A BAKIN WAWA 35

A BAKIN WAWA 3
A BAKIN WAWA 3

Advertisement

 

35

 

 

Output – Portal Crack

Tace’ you?

 

Runtse idansa yayi ya Danna Kiran wayarta Sai dai bata daga ba,ya kuma Kira namma haka ahaka yayita jera Mata Kira daga karshe ya bude abunda tayi typing yafara karantawa,

 

Sameera tace’ idan bazakayi magana fine your out,

Advertisements

 

Numfashi ya ajje sannan ya zaro kafarsa guda Daya waje cikin wani murmushin da kana gani kasan na yake ita kanta Sameeran tasan na yaken ita da akayiwa bare wani kuma,

 

yace’ Hello,

 

Banza tayi dashi ta kauda kanta gefe,

Zuciyar sa yaji ta tsinke ji yayi kamar ma ya koma, kallan wayar sa yayi,

 

Yace’ am sorry

 

Tace’ yanzu kuma me zaka zo kamin,wancan Ka rabani da saurayi na yau kuma fah? Dame kazo?

 

Advertisements

Runtse Ido yayi sosai ya Dan kalli wayarsa,

yace’ am kiyi hakuri bansan hakan zai faru ba,daga maki magana?

 

Tace’kaga ya isa haka,tunda Baka da tace zaka iya tafiya,nidai nasan bansan Ka,bamma taba ganin ka,

 

Yace’ Insha Allah yanzu zaki sanni idan kin bani dama,

 

Mtsww kaga Ka tattara inaka inaka Ka barmana gida Bana San na Kara ganin Ka makaryaci kawai,

 

Kallan wayar Shi ya danyi kafin ya juyo ma har tayi nisa,daga murya yayi yarda zata ji Shi

Yace’ ki gaida yayarki Ummusalma,

 

Cak ta tsaya ita bata juyo ba ita batayi gaba ba, Gabanta na wani irin faduwa tabbas tana da yaya fa Ashe ko? Amma tana ina? Ya akayi ta mantata? A hankali ta juyo ta kalle Shi Yana kallan wayarsa irin Zama ki dawo, dawowa tayi,

 

tace’ ya’akayi kasanta?

 

Yace’ to ai nazaci ke ita ce ma a wancan ranar shiyasa am sorry,

 

Tace’ kuma meyasa Ka ambaci sunana,

 

Yace’ na tuna tace tana da kanwa Sameera shiyasa dakika muna Baki sanni ba Nayi tunanin kece,

 

Tace’ na manta da ita Sam bansan ya hakan ta faru ba,

 

Yace’ bata nan ne? Rabona da ita shekara shida Kenan,

 

Tace’ Nima bansani ba, amma Zan tambayi Mama naji? Nifa na manta da ita Sam,idan ba yanzu da kace yayata ba,na tuna ina da yaya Ummusalma yaya salama,

 

Sauke a jiyar zuciya yayi yace’ ina San Ummusalma sosai Bata da matsala ko ta sisin kwabo,kowa zaiyi alfaharin samunta a matsayin Abokiyar sa,Amma ya akayi ta bata?

 

Tace’ wallahi bansani ba nifa nace maka na manta ta,a babu rayuwata a wuri daya nake tunata duk sanda Naga abinda bata so ko abunda take so ta shine Zan ce nikuwa wama yake San wannan abun? Amma Zan manta sunan,

 

Yace’ to mai Hana muyi wani Abu?

 

Tace’ name fah?

 

Yace’ karki sanarwa da mama ko Abba naji kince zaki sanar musu, please karki hakan, maybe Suma sun mantata,

 

Amma meyasa?

 

Sabida ina so mu nemota kingane?

 

Nafa manta kamarta,

 

Karki damu ni ban manta ba,

 

Tace’ nasan Mama zatayi farin ciki duk ranar da na kawo Yaya salama sosai ma kuwa,

 

Murmushi gefen Baki kawai yayi, nashi kadai yasani,Abu biyu ne suka hade masa abinda yake karantawa anan ta tsaya,besan bezaice ba kuma, shiyasa yace’ to ni Zan tafi,

 

Tace’ da wuri haka?

 

Yace’ ehh Zan tafi Lagos ne yanzu fa inaga ma Sai dare gaskiya,

 

Tace’ to shikenan,Amma sunanka fah?

