A BAKIN WAWA 29

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisements

_____

29

 

 

 

Itama fara neman ta tayi Saida babu ita babu dalili ta gajiya tayi,

 

tace’ Ka saya abinda zaka saya mu tafi,

 

Advertisements

_____

Yace’ nagama siyan kayana, muje ki dau ice cream dinki mu tafi,

 

Fitowa sukayi bayan ta dauki ice cream din ya biya kudin, tunda ta fito kafin su karasa wurin motarsu taji ana kallanta daga Baya tsaya tayi ta juyo Amma ba kowa,gaba tayi ta duba namma bataga kowa ba zuwa yayi

yace’ lafiya kuwa?

 

Idanta ya cicciko da hawaye,

tace’ indai da gaske  Neena kake tunanin Ka gani to tabbas itace kuma yanzu ma itace take kallona,idan baza zo inda nake ba nagama nemanta a rayuwa ta har a bada ko naganta Zan nuna ban Santa,

Ta karashe  tare da goge hawayenta ta tafi ta barshi a tsaye, Saida taje wurin motar Yana kallanta sannan shima ya yafi,

Sun dau hanya,

 

tace’ taya Ka gane Neena ce bayan kuma kace bakaga fuskanta ba,

 

Yace’ ina tsaye a wurin cashier wata tazo bazata wuci kiba a tsayi sai dai da Nikaf a fuskarta itama ta tsaya tana jiran a Gama min itama a Mata zoben hannu na ya gani,

tace’ Zoben Ka yayi kyau a’ina Ka siya don Allah,

Advertisement

_____

 

Nace’ ba siya Nayi Bani akayi,

 

Tace’ Zan iya sannin don Allah waya Baka?

 

Kinsan data min tambayar nan sai da ta kalleta?

 

Nace’ meyasa Zan fada maki?

 

Tace’ kawai ina San sanine Naga de zobem kamar na Mata,tunda yawanci irin wannan Yana zuwa da bracelet shiyasa, to bansani ba ko Kai naka yazo iri guda daya ne,

 

Nace’ Bani akayi,kuma itama bata akayi,

 

Budar bakinta sai ca tace’ irin na Ummusalma sak, sannan ta tafi ko gama biyan kudin ma batayi ba, sai da ta tafi wani tunani yazo min, nace’ tabbas itace shine fa na fara duba mai irin kalar hijabinta,

 

Yace’ kuma kinsan Nima nakaina nayi mamakin yarda na zage ina zabga Mata surutu Bana tantama itace,

 

Murmushi Ummusalma tayi,bata ce komai ba ganin sun dawo hanyar gidan Umma yasa,

tace’ lafiya?

 

Yana karya kwana yace’ kinyi mantuwa,

 

Ni babu abinda na manta fa,

 

Idan munje zaki gani ai,

 

Shiru tayi don itakam yau taga ta kanta daman ma bata zo ba, a waje yayi parking, ya zagayo ya bude Mata,

yace’ fito,

 

Tana kumbara Baki ta fito tare da gunguni be kulata ba ya shige suna Shiga parlour suka tarar da Hadaimai suna kallo suna cin abinci Basu fito ba sai da suka tabbatar da sun tafi sannan suka lallaba suka fito, sauran abincin da sukaci suka rage shine suke ci, ko kallan inda suke basuyi ba kamar yarda Suma Basu kalle su ba, sai da suka ce Saima,

tace’ shegiya karuwa mai kama da ifritu,

Sairai Ummusalma taji ta kasancewar itace a Baya shine a gaba, bata tanka Mata Har suka Shiga daki, yaja  ya tsaya

 

tace’ mena manta to?

 

Zama yayi Akan kujera

yace’ a haka zaki tafi? Bata ganki ba sanda kika fito?

 

Tace’ wa?

 

Anty safiya,

Yafada Yana Danna wayar Shi,

 

tace’ to daka dawo Dani mezanyi?

