kwanciya bacci ya dauke Shi.

✨✨✨✨✨✨✨

Da safe da ta tashi ba kowa duk Basu tashi ba har yaran gidan,part din Anty safiya ta gyara tsab( dayake tana da abokiyar zama?) Ko ina ta kunna burner tayi turaren, dayake jiya taji suna zancen Dan wake zasu ci yasata,kwabawa tayi tayi masu tare da dafa kwai ta Kai parlour inda sukaci na jiya ta ajje, har lokacin Basu tashi ba wanka tayi ta shirya cikin kayanta na kullum, doguwar Riga, tashin Nafisa tayi dakyar ta tashi lokacin ma shadaya saura, wayarta ta dauka ganin game a wayar ta tasan kila jiya yaran suka tura game din ta hauyi tana cikin yi sai ga Anty safiya tazo,

tace’ sannunkin fa da aiki irin wannan aiki haka?

Advertisement

_____

Gaisawa sukayi sannan Antu tace’ fito muje muci abinci to,
suna tafiya Anty tace’ Ai da weekend Bama tashi da wuri sai mu Kai shabiyu muna bacci abinmu muna tashi kawai abincin Rana za’a daura kuma har yaran,

Karasawa sukayi suka zauna a wurin dining sai dai ba’asa dining ba a kitchen ta ga ansa Shi, Ummi ma ta tashi har an Mata wanka,Basu jima ba sai ga Nafisa tace’ Ina kwana tana kallan Ummusalma,amsawa tayi, tace’ Mommy ina kwana,

Anty safiya ta kalleta tacet yau kuma kece da gaidani Haka?

Tace’ Kai Mommy kema de kinsa ai mantawa nake shiyasa ai,

Anty safiya tace’ Ai bakya manta da gaida babanki ko?

Ai wannan special ne ina zan manta dashi?

Ohh nikuma ba special ba ko?

A,ah kefa ta dabance,

Kinga zuba mana abinci ba wannan surutun zamuci ba,

Tana kokarin zuba abinci, tace’ Anty yau mun tashi da wuri ko Dan muna da bakuwa kar tace mana makararru shiyasa tana tashina na tashi,

Anty safiya tace’ yanzu ma hakanne don ba abinda kikayi ai du ita tayi wannan aikin har abincin da kike zubawa, wani ana tashin ki da bansan hali ba de,

Shiru tana cuno baki irin haba din nan agaban bakuwa kuma?

Ummusalma kallansu kawai tun jiya idan suna dramar su, ta lura akwa shakuwa sosai a tsakaninsu ko ajiyan sai da ta tuna Mama a lokacin da take taken shagwa arta sai dai kuma a yanzu tasan tayi bankwana da wannan abu, sai dai ina a lahira idan anayi, suna cikin ci wani yaro ya shigo ya girmi ummi sosai don zaiyi shekara goma,ummi tana ganinshi ta hade Rai karasowa yayi,,
yace’ mommy ina kwana,

Anty safiya tace’ lafiya qalau Ka tashi lafiya,

Yace’ laaa Momy ina zanci ,

Tace’ Baka gaid a bakuwa ba,

Juyawa wurinta yace’ ina kwana, da lafiya ta amsa,

Ummi tace’ Kai kullum kullum sai kazo ko ba makaranta ko?

Yace’ eh din sai nazo din wurinki akace nake zuwa kome? Ko gaida ni bakiyi zaki fara ko? Sai na mauje maki Baki marar kunya kawai,

Shiru tayi tasan yanzu tsab sai Anty safiya tasa yamata duka don babu reni a tsakanin yara gidan batasan dalilin dayasa reni ya Shiga tsakinta da Yaron ba,
Babu Wanda ya Kara magana har suka Gama sai da suka Gama Nafisa ta kwashe kayan ta Kai kitchen ta wanke su tas, tace’ Bari taje ta gaida mutanen gidan, da to kawai ta masa mata, parlour suka dawo suka zauna suka kunna kallo suna yi, Ummusalma ta kalli Anty safiya

tace’ Anty safiya maman Shi fah,
Kallan Anty safiya tayi

tace’ laa wai Ahmad, Ahmad Cousin din Ummi ne gidan Suma ba a jikin gidan nan yake kuma akwai kofar da ta shigo tana shiyasa kullum Yana nan idan banfita aiki ba shiyasa,

Ummusalma tace’ Anty safiya shifa,

Wakenan?

