NAWA BANGAREN 10

NAWA BANGAREN
NAWA BANGAREN

Advertisements

_____

€pisode 10…………….✍️

Barhana da sarki Zawatundma ya aika zuwa garin Mubanuwa kuwa da sauri ta fara keta hazo har ta isa garin Mubanuwa inda wani mahaukacin iska mai matuƙar ƙarfi ya fara girgiza manyan duwatsun dake cikin garin. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duwatsun suka fara tsagewa, garin ya rikiɗe, sai iska da ke ta kaɗa abubuwa, yana kwasar kayansu zuwa sama.

Take ƴan garin suka fara gudu suna neman mafaka, musamman da labari ya zo musu cewa babban dutsin garin wanda wani bai taɓa hawa ba saboda yadda suke girmama dutsin, akasari ma wasu daga cikin ƴan garin wannan dutsin suke bauta ma, tun da suka ji labarin ya rabe biyu kowa ya san yau tashin hankali zai afku a wannan garin, dan duk wanda ya girma ya tashi ya san da zaman wannan dutsin da suke kira MIRACLE STONE.

Tsuntsun da Naheel ke kira Baharadi ne ya shigo da guguwar zuma mai matuƙar yawa da dafi, zuuuuu zuuuuu haka zumar suka dinga kuka, sun fi ƙarfin minti talatin kafin suka fara saukowa, domin har gitsa garin Mubanuwa kamar yadda Yareema Naheel ya umurta.

Zuma nan ta dinga shiga kunnuwan aljanun garin tana gigita musu lissafi, yayinda duwatsun da Barhana ta suka suka fara gangarowa suna danne ƴan garin, gidaje suka riƙa rushewa, duk yadda aljanun garin suka kai ga tsafi yau sun ga wutar dafa kansu, dan komai ya gagare su sai gudu.

Wasu sai gudu suke, amma duk yadda ka kai ga gudu wannan dutsin sai ya cimma maka. Cikin mintuna da basu wace talatin ba Barhana da Baharadi suka shafe tarihin garin baki ɗaya. Babu ko halitta ɗaya da ta rage a garin ko da kuwa halittar tsuntsu ce.

__________________

“Naheela! ” Naheel ya kira sunanta da ƙarfi, kamar an taɓata ta buɗe Idonta ƙyar ta fara yunƙurin tashi ganin abun ƙaunarta tsaye gabanta.

Advertisements

_____

Hannunshi ya kai Saiti da inda mashi ya cake ta ya rufe idonshi, a hankali ya jaye hannun, da kallo ta bi wurin da Naheel ya taɓa, bata yi mamaki ba dan ta ga babu Ko alamar tabo a gurin, miƙewa tayi yayinda Naheel ya juya zai wuce.

“Abbana ka mishi godiya na san bazai saurare ni ba ” tayi maganar Idonta na zubar da ƙwalla.

Juyowa Naheel yayi ya ce “ki Adana kalamanki, zasu miki amfani wani wurin ba nan ba, bana buƙatar godiyarki”.

Wani farin haske Naheela ta aika ma Naheel daga cikin Idonta nan take ya tsaya cak.

Cikin taku na isa ta ƙarasa gabanshi, wanda yake jin wani mugun zafi na tunkaro shi.

“Ka san miyasa ban tilaska zuwa gare ni ba yau? ” tayi maganar tana shafa mishi ƙirji da yatsunta guda ɗaya.

Ta san ba zai iya yin magana ba saboda ta dakatar da shi daga yin motsi haka yasa ta ci gaba da magana.

“Saboda ka zo ceton raina ne, ya kamata na saka maka da alkhairi ba akasin haka ba, ka sani ni Naheela ba a haife ni dan in gaza ba, burina na zama ɓangarenka sai ya cika, kai NAWA ƁANGAREN ne, babu kowa a ɓangaren Naheela sai kai ” tana kai ƙarshen maganar ta hura mishi iska a fuska.

Hannunshi ya ɗaga ya nuna ta da shi “kin san ba dan ke na zo nan ba, na zo nan ne Saboda al’ummar garin Zawatu, na san idan kika bar duniya Zawatu zata samu jakadu, dan haka ne cece numfashinki ne saboda al’ummar Zawatu  ” ya faɗa

“Hahahahahahahaaaaaaa!” Naheela ta ƙyalƙyale da wata mahaukaciyar dariya, da ta saka dajin ruɗewa.