 

Yace’ to shikenan Bari mu tafi idan tagano munyi wani Abu kinga gobe ina zuwa zata Bani ke, Bari mu tafi,

 

Itadai harga Allah bata gane Kan zancen sa ba, to me

Sakayi ganin ya Kai bakin kofa yasa ta bishi har zata bude itama ta fita wani Abu ya fado ranta, ai bashiri ta koma  ta canza kayanta data zo dashi ta fito tana tamke fuska, ta Shiga mota dariya ce cinsa Amma ya Maza yayi murmushi kawai sun fara tafiya,

 

yace’ ai dakin koma da wancan kayan meye laifin su kuma?

 

Banza tayi dashi, Tama kawar da kanta daga gareshi,

yace’ fine, kici gaba kinsan ba ganin ki kikayi a parlourn Anty ba ko?

 

Yana rufe Baki

tace’ Haba Mai gida yanzu menayi? Kawai de maganar ce ban gane ba shiyasa,

Ta karashe da yake a fal fuskarta ita dai burin ta ta ganta a gida,

 

Shiru yayi be Kara magana har suka kusa zuwa, yaji

tace’ Ummu tana cikin damuwa sabida sace su yusseer gobe zasu koma,

 

Wacece hakan?

 

Yarinyar da suka zo gidan ku ranar nan,

 

Yace’ ohh nagene, me dinsu ce?

 

Kawar suce,

 

Waya fada maki halinda ta Shiga,

 

Wanda muke nema,nafada maka daman niece dinshi ce, kuma baya ga haka ma gashi an barsu abubuwa dayawa a school, na zalince su,

 

Bakomai, Insha Allah komai zai daidai,kin ansa numbern Shi?

 

Ehh ya Bani,

 

Saida yaje gidan mai vadi ya bude masu suka Shiga yayi parkin,

yace’ Bani numbern,

Bashi tayi yasa a wayar Shi, sai anan yaga miss called din ta, beyi magana suka fito tare da daukan kayan da ya siyo sukayi part din Anty safiya,

Dukan su suna zaune a parlourn 10:30 babu Wanda yayi bacci har Ummi suna kallan king of heart Ahmad ma yana nan sun kwalalawa tv Ido basa su seen daya ya wuce su idan ba talla aka tafi ba, Da sallama suka shigo amsawa sukayi Amma idansu nakan kallo,

Saida ta  zauna ta kalle su yarda kowa ya kwalalo Ido yana kallan yarda abin zai kasance inda roushini tayi accident Shabnap ta dauko ta Amma ba a Nuno fuskar ba shima Binaif tsayawa yayi daga tsaye Yana kallo kawai ta canza channel zuwa sofiya the first, su Duka juyowa sukayi Nafisa ce ta fara magana,cikin marairaice wa,

 

tace’ Haba Anty  don Allah ki bayar mana ankusa gamawa saura talla biyu agama Dan Allah please kinji ?

 

Anty safiya ta fito tace’ a,a kundawo Amma de yanzu nan don yanzu na tashi naje nayi waya,wai kar in zauna anan basa sun abinda ake fada sunayin missing word,

 

Ummusalma tace’ yanzu nan nadawo Nayi sallama babu Wanda ya amsa shine na canza,

 

Binaif shima zuwa  yayi ya zauna kusa da ita,

yace’ har wani yanzu kika zo ca zaki ce yanzu makazo nida mijina,

 

Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un Sam Baya kunyat fadar wannan kalma ita kuwa nauyi take Mata abakin wai mijinta,

 

Anty safiya girgiza Kai kawai tayi,

tace’ can gidan kikaje ne?

 

Yace’ a,a haduwa mukayi da ita a traffic suna cikin adaidaita sahu ita da kawarta suna Rabin IV shine fa Mata waya suka dawo mota ta nake kaisu shine na kaita gidan su kawar tasu da suka Gama kuma sai yanzu tace nazo na maida ta gida,

 

Anty safiya ta yarda 100% da zance shi,ita kuwa Ummusalma sake Baki tayi tana kallan ikon Allah wannan zubit ma’aruf din ai,mintsinta yayi tare da Mata signal din tadena kallan Shi,

 

Nafisa tace’ dan Allah ki mayar mana muga Wacece, kinji?

 

Shine ya dauki remote din ya makiwa  Nafisa yace’ gashi yi kallan ki, tazo ta takura maku haka akeyi?