Ehhm Bi…bi…bi…na..nai…f

Numfashi taja tace’ nagane,
Hannunta taja suka je daki hotuna ta dauko ta ajje mata Akan cinyarta,Zama tayi a kusa da ita cikin nuna halin nadamuwa,

tace’ Binaif be taba tambayar mahaifiyar shiba, Bansani ba ko ya tambayi Rukayya wacce ya tashi a wurinta,
Shiru tayi sannan tace’ ki bude hotan mahaifiyar sane,

Bude hoton tayi wata budurwa tagani fara da ita kyakykyawan kallo daya zakayi Mata Ka gane hakan,idan Ka kalli idan ta kuma zakace Mata bafilatana,suna kama da Binaif sai dai idanshi ba irin ta bane nata kana ne na Fulani shikuma idansa ba madaidaici ne,bakinta yafi nashi pink shape dinne irin daya,kallon take sosai tana kare matar kallo hannunta kuma rike da jariri kallanta ta dawo kan Anty safiya wacce take kallanta,

tace’ to tana ina?

Kwallace ta taru a idanta ta share,
tace’ babu Wanda yasani,ko ta mutu? Ko tana da Rai? Bamu sani ba Sai Allah,

Da’alamar tambaya ta juya kallan kallonta,

tace’ bangane ba?

Anty safiya tace’ bazaki gane ba idan ba bayani aka maki ba,

Tace’ zaki iya Bani labarin ?

