A BAKIN WAWA 31

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisement

31

Da wani irin sauri Daddy ya Danna alarm sai ga doctors sun zo, fitar da su akayi waje suka hau kansa, a waje kuwa Yaseer ne kadai mai kuka Banda Shi babu wani mai yin kuka a cikin su, sunana har akayi magriba shiru akayi Isha,sun dawo daga sallahn Isha sun zaci sun fito Amma suka jo shiru sai anan Ummu ta fara kuka gani ma take duk laifin ta ne ita tace masa yazo da safe da duk hakan bata faru ba, tama da cewan indai Allah ya kaddaro Abu babu Wanda ya isa ya kawar dashi, Basu suka fito ba sai Karfe 10 na dare da wasu mintuna sannan suka fito Baba dayake matsayin sa na likita shima kansa fitowa yayi bazai iya yiwa dansa komai ba, Dade ace ma Zainab ce zai iya Basu wani shaku da ita ba kamar yarda ya shaku dashi, Baba da Umma sai Anty su kadai ne sukaje wurin likitan Yaseer da har yanzu kuka kawai yake Bama ya iya magana bare ya tashi yaje yaji ba’asi Ummu da Yusuf kuma basa san suji abinda kunnansu Baya son ji, ga kuma doctors din Basu fito da fara’a ba,
Office sukaje na likitan,
yace’ sai dai kuyi hakuri yaran ku Yana cikin wani hali numfashin sa na barazanar daukewa sannan kuma Yana inner bleeding, sakamakon bugun da zuciyar sa tayi Allah yasa bata fashe ba, sai kuma kansa dashi ma ya bugu yanzu de anyi masa aiki, sosai fatan mu daya Allah yasa kar ya Shiga comma idan kuwa ya Kai kwana daya zuwa biyu be tashi ba zamu karayi masa wani aikin, muga yarda Allah zai kaddara Allah ya sauwake, numfashi Baba yaja wannan al’amari da yafaru sai kace a mafarki? Ikon Allah Kenan, fitowa sukayi babu Wanda ya iya magana, Baba ya kalli su Ummu da yaseer da suke kuka ya kuma kalli Yusuf da ya zabga uban tagumi,

Baba yace’ kudena kuka kudena duk wani tunani haka Allah yake ikon sa, ki maida komai ba komai ba, mu godewa Allah da be mutuba da sauran ransa a gaba kuma muna fata Allah zai bashi lafiya yanzu da kuke kukan nan kunyi masa addu’ah ko sau daya ne?

Girgiza Kai sukayi, yace’ to kungani? Amma kun zauna kuna kukan da beda amfani ko kadan,yanzu da mutuwar yayi haka zakuyi ta kuka? Shine zai nuna kuna San Shi? Zaiyi alfahari ne daku? Bazaiyi ba, ku maida komai ba komai ba, ku dauki matsayin yayi tafiya mai nisa,tafiyan da bai Fadi ranar dawowar saba, kude na tunanin wai Yana kwancen a asibiti, kunji ko? Hakan da zakuyi shine zai nuna kuna kaunar sa kuci gaba da walwalar ku mutuwa ma bata Hana komai bare kuma jinya, duk Wanda na Kara gani yayi koda tunani to zuwa dashi ma bazan karayi ba,yanzu ku tashi mu koma gida,

Jiki kowa a sabule babu kwari haka suka mike sai dai anyi nasaran da Yaseer ya dena kuka haka ma ummu sai dai sunyi shiru ne kawai, walid Baba ya Kira yazo ya tafi da wasu shima ya dau wasu koda sukaje gida sai da Baba ya Kara masu nisiha sosai sannan suka da ware harda suncin abinci Basu suka kwanta har shabiyu suna nan suna jimamami Amma a zahiri kallo suke, a parlour yusseer da Ummi suka kwana batare da sun Sani ba, washegari Banda su aka koma Shiyasa suka ware suke abubuwan su, ahaka sai da akayi kwana biyu bai tashi ba, zasu sake wani aikin Baba yace a barshi zasu koma dashi London acan za’a cigaba, aikuwa haka akayi ya nemi visa da komai ranar Wednesday zasu daga zuwa Londo sukuma su Ummu su dawo gida don makarantar su, ranar da zasu tafi jirgi daya suka hau,don su Baba a Abuja zasu tashi,sukuma sai sunje Abuja zasu wuce Kano,

