A BAKIN WAWA 27

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisement

27

 

 

 

Baba be saurareshi yaci gaba,

yace’ ranar da muka tsinceka acan wani kauyen ne, kusa da Adamawa ba nisa, mun tsaya don zainab tayi fitsari taje zatayi taga wani jariri a wuri dayake yarinya ce a lokacin sai da tayi fitsarin ta dauko yaran ta kawo tace Baba kaga a can wurin na ganshi,karbar Shi nayi na Kare masa kallo, ya kurkurje kuma idan ba lura kayi ba dakyau tsab zakace Baya numfashi, da kuma hannu sa Wanda ya kumbura,dayan hannun kuma shaida ce ta daga asibiti aka dauko Shi Wanda ake mannawa yara shaida, da number, ita mahaifiyar ta ma tazaci ya mutu,  mukaje muka duba ta nuna mana inda taga yaran ga kuma towel can a gefe, daukan towel din mukayi,ta rufe Shi tace ya mutu,nine nace Mata be mutu ba,gashi kuma bakowa a wurin mu ba gidan dagaci muka sani ba, tausayin yaran yasata cewa mu tafi dashi,haka ma zainab banki ta tasu ba muka dawo dashi Amma sai da mukaje asibiti aka bashi taimakon gaggawa tukunna, sa’a Muka wucs gida,sai muna zuwa gida labari yasha banban, tsab ya kwashe komai ya fada masu har zuwan da yake yi da kuma zuwan Shi na karshe sa’a nan yayi shiru,

 

Tunda Baba ya fara yake sauraran Shi be taba sanin saboda dashi ne basa zuwa wurin Anfa da Fendo, hawaye ne ya fara zarya a kumatunsa Shi shikenan beda uwa be da Uba? Gashi de wulgar dashi akayi ai kuma mutane sun shaida haka? Sun San basa son sa meyasa suka haifeshi da hanzari ya dade da mutuwa da ba’a ceci rayuwar Shi ba,tunda aka fara ya fara comparing rayuwar sa da ta Ummusalma beda iyaye kamar yarda itama bata da iyaye inama zai ganta.

 

Anty ce ta kwantar da kanshi a cinyarta,

Advertisements

tace’ lokacin da naga hoton Ummusalma na hango tsan tsar kamar ku, sai dai Kai Baka ga hakan ba sam,tun a sannan na dasa ayar tambaya a kanta shin Baku da alaka ne? Har hotan na turawa Baba shima kuma ya gani sai dai yace’ min yana yawan ganinta a airport din London tana raka wata ita kuma sai ta dawo, Ashe shima Yana tunanin kamar yarda nake, daga baya ne yadena ganinta besan dalili ba, beyi wani Abu akai ba Shi a zatan sa ‘yar can ce. Koda yayi bincike a kanta sai ya tarar ba haka bane ba, ba iyayenta bane sai dai be tsananta binciken ba ya barshi iya haka.

 

Baffa dake sauraran kowa yace’ ita wannan din da kuke fada Wacece?

Anan suka bashi labarin abinda suka sani, sannan ummu ta Basu kaf diary dinta da ga karanta sosai kuwa abin ya Basu mamakin haka ga kuma news din da sukaji ranar Saturday Amma ita ummu bata ma San anyi ba. Shiru kowa yayi Yana tunanin wani Abu ransa, shidai Uncle abinda yake ji kadai ya ishe Shi,

 

Ummu tace’ Baffa da mukazo naji kace Kanwar Shi kun Santa ne?

 

Baffa yace’ tabbas tazo anan ta kwana, yau da safe ta tafi kuma bakowa ne yace ta tafi ba sai ni,nine tun farko naja komai me ake da zuciya irin tawa?

 

Baba yace’ Anfa kadena fadar haka mana, Wacece ita har tazo nan?

 

Baffa kasa magana yayi gani yake duk Shi yaja komai da ace bece ta tashi ta fita ba da duk haka bata faru ba,

Advertisements

 

Inna tace’  Yarinyar tazo gidan nan,itace ta fara ankarar mu abinda babu Wanda ya fada mana, itace ta daidaita komai tsakanin mu da ku, itace silar komai, gashi ta tafi, sai dai tace’ ita Sirakace a gare mu domin Dan zulaihat take aure.