Ganin tayi shiru alamar tunanin yasa Ummusalma kamo hannunta, tace’ don Allah,
Asalin mu mu ‘yan kauyen Alkaleri karamar hukumar Bauchi, mu hudu iyayen mu suka haifa Dan Lami shine Mahaifimu Amma asalin sunasa Ahmad Bansan dalilin da yasa ake fada masa haka ba, Ada can ma Shi Dan kasuwa ne kuma Yana tafiye tafiye da ada tafiyar tana daukan lokaci kafin aje inda za’aje a kuma dawo, mahaifiyar mu Zainab wacce ake Kira da Hajja Abu wasu kuma suce Mata mai tagwayen suna, Hajja Abu tun tana karamar ta take da masifa rashin hakuri,rashin gani ta kyale komai ta hada ba ruwanta da Kai ko waye, dayake a da ne kuma ana yiwa Mata auren wuri shiyasa aka Rasa me aurenta sai Dan Lami Wanda yake Dan uwa a gareta,kwata kwata halinsu bezo daya ba,Amma da yake Shi mutum ne mai karamci iya Zama da mutane yasa Shi Jan ra’ayinta suke zaune, Dansu na farko Usman sai da aka shafe kusan shekaru hudu Allah yabasu Adam, Usman da Adam kusan tare Baba yasa su a makaranta dake cikin garin Alkaleri,Shi beyi ba shiyasa yasa ‘ya’yansa, dukda za’a iya cewa usman kusan halin Baban Shi ya dauko sai dai Sam Shi magan a baya dame Shi gashi kuma da dankaren zuciya, shikuma Adam tun Yana yaro yake da Jan magana shiyasa basa jituwa shida Umma, sai kace ba halinta ya biyo ba, har sun fitar da ran Kara haihuwa bayan shekaru goma aka haifeni a lokacin suna Usman Yana da shekara sha biyar Adam nada goma Usman Yana makarantar secondary sannan kuma Yana koyar da primary dayake da haka akeyi idan Ka gama Zama koyar kafin Ka tafi jami’a, Nima koda na taso sai ya kasance halina dana Adam ba daya ba,nafi sabawa da Usman a haka muka taso sai nayi shekara uku aka haifi Ruqayya itakuma sai ya kasance Adam ke dawainiya da ita komai shike Mata sai da shekara shida aka sani a makaranta lokacin tana Shekara uku itama sai da tayi shida aka sata, mun taso cikin so da kaunar junanmu tare da tarbiyar iyaye sai de kuma bamu da wani lokaci Wanda ya wuce na karatu,muna tasowa daga boko zamu tafi ta Allo dayake da duk shi akeyi, har gwara mu muna da Dan lokaci Amma su Basu da wani lokaci idan ba dare ba shima sai can dare suke dawowa saboda sana’ar dasukeyi don su taimakea kansu su ragewa Baba wani abu, bayan wani lokaci Yayinda Usman yasamu wani aiki a Ilorin na man fetur kawo lokacin akwai mota jefi jefi,shima kuma Adam yasamu aiki a Kano na koyarwa dayake Shi fanin education ya karanta,yayin da nikuma bami cigaba ba, Aikin da suka samu Baba beso ba sai dai kuma Jin Adam a Kano yake yasa Shi Jin damadama,Yayinda Umma tayi tsalle ta diri tace Adam bazaije Shi ba yayi nesa da gida a gida ma tana fama inga ya fita wani wuri, duk yarda akayi da ita ki tayi kawai sai Baba yace mu tafi tare tunda Yana zuwa acan yayi ya cigaba da sana’ar Shi, wannan shine dalilin tasowar mu daga cikin dangi muka dawo nan kano Yana aikin Shi koyar a gidan da aka bashi Wanda akwai komi da komi aciki ba bukata daga nane Baba ya fara sana’ar Shi kuma ta karbe Shi don har gidan kansa yayi,muna cikin haka mane ma suka fara fitowa inda Baba yace Yana so ne mu karanci bangaren lafiya, Adam ne ya samu mana nursing a BUK anan muka fara karatu, a Yayinda aka yiwa Adam transfer ya koma Alkaleri kuma aka Kara masa matsayi, ba yarda Umma ta iya ta hakura ta barshi bewani jima ba aka kuma maido Shi,Yana dawowa kuwa ya yace’ ya Sami matar aure Amma yaran Giwo ce,ba haka Umma taso haka de ta hakura tayi shiru Amma ba tasan auren nan Allah Yana ya gani bayan anyi aure ta jima bata haihu ba, sannan kuma bata zuwa gaida Umma ita kuwa Umma daman can basanta take ba shiyasa ko bi takanta batayi, Sai da ta shekara uku ta haifo ‘yarta mace,a haihuwa ta biyu ma mace ta haifa, anan kuma aka masa transfer ya koma Adamawa aka kuma Kara masa matsayi saboda haza karsa a wurin aiki zuwansa Adamawa a inda yake aiki ya hadu da wata zulai
Ihat, dayake mutanen da akwai rike amana ganin sa mutum kamili da Shi yasa suka bashi aurenta sannan kuma aka taho da iayenta, a tunanin sa umma zatayi wani Abu sai dai kuma ganin ta nuna bakomai yasa Shi Jin dadin haka satinsu guda anan gidan su sukace zasu koma Suma su Umma suka biso don ganin wuri, Babu ta inda yasamu matsala sai a wurin matar Shi Hajiya Kenan tayi borin ta kada ta Raya Amma a banza, zulaihat yarinya ce mai hankali da girmama na gaba sa’ar Ruqayya ce shiyasa komai nasu yafi zuwa daya ba ta da matsala ko kadan kowa Yana santa, sai alokacin Usman yace’ zaiyi aure,dayake Baba bame matsawa haka ma Umma ita dai kawai barta a fada kosa ya shaida da wannan musamman idan kayi Abu baka nemi shawarta ba, a lokaci ne kuma mutuwar Baban Umma ya riske mu gabadaya muka tafi a motar Usman bayan wani lokaci aka daura auren Usaman da matar da ya gani acan kauye a kauyen aka daura ya dau matarsa suka tafi Ilorin,

