A BAKIN WAWA 30

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisement

30

 

Dagowa sukayi suka kalle Shi Dan murmushi yayi Wanda iya fatar bakin ya tsaya beje ko ina sannan ya samu wuri ya zauna ya Dan kurbi lemu, gaban Shi faduwa kawai yake,

yace’ sannu fa,

Namijin yace’ Hi,

Karar wayar Shi yaji yasa Shi daga wa ganin ita ce,

Tace’ banga kana wani abuba sai San lemu Allah zamu tafi mu barka,

Adan wayince ya juyo ya kallesu,ya juyar da kansa,

yace’ sannu fah,

Namijin yace’ ina de lafiya?

Advertisements

Sameera tace’ Kawai kazo Ka samu a gaba?

Tace’ baeb mu tafi abimmu,

tashi sukayi zasu tafi Yana rike da hannunta ta gaban Shi suka zo zasu wuce mesan what comes his mind ba yade ba daga zuciyar Shi shawarar ta fito sai gani yayi ya rike hannunta, juyowa tayi ta kalle shi,

tace’ wai Kai lafiya?

Namma shiru yayi Shi kawai hannunsa yake kallo da ya rike Yama kasa magana,dakyar ya samu kalma biyu,

yace’ yi hakuri,

Cikin fasifa tace’ sake min hannu ko na zabga maka Mari a nan wurin mu jawo ‘yan kallo,

Sakinta yayi
yace’ am daman a wannan Kaduna,

Wayarsa dake hannunsa tayi kara message ne ya shigo kafin ya dago ya gansu sun gifta Shi, binsu yayi Yana Kara Karanta abinda ke ciki, ta kusanta ya je,

yace’ am daman fa a Kaduna na sanki,nazaci wacce nasani ce shiyasa ma har na rike Mata hannu,kiyi hakuri fah,

Namjin yace’ Kai tafi a anan wurin ba ita bace,

Besaurare Shi ba don beda abinda zai fada masa, shiyasa yayi shiru sai,,
yace’ kiyi magana mana koba Sameera bace?

Advertisements

Ja tayi ta tsaya tabbas kuwa ya Santa Amma ita batasan Shi ba ai, shima tsayawa yayi ya Dan kalli wayarsa,

yace’ Nasan kece wacce nasani ai, bazaki tuna ni ba ai, Amma ni nasanki,

Namijin yace’kar ki Rena min wayo mana, Sarai kin San Shi Ashe daman bani daya kike kulawa ba ko?

Message yaga ya shigo wayarsa,
yace’ ni zan tafi sai wataran Kenan?
Bejira amsar ta ba yayi gaba ina ruwan Shi abinda aka sashi yayi besan cewa fada tasa Shi hadawa ba,

Sameera tace’ aww daman kana tunanin Kai daya nake kulawa? Nasan cewan kana da ‘yam Mata kalata sunkai goma ko fiye dahaka bakai daya bane,

Yace’ Naji karki Kara kulani tunda ke mayaudariya ce kuma zaki sane kinyi Dani,

Tace’ nasaba Jin Kalmar nan a bakin mutane da yawa,wato ga banza ko? Kai kuma mene? Har gwara ni Bana lalata da samari Kai fa? Meye bakayi ? Waye besan halin Kaba? Kowa ya kama rabansa medame ni ba, banza kawai shasha,
Tasa Kai tayi gaba abinta,shikuwa Yana tsaye kamar gunki tunda yake da mace sai dai ya gama amfani da ita ya yar a bola bolarma wacce za’a Kona bazata anfanu ba, Amma wannan babu abinda yayi da ita niyyar Shi yau yayi duk abinda yi da it gashi yanzu komai ya wargaje beje ga komai ba, beyi tunanin ma bata sanshi haka ba,tunda suke bata taba daga masa murya ba sai yau, shima tafiya yayi ya bar wurin,