 

Mas’ud,

 

Kawai?

 

Adam Dan Lami,

 

Dan Lami?

 

Eh,ko kinsan wani haka?

 

Kamar de munyi school tare da wasu amma seniors Dina ne, Aneesa Dan Lami da Ameera Dan Lami,

 

Wani murmushi yayi murmushi irin akwai kura Kenan, shifa ta barshi ya tafi haka, babu abin  cewa kuma,

 

Tace’ number fah? Gashi ban fito da wayata ba, kawo na Sama sai Ka kirani,

 

Yace’ no karki damu Fadi kawai, sai nasa,

 

Tace’ rowar wayar kake ne?

 

A,a ba komai,kawai de ki fada kinsan sauri nake,

 

Fada masa tayi ya rufe kofar sa,

tace’ yanzu kuma sai yaushe Kenan?

 

Sai next week in Allah ya kaimu,

 

To Allah ya kaimu Allah ya kiyaye hanya,

 

Murmurshi yayi yace’ ameen na gode,

 

Sai da yaga ta Shiga gida ya sauke ajiyar zuciya yace’ ko taya sani? Wannan yarinyar daman Aljana ce nafada ai, Bari naje gidan,

 

Horn yayi aka bude masa gate,zai go saiga su Ummu nan da yaseer zash shigo sai da ya Bari suka shigo tukunna dayake glass din a sauke yake sai da suka gaida Shi sannan ya suka wuce, shima ya wuce yana fita ya hango mus’ab yaje ya dauke Shi,suka wuce, kayansu suka hada  lokacin ma Magriba tayi hakan yasa sai da sukayi sallah sannan suka nufa gidan bb lokacin ana nema ayi Isha,

 

Mas’ud yace’ Anya fav zamu samu flight kuwa?

 

Mus’ab yace’ mezai Hana sosai ma,kasan ai gobe Monday kuma duk manya manya nan zasu tafi wasu ma kasar zasj bari kuma dole sai sunyi landing a Abuja ko Lagos sannan wasu kuma direct ne,

 

Mas’ud yace’ Kai Nima fa inasan naji wataran ana ga Alhaji Mas’ud nan tafe, Alhaji Mas’ud kaza Alhaji Mas’ud Malam lokacin Zan baza hajata nake fada maka,

 

Mus’ab yayi dariya yace’ zaka baza haka da ‘yan Mata kace,

 

Wawan burki ya taka Allah yasa lokacin sun shigo anguwa ne babu mutane sosai, San yayi gaba yace’ Kai ana zancen hankali kana wani zance naka da daban abinda yafi so banza kawai ana maka zancen irin idan Nayi kudin nazama Alhaji sai anjirani idan jirgi zai tashi muma yarda ake muke jiran wasu,

 

Mus’ab yace’ Kai wallahi na tsani Abu nan,Kai kaji takaici waifa kaga wannan tafiyar Sai da mukayi awa biyu a zaune a cikin jirgi, tafiyar da bata 30 min ba, Amma sai da mukayi awa biyu muna jira daga karshe har yazo yafa Shiga kawai ya fito, yace yayi mantuwa, yasha Allah ya isa ba laifi nake fada ma,kuma beyi tafiyar ba,

 

Mas’ud yace’ Allah sarki kace shiyasa ranar naji muryan Ka wani irin Ashe ashe,

 

Kaidai Bari twinny, Yana ga Ka kawo mu gidan Anty Safiya bayan munyi Mata sallama tun dazu?

 

Yace’ Kai yunwa nakeji idan munci sai mu ansa nasu mu kaima su,

 

Hakan yayi kyau,

 

 

 

 

✨✨✨✨✨✨✨✨

 

 

 

Bayan sunyi sallah sun kwanta,tana kwance a pillow shikuma yana kwance Yana kallanta ya dafa hannun sa da fuskar shi,ita kuma ta rufe Ido,

 

yace’ to fada min mun Zama daya ko a,a?

 

Rufe fuskarta tayi da kirjinshi,

tace’ a,a ai bazamu Zama ba,

 

Yace’ Kai dan Allah kice de har yanzu da saura,to Bari na kara kinga sai muzama Daya dakyau dakyau kingane ai,

 

A sukwane ta dago tace’ wallahi mun zama Bama Daya ba, mun Zama abinda yafi Daya Allah kuwa,

 

Dariya yayi yace’ a,a daga baya kenan,ban yarda ba gaskiya, ya fada Yana pecking dinta a goshi,

 

Tace’ a,a fah,

 

Kwanciya yayi ya daura kanta a kirjinshi yace’ Mi Amor?