A bangaren zulait da Umma babu zancen zaman lafiya amma babu Wanda yasani sau uku tana yin Bari daga nan kuma bata sake yin wani cikin ba, Amma Umma tace ya daukota ya dawo da ita kusa da ita, a lokacin mun Gama makaranta mun gama ba jimawa Nayi aure, na tafi bagan aurena da wata biyar Allah yayiwa Baba rasuwa mutuwar ta girgiza mu kuman dauki hakuri, bayan wata uku matar Usaman ta haihu Dan ba Rai kuma bata da lafiya a dole Umma ta ta shirya tace zata je karma a dagawa Yan uwa hankali Ruqayya da Zulaihat suka koma gidan Adam da zama Zuwan Ruqayya ne yasa kowa sannin halinda ake ciki Ashe bakar azaba Umma ke ganata Mata ganinta mai hakuri a, koda Umma ta dawo Ruqayya tace baza ta koma ba zata Kula da Zulaihat tunda kamar ga ciki nan a jikinta batayi musu ba ta barta, sanda aka zo neman Ruqayya da aure sai dai idan an daura auren zata tafi kasar waje ne mijin kuma ba ita kadai bace itace ta biyu,ta nemi alfarmar a Bari sai zalaihat ta haihu sai ayi auren haka aka kuwa aka Bari sai ta haihu.
A ranar da ta haihu a ranar tayi rubutu a paper ta ajje ta tafi, bamu Kara ganinta bamu Kara Jin labarinta ta tafi ta bar danta, babu wanda yasan dalili sannan kuma Adam ya sauyawa Ruqayya kwata kwata dukda ita tace rike da dan da ta haifa ta Bari taki ta bawa kowa Haka Hajiya tayi tayi tabata amma a banza bata bata ba,ko Umma bata bawa bare ni,haka ta rike Shi gam ta Hana kowa Shi ko bandaki zataje dashi take tafiya,

Adam kuwa yayi neman duniya babu ita babu labarin ta har Adamawa yaje Amma shiru babu ita Suma sun tabbatar da bata zo ba Yayanta shima Wanda yake zaune a kano ya tabbatar da bataje gidan saba sosai abubuwa sun rikice cikin kuwa harda canzawar Adam kwata kwata ya canza ya dena walwala,
Bayan sati har Anyi nema an gaji kowa ya hakura ya fawwala Allah kuma har lokacin Ruqayya bata yarfa da kowa ba Ya dauki yaron ba ko huduba mahaifin Shi bemasa ba Usaman da yazo shine ya masa babu Wanda yasani, duk yarda Adam yayi da San ganin dansa taki yarda bata bawa kowa Shi bare a dauka,sai da sati yazo kowa yasan sunasa Abdulshakur,Wanda ta masa lakabi da Binaif ko taron suna ba’ayi ba don firgicin da ake ciki, bayan wata uku kuwa aka daurawa Ruqayya aure sai dai ko kafin a daura sai da tabbatar wa mijinta cewam tare da Binaif zata tafi,kuma ya yarda sannan aka daura auren. Tunda ta tafi bata taba zuwa gida ba duk mace macen da ake da biki bikin da ake bata taba zuwa ba, sai da zata rasu tazo anan ta rasi abinta, sannan shima Adam Bansani ba ko Yana zuwa, ko Baya zuwa inda ya Kara aure ya auri wata ‘yar kano har ya haifi ‘ya’ya goma Duka Mata,yayinda yanzu Usman Yana da yara hudu biyu Maza biyu Mata Matan kusan sa’anin su Mus’ab ne mazan ne zakuyi kai daya dasu, ban Baki labarin suba nasan Umma tabaki watakil nikuma ‘ya’ya biyu Allah ya bani alokacin da na fitar da rai ga samu,Nafisa da kuma Ummi mai sunan Ruqayya,

Numfasawa tayi tace’ yanzu kinji komai ko?

Daga Mata Kai tayi sannan tace’ Amma me ta rubuta ajikin papern data Bari?

Anty safiya tace’ ca tace kar a nemeta kar kuma a fadawa danta Yana da uwa. Ta tafi tayi nesa da gida Kar kuma akai danta wurin Yan uwanta a bawa babansa, sannan asawa Danta sunan Kakanta Abdulshakur Kenan,
Amma abinda yabawa kowa mamaki irin yarda Ruqayya ta Hana kowa Binaif ta riki Shi gam ta Hana to dayake sun shaku sai ake ganin kamar shakuwar ce tasa haka,

Ummusalma tace’ kinsan unguwar su a Adamawa ?

Nasani sosai don muna yawan Kai masu ziyara ma,

To yayanta fa na nan kano?

Gaskiya shima tun lokacin nan befi da wata ba shima da mukaje akecewa ya koma London daga nan de zumunci yayi karanci shima kansa Adam din inaga beda numbern sa ma.
Amma je gaskiya Amma Bansan Adam ba,

Ummusalma tace’ A ina suke to a Adamawa?