Yana zuwa ya samu waje ya zauna Yana sauke ajiyar zuciya nishi kawai yake Kai kace yayi gudun tsere ne, a zaton Shi zasu haushi da fada shiyasa ma ya kulle idan sa, so bega abinda yake faruwa ba a tsakanin su,sai da suka tafi Ummusalma tace’ ya kamata a Nemo wannan mutumin bazai barta haka ba,

Uncle yace’ to amasa me kuma? Bacin kina gani de da’alama sun rabo,

Tace’ ehh da’alama ba? Amma Shi bazai kyaleta ba ai, idan Ka lura sanda ta tafi kamata yayi acd shima ya tafi amma sai ya tsaya yayi wani Dan tunanin kadan, ayarda suke fadan zaka San beji dadi ba Ka gane?

Yace’ na fahimta,

Kallan mas’ud tayi tace’ Chatty kafa Kayi kokari fa sosai da sosai Allah ya Kara jarumta,

Ba shiri ya bude ido yace’ Kai haba da gaske? Kice nazama expert Kenan ho ni ho hoho, na bar wani a Baya first time in history nayiwa mace magana Bama maganar komai ba maganar soyayya na bar wani wallahi,

Mus’ab yace’ ji banza waka Bari din? Ai ni de kasan Zan iya wallahi,

Ummusalma tace’ meye maganar soyayyar tukunna ma wai? Kana nufin wannan abun daka fada Mata shine love din?

Dariya suka sa masa,shikuwa kumbura Baki yayi, dayake mus’ab ne marenin wayan sa shi ya tashi zai buga aikuwa suka fara gudu wannan yayi ta nan Wannan yayi tannan,
Murmushi fal fuskar uncle bazai iya fassara yarda yajiba Amma kuma dadi yaji meyasa aka raba su? Kwalla yaji zata fito daga idansa bema sani ba sai Jin hannu yayi Ya share masa kwallar hannun yabi da kallo yaga Binaif Yana masa murmushi,

yace’ kayi hakuri kowanne bawa da irin tasa kaddaran ku taku sai tazo da sauki Allah yasa kun hado,amma ni tawa,
Murmushi yayi Mai ciwo,
yace’ har yau banyi wani Abu ba,Bm Akan neman mahaifiya taba ( a lokacin da aka bada labarin uncle Yana cikin damuwar labarin da aka bashi to besan sunyi zancen ba kawai jinsu yake bazai ce ga me aka fada ba),

Uncle yace’ kayi hakuri komai zai wuce kaji ko?

Murmushi kawai Binaif yayi bece komai ba beda abinda zaice shiyasa ya zabi da yayi shiru,
yace’ kalle su Ka gani?

Kallan su yakai wurin da suke guje guje har Ummusalma suna dariya kamar wasu yara tun sunayi su kadai har suka gayyato yaran wurin Suma suka fara dole wai sai Mas’ud ya kama su ya nada sai kace wani ubansu, sukuma sunki shine yara ma akazo,

Binaif yace’ Shekaru hudu Baya da muka hadu da su bata magana bare tayi dariya, bacin na taba ganinta tana yin hakan,

Uncle yace’ ni Zan fada maka,ko presentation ne fah batayi ance min kurma ce shiyasa sai na bata assignment a maimakon shi,Ashe ba kurma bace tsantsan rashin son magana ne,

Murmushi binaif yayi yace’ Ina San farin cikinta ina san ta kasance cikin farin ciki a koda yaushe bansan bacin ranta, bansan tayi ta tunani idan ta zauna ita daya,

Uncle yace’ idan haka ne why not ku zauna tare dasu?