 

Ummi da ta kwalala Ido tana kallan cartoon aikuwa tasa kukan baza’a canza ba,

Yace’ lala aikuwa Nafisa sai dai kiyi hakuri baza’a canza ba, mayar da Aljanunan,

 

Nafisa tsabar takaici harda su kwalla,tashi ma tayi ta bar parlourn ta Shiga daki,

 

Anty safiya tace’kin gamu da aiki kuwa na tsani wannan kallan da Baya karewa, Abu a yi tayi de bazai kare ba?

 

Itama Ummusalma tashi tayi ta bar wurin sai anan ya gaida Anty safiya sannan sukayi wata hiran yace gobe da yamma zai zo ya dauketa su fita.

 

 

 

Kwanciyarta Kenan taji wayanta na vibrating daukowa tayi taga Yaya dagawa tayi suka gaisa sannan kowa yayi shiru sai can,

yace’ Kinyi aure ne?

 

Waya fada ma?

 

Shine ya kirani yanzu yana so mu hadu gobe,

 

Ok, ina ummu?

 

Tana Adamawa Nima yau nazo rabon zamu hadu ne,

 

Tun yaushe Kenan?

 

Tun ranar da kika taho daga can,Ranar muma mukaje,

 

Jinjina Kai kawai tayi, kamar Yana ganin ta,

 

Yace’ Saida safe nakirane nafada maki ne daman,

 

Ok shikenan,Saida safe,

 

 

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

 

 

 

 

Kun Shirya Duka kayan naku?

 

Yaseer yace’ mun shirya,Amma oga ina zaka kaimu haka da safe kaga fa 8 ma batayi ba,

 

Oga yace’ Zan canza maku wurin zamane bazai iyuba ace kuna zaune wuri guda ba,

 

Sabida haka ku kwashe kaf kayanku har ps dinku idan kunaso,

 

Yusuf daman beyi magana ba kume beda niyyan yin magana daki kawai ya Shiga ya dauko jakar su wacce suka hada kayan su tun jiya da aka fada masu,

 

Shima yaseer wurin TV yayi ya hada ps din yasata a kwali yasa a cikin Leda ya rike, suka nufo kofar parlour ji sukayi an rufe su masu Ido da bakin Abu, an karbi kayan hannun su, nasuyi musu ba suka bisu ba, ana masu jagora, motar daf take da kofar gidan suna fita aka sasu a cikin sannan suka dauki hanya Basu San ina ake tafiya ba sai da aka bude musu fuska suka gansu a airport an San sa musu fuskar wasu mutene sannan suka fito kowa,harda ticket dinsu suna zuwa basu wani jimaba jirgi ya daga har suka isa inda zasuje su de Ido ne kawai nasu,

 

 

 

Tana kwance kamar kullum yau hoto take gani su uku a ita tsakiya sanda sukayi birthday dinta babu Wanda yazo sai su kadai Anty ma ca tace baza tayi ba shine su suka Kira mai hoto da kudin su ma suka sai cake din lemuka kuma a gida suka kwasa dukan su suna dariya sun goga cake a fuskar su, tayi nisa cikin tunanin ta Inna ta shig, cikin fada,

 

tace’ ke! Fita waje bazan iya ba yau zaki koma gidan Ubanki ina dalili haka?

 

Bata tanka Mata ba don tasan kwanan zancen tagaji da biyota da abinci har daki shikuma Baffa kullum sai yace a kawo Mata shiyasa yau tazo da wannan tijarar harda zagin uba, tashi tayi ko Dan kwali babu ta fita tsakar gidan ta zauna a kusa da Baffa ta fara cin kosan badan Yana Mata dadi ba sai kawai Dan jarabar Inna data lura kullum karowa take, dayan da ta dauka a hannun ta shine bata cinye ba,kamar tana cin magana me da Karen daci haka takejin sa a hankali ko magana ne ma ai zakayi sauri Ka tauna haka take ci, sallama akayi tare da shigowa ko Suma tayi ta farka wannan muryan bazata taba bace Mata ba, daga Kan da zatayi kuwa tayi tozali dasu wani wawan ihu ta daka ta Mike a guje ta rungume su,Suma rungume ta sukayi sai suka saki kuka a tare .(🤧)

 

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

 

Mama ce zaune a parlour tana kallo kamar ma babu abinda ya faru da ita hankalin ta nakan  kallanta, Sameera ta zo tace’ Mama ina kwana?