Fada Mata inda suke tayi tace Amma Bansan ko sun tashi ba,

Shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa a ransa Anty safiya tace’ kinga Bari naje bangaida kowa ba,

Ummusalma tace’ Zan iya tafiya da wannan?
Tafada tana nuna hotan hannunta,

Daga Mata Kai kawai tayi ta fita, itama Ummusalma fitowa tayi daga dakin takoma dakin Nafisa, ta kwanta tana tunanin wannan lamari, Nafisa ce ta shigo tana kuka ita da Ummi sai Ahmad a bayansu, tashi tayi zaune,

tace’ Nafisa lafiya kuwa?
Bata bata amsa ba tacigaba da kukanta, Ahmad kuma Yana rarrashin Ummi Yana bata chocolate wai tayi shiru, hannunsa ta janyo,

tace’ me yafaru?

Yace’ Hajja ce tasa su kuka, daman Kullum idan sukaje sai ta daki ummi wai tana Mata barna,

Wacce Hajja?

Kakar muce, bata San Mommy itama mommy kullum sai ta fada Mata magana idan kuma bataje gaisheta ba nanma ta ringa fada,kuma ita Anty Hauwa ba kullum take zuwa gaidata ba,

To meyasa take masu haka?

Nima bansani ba sai dai naji tana cewa mai kashin tsiya bata haifi yara ba lokacin da ake so sai yanzu, haka kullum take fada, Mami na ce kawai kawarta shine itama ta dena sonta,

Shiru yayi yace’ Nima kuma Bana Santa idan na girma daman soja Zan Zama wallahi harbe hannunta zanyi kowa ma ya huta,

Meyasa zaka harbeta? Kakar kace fa?

Ummi fa take Duka kullum kullum sai ta duke ta,

Abun ya bata mamaki Bama Maminshi da ba’a soba a’a don ana Duka Ummi, sunkuyo wa tayi daidai kunna sa,

tace’ kana San ummi ne?
Ta fada da Dan murmushi a fuskarta,

Shima cikin rada,
yace’ taya kika sani?
Murmushi tayi tace’ Ganewa nayi,

Tace’ yanzu tunda kana Santa mezai Hana muyi wani Abu,

Hannunta ya kama suka fito parlour ya jata ta karamar kofa suka fita wurin kamar hutawa ne haka yayi kyau ya kawatu suka zauna a kujera,

yace’ kinga anan Yaya Abdul yake hutawa shima saboda Hajja yadena zuwa,

Waye haka?

Ya Abdulshakur,

Shiru tayi bata Kara magana ba ganin haka yasa Shi

cewa’ kika ce muyi wani Abu?
Me Kenan?

Tace’ soja kake son Zama ko?

Daga Kai yayi tace’ soja bashi da tsoro, ko kadan kasan me zakayi ?

Yace’ a,a

Tace’ to farko Ka fara zuwa Ka tambayi Hajja dalilin tsanat da takewa Momy idan ta fada maka ,sai kazo Ka fada min nikuma Zan fada maka abinda zaka fada Mata.

Yace’ to shikenan yanzu?

Tace’ a,a ahankali zamu bi abin ai,

Yaron ya birgeta bakadan,sosai ya Shiga ranta sai take ganin kamar Yusuf sanda Yana karami shima akwai wayo da bin kwakwafi, shafa kansa take yarda yake zuba Mata surutu tana murmushi tana shafa kansa kaunar yaron taji sosai ta Shiga ranta, har wani hadawa yake da hannu idan Yana Mata bayani.

Da daddare kasa kwanciya tayi tana juya labarin a ranta mekenan? Gaba daya komai tana da Karin bayani Inama ace Anty Ummi tana da rai, da duk amsar tambayar nan tana dasu, bata kwanta ba sai da ta tabbatar ta Gama duk wani Abu da zatayi,

Washegari da tunda asuba bata koma ba dayake ta fadawa Anty safiya zataje ta fadawa kawayenta kafin a fara gyaran jiki, Kuma ta yarda ta amince ita da kawarta zasuje ta kirashi wai ta fada masa, shiyasa bata koma ba, tayi shirin ta tsab tasa kayanta kalla uku da Abubuwan bukata fitowa tayi ta fadawa Anty safiya cewan zasu tafi don su Gama da wuri su dawo,

Anty safiya tace’to Allah ya kiyaye Banda shirme de Ummusalma kinji ko?