Binaif yace’ wannan daman shine ra’ayi tun kafin nasan Zan yi aure, ko Dan suji suna rayuwa cikin ‘yan ci, suji suna rayuwa acikin gidan su,tunda suka taso suke fuskantar matsala, tafiyar su Spain ya Dan lafa suna dawowa komai ya cigaba, daga karshe suka dawo gidan Kakar mu ananne suka Samu freedom bayan an koresu daga can gida,

Murmushi kawai uncle yayi Yana cigaba da kallan su,
Wani Abu ya fito da Shi a cikin Dan box box din ja ce mai ba’a kuma ganin abinda yake ciki, ya mikawa Binaif

yace’ wannan abun shine abinda aka gani acikin towel din da aka yar Dani bayan sun duba sun gani Ka rike Ka hada Shi da takardun wajenka, maybe zaiyi amfani gaba,

Meyasa Kai bazaka rike ba?

Inaji kamar wani Abu zai faru,kamar wani Abu zai sameni, godiya ta ga Allah dayace dayasa na ga ‘yan uwana da yasa nasan gaskiyar komai, Ka rike Shi a wurinka abun Yana da mukulli amma babu key din haka suka ga abun, ko ya fadine Basu sani ba, box Mai kyau gashi karami kamar na zobe na zobe ma yafi girma karba yayi yasa a aljihu bekara magana ba daga nan, suka zuba musu Ido suna kallan su. Waya akayiwa ganin Baba yasa Shi dagawa,

yace’ Baba an wuni lafiya,

Daga can ummu tawaikwayi muryan Baba irin shine din nan,
tace’ Lafiya qalau yarona,

Yace’ ummu ranki zai baci, fa

Tace’ Uncle saban labari su besties sun dawo fah tunda safe sai ga su sunzo Amma fa Wanda yasa ce su ne ya kawo su sannan kuma Ance kar Abie yaji donmma Kar yayi wani bincike kasan halin Abie da Dan Karan bin kwawwafi daga karshe de yaushe zaka dawo, Amma idan zaka tafi can London tana nan zaka wuce sannan kuma Kai daya zaka koma Allah sarki My Uncle,

Yace’ kekam Ummu bazaki canza ba ko? Daga dawowar su har kindawo normal,yanzu bakin Anty zai fara ciwo,

Laaa kaga ni bazan iya Bama kwasar su zanyi inkai su gidan Hajja yalwa itace babu ruwanta ko fada bata maka idan kayi lefi sai dai

tace’ yanzu Kaine kayi kaza kayi kaza to kar ka kuma Zan Zane Ka idan kayi,
Cikin sanyi take maganar shiyasa itama tayi magana yarda takeyi,

Murmushi yayi yace’ hmmm ba ruwan keda Umma idan taji ki,

Yaushe zaka dawo de,

Gobe Insha Allah zuwa rana haka? Zan dawo

Tace’ Haba de Rana ai yayi nisa dayawa ina laifin zuwa safe haka kayi break fast anan dakaina Zan girka maka abinda kake so,

Shikenan Zan duba nagani,idan nazo akwai labari dayawa,

Kai Amma naji dadi sosai sai kazo idan Ka zo kamin waya da wannan wayar Baban, Amma kace ni kake nema Kar Ka Kira Shi ku fara gaisawa kaji ai?

Numfashi yaja yace’ Naji second mom din na,
Sannan sukayi sallama murmushi fal fuskar Shi,

Ummusalma ce tazo ta zauna tace’ nagaji dayawa,nayi gudu, tana sauke numfashi,

Mus’ab ma zuwa yayi ya zauna shima, mas’ud kuwa wasan sa yayi tayi da yaran sai da Iyayen su suka zo suka dauke su sannan shima ya dawo yana Nishi,

Binaif yace’ ku tashi mu tafi gida magariba ta gabato,

Mas’ud yace’ sai da kukaga nazo Zan hutar sannan za’ace a tashi a tafi gida?
Wannan in justice ne, daman nasani ba’a Sona ku Duka kuwa,

Babu Wanda ya kula Shi Dan sun San halin sai uncle shikadai ne ya masa magana sannan ya tashi, sai da sukaje inda sukayi parking Binaif ya juyo ya kalle su,

yace’ kubi bros ku tafi baza’a takura min ba, a tafiya na rage hanya a komawa kuma bazan rage ba,

Kallan juna sukayi sukace’ mekenan?