Da fara’a ta amsa Mata suka gaisa,

Mama tace’ lafiya naganki a shirye haka? Ina zaki kuma?

 

Sameera tace’ a,a mama zani gidan su kawata tun jiya nace maki zani fah,

 

Mama tace’ Sameera Bana San fini fah,ki Rasa yaushe zaki je gidan su kawar sai da wuri haka? Ina laifin ki Bari sai da yamma sai kije,

 

Sameera ta turo Baki gaba tace’ Haba mama tun jiya fa na fada maki zani, kuma na fada Mata ganin nan kinsan daga nan Zan wuce gidan Hajiya Yaya fah datazo ta, kuma yau juma’a kinsan de gidanta yafi dadi da yamma kowa yazo Mata ayi ta hira,

 

Mama tace’ da wannan kuma,to Kide kiyaye Bana San fitina banasan tarkace tarkace damma kuma Naga yarinyar tana zuwa Amma yawon ki ya isheni haka, tam kuma kidawo da wuri bazan Kara Bari Bama kike kwana a wani wurin,

 

Sameera tace’ Insha Allah mama Zan dawo, ke yau bazaki fita ba?

 

Jiya naje babu inda zani, Allah ya kiyaye,

 

Tace’ to mama abani Dan kudi,

 

jeki dauka a daki a cikin jakata ki dau ki dubu daya ta isheki,

 

Komawa tayi tadauka takara yiwa mama sallama ta wuce, tana fita ta kira driver ta fada masa inda zai kaita gidan su kawarta bikinta za’ayi shiyasa zasu fara Shirya abubuwa tun yanzu saura sati biyu ya rage bata wani jimaba ta Kira saurayinta suka tafi shan iska sukayi ta yawon su a gari daga nan suje nan daga karshe sukaje park lokacin har yamma tayi yara kowa sai wasan sa yake,

 

Sai da sukayi mai isar su babu Wanda ya tanka masu har  su Anty da sukaji ihunta daga gidan su Wanda yake Jin na su Inna suka ce baza su koma  ba ana zasu zauna, suma sun zo suna kallan ikon Allah,

Taja hannun su ta zaunar ta Shiga tsakiyar su, Koko da kosan ta kalla,

 

tace’ Inna yanzu fisabilillahi waye ya zubar da wannan abun? Sai kace marar hankali,

 

Takaici da haushi Inna taji takasa Mata magana Baffa

yace’  idan Banda abinki mai sunan manya ai ke kika zubar kece kiyi wannan ta’asar kina ihun ganin yaran Gobe,

 

Sude kallanta kawai suke bako kiftawa  yarda da ta rame tayi duhu, kanta tun kitson da suka Santa dashine shine de babu canji,

 

Anty tace’ ai kece marar hankalin mutum ayi kamar mai aljanu,kunga ki tashi muje kuci abinci kamar nasani yau favourite dinku nayi, Maza ku tashi mu  tafi,

 

Ummu tace’inaa ai mama wallahi Nima sai naje,yunwa nakeji nima,

 

Babu Wanda ya tanka mata suka tashi suka fita har sunje zaure yusuf,

yace’ haka zaki fita?

 

Sosa keya tayi tace’ ku jirani ganin zuwa,kar ku tafi, ja sukayi suka jiranta da gudu ta koma ta dauko hijabin Inna ta sa a zauren ma ta karasa sawa, a parlour suka zauna Anty ta kawo masu abinci Suma daman Basu ciba su Inna ne de masu ci da wuri kuma kullum  Koko da kosai sai kace Ibada, Suma acan favourite din su ake Basu duk wani Abu ana musu, sosai suka zage suka ci abinci har itama Ummun abinda bata taba yi ba Kenan tunda suka tafi sai yau da suka dawo aikuwa tafi kowa haka sai ci take zuba surutu ita da yaseer kamar babu abinda ya faru Baba kawai Jin su yake tare da nazarin yaran lalle akwai laka Mai karfi a tsakanin su, Saida suka ci suka gyatse sannan Anty

tace’ Yusuf ya akayi hakan ta faru?