Murmushi kawai tayi,kudi Anty safiya tabata

tace’ gashi inji mijinki,
Karba tayi tayi godiya ta fice,tana fita ta kira waya tace’ kana kofar gida? Daga can aka amsa da eh,

Tana fita daga babbam gida kuwa ta hango bakar mota,nufar wurinta tayi ta Shiga Baya,

Yace’ ina muka nufa?

Tace’ ADAMAWA

✨✨✨✨✨✨✨

Da sassafe yayi shiryansa tsab ya fice agidan beyiwa kowa sallama bare ya su San ya tafi, hanyar Jigawa ya dauka,bashi ya isa ba sai goma sabida irin tafiyar da yake yi address din da ya rubuta yake bi har ya karaso wurin, kana gana zakasan company ne karami don ko Rabin Wanda ya siya beyi ba,
Knocking yayi mai gadi ya fito,sai da suka gaisa,

yace’ don Allah shugaban wannan company din nake nema,

Mai gadi yace’ to kaga de yau lahadi bazaka Sami kowa ba,

Yace’ to ko Zan iya samun sa a gida?

Ehh zaka iya, samunsa Baya zuwa ko ina idan na uzuri ne ya taso ba,

Yace’ am ina ne gidan nasa?

G9 zaka je,

Ai Bansan G9 din ba,ni bako ne,

To kuma kaga bakowa anan kusa da sai nasa a raka Ka,amma Ka jira kadan wanda zai karbeni zaizo sai mu tafi in nuna maka,

To shikenan nagode badamuwa Bana jira din,

Basu wani jima ba dayawa wani yazo ya karbeshi, suka tafi,tafiya suke Yana nuna masa hanya har suka isa kofar gidan nan sa,sai da suka fita sannan mai gadi yace’ to ga gidan nasa,ni na wuce,
Kudi ya Ciro ya bashi ya kuma yimasa godiya,

Karasawa kofar gidan yayi tare da knocking,Jin shiru yasa ya karayin wani namma de shiru karawa yayi sannan yaji ance waye?
Shi besa ba da wani waye ba,hasalima yasaba kawai door bell zai Danna yazo a bude,
Amma wani waye? Shiru yayi don besan mezai ce ba,

Zuwa tayi ta bude masa, yace’ mai gidan nan?

Eh Yana nan,

Kice yayi bako,

To,

Ta koma bata jima ta dawo tace’ ance Ka shigo,ita ke masa jagora har cikin parlourn sannan taje ta kawo masa drinks da snacks, duda da safe ne.

Wani mutum yane ya fito kamili babba dashi, wuri ya samu ya zauna suka gaisa sai kuma sukayi shiru, mutumin yace’ ban shaida kaba,

Binaif yace’ ai baka sanni ba, amma wala’allah idan na Baka tambaya zaka iya tambaya hadina da komawa waye,

Mutumin yace’ wannan wacce irin tambaya ce haka?

Murmushi kawai Binaif yayi,
yace’ game da companyn ka, bayan Kai waye shugaban Ka?

Sosai mamaki ya bayyana a Saman fuskar mutumin nan, yace’ Kai waye din Muhammad ne?

Fadada murmushin sa yayi yace’ Sirikinsa ne, nasan daman tambayar Kenan,

Yace’ siriki? Kai yaro Muhammad daga har ‘ya’yan sa guda biyu da matar sa sun rasu, da dansa kace min ne ma Zan yarda,

Binaif kamar yarda na fada maka ni sirikin sane kuma Ka yarda dani, ‘yar sa nake aure Ummusalma koba ita bace?

Sosai mamaki ya lullubi mutumin yace’ ‘yarsa? Bata mutu ba? Tana ina? Ina take?

Yace’ bata mutuba,Abu daya nake so da Kai shine Ka fadamin Kai waye din shine? Aboki ? Dan uwa? Kode wani Abu haka?