 

Dan zulaihat ?? Baba ya maimaita,

Jinjina masa Kai tayi tace’ ehh haka ta fada mana,

 

Anty tace’ me tace maku sunanta ?

 

Ummusalma tace, kuma a gaskiya Nima Naga kama sosai da sosai Dan Zama a Iya cewa ‘yan biyu ne,

 

Mijin Anty yace’ to ya akayi kuka barta ta tafi?

 

Inna tace’ kayya yaro kuskure an rigada na tafka Shi sai kuma gudun yin wani,

 

Yace’ to Baku tambayeta komai game da ita ba?

 

Gaskiya bamu tambaya ba, bamu Sami damar yin hakan ba,

 

Shiru yayi Yana nazarin wani Abu,kowa shiru yayi can ya dago,

 

yace’ kunsan ita zulaihat dinne? Da tace’ danta take aure?

 

Inna tace’ ‘yar muce zulaihat wacce ta bata shekara da shekaru,

 

Yace’ to ko kunsan inda take? Nufina gidan mijin ta ?

 

Baba yace’ gaskiya bazan ceba,don nikam rabona dashi na manta ko a hanya zai iya wucewa na wuce bamu gane juna ba, ko gidan ma ni bazan iya kaika ba,

 

Inna tace’ Ada suna zuwa daga Baya ne kuma suka dena muma kuma muka dena shikenan zumunci yayi nisa kuma,

 

Shiru yayi yace’ yanzu dole muna bukatar saninin inda gidan yake,dole sai anyi bincike indai muna San mu San idan suna alaka da Abdullah,

Kowa kuma yayi na’am da zancen sa daga nan kowa shiru yayi shidai uncle ba Baka sai kunne Shi bega amfanin Nemo subama tunda sune suka yar dashi ai.

 

Sai bayan sallahn Isha Baban Ummu yacet zai tafi hakan, zai barsu anan don su ga ‘yan uwa da abokai, tunda Yana da wata matar,ita de ummu bata so ba, gashi lokacin basirar ta ta dauke batace makaranta ba,haka ya taho a jirgi Allah yasa ya tafi da passport din Shi ya barsu ba ranar dawowa .

 

 

 

🌼🌼🌼🌼🌼🌼

 

 

Yusuf ne da Yaseer suna zaune a tsakar gidan su,kowa yayi jigum Yana kallan wani wuri, suna wani tunanin na daban, gaba daya sun rame sabida tunanin da suka sawa kansu danma suna Dan debe kewa idan da nepa,to yau kusan sati ma babu nepar  Shiyasa suka fito suka zauna,

Yusuf ne ya kalli yaseer,

 

yace’  kasan menake tunani?

 

Yaseer yace’ a,a sai Ka fada,

 

Ina tunanin Ummu ne,nasan tadena surutu yanzu sabida rashin mu,

 

Yaseer yace’ nasan dahaka,Amma Kai Baka tunanin Mama?

 

Murmushin takaici Yusuf yayi yace’ me zanyi tunanin akai? Ita da suka raba uwa ‘da, uba da ‘da?

Karka manta sune suka raba yaya salama da Babanta da kuma yayunta guda uku,har ‘ya’ya hudu? Hakan be ishe suba sai da suka nemi su watsa Mata tarbiyar ta a matsayin ta na mace,hakan be ishesu ba suka kuma turata karatu Akan manufar su,ko ca aka ce masu  kowannne dane ake turawa yake watsewa oho, kuma kana min zancen su? Banyi ba kuma bazanyi ba,

 

Shima yaseer murmushi yayi yace’ nagode daka tuna min hakan,Amma kasani no matter how bad they are, they still our parent, don’t ever forget mufa maza ne aljannar mu na kasan su,ba Mata bane da aka ce aljannar su na kasan mijin su, koda matanne ma ba’a ce sabawa iyayen su ba, and kuma idan ma duba acikin 100% Maza kalilanne ke bin iyayen su musamman idan basuyi dacen Mata ta gari ba, Mata kuwa zaka samu kusan rabi da kwata basa bin iyayen su, Bana so mu Zama masu sabawa iyaye kuma fa sun bamu gwargwadon ikan su, suna San mu fiye da tunanin Ka,