Suna zuwa suka zarce gidan Anty, sai da suka taya ta aikim gida tsab komai da komai suka huta sannan suka wuce nasu gidan, fargaban Shiga suke Basu San bezao faru ba kuma, lokacin da safe sukazo Amma Basu fito ba sai da yamma a hankali suka tura kofar gate din suka Shiga babu kowa a harabar gidan suka sa Kai suka Shiga ciki, Sameera ce a parlour tana waya da Wanda bata sani ba Wanda tasa Maza preacher mutane ta gani kamar su yusseer mantawa ma tayi tana waya

tace’ Wa….w…a.na..ke…ga…ni?
Mama ta kwalla Kiran mama,
Mama ki fito wallahi Mama ki fito da sauri Mama!!!! Ta Kara kwalla Mata Kira,

Fitowa mama tayi tace’ ke banasan shirmen banza da hofi ba,meye kike wani kwal…..
Wanda tagani ne yasata saurin karasowa tace’ yu…u ..yu..yu. Si..f,

Yusuf yace’ wai ca aka ce maku mun mutune ko yaya?

Yaseer yace’ mundawo baza’a yi welcoming namu ba,

Advertisements

Mama tace’ kune? Baku mutuba? ‘ya’yanah kun dawo gareni?

Sameera tace’ kamar ya? Baku mutuba wai daman?

Yusuf yace’ Wanda ya mutu idan Yana dawowa to mun dawo,

Yafada tare da zuwa ya zauna shima yaseer zuwa yayi ya zauma,

Mama tace’ ku fada mana ya akayi haka?

Yaseer ne ya Basu labarin komai,

Sunyi jimami bakadan ba,
Mama tace’ dakunje gidan su Ummu yarinyar nan ta damu,Tama fini Shiga damuwa,

Yusuf yace’ munje ai,Basu jima da dawowa ba daga Adamawa uncle dinta ne yayi accident ya Shiga ana zaton ko ya Shiga comma ne ba’a sani ba shine aka tafi dashi London shine yau suka dawo,

Mama tace’ subhanallahi dole naje gaskiya Nayi musu jajaje wannan Abu har ina haka? Allah ya kiyaye Amma ni bamma San shi ba gaskiya,

Yaseer yace’ mama idan kika ganshi kamar su daya da ya……

Yusuf yace’ yaya sameera, yarda kuka ganta haka take,sai dai Shi Baki ne ita kuma fara ce,
Yusuf ya aikawa da Yaseer wata uwar hararan Baka da hankali shima ganewan da yayi me yasa Shi wayem cewa ( yaseer akwai gane Abu πŸ˜†)

Yace’ wallahi Mama Nima da ganshi fa nashiga comfuse sosai,

Advertisements

Yusuf yace’ dalla yimin shiru babu wani kama suke ba,ni karya ce Bana so,

Sameera tace’kuma kace muna kama? Shi baki,nikuma fara,

Yusuf yace’ a cewar yaseer ba? Haka yake cewa kuma nasan hakan zaice,

Mama sai nan nan take da su haka itama Sameera dukda babu shakuwa a tsakanin su Amma a kwai respect da fahimtar juna, koda Abba ya dawo shima yayi mamaki wannan lamarin.

 

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

 

Da gudu ya fito daga dakinsu Yana
cewa’ bb bb fav kuna ina, basa Parlour hakan yasa ya wuce daki namma basa nan sai kawai ya fito waje suna wurin Shan iska da gudu ya karasa

yace’ bros yayi accident wallahi yayi accident Allah shiyasa Bama samun sa, shikenan,
Sai kuka ya rungume bb da suka tashi tsaye tun kafin ma ya karaso Jin Kiran su da yake, shima Binaif din rungume shi yayi

yace’ cool dawn, fada min taya kasani,

Yana shashshekar kuka
yace’ muna waya da Sameera sai suka dawo kuma bankashe wayar ba lokacin ina typing Abu a system to a speaker nasata shiyasa ban kashe ba, naci gaba dajin zancenta, har na fara Jin zancen su anan naji abinda yake faruwa,

Sai ya Kara fashewa da kuka, shima Mus’ab kukan ya farayi ya rungume bb shima bbn rungume su yayi,Suma sunyi kika ina ga Ummusalma kuma? Ajiyar zuciya ya sauke yaja su ya Kai lilon ya zaunar su shikuma ya tsaya,