 

Yusuf ne ya Basu labrin yarda komai ya kasance har zuwan su Adamawa,

 

Yaseer yace’ a airport muka neme Shi Muka Rasa sai mai taxi ne yazo yace ance ya dauke mu ya kaimu wani wurin dayake bamu taba zuwa Adamawa a jirgi ba yasa bamu San ita bace sai da aka kawo mo kofar gidan nan aka ajje mana kayanmu ya bamu kudi yace inji Wanda ya kawo mu yace amu,

 

Anty tace’Yanzu baza ku iya gane shiba?

 

Yusuf yace’ Antu babu wani sauran bincike tunda mun dawo lafiya shikenan ai,

 

Yaseer yace’ kwarai kuwa ai Bama za’ayi ba gaskiya kar ma Abie( Baban Ummu) yasan da wannan zancen,

 

Baba yace’ kamar yafa? A sace ku kuma kuce kar asan da wani zance zancen banza Kai,

 

Ummu tace’ kufa bayin Allahn nan kunfiye gardama,tunda sunce yafe a barshi ai shikenan, agarin bincike nan a wannan Karon na tabbata Ida aka sace su sai dai wasu ba suba nikuwa mutuwa zanyi daman,

 

Kowa kuwa yayi na’am da maganar ta karma aje garin nema gyara akara batawa, ahaka suka ci da hiran su Itadai Anty Ummu ta bata mamaki bana wasa ba ace daga dawowar su har ta ware haka?

Suna nan Basu suka tashi ba Saida suka ji Kiran sallah, Ummu tace’ laaa yau nice wai banyi wanka ba har aka Kira sallah,

 

Anty tace’ kijimu da ‘ya da wanka kike?

 

Yaseer yace’ haba shiyasa tunda nazo naji wani bashi bashi haka Ashe Ashe de,

 

Yusuf yace’ Nima naji Ashe de da walakin gyada a miya,

 

Remote din kusa da ita ta dauka zata wurga masu,

 

Umma tace’ a,a ajje min bazaki lalata min ba kunsa Saba bata na gidan uwarki ajje min,

 

Tura Baki tayi, tace’ daman ni an tsaneni a gidan nan haka kawa suke tsokana ta harda cewa wai da walakin goro a miya,

 

Yusuf yace’ a,a gyada a miya fa nace,

 

Yaseer yace’ yaushe kika gyara kuma?

 

Dariya tayi tace’ ina ruwanku kuma da yaushe na gyara ba fa nasan sa Ido,

 

Baba yace’ ku tashi mu tafi masallaci kar a Shiga muna nan, dukan su tashi sukayi kowa yayi nasa wuri Baba ya nuna masu wani daki suka Shiga, ita kuma ta shiga dakin Anty wanka tashiga tayi ta fito bata da Kaya daman kayan Kala biyu ne Basu San zasu jima haka ba, da sukaje siyo kayan ma ca tace baza ta jeba, babu Wanda yabi ta kanta kuwa sukayi tafiyar su, akwatin Anty ta buda luckily kuwa taga Kaya size dinta harda inner wears dogayen riguna guda uku kowanne da mayafinsu sai atampa guda hudu da takalimi Bama tabi ba’asi ba ta yanke hukunci nata ne, takuwa sa tayi sallah ta fito har lokacin Basu dawo ba kallo takunna ta fara yi yaushe rabon da tayi kallo yau wani shadi takeji ita kanta ta yarda soyayyar su daga Allah ne ahaka suka dawo suka sameta tare da kayan su suka shigo suka Kai daki sannan suka dawo suka zauna,

 

Ummu tace’ ku kunga yarda kuka rame kuwa? Yarda kuka San tsinke haka kukayi,kamar na ture tsinke da Dan tsaya na guda daya haka kuka koma,

 

Yaseer yace’ lalle yarinyar ke Baki ga kanki ba ?