 

Murmushi Yusuf yayi yacet ehh lalle Kace min ka girma u know all this,Nima kuma nasani, Amma abinda sukayi sun kyauta ne? Mema ya kawo wani bin iyaye, inama Ka zancen Ummu ne fa,

 

Yace’ nasani na fada maka ne don kar wata rana kana irin wannan maganar Ka fada masu ba dadi, shiyasa Amma kayi hakuri,

 

Yusuf yace’ a gaskiya nafi damuwa da Ummu Akan Mama Nima kuma bansan dalili ba haka kawai, nasan ummu itama hakanne, mama kuwa nasan na wani lokacine,mun fi kowa sannin halin kayanmu,

 

Murmushi mai kamar dariya dariya yaseer yayi yace’ dude just tell me u fall in ……. Lemme keep my mouth up,

 

Kai mekake nufi?

 

Abinda Ka kake nufi Nima Shi nake nufi ai,

 

Ka kiyayeni wallahi,taam

 

Ahh ai dole na kiyayi Yayamu,

Yafada da dariya Yana matsawa daga wurin Shi yasan yanzu sai a kawo masa mazga,

 

Yusuf yace’ Kai wallahi ba abind kake tunanin bane ba,kawai de ina adanawa wani ita ne?

 

Ohhh shiyasa kake koremata samari ko? Allah ya komar mu can gida zan nuna ma yarda kakeyi idan mun shiga school kar a ma zo wuri mu Banza yayi dashi, shikuwa yaseer cigaba yayi da zancen sa ganin de ba shiru zaiyi ba yasa Shi,

 

Cewa’ Kai bafa abinda kake tunani bane ba,ni kawai wani Abu nake hangowa ne kawai kuma nasan it will work,

 

Ehhmmm time will tell,

 

Daga nan kuma akayi shiru aka fara tunanin yaushe ne ranar fitar su? Sun tunda suke Basu taba gani an dauke masu wuta ba,gashi de a unguwa suke sometime suna Jin hiran samari da yamma ko da dare

 

✨✨✨✨✨✨✨

 

 

 

Umma tana zaune a parlour Daddy ya shigo sai da suka gaisa,

tace’ yawwa Kai zaka Kaine ko direba ne? Yanzu nake so na tafi kaga de Tara tayi,

 

Yace’ driver ne zaikai ki ni sai ranar jummu’ah idan za’a daura auren ‘yar mai gari zanzo,

 

Ummu tace’ afto kaga ni nama manta shaf da zancen auren sa to shikenan hakan yayi kyau Allah ya kaimu,

Tace’ kaga ni Zan tafi kuma bazai iyu na tafi da ‘yar mutane ba, sabida haka idan kaje gida Ka turo Saima ko su Ameera sai su zauna tare da ‘yan albarka kagane ai,

 

Yace’ to shikenan badamuwa,nace Umma yanzu idan kika tafi sai yaushe Kenan?

 

Umma tace’ af zancen banza Kenan,ai idan na tafi to sai kawai sai kun ganni Dan bazan dawo ba yanzu ah to,

 

Idan kunga anyi biki Nayi wata bandawo ba to kawai salin alin ku sallami mai aiki su kuma su koma gidan yayansu audushakuru bazan lamice zaman su su kadai ba ake cewa gidana gidan Maza,

 

Shidai Daddy shiru yayi don besa tacewa Yana magana zatace zata koma can da Zama shikuma Allah ya gani Baya so yafi so yake Jin ta a kusa dashi,  sai can,

 

yace’ sadakin wannan yarinyar fa na Baki kya bata ko kuma na Bashi,

 

A,ah  safiya zata karba sai ta bata ko kade? Kaga tashi kaje Ka Kira min ‘yan albarka Maza Maza, Zan tafi,

 

Tashi yayi yaje kofar dakinsu yayi knocking sai da yayi da karfi sukaji, Mas’ud ne ya taso ya bude mai kofar yana mistsika Ido,ai yana ganin Daddy yayi wani Wawa tsalle tare da ihu ya rungume shi, shima Mus’ab tasowa yayi ya rungume shi,

 

Binaif dayake shiryawa Jin ihu ya fito a dari ganin su da Daddy yasa Shi karasawa Yana mai Dan Jan tsaki sai da ya gaida Daddy, yace’ ku har yanzu bazaku dena shirme bako?