Yace’ baza ku iya Kula da ita bakena ko?
Shiru yayi sannan yaci Gaba,
yace’ kunsan me kukeyi kuwa? Kuka fa kuke? Ko Baku sani ba? Ehh?
Iska ya furzar yace’ kun fita shekaru ina ganin zaku fita hankali da tawakkali Ashe nayi kuskuran fahimta, yanzu idan nace kuje ku fada Mata mezatayin tunanin ya faru idan kukaje kuna kuka? Tunani zatayi mutuwa akayi, shine abu na farko da zata kawo aranta,kuka beda amfani, na farko zakuyi asarar lokacin,na biyu zaku sa kanku a damuwa na uku zakusa zuciyar ku ta cunkushe, na hudu da kukan da kuke inama zaikiri kuke? Kuka ma Kala Kala ne, bako ina akeyiwa kuka ba, akwai abin kuka a lokacin baza ku iya kukan ba Alhali kuna so kuyi Amma ba halin yi,ku tana da kukan ku, zaiyi maki amfani, kuyi masa addu’a Allah ya bashi lafiya itace kawai addu’ar,

Shiru yayi yace’ yanzu kuma itama taje tayi Mata kukan, hmmm,

Yasa Kai ya fice Jin ana kiraye kirayen sallah, sun jima a wurin don sai da aka kusa idarwa sannan suka tashi suka tafi, a masallacin sukayi alwala Dan kar ma su Kara makara.
Saida sukayi Isha sannan suka dawo ‘yan gidan sun handeme a parlour damma yanzu sun warke Amma Aneesa har yanzu kugunta ciwo yake, darurarta daya Allah yasa ba illa ya jawo Mata ba, suka shigo suka wuce kowa yayi dakinsa, a kusan tare suka fito,yau bejin San Jan mota shiyasa yabawa Mus’ab key din yaja shikuma ya Shiga Baya, ya lumshe Ido so yake kawai yajita a jikinsa wata kasala yakeji da kewanta yarasa wanne daga ciki ya rinjayi daya, idan sa a rufe sukuma sunyi shiru ko radio babu balle waka damman Shi ba kunnawa yake na kar gwara radio Yana saurara, har suka isa yayi parking sannan suka fito parlourn Baban su Nafisa suka Shiga na bangaren ta ganin parlourn ta da Baki shiyasa suka wuce suka Shiga,Anty safiya ta gansu kuma sai taga kamar wani Abu nadamun su,ta taso Dan taje taga kiranshi, tashi tayi ta Shiga parlour gaisawa sukayi,

tace’ lafiya?

Binaif da ya kwanta yace’ lafiya qalau yunwa mukeji kawai ASA akawo min abinci su inaga sun koshi,

Mas’ud yace’ haka muka ce ma?

Yace’ haka nagani de,

Anty safiya tace’ to Bari masa Nafisa ta hada maku ni nayi Baki,

Tashi zaune yayi yace’ Nafisa kuma? Ina take ita?

Sarai tasan wayake nufi tace’ kaga ni Bani da wata gidannan kowa Yana da sunan shi Bari naje,

Tatashi tafita, mas’ud da Mus’ab kuwa hada Ido sukayi suka basar Sarai ya gansu ya koma ya kwanta ji yayi ma Shi ba dadi wallahi, Shi kadai yaka fa Jan tsaki,ya jima beja tsaki ba daman,aikuwa ya fara Mita shikadai a ransa,

Nafisa kuma bata nan tana wurin Hajja Dan yanzu wayancj suna can har itama Ummusalman tana zuwa Amma ba sosai ba,sai dai yanzu suna can su Duka, don haka tayi hanyar part dinta, da sallama ta Shiga, Hajja ta amsa, suka Dan gaisa,

tace’ Nafisa tashi kije ki hadaw su Binaif abinci su uku ne Maza ki Kai masa,

Hajja tace’ a,a zancen me nakeji? Ina kince min wannan ce matar tashi salamatu?

Tace’ ehh itace,

Hajja tace’ to iya zata Kai masa,Maza tashi kije ma ki hada masu anan, Nima nayi tuwom ai,

Nafisa tace’ kinyi tuwo ko kuma kinda anyi tuwo?

Hajja tace’ kome kika dauka duk haka ne,ja’ira kawai,

Badan Ummusalma taso ba itama tashiga kitchen din Hajja Nafisa ta taimaka Mata, ta jera komai a tire sannan ta fito ta kofar baya ta shigo sabida mutune dake parlour, ciki ciki tayi sallama idan sa a rufe har tazo ta dire a gabansa besani ba,sai dai yasan anzo Dan wani kamshin turaren wuta yaji mai sanyin dadi Yana tashi, sai ya Kara lafewa a jikin kujerar, ajjewa tayi zata fita har taje bakin kofa,