 

Yusuf yace’ kyaleta ita bacin Rama harda Baki,bakin kuwa irin wani shuni shuni takeyi,

 

Wallahi kun rena min hankali ma kunsan de na fiku fari tunda kufa farin Rama kukayi inaga ma ba jini ajikin ku,

 

Shiru sukayi babu Wanda yayi magana sun Rasa meza suce  Mata ne kawai,

yusuf yace’ a kaima Wrestling ko kuma jikin wata ya fada Mata,

 

Gaskiya wani yayi formatting ina aka taba ganin wrestling da Rana tsaka haka?

 

Yaseer yace’ to a canza mana wannan aljanun akai mana Bollywood,

 

Tace’ yawwa wannan kuwa,

 

Bollywood ta Kai sai dai Fan akeyi sukuma su dukan su sun tsani film din aikuwa,

 

tace’ wowww my best film ever,

Harda Dan tsallenta,

 

Yusuf yace’ kinawa Allah ki canza mana kinsan munsan bakya so ko?

 

Tace’ ohh sorry lokacin da aka sace ku shine fa nayi ta kalla Nayi ta kalla shine naji insa Shi ai,

 

Anty da ta shigo tace’ ke wai dan Allah ko kunyar Karya bakya ji ne?

 

Yaseer yace’ yawwa Anty fada Mata de nikuwa kinga ba ruwan ai,

 

Anty tace’ da ban San asalin barbela ba sai na..

 

Ummu ce ta katseta tace’ sai kice daga Ghana tazo ta ko?

 

Dariya yusuf da yaseer sukayi Anty kuwa tashi tayi ta wuce kitchen bazata iya wannan kayan abun haushin ba,

 

Yusuf yace’ kasan yaseer yanayi missing moment din nan dayawa?

 

Yaseer yace’ ai bros ni Zan fada maka,su oo ana so ayi haua proverbs ba’a iya ba,

 

Yusuf yace’ ahakan har littafin su aka suyo aka Hana mu kar mugani,

 

Yaseer yace’ ehh mana kaidai Bari idan ma mutum zai koma English dinshi ya koma Dan yafi masa,

 

Yusuf yace’ sosai ma karma muje a kwafasa mana idan munje wani waje,

 

 

Tana jinsu tayi banza dasu ta mayar da cartoon dinta tacigaba da kallo bata tanka masu ba,tasan zata fanshe ko bakwai ai ana tare, har aka Kira la’asar sunan daga wannan hiran su dauko Wanana har lokacin Baba bedawo ba itama Umma ta tafi gidan su sai rage sai su kadai ne sai Anty, bayan sundawo sannan sukaci abinci,

 

Anty tace’ waya Baki kayan jikinki?

 

Sosai Kai tayi tace’ dauka Nayi Naga kamar nawa shine yasa,

 

Anty tace’ baca kikace bazaki ba?

 

To mama kiyi hakuri kinji,? Ki Bani yanzu na siyo kinga drivers Dina sun dawo,

Ta karashe da dariya a fuskarta,

 

Anty tace’ kudin Bana banza bane bazan bayar ba aje a siyo min kayan shirme kizo ke ba kwalliya ba bakomai ba da tarin ajiya,

 

Haba Mama kayan Amfani Zan siyo fa, idan na hauka na siyo kawai ki bayar kinji my sweetheart mom,

 

Anty tace’ naji Zan Baki,

Tace Yusuf idan ta siyo kayan shirme karka biya kudin Kai zanbawa kuma sai ku siyo abinda Baku da Shi,

 

Tura Baki tayi tace’ haba Anty kibawa Yaseer mana yaza’ayi ki bawa yusuf,

 

Tace’ daga ke har yaseer banga me hankali ba shiyasa,

 

Sun Shaka shiyasa ma Basu tanka ba.

 

 

 

 

✨✨✨✨✨✨✨

 

 

 

 

Su Duka suna zaune a park wurin kujerun hutawa sai table a tsakiyar su ita tana Shan ice cream gefenta Binaif ne sai kujeran dake facing dinsu su uku ne  akai Mus’ab da Mas’ud sai Uncle bayan sun Gama bashi labari da abinda zasuyi shima ya jinjinawa lamarin beyi tunanin abun zai zo cikin sauki ba haka a yanzu da yake Jin ‘yan uwansa a jikin sa damuwar Shi ta raguwa zai iya cewa beda damuwa ko daya a halin yanzu kuma ya yarda ya gamsu Yan uwansa ne koba ma Yan uwansa bane zai karbe su hannu bibbiyo ko matsanan ciyar kamar da suke shida Ummusalma da Mus’ab, sai yanzu yake ganin kamar su sosai da sosai, zai tambayi kuma Bab yaji shaidar wanne asibiti ce aka cince Shi a hannun sa, indai akwai number to akwa shaida, daga nan kuma sukaci gaba da tattauna yarda Abu zai tafi.