Babu Wanda yayi magana sai sunnde Kai tsaki yaja ya wuce, komawa parlourn l sukayi Umma ta masu sallama har mota suka rakata da kayanta daga nan shima Daddy y wuce suka dawo cikin gida Umma ta fada masu zuwan Saima ko su Ameera baza su iya cewa ga yarda sukaji ba,sai dai baza su iya musu ba, shiyasa suka nuna bakomai hakan, dadin su daya bb Yana nan sai dai kuma yanzu sun lura yana fita aiki idan kuma ya tafi fa? Allah yasa ma zasu tafi interview shine kadai saukinsu,

Yana fitowa yagan su a parlour sunyi jigum kowa Yana saka abubuwa dayawa a ranshi har zai wuce sai kuma ya dawo ya tsaya,

 

yace’ meke faruwa?

Mus’ab yadago yace’ babu komai kawai de muna Jin tafiyar Umma ne,

 

Murmushi yayi yace’ waya Riga wani zuwa duniyar ?

 

Mas’ud yace’ Saima ce zata zo ta zauna anan ko ita ko zu Ameera,

 

Yace’ sai me Kenan?

 

Dagowa sukayi suka kalle shi,

Ya jinjina Kai alamar eh,

yace’  idan Baku dena wannan abun naku ba yanzu sai yaushe zaku dena,to idan Baku dena ba wata rana sai kunyi Dakunsa, Dana sani kuwa keyace,

Yasa Kai ya fice ya barsu sude haka suka kare wuni guda babu walwala sai da yamma ne suka Samu suka fita.

 

 

 

Bata dawo ba sai Yamma shima a gajiye ta dawo zaman mota ba sauki, a kofar gida ya ajje ta ta shiga bakowa a gidan da’alama Basu dawo ba daki ta wuce tayi wanka sun tsaya a hanya sunyi sallah, kitchen ta wuce ta zuba abinci ta dawo parlour ta zauna wayarta ta dauka ta Kira, Maman Sadiq daga can maman Sadiq data dauka,   tace’ kwana dayawa,

Sai suka Gama gaisawa,

 

tace’ kindawo ne?

 

Maman Sadiq tace’ ahh haba de yanzu fa dududu sati befi uku ba sai na cika watan nan ai Insha Allah Zan dawo,

 

Tace’ to shikenan numbern iya ladi zaki taimaka min dashi Dan Allah,

 

Okay badamuwa Bari na turo maki, sai da suka Kara gaisawa sannan sukayi sallama,

 

Tana cikin cin abinci kuwa sai ga number ta shigo sai da suka gaisa tatada Mata abinda zata fada mata sannan sukayi sallama ta kashe wayarta,

Iya ladi ce kadai yanzu hope dinta idan itama ta kasam shikenan kuma batasan me zai faru ba, Nafisa ce ta fafa dawowa sai ummi da Ahmad,

 

tace’ Anty fa ina taje?

 

Nafisa tace’ asibiti taje ta inaga yau sai dare zata dawo tunda bata je ta dauko muba,

 

Tace’ daman tana kaiwa haka?

 

Indai aikin suna da patient din da babu mai kuka dashi suna kaiwa mana sosai ma sai Wanda zaiyi na Dare yazo sannan sai su dawo,

Jinjina Kai kawai tayi bata iya magana ba,

 

Nafisa tace’ Anty Dan Allah gobe ki tafi dani raban katin kinji?

 

Tace’ kuma makarantar fah?

 

Anty anyi fa hutu ko kin manta ne?

 

Aikuwa de na manta gaskiya,

Amma nikam nagama nawa gayyatar sai na rakaki kiyi naki,

 

Dagaske zaki rakani?