“A ɗaga sama! An yi wa wada ƙwace, In ban da abunka waya ce maka ƙarfinka ne ya ceci numfashina ” ta faɗa, sannan ta girgiza kanta “samsam ba haka ba ne, da ace ƙarfi ke ceton rayuwata da Binaf ta cece ni kafin ka zo, da ƙarfi zai iya ceton rayuwata da Abbana Masoyina ya bani rayuwarshi da iya ƙarfin da yake da shi” ta faɗa tana ƙara taku, sannan ta ce “soyayyarka ita ce bugun Numfashina, kusantata da kayi shi ne Maƙasun yin numfashina a yanzu ƙarfinka bashi da tasiri a kaina, ba wani mai wannan ƙarfin ”

Ji yake kamar ana soya shi da ruwan mai, ga wani mugun zafi da yake ji har cikin jijiyoyinshi. Da ƙarfi ya ce “Wannan wane irin bala’i ne, na tsane ki, wallahi na tsane ki, ke ba wata ba, ke dai Naheela wallahi, wallahi bazan iya rayuwa ba ki daina kusanta ta mutuwa ita ce aminiyata idan kina kusanta, me na miki da kike azabtar da ni”.

Murmushi tayi, sannan ta ce “zaka saba da ni a matsayin abokiyar rayuwa “ta faɗa.

Ɓat ya ɓace dan bazai iya ƙara fitar da numfashi ba in dai Naheela na a gefenshi.

Advertisement

_____

Juyawa tayi ta kalli Abbanta da tun ɗazu yake kallonta.

Murmushi ta mishi ta ce “na san abun da kake ƙiyastawa a ranka ya masoyina”.

Sarki Zawatundma ya ce “ina duba gaskiyar abun da ya faɗa ne “.

Numfashi ta sauke ta ce “to me ka gani”.

“Da gaske ne yana ƙonewa idan mace ta kusance shi ” ya faɗa.

Zuwa tayi ta jera da Mahaifinta, tare da gaɗa mishi kai ta ce “ na san wannan, amma kuma ina so ya saba da ni a tare da shi”.

Gaɗa kai Sarki Zawatunduma yayi ya ce “Eh na ga gaskiyarki ai, na fahimci zaki iya “.

“Ka san zan iya, amma kuma ta yaya?” ta tambaya, suna ƙara matsawa gaba.

Numfashi ya sauke ya ce “ƙarfin da kike da shi zai iya yin komai, kawai ki san yadda zaki yi amfani da shi”.

“Haka ne Abbana zan yi yadda ya dace “.

_____________________

Yaran Bobbo ne waje suna zana Ƴar gala-gala, suka hango Bobbo riƙe da ƙaramin Sadauki, da sauri suka nufo shi suna faɗin “Sannu da zuwa Bobbonmu”, shafa kansu ya dinga yi da ɗaɗ-ɗaya, sannan ya ba ko Wannensu naira goma-goma.

Dama can abunda ya saba musu kenan ko wace ranar Juma’a, yau ma haka yayi, sai tsalle suke yi.

Da gudu suka nufi wurin Ade mai aya. Wata tsohuwa ce ke kasa kayan ƙwalam a wajen gidanta.

Aka yi sa’a lokacin da gama ƙulla Ayar, ai ko nan take suka siye ƙullin Ayar da tayi.

Ɓangaren Bobbo kuwa cikin gida ya shiga, kai tsaye ɗakin Mamma ya nufa, in da ya tarar da Mamma………………….

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 29

Advertisements _____ BABI NA ASHIRIN DA TARA. “Ta zame min mara amfani, wanda ba zan kuma amfanar rayuwa…
KALLABI
Read More

KALLABI 28

Advertisements _____ BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS “Karya ne!” Rike hannun shi Waziri Zakaria yayi yana mishi alama…
KALLABI
Read More

KALLABI 27

Advertisements _____ BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI Inna Marwa bata yarda zai iya daina zuwa fada ba, sai…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 18

Advertisements _____ €pisode 18…………….. Bayan wata ɗaya . Tun daga Ranar da Naheela ta karɓi mulkin Garin Zawatu…