 

Ummusalma ce ta hango wata kusa da daga nesa kadan ita da wani saurayi harda su tafawa kuma suna hira suna dariya, kamar ancewa yarinyar ta juyo kuwa, afili Ummusalma ta furta”‘ Sameera???

 

Kallanta sukayi sukace lafiya,

Nuna musu ita tayi,

 

Mas’ud yace’ itace wacce zanyi dating? Naji kince Sameera?

Daga masa Kai tayi,

 

yace’ yanzu wannan abar zanyi dating? Gaskiya bazan iya ba,

 

Tace’ dole kuwa kayi,idan akace mus’ab ne zaiyi to zata kamar da muke dashi,

 

Yace’ to Abu mai sauki kisa mijinki Yayi kawai,

 

Kara tamke fuska tayi,

tace’ Kai nace kuma Kai zakayi nagama magana,

 

Dariya ce ta ciwo Mas’ud,

yace’ ohh jealousy, ko?

 

Mus’ab yace’ to kar tayi? Abinda ake shi akewa kishi ai,

 

Murmushi kawai uncle yayi wannan yara bade surutu ba Shi haka yake beda magana sosai Ummu ce ma take sa Shi magana,

 

Shima binaif murmushi kawai yayi, na irin ana kishi nan nawa,

 

Ummusalma tace’ Chatty ina so kadawo da Sameera yarda take a da,nasan hakkina ne zai bisu Akan ‘yar su Amma ni Bana so ina ganin Sameera tamkar su yusseer ne,ina kaunar Sameera kamar yarda nake kaunar su bana San wani Abu ya faru da ita, a yanzu tana zuwa duk wani night event tana zuwa duk wani party koba ba a garin nan ba, Bana so ta fara kwana a waje idan ba gida ba,dukda wani lokacin tana kwana a gidan su kawayenta wani lokacin kuma a gida take kwana to Bana San tafara kwana a wani wurin, gwara komai ya   tsaya daga haka, help me please,

 

Gaba dayansu kallan ga suke what’s kind of heart she’s have,she have a pure heart, kallansa ya Kai wurin Sameera yaga yanzu ma a wuri daya suke dayake a nesa yake bega wani gap dake tsakanin suba,

Rufe Ido  yayi ya jingina zuciyar sa bugawa take be taba zuwa yacewa wata Yana Santa Bata duk iskancinsa Akan Maza yake karewa koda kwa tsokana ce da hausa lokacin Yana Spain sanda suke karatu,

 

Tace’ ka dauke Sameera kasa sunana Ka dauke kammar ta kasa kamata Ka dauki matsayin nice ita, zaka so ka ganni ahaka? Ko kuma zaka so kaga ina yawon zuwa club,party gari da gari? Zuwa night dinner? Zaka so na kwana a wani wurin koda kuwa gidan wasune ba namu ba?

Yanzu kayi imaging nice waccar a zaune ya zakaji? Please Ka taimaka Mata badanni ba Dan Allah zakayi baya ga haka zata taimaka mana sosai idan ta kware maka zata taimaka mana sannin yau Yana ina,gobe Yana ina,jibi Ina zaije?