 

Idan kina so zan rakaki mana,

 

Amma kuma Anty safiya bazata Bari ba,

 

Zata Bari mana,

Amma wai meyasa kike cemata Anty nagade mamanki ce,

 

Dariya tayi tace’ mamana ce Amma itace komai nawa, she’s my best friend,my friend,my mom, my everything,

 

Murmushi Ummusalma tayi a zahiri a badini kuwa kuka ne yake San zuwa mata,meyasa bazata tuna komai ba wai? Sanda tana karamar nan,meyasa bazata iya tuno iyayenta ba when’s she’s two years,

Bama taji abinda Nafisa ke fada Mata ba,sai ji tayi Anty na magana tana fadan ba’a cirewa Ummi Kaya ba ita da Ahmad daga nan de ita tashi tayi ta mai da kwanan kitchen   sanda tadawo itakuma Anty tana daki, lokacin kuma anyi magriba, shiyasa ta koma daki itama.

 

 

✨✨✨✨✨✨✨

 

Bayan kwana uku, suna zaune a can wurin hutawar su ita da Anty,

 

Anty tace’ ummu ya kamata ki Gama duk wani zirga zirgan ki daga yau zuwa gobe Dan inaso a San me za’ayi kinga har anci sati daya yanzu saura sati biyu gashi kuma Umma tace’ ana sauran  kwana hudu zamu tafi kije ki ga ‘yan uwa Suma su ganki, don ita Tama yi gaba abinta,

 

Murmushi tayi tace’ shikenan Insha Allah zanyi daman ina San na fita idan yamma tayi sai na fita nan ba nisa ne ma gidan,

To shikenan tace,

 

Suna nan zaune aka aiko da dambun nama wai inji Hajja, karba tayi ita daga jiya zuwa yau  tana ganin canji daga hajja ko tace Tama ga canji jiya an aiko da tuwon biski yau kuma an aiko da dambu, Anya bata Shirya wani Abu kuwa? Kuma dazu ma da taje gaida tmda Rana nan da fara’a ta amsa haka Suma yau Basu dawo da kuka ba da sukaje da safe, itakam abin ya ba mamaki,

Ummusalma tace’ Anty lafiya de?

 

Yake tayi tace’bakomai kawai ina tuna wani Abu ne shiyasa,

 

Murmushi kawai tayi tace’

Anty me aka kawo daman kwadayi kwadayi nakeji, tafada kawai don ta kawar da tunanin da takeyi tasan daman a

hakan zata faru ga mutumin da Baya Sanka kuma yanzu yake kyautata maka,

Budewa tayi suka ci ita de antu kadan taci  ta tashi,itamannawani dayawa taci ba dan daga ji na sayar wane.

 

Bayan sunyi sallahn la’asar ta Shirya tsab cikin shigarta ta kullum doguwar Riga tayi rolling ita kanta Anty taga tunda tazo sune kayanta batasa antamfa, sallama tayi Mata ta fita,

 

Anty tace’ kibari driver ya dawo sai ya kaiki,

Tace’ a,a Anty Zan tafi kawai,

Allah ya kiyaye Anty tace,

 