Mas’ud yace’ ya zaki tafi Baki zubawa mijinnaki abinci ba? Kinsan fa ajebo ne,

Ai bashiri ya tashi zaune Jin ance miji aikuwa itace da Shigar ta ta kulluma bata da Kaya sai doguwar Riga sai kace mai ciki(πŸ˜†) a yarda yace, dawowa tayi tana gallawa mas’ud harara, ta tsugunna ta zuba masa ta Mika masa,Yana kallanta it’s komai nata da sanyi takeyi Amma ta iya fada da sauri har tana kamar ta sarke Dan bala’i, ganin ta miko masa bata ko kalleshi ba yasa Shi kin karba, ganin be karba ba yasata karawa ta mikawa su mus’ab mas’ud ne ya karba tare da daukan spoon,

yace’ fav zomuyi nan,
A tare suka fita, Kara zubawa tayi ta Mika masa bata kalle Shi ba, namma kin ansa yayi dagowa tayi suka hada Ido ya kauda kansa gefe,

tace’ Ka ansa,

Yace’ nagani ai, Amma gani nayi ba’asan naci abincin shiyasa,

Tace’ ni banceba,

Nima bance kince ba ai

Gashi kuwa Ka fada?

A,ah nace gani Nayi,Alana nagani ai shiyasa na fada hakan,

Tace’ Wacce alama Kenan?

Kinga na farko kinzo ba sannu da zuwa ba gaisuwa ba ya aiki ba ya gajiya ba komai, sannan sai da aka fada maki aikinki tukun kika dawo kika yi sannan kuma the worse ko kallo na ma babu,

Tace’ to naji, na gyara ina yini,ya aiki,ina gajiya,kazo lafiya?

Yace’ lalle ma ke din nan haka ake ?
Ba fadar sunana bakomai taab, koda yake daman ni fa Ashe Kai ake cemin sai kace Mai karaton kai,

Gajiya tayi da tsugunna da mitar Shi,Zama tayi a kusa dashi,

Yace’ kinga?

Menagani?

Ko iya Zama ma bakiya a kusa da miji,

Tace’ wai dan Allah ya Jake so Nayi ne?

Yawwa ba wahala abin, nakoya maki?

Daga Kai tayi, yace’ good, na farko za’a fara da Zama ne,idan zaki zauna to a kusa na zaki zauna kingane?

To yanzu a,ina na zauna?

Taab kallafa ratar ai dayawa,

Nikam nagaji yunwa ma nakeji,

Yace’ Nima haka ai,
. Abinci ya dauko ya matsa daf da ita ya debo a spoon yace’ haaa

Bude bakin tayi ta zuba Mata Yana yi Yana zuba zancen Shi har ta koshi,shima ya Mika Mata batayi musu ba ta ansa ta bashi Yana Gama ci Anty Safiya ta shigo

tace’ yawwa daman ina San na fada maka cewan Umma ta Kira tace gobe na kaita,Kai kuma sai ana sauran kwana biyu sai kaje,

Bata fuska yayi yace’ kika ce kuma sai saura kwans hudu?

To ta zanja shawara haka tace da Baka zo Bama tafiya zamuyi, ta tashi ta tafi abinta,

Kwanciya yayi a cinyarta yana kallanta itama kallan Shi take, a hankali tasa hannu ta fara shafa masa sumar sa da har yanzu be rage ba,shikuma ya rufe ido kallan sa kawai take Jin yarda yake sauke numfashi a hankali yasata yi masa peck a goshi,zata dago Kenan yasa hannun sa ya dunkufar da kanta tare da

cewa’ ba’a nan ba,

Zaro ido tayi tace’ daman bakayi ba bacci?

Yace’ Nayi mana wani Abu naji Wanda ya tada ni shiyasa,

Tace’to ni sake min kaina, zaka…..

Jin wani bakon al’amari tayi Yana Wanda ya fi nada,Ashe bakomai Akayi ba.

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 29

Advertisement *page 29* Bayan sun k’are tattaunawar ne Abba, ya kira umma suka gaisa mutunce, umma sai faman…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 38

Advertisement 38 Valhalla VintageVerb VST Crack Ya Rasa yarda zaiyi? Yasan Yana San Binaif,Baya so yake nuna son…
Read More

TARTSATSI 17

Advertisement *Page 17*     ********************     Ana cikin haka, saiga Abba ya dawo, Hafsa ta yi…
KALLABI
Read More

KALLABI 17

Advertisement BABI NA SHA BAKWAI *GAISUWARKU CE A WANNAN SHAFIN MASOYAN KALLABI NAGODE SOSAI* “Fita aka ce maka,…
KALLABI
Read More

KALLABI 48

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA TAKWAS Tun bayan dawowar shi, baki daya ya kasa sukuni, asalima ko wurin…