 

Tace’ nasan cewan it is not always easy to gather the courage to speak to a woman. But chances to make a good impression are often limited,so saying the right thing from first moment is important. I want you yanzu kaje kayi Mata magana tuna Allah yasa mum hadu kaji? Please,

 

A hankali ya bude idonsa da yayi ja, ji yayi bazai iya barinta ba kamr yarda tace yayi imaging itace hakan yayi, kallan mus’ab yayi mus’ab ya daga masa kai ya kalli uncle,

 

Uncle yace’ babu abinda yafi karfin Dan Adam sai Wanda yace bazai iya ba I want to you to put it on your mind cewan u can do it,u can do it, u can don’t ever Star saying u can’t I know u can, Ummusalma my daughter ko bata iya Abu ba tana gwadawa, Ummusalma  kanwata kuwa she’s heroine,bare kuma Kai Namiji,

 

Kallan Binaif yayi,wani murmushi yayi masa, yace’ bansan me wannan me wannan chatty din ba yake so nace, me zance,

Shiru yayi alamar tunanin, yace’  bb naganni nan ko? Umm wallahi Zan iya komai amma kaga fav bro babu abinda zai iya ya cika tsorom tsiya kamar farar kura,

Murmushi yayi sosai yace’ is now a time that u will show me u can do it, shine kuma Zan yarda oya move on,

 

Numfashi ya ajje ya tattaro duk maganar su, sannan,

yace’ me zanje nace Mata yanzu?

 

Gaba dayansu Ido suka zuba Mata,

tace’ a,a lafiya kufa ya tambaya kune maza yaza’ayi ki zuba min Ido,?

 

Mus’ab yace’ ai tunda kikaga haka to babu Wanda ya taba zuwa wurin budurwa,

 

Tace’ ni ai na taba zuwa wurin saurayi,

Da zakuce min wani Abu,

 

Binaif yace’ kifada komai b, yanzu de me zaice,

 

Tace’ kaje kawai,

 

Yace’ naje na masu me wai? Nace me? Nace’ mai da yaji kome,

 

Tace’ idan kaje kayi musu sallama kar kad hi ko Hello Ka kagane?

 

Yace’ sosai ma sai me kuma,

 

Sai Mika masa hannun ku gaisa, Ka nuna Ka Santa a wani wurin haka,

 

Yace’ gaskiya bangane wannan ba, a,ina nasanta?

 

Daure fuskayi tace’ gaskiya Kai kana da matsala wallahi ahaka Zan koya ma ?

 

Uncle yace’ idan fada zakuyi bazaku tsaya yi abinda ya kamata lokaci fa jiran ku zaiyi ba,munan za’ayi magriba su tashi muma mu tashi,

 

Yace’ to ai itace  bani ba,

 

Tace’ Kaine de,

 

Mus’ab yace’ kunga wannan haka suke basa jituwa,

 

Tace’ kaje kuma karyi masu surutu Ka ja ajinka,Banda rawar Kai da kafa,Ka zauna a kusa da ita kaji ai? Sannan kace Ka santa Ka taba ganin ta a Kaduna da taje partyn wani saurayin ta,

 

Samarin mata Har nawa e haka?

 

Kai zaka Nemo wannan kuma, yanzu tashi Ka tafi,

 

Tashi yayi a hankali Yana tafiya yana juyowa Yana kallansu kamar yarda suke kallanshi sai ya tafi sai ya dawo sai ya tafi dawo idan zai dawo harda gudu yake hadawa a na karshe ne yadawo ya,

 

tace’ danzo na fada maka wani Abu,

 

Zuwa yayi harda su sunkuya daidai kunnasa, kunnan ta kama,

 

tace’ karka manta wallahi,taam,

Ta dauki lemo ta Mika masa tace’ ungo wannan Ka rike a hannun Ka kar Ka dawo har sai sun lura ma damu,

Karba yayi yayi gaba sai da yakusa zuwaya juyo alamar zai dawo ai gaba dayansu rufdugu suka masa na Harare ba shiri ya juya ya bude lemon sa yaje wurin, zuciyar sa bugawa take shidai besan ya zaice,yama Mata abinda tace masa yace sallamar kadai ya rike,

 

Cikin wata irin voice mai cike da sanyi da fargaba sai dai bazaka ce yana cikin fargaba ba,

 

yace’ Assalamu Alaikum……..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 25

Advertisements _____ BABI NA ASHIRIN DA BIYAR Sosai Innayoh ta tura aka gyara daya daga cikin yan matan,…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 20

Advertisements _____ 20 Tana kwance a dakinta ta fara jiyo hayaniya tun daga waje,bata yi yunkunrin tashi ba…