Allah ya taimaketa tana fita taga mai napep ta hau tafada masa inda zai kaita,

Yana ajjeta ta bashi kudin Shi ta Shiga gidan, bakowa a parlourn sai TV gidan de gashi nan yayi wani kaca kaca da shi duk an bata an zurzubar da abinci, a fili tace’ ohh sai kace marar hannu idan ya zubar da abinci bazai share ba, tsaki taja ta wuce dakin su, gadan ba’a gyare ba dakin ya danyi kura gashi nan ga kuma takardu daya barbaza a wurin kujera da kasan carpet rolling din ta cire ta cire doguwar rigar ta tasa wata yar Riga marar nauyi iya Ka gwiwa armless mai laushi da ita, ta fita ta dauko kayan aiki ta fara gyarawa sai da gyara tsab ta goge na gogewa ta tattare komai ta adana, toilet ma ta Shiga ta wanke Shi tass danma de taga kamar Yana wanke toilet din amma de wanki ta yafi nashi sau dubu ma kuwa, ta hada kayan shi kanana ta wanke su tas ta  shanya a toilet din, fitowa tayi daga dakin ta dawo parlourn har zata wuce sai kuma tace bari ta gyara shima tas ta gyara ta goge komai tayi mopping kitchen taje ta zubar da ruwan ta kofar baya ta kitchen gayayi tagani tare da kasko a wurin,dauka tayi ta ta kunna gas ta daura Shi akai ta barshi ta dawo tayi arranging Abubuwan da wargaza tana aiki, sannan ta koma ta duba dayake ta sa wuta kuma a bushe yake tuni ya kama ta zuba a cikin kasko windows ta firo parlour wurin turen wuta ta nufa tasa Wanda zata sa tashiga daki har toilet tayiwa turaren wutar ta dawo parlour shima tayi Yana karewa tana sa wani a haka har ta gaji taje ta ajje a lungun dining tare da kunna ac, dawowa daki tayi ta kunna ac sannan ta Shiga wanka bata jima bata batasan ya dawo ya tarar da ita shiyasa ma ta fito da wuri gashi yanzu biyar tayi, body spray kawai ta fesa ko mai bata fesa ba, sai dai kuma tunda ta fito takejin hayaniya tana tashi a parlour ita Tama zata tv ce sai dai kuma tunawa da tayi ta kashe kuma muryan mace takeji tana fada, wardrobe ta bude don sa Kaya taga hijabinta kawai tasa ta fita turus taja ta tsaya a bakin kofa ganin mutanen, ita kuwa Saima cigaba tayi da fada,

 

tace’ wato don kun rena ni ina magana kunyi min shiru ko?

Sannan ba’a samu Wanda zai dauka kayan nawa ba ya wanke kome?

 

Ameera tace’ Wallahi sun mugun Rana mana hankali banzaye ‘ya’yan shegu kawai, daman fa kinsan halin ‘yan Dan kauye idan yayi klin bada sunan wani abu ba,

 

Tace’ bedamena ba nidai kawai adau kayana a wanke mun kuma wallahi duk sanda kuka Kara kunnawa mutene wannan hayakin sai ranku ya baci,an koreku kunki korowa a Karo na ba adadi shegu dagin matsiyata, Mus’ab yace’ kiyi hakuri zamu wanke,

Wani wawan Mari ta saukar masa,

 

tace’ hakuri? Kana da bakin bada hakuri Amma Baka da abakin amsa? To ni Saima sai naci uwar mai ……

 

Jikake tas,  an wanke ta wani azabban mari,bata Gama Jin azaba aka kuma sauke Mata wani,ko bata tambaya ba tasan Binaif ne sai dai dagowar da zatayi sukayi four eyes da wata yarinya fuskarta a dauke tamau tana Mata wani irin kallo,kallon da bazata ta iya cewa na menene ba,

 

Fuska a dafe tace’ Wacece ke?

 

Ummusalma ta Kara daure fuska gashi daman fuska a daure an Kara tamketa tamau, ta hada gira idan nan ya Kara fitowa tayi folding hannayenta a kirji,

tace’ mace ce kamarki,sai dai ba ballagaza ba,marar hankali, shashan ba kamar ki.

 

Daga hannu tayi zata mareta taja Baya,

tace’ wanne zunubi nayi da zaki mareni?

Hahaha ba’a marina,ba’a dukana,ba’a fada min magana ko anyi bashi ne, bakisan Wacece niba kamar yarda basan Wacece keba sai dai yanzu nasan ke Wacece,

 

Ameera dake gefe tana kallan ikon Allah ta matso tace’ Wallahi tunda kika mareta sai kinhi dakin sani banza karuwar su mai kawo Ka…….

 

Bata karasa ba itama aka sauke Mata nata raban, ita har sau hudu,

Ummusalma taja ta tsaya a tsakiyar su,

 

tace’  idan naji wani ya Kara magana kuma ban Gama magana ba hmmm bansan mezanyi ba,

 

Saima tace’ uwarki zakice kina magana sai kace kin haifemu shegiya karuwa mai kama da…

 

Murmushi tayi ta matso daf da ita tace’ Naji ni karuwance  a gidan aka ganni Wanda za’a iya cewa ni matar gidan ce,ke kuma fa?

Ehhh?