 

Tace’ uhm,

 

Baki tuna sanda muka fara haduwa bako?

 

Uhm,

 

Kina so Kiji?

 

Uhm, Amma sanyi nake ji,

 

Ohh kindena Jin zafin?

 

Danace ina ji?

 

Kin manta?

 

Uhm,

 

Bari to idan mun karayi zaki tuna,

 

Nifa na tuna,

 

Yace’ wai na tambayeki?

 

Uhm,

 

Wai daman kina da kunya ko kuma de yanzu ne kunyar tazo?

 

Kara  dukar da kanta tayi a jikinshi,ta rungume Shi dakyau, batayi magana ba,

 

Zaiyi magana wayar sa tayi kara,

 

Hannu ya Mika ya janyo wayar ganin Mas’ud yasa Shi dagawa, daga

 

Yace’ yane? Har kaje Ka?

 

Daga can mas’ud yace’ naje ina?

 

Binaif yace’ kamar ya? Lagos mana bacan zaka wuce ba,?

 

Yace’ Amma kayi formatting ko bb?

 

Mus’ab ya ansa yace’ ai bejeba Amma yazo cikin gidan Ka,kuna ina ne haka kuka bar gidan a bude kuma kuka fita?

 

Binaif yace’ bangane muna ina ba? Muna gida mana?

 

Atare suka ce wanne gidan,?

 

Bansani ba, kashe wayar yayi yace’ Bari na fita, ina zuwa kinji?

 

Tana lumshe Ido alamar bacci ta daga masa Kai,ajjeta yayi a pillow ya zura rigar Shi ya fice,

 

 

A zaune a parlour ya gansu, yana fitowa suka zuba masa ido,murteke fuska yayi irin ba wasan nan,sai dai kuma wani irin kwantaccen annuri suka hango kwance a fuskar Shi Wanda Basu taba ganin irin sa ba,

Yana karasowa yace kallan fah?

 

Mus’ab yace’ ah bakomai nidai kawai gani nayi yanzu nan kamin kyau,

 

Mas’ud yace’ ah Ashe de Ka gane,

Zuwa mukayi kakaimu airport zamu wuce,

 

Yace’ to meye na wani zuwa? Ku tafi mana,

 

Mus’ab ya zunguri kafar mas’ud ganin ya kalle Shi be gani ba, juyowa yayi ya kalle Shi,da Ido ya masa alamar tana ina?

 

Mas’ud yayi gyaran murya yace’ ina aljanar matarka?

 

Bacci take,Dan Allah ku tafi nikam,wai sai kunyi dare ne?

 

Mas’ud yace’ dare na wa kuma ai sai dai na gobe kuma,

yace Allah inaga matar Ka aljana ce kamar tasan abinda zai faru kawai ta fada min yarda zance, nidai ban yarda da ita ba, Ka kaita Amata rukiyya kafin mu dawo,

 

Throwing pillow ya dauka ya jefa masa yace’ oya fice min a gida, kafin ranka ya baci fita nace,

 

Mus’ab yace’ Haba bb kaifa zaka kaimu ina zamuje kuma?

 

Yace’ ku hau napep mana, ni kun dame nine,

 

Ehh lallene,damma de Nima very soon zanyi wannan auren kuma kar naga kafarka a gida na tunda korar mu kake, fav tashi mu tafi,

 

Mus’ab yace’ bb kasamu motarka a airport Dan mu munyi nan,

 

Idan mu bamu hau napep ba wani zai hau,kuma gobe Kwama yi abinci don na fadawa Anty safiya cewan kace nace basai na aiko da abinci tunda gobe Yan makaranta zasu koma kuma ba driver idan anga dama to,

 

Kara wulla masa wani pillow yayi yace’ ku fice kunzo haka kawai kun dameni,

 

Fita sukayi Basu ce komai ba Amma bakin Mas’ud Yana motsi alamar sonyi magana Mus’ab ya hana Shi,

 