Ummusalma kuwa bata ma San me yace ba Dan har ya Shiga mota abinta shima shigowa yayi ya kyalesu suna sun hangame baki,

Tace’ yanaga Baka shigo da suba?

Yace’ kyalesu sun fiye sa Ido ganawa zanyi da mi precioso,

Shiru tayi ta kyale shi bata San mezata ce ba,
yace’ Kinyi shiru lafiya?

Tace’ uhm

Uhm kadai?

Wasa wasa fah Surutu dakai

Ohh really?

Shiru tayi bata Kara magana ba, itama ta kyale shi kawai,
Har suka zo gida babu maganar arziki a tattare da su.

 

๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

 

Sai da ya sauka a airport ya Kira numbern Baba Yana Kira tana dagawa

yace’ gani fah nazo nama kusa zuwa gida kinji ?

Tace’ Amma ai da nazo na daukeka,

Karki damu nama kusa gani nan,

To shikenan sai Ka Kara so, Allah ya kawo Ka lafiya,
Ta kashe wayar tace’ Baba wai har yazo,ina so yaga besties dina sun dawo lafiya sai dai sun rame fah,
Baba yace’ hmmm ke bakya gajiya da magana,

Dukansu suna parlourn sunsa abinci a gaba Shi kawai ake jira yazo yaci,ummu ce tayi abincin kuma ta hana kowa ci Baba kuwa ya biye Mata sai yazo din, hira sukeyi mai cike da annashwa babu wata damuwa a wurin su,

Wayar Baba aka Kira ganin sunan Uncle yasa Shi dagawa, beyi magana ba daga can akayi magana,

yace’ Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un, wanne asibiti aka kaisu?
AAA hospital, ne asibitin Shine,
Yace’ gani nan zuwa kuwa yanzu nan, ya kashe wayar,

Dukan su Ido suka zuba masa,suna San Jin ba’asi,
Yace’ wai Abokina ne yayi accident Wanda zai so muyi magana dashi yanzu Yana asibiti, Zan Kira yarona sai ya wuce mu hadu acan din,kun gane?

Umma tace’ Allah ya kiyaye,
Yana sauri ma be amsa addu’ahr ba, sai dai duk jikin su yayi sanyi qalau a haka suka ci abincin su tunda ba zai zo ba asibiti zai wuce…

 

๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

Sameera ce a zaune a parlour tana kallo babu abinda take tunawa sai abinda ya faru jiya waye Shi? Duk iya tunanin ta takasa samu waye Shi kaf samarinta idan ta hada babu mai kamar shi, bata taba yin mai kalar Saba ma, ya zatayi? Gashi ko sunansa be fada ba, tana zuwa Kaduna suna party amma takasa Nemo Shi, ajiyar zuciya ta sauke,ga kuma wannan yace zata gani mezata gani? Anya ba tarko aka Dana Mata ba kuwa? An rabata da saurayinta daman de bawani San Shi take ba, tanda Wanda take so tana ganin shine daidai da rayuwar ta, shine Wanda zata tsayar a mijin aure nan gaba, ga kuma ya zo, ya zatayi yanzu?

Mamace ta fito da tun daki take kwala Mata Kira Amma a banza tajiba sai da ta fito ta daka Mata tsawa Sannan ta dawo hayyacinta,

Mama tace’ me kike da ina kiranki Baki ba ?

Allah ya taimaketa American film din da ake mai fada ne shiyasa,

Tace’ mama kallo nake, banjiba ne yi hakuri,

Kallo ta watsa Mata tace’ wuce kije ki gyara dakinki da nawa ki wanke toilet tas jiya bakiyi ba yau kuma dole kiyi wuce, banasan kazanta a jima kuma kizo ki daura abinci,

Batayi magana ba ta wuce ita dai kawai a kyaleta tayi tuna Wannan bawan Allahn, sai data Gama tas ta sauko ta daura abinci lokacin 11 da ‘yan mintuna ta daura abinci ta kafin daya ta gama abinda ta girka ta jera a dining, sannan tayi wanka ta kwanta wayarta taji tana Kara dauka tayi ganin number yasa ta ajjewa bata daga ba, sai da akayi four miss called ana biyar din ta daga kuma tayi shiru, daga can,

yace’ Assalamu Alaikum,

Tace’ Hello?