Numfashi mutumin yace’ sunana Munir Yakubu, Dan asalin garin Gumel mahaifiya ta rasu tun ina yaro Babana Shi ya rikeni dukda mitar yayi aure da ake masa Amma yayi biris da zancen kuwa, Shi yaciga da Kula Dani har na Kaiga nagama Nce dina,Amma babu aikinyi a lokacin Babana ya fara ciwo kafa dayake Nika yake yi sai naciga dayi sabida aikin da za’a masa
Gashi kuma injin bayayi kullum Yana cikin gyara wayanci shike cinye mana kudin,kawai na saidashi na tafi Lagos don samu kudi,sai dai kuma kasan cewata sabon Shiga aka sa cemun kudi ga babu wurin kwana ga yunwa da wahala zafi komai ya hade min,nasami gafen titi na zauna kwatsam wata mota tazo ta bigeni tayi gaba Allah ya rufa asiri ma banji ciwo ba sai dai naji jiki,jiki ya kama ciwo Bansan meke damuna ba, idan nace zanyi dako kafin na dauka har andauke anyi gaba,ga ciwon kafa Ashe nayi tagade ruwan da zan shama aiki ne, ina kwance a gefen titi awannan lokacin mutuwa kawai nake bawa kaina,sai ga Ya Muhammad da Matar sa Sunzo sun taimaka min sun kaini asibiti bayan na warke suka tambayeni inda nake na fada masu na kuma Basu labari,shine ya biya kudin aikin sannan yace zai Samar min aiki a kusa da gida don nake zuwa ina Kula da mahaifina,banyi musu ba na yarda bayan anyiwa Babana aiki yazo da kanshi ya daukeni ya kawo ni nan garin ya nuna min komai da komai da shagunan sa da inda yake da Zama gidajen sa komai nashi wai gudun bacin Rana, koda na tambaya shi Baya tsoran na cuce Shi? Sai yace duk Wanda ya cuci wani kansa ya cuta ba Shi ba,da wannan Babana kullum yake Kara min nasiha Akan kar na yaudareshi na rike amana ko a zuciya ta Bani da buri cutar sa, a haka muka shafe shakara uku ina masa aiki duk wani Abu da yayi sai ya fada min, sai dai Mahmud Baya San haka ko kadan Amma be taba nunawa ba,ya daukeni tamkar kaninsa haka itama matarsa, lokacin da ta samu ciki ya sai wani fili yace duk Wanda aka haifa yazama nashi, ranar da ta haihu ranar amaida wannan fili sunan Dan da Umar don ni har na manta ma da anyi zancen, sai dai washegari da za’a sallame mu a asibiti aka nemi da aka rasa daga karshe aka gano sace Shi akayi kuma ya mutu, bayan anyi hakuri suka kuma samun wani ciki suka haifi twins mas’ud da mus’ab sannan suka dawo Abuja inda ya cigaba da kasuwancin sa,Iyayen matar sa sune suka rike Shi don Shi don Shi a hannun matar uba ya tashi mahaifinta ya daukeshi da suke unguwa daya a yarda ya ban labari Kenan, sai da twins suka shekara hudu Allah yasake a zurta su da Ummusalma suna Santa, tana da shekara biyu a duniya aka nemi yayunta aka rasa kosama ko kasa ba’a gani ba, anyi haka da sati daya gidan su ya kama da wuta, inajin labari washegari na tafi Abuja ganin gidan su ya kone kuma babu kowa da yake zaman makoki yasa na tafi kafancan Inda Iyayen su suke sai dai na iske babu kowa a gidan sun tashi, haka na dawo jikina ba dadi, ga kuma wani labari da ya riskeni cewan Mahmud ya mallake duk wata kadara ta Shi,banyi mamaki ba don nasan zai aikata hakan, sai dai bai san shagunan sa na nan ba da wani dake Paris shima besani ba Dani da Wanda yake Kula Dana Paris muka cigaba da Kula da komai dake hannun mu bayan na fada masa halin da ake ciki.
Shiru yayi na wani lokaci sannan yace’ gashi kazo Kace min Kai siriki sa ne taya?

Binaif da labarin ya Dan daure masa Kai Yana so ya bi komai a hankali ne, numfasawa yayi,

yace’ shine ya dauke ta ya so ya lalata Mata tarbiyar ta, sannan ya turata karatu don tarbiyar ta ta war gaje, sai dai Allah ba nufa ba hakan bata faru ba, sannan Yan uwanta Suma duk suna nan da ransu Umar ne bansan inda yake ba,Amma shima na tabbata Yana da rai,

Taya zakace Umar na Rai?