Ai batayi aune ba taji ta a kasa  Ummusalma ta korfeta ta fada,gashi unexpected ne,ga titles har kanta da hannunta sai da suka bugu kasa daga hannun tayi,

 

Ummusalma tace’ waya fada maki ana karya doka ta? Ehh?

 

Murmushi tayi Wanda idan ba kallanta kayi ba bazakace tayi ba, idan ma kallan nata kake to sai Ka lura don ko second daya beyi ba ya bace a bakin ta, kayan dake kasa ta kalla inner wears ne ma Dan tsabar tambada Namiji zai wanke sai kace Dan daudu, mus’ab da mas’ud ta kalla Wanda suke kallanta tun fitowar ta suna mamakin ta inda ta fito sude basuga zuwanta ba kawai Marin suka gani, wata uwar harara ta maka masu ba shiru suka dukar da Kai kasa,

 

tace’ kwasu min Kaya,

 

Mas’ud ne ya kwasu ya Mika Mata shima Mus’ab ya kwashi sauran duk suka Mika mata,wata harara ta maka masu

 

tace’  bata,

 

Kallanta sukayi irin taya zamu bata Abu a kwance,

 

Tsaki taja tace’ ku watsa Mata mana,ita din uwar kuce?

A tsawace ta fada ranta yakai koluuwar baci ta tsani abun haushi,

 

Da sauri mas’ud ya watsa mata  shima haka mus’ab din, tsaki taja dawo da kallanta ga Saima wacce take kwance ta kasa tashi daman ga aba raguwa ita kuwa Ameera tunda taji Marin da bata taba jiba tasawa kanta salama ta bar wurin Aneesa ce ta fito itama data ta rashin kunyar,

 

tace’  Waccs tsinanniyar ce take tada mana hankali ne ? Ina bacci ana min tsawa zanci uwar yarinyar fah  ba ruwana,

 

Idan ba saita su tayi ba bazata bar gidan nan ba wato itace tsinanniya,hmmm shiru tayi sai da ta Kara so,

 

tace’ karuwa ce da dukan ‘ya’yan masu gida?

Mas’ud ta kalla ta gallawa harara cikin fillancin,

 

tace’ mareta?

Zaro ido sukayi alamar bawanda zai iya,

 

tace’ Ka mareta nace ko? Sai na mareka ni tukunna kaji zafi sai Ka mareta?

Ganin shuru yana bata  Mata lokaci  zatayi magana taji  saukar Mari a fuskarta,ai batsan sanda ta dauki hannu ta zabgawa mas’ud wani lafiyyan Mari ba, zafin da yaji yasa Shi Marin Aneesa tare da korfeta ta fada, faduwar ta ma tafi ta Saima tsabar rudewa kasa ihu tayi sai dai hannuna yenata gaba daya data kasa kasagawa, ( taji Maza 😆 )

 

Ameera data fito daukan ruwa ganin abinda ya faru a gaban idanta ba karamin mamaki taji ba,Ashe de kowa Dan iskan kansa sane samu ne kawai basuyi ba,

 

Ummusalma tace’ barganin ya maki wannan abun danawa Yana zuwa a gaba daga ke har yayar ki,ga kayan nan inaga ko ba kutafe bane,  juyowa tayi takara maka masu wata hararan tare da masu kallan uku saura kwata ta wuce su da kallo suka bita har ta Shiga daki kallan kallo sukayi ganin inda ta Shiga,Saima dakyar ta iya tashi ta shiga daki ita kuwa Aneesa sai rarrafe tashiga, dariya sukaji a bayan su hakan yasa suka jiyo wurin kofa ganin bb Yana dariya sosai yasa suka karasa wurin sa,

 

Mas’ud yace’ ya kake dariya haka? Kana gani ta mareni?  Ai baza taci bulus sai na Rama,

 

Binaif yadan tsagaita dariyan sa yace’  me zaka Rama?

 

Marin da mun mana,

 

Killer smile yayi yace’ Wallahi ko a mafarki, sai dai Ka rame,

 

Ya kallesu yace’ sannu da jiki fa, ganin sunyi shiru suna wani kumbura Baki yasa Shi yin wata dariyar,

yace’ Wallahi Dan na manta waya na a mota kuma kar na koma show daya ya wuce,daman da baka mareta Bama ni Zan mareta,

 

Mus’ab yace’nifa banganeba  Naga ta Shiga dakinka?