Bakya amsa sallama?

Bada muwar Ka bace,

Nasani sosai Amma kuma ai zaki samu lada, ko bakya so?

Shiru tayi bata tanka masa ba,
Yace’ Baki San Hadithin manzan Allah SAW ba? Dayake cewa a bazaku Shiga Aljnnaba har sai kunyi Imani baza kuyi Imani ba har sai kunso junan ku,
Yake cewa shin bazan fada maku wani Abu ba? Idan kuka aika tashi zaku so junanku, sannan yace…

Ta katse Shi da cewa’ Afshus salama bainkhum, kaga nasan wannan sai me kuma? Mema ya kawo wannan? Kawai Dan ban amsa ba? Ina ruwank Dani?

Yace’ subhanallah ba kawai bane kinyi hasara babba samun lada fah idan kikayi ko kika amsa, meyasa zaki ce haka? Gashi kince kinsani, tunda kinsani sai kike aikatawa kinji?

Wai Kai Dan Allah waye kazo Ka takura min me kake Dani ne wai?

Yace’ am sorry bansan Zan takura maki ba ai, da kin amsa min sallama ta da duk haka bata faru ba, abinda nake so dake shine kiyi hankali da duniya, duniya makaranta ce.
Ki huta lafiya,

Ya kashe wayar bin wayar tayi da kallo tana tunanin waye Wannan din? Ya ilahi.

 

๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

A asibiti kuwa Har yamma Baba be dawo ba shida uncle sai yanzu da ya Kira su yace’ su kawo abinci su Dukan su suzo su duba Shi su koma, hakan kwa akayi Yusuf ne ya jawo su Umma na nuna masa hanya har suka iso asibitin, sude jikin su yayi sanyi tun wayar dasuke Kira ba’a daga wa sai da Baba ya kirasu, suna zuwa yazo ya masu jagora suka fito da kulan abinci suka nufa dakin marar lafiyar Dayake Baba ne a gaba sai ya tsaya a bakin kofar yace’ Banda kuka,Banda kuka,Banda kuka, duk Wanda ya min kuka zai koma,

Yusuf yace’ Baba ina Yaya banganshi ba yana ina ? Ko ya fita?

Baba yace’ Yana ciki, ku shigo,

Umma ce a gaba sai Anty Ummu da Yusuf a tare suka Shiga yaseer ne na karshe, gaba kidayansu saranda sukayi suna kallan shi kamewa sukayi suka dena aiki jininsu yadena zagayawa kwakwalwar su ta dena motsi zuciyar su ta tsaya komai Ido yadena kiftawa kunne yadena ji kaface kawai ta tsayar dasu tamkar statue haka suka tsaya cak sakamakon ganin Abdullah Abdullah a kwance babu mara barshi da gawa oxygen a bakinsa badan zuciyar Shi da suka ga tana harbawa ba tsab zasuce beda Rai,ga karaya a kafa Duka biyun da hannu guda daya, Duka kansu babu Wanda yadawo dai dai Saida sukaji kukan yaseer sannan Suma suka dawo sai kuma sukayi kansa ganin zuciyar sa tana nema ta tafi zero ga wani tari da yakeyi ji sukuyi abin Yana ‘DI’DI ‘DI’DI alamar ya tafi zero,

Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un…….๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ uncle ๐Ÿคง๐Ÿ˜ญ

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 18

Advertisement โ‚ฌpisode 18…………….. Bayan wata ษ—aya . Tun daga Ranar da Naheela ta karษ“i mulkin Garin Zawatu wani…