Sabida ta taba ganin wani, ba wannan ba ina so ayi wani abu ,ya saida min da company guda daya dake Kano ya kuma bani takardun karya a matsayin sune na gaskiya nikuma ina da na gaskiyar a hannu na ina so mu hada karfi da karfi mu yaki karfe,kayi wannan sadaukarwa ga abinda ya maka,

Koba baka fada ba yaro, zanyi komai Insha Allah indai komai Nasu zai dawo, bawan nan ba gidan marayun dake Lagos ya sayar dashi yanzu duk yaran da aka Kai can to idan suka taso kasar waje ake tura su, wasu suna aikin miyagun kwayoyi wasu kuma fashi, Mata kuma a tura su bauta gida Jen aikin reno wanke wanke da dw sauran aiki,sa’ar daya ce basa bata Mata masu rayuwa sai dai Basu San inda zasu tsinci kansu a ciki ba,ga kuma yunwa da suke fama da ita,
Ina so mu fara daga nan kafin muyi komai,

Binaif yace’ to shikenan Insha Allah daga nan zamu fara amma abinda nake so daki Ka fara nemo mana wanne percentage ake bashi,

Taya Zan iya Nemo percentage din da ake bashi? Baya ga haka ya sayar dashi,

Murmushi Binaif yayi yace’ koda ya sayar dashi bazai Bari haka kawai ba, dole za’a bashi wani Abu daga ciki, zaka iya nemowa tunda ka iya sannin an sayar dashi,

Zan duba na gani,

Cigaba da magana sukayi har biyu tayi masu sani ba, bayan sunyi sallah Binaif yace’ zai tafi
Dakyar ya tsaya yaci abinci sukayi exchanges numbers daga nan ya dau hanya Yana tafiya yaji Karan shigowar sako be Kula ba, wannan Karon yayi gudu a hanya don uku da rabi ma acikin kano tamasa kafin ya karasa gida anyi la’asar Yana zuwa bakowa a parlour jakarsa ya dauka ya Shiga ciki sai da yayi wanka yasa kayan shan iska yayi sallah sannan ya kwanta ya janyo wayar sa ganin message din ta yasa Shi budewa,

Nayi tafiya zuwa Adamawa, take care.

Besan abinda yaji ba don bazai iya fada ba, take care Shi yafi bashi haushi ma, ba gaisuwa bakomai sai take care juyi kawai yake Yana maimata take care din nan ina laifin ma ta Dan masa message din na morning ko yaji sanyi a ransa,Amma sai take care da ce masa,tsaki yaja a Karo na ba adadi wayar ma ajje tayayi Yana tunanin su Mus’ab ne suka shigo banza yayi masu ya cigaba da abinda yake,

✨✨✨✨✨✨✨✨

Bayan sun tsaya sunyi sallah tayi tunanin tura masa message shiyasa ta tura masa Amma ba reply daman tasan bazaiyi ba mene na damun kanta, sai yamma lis suka isa da tambaya sukaje unguwar har suka karasa kofar gidan, gida ne matsakai ci na rufin asiri gefen sa kuma gidane mekyau ba laifi, sallama tayi a kofar gidan aka amsa shigowa tayi matar dake zaune ta tashi tana Mata lalle da fillanci ta bata wuri ta zauna ta kawo Mata ruwa mai sanyi ta ajje mata suka gaisa cikin fillanci, cikin fillancin matar tace Mata ‘” ban gane ki ba Bingyal daga ina?

Itama cikin fillancin ta mayar Mata tace’ Baki sanni ba, sai dai ina tambaya nanne gidan Abdullah Abdul shakur? Da matar sa Mariya ? Suna da ‘ya’ya biyu zulaihat da kuma Abdallah,

Cikin mamaki matar tace’ eh nan ne ke wace?

Wani dattijo ne ya fito Yana dogarawa yace’wai me nake ji ne, ji nayi ana anbatar zulaihat da kuma Abdullahi,
Matar ta tashi ta karaso da Shi ya zauna sannan ta fada masa abinda akace da kuma tambayar da ta Mata,shima yace’ fada mana ke wace?

Ni matar jikanku ne wanda ‘yarku ta tafi ta bari,

A tare suka ce a tare suka ce TASHI KI FITA……….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 18

Advertisements _____ 18   Zirga zirga kawai yakeyi a cikin rasa yanda zaiyi ya bullowa wannan lamarin shidai…
KALLABI
Read More

KALLABI 13

Advertisements _____ *<Babi Na sha Uku>* Bayan shekara biyu. Wanke mata kai Innayoh take, tayi shiru zaka dauka…