 

Murmushi yayi yacet zaku gane very soon,

Yafada Yana tafiya,sai kuma ya juyo da Baya Yana tafiya, yace’ bye byee,

Da murmushi a fuskarsa Yana daga masu hannu,

 

Shiru sukayi suka Samu waje suka zauna mus’ab yace’ twinny kamar shati shati nake gani fa?

 

Shafa fuskar sa yayi yace’ai saura kadan Nayi kuka kawai Dan kar ta renani, Amma to meyasa zai Shiga  dakin bacin tana ciki?

Don ya kauda maganar Marin,

 

Mus’ab murmushi yayi yace’ Kai Baka gane ba?

 

Yace’ bangane ba,

 

Duk rashin kunyar taka? Baka gane ba?

 

Kai ni Ka fada min, meye Ka gane din?

 

Dariya yayi yace’ a,ah bazan fada ba tunda baka gane ba sai Ka Bari idan sun fito Suma bayani ni ga tafiya ta,

ya fada Yana tafiya dakinsu,

 

Shifa harga Allah be kawo komai ba,kawia tambayar Shi anan shine taya suka san juna?

 

 

 

Tana Shiga daki ta cire hijabinta, taje gaban wardruppe ta tsaya tana kallan kayanta, Tama Rasa wanne zata sa,Duka kayan nata sai Riga da wando sai skirt  da rigunan bacci ta kwashe dogayen rigunan ta tafi da su, ita kuma  bata so tsaki taja ita kadai gashi yanzu tana san hira dasu,tana so su tattauna abin yarda zai kasance, kuma tana San hutawa kafin ya dawo, duk kayan da ta dauko sai mayar duk kayan da ta dauko sai mayar Basu Mata ba,itakam ta gaji, rike kugu tayi tana kallan kayannata,

 

Da murmushi ya shigo a fuskarsa da daya shigo fuskar nan a murtuke take ga yunaa da gajiya ga hayaniyar da ya tarar gashi ancewa matarsa ta Sunna karuwa a lokacin tunanin yarda zaiyi da su yake Amma ganin abinda ya faru yasa komai tafiya, ganinta ma gabadaya ya mantar dashi komai, ya jima Yana kallanta ganin ta kasa zabar kayan yasa Shi karasawa wajenta,batayi aune ba taji a rungume ta tabaya ya Dora kansa Akan kafarta tare da zagoyo da hannunsa ta cikinta, gaba daya komai Mata tsayawa yayi Tama Rasa mezatayi, tunanin ma ta fara me ya kawota gidan???

Ajiyar zuciya ya sauke yayinda itama ta sauke boyayyiyar ajiyar zuciya,ga gabanta da yake faduwa kadan kadan,

Dukda a boye ta sauke amma yaji, lumshe Ido yayi Yana shakar kamshin turarenta, cikin wata kasalliyar murya saitin kunnanta,

 

yace’ duk missing dinne haka?

 

Itama rufe Ido tayi,Jin muryarsa a cikin kunnenta daman gashi ta gaji sai yasa Mata kasala ta rufe Ido bata san sanda ta jingina dashiba ta rike hannunsa dake cikin nata jinta dayayi da ajikinsa sosai yasa Shi bude nasa Shi idon Yana Kara meta kallo kamar ba ita tagama masifa ba yanzu,Kara maida kansa yayi ya kwantar,  ahankali ya raba hannun sa da nata yakama towel zai kunce don har ya kunce Shi daga inda ta daure a sukwane ta tashi,

.

tace’  mezakayi hakan?

Gabanta Yana dada faduwa,

 

Yace’ abida kike so mana?

Zaro ido tayi tace’ ni? Mena ce ina so?

 

Murmushi yayi ya na Kara kama………

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 16

Advertisement BABI NA SHA SHIDA D’ago fararen idanun ta, tayi tana kallon shi cikin sanyin jiki, a hankali…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 17

Advertisement €pisode 17…………….. Garin Zawatu ya cika dam da mutane . Kowa ka gani yayi kyau sosai cikin…