Bayan sun fita har zai dawo sai kuma ya fita zai rufe gate yaga mas’ud da coolern abinci,ya Mika masa tare da yi masa wani Dan iskan smirking da kanne Ido daya,bema Bari ya ansa da hannunsa ba ya ajje ya koma da gudu, murmushi kawai bb yayi ya karasa ya rufe gate din ya dawo ya dau coolern abinci ya Shiga parlour ya rufe ko ina, sannan ya wuce kitchen ya dauko plate yashiga dakin,

 

Tana kwance yarda ya barta sai dai tayi bacci don yana fita tayi bacci, dayake ba Haske a dakin sai ya kunna,yana kunnawa tana tashi sai dai batayi wani motsi ba, kara sowa yayi ya daga ta ya zaunar yace’ tashi kici abinci,

 

Idanta a kulle bata bude ba don itakam Allah ya gani batasan hasa Ido dashi yanzu,Kai kawai ta girgiza,tare da cewa” na koshi fah,

 

Kici kadan kinji?

 

A,a nidai na koshi gaskiya,

 

Baya so ya matsa Mata shiyasa yace’ to me zaki sha ? Hollandia? Ko fresh milk? Ko kuma yoghurt?

 

Daga masa Kai tayi zata kwanta,tashinta yayi yace’ ki tashi Bari naje na kawo,

 

Abincin ya dauka ya fita da Shi yasa fridge Kar ya lalace sai anan ma yaga sauran naman jiya da suka ci Shi yama manta yogurt din ya dauko ya dawo tana kwance ta daura kanya pillow shigowa yayi yace’ ta so kici,

 

Ahankali ta tashi zaune ta sauko da kafarta tana takawa har ta karaso inda yake zaune ta zauna a gaban shi,tunda ta taso yake kallanta yarda take tafiyarta a Hankali bata wani dingishi Sai dai yanayin tafiyar da take a hankali kamar bataso,

 

Kanta a sunkuye ganin kallan kurillan da yake mata,tana wasa da bracelet din hannunta, looking so innocent, murmushi yayi Yana Mika Mata robar, sha tayi taji dadin ya Ragu, shiyasa ta rike a hannun ta bata kuma dago ba,

 

Yace’ yayi sanyi da yawa shiyasa Nayi diluting dinshi da ruwa marar sanyi,

 

Yatsine fuska tayi,har zatayi magana tayi shiru,ahaka tasha shidai a wurin ya barta ya tafi daki Shi, har ta Gama be dawo ba,shiru shiru har ta sake wanka takwanta bedawo ba,tashi tayi a hankali tana tafiya ta fito da tana dubawa ganin kofofi yasa ta tsaya tana tunanin wanne zata Shiga? Dakin kusa da nata ta tashi ga Baya nan,tayi tafiya kadan ta shiga wani wannan ma baya nan,gajiya tayi,zata koma ta tuna dazu taga kujera a kusan dining maybe Yana nan, wurin taje ta kunna fitila bags ganshi sai kofar da ta gani yasa Karasa wa bude ta Shiga, parlour tagani daidai misali  yayi kyau bakadan Dan kayan ciki sun kawata tashi gashi karami bame cika Ido ba, daki ta wuce taga ganshi a daga can wurin kujera ya zauna yana aiki a system,zuwa tayi ta zauna a bakin gadan,dagowa yayi, ya ganta sai sauke numfashi take,

 

yace’ am sorry na barki ke Daya ko?

 

Batayi magana kawai ta kwanta ta rufe Ido,badan wai bacci na sai dai yanayin dakin ya burgeta daku kamshinsa, tashi yayi ya rufe system din ya gyara Mata kwanciya taje ya kashe fitilar da bedside lamp, shima ya kwanta,

 

Yace’ Kin biyo mijinki Kenan?

 

Juyar da Kai tayi gefe bata tanka masa ba,

Yace’ to shikenan da’alama bakya sanjin labari ko?

 

Girgiza Kai tayi, yace’ to dawo nan,yafada ya na nuna kirjin sa, ba yarda ta iya bazata iya musu ba,ko tayi ma yanzu sai ya kawo Mata maganar da batace ba, dawowa tayi tare da rungume shi, shima rungume ta yayi suna shakar kamshin turaren juna kowa shiru yayi babu Mai magana, cikin murya kasa kasa,

 

yace’ zaki iya tuna ranar da kikaje wellcare?

 

Tace’ Ai ba sau daya naje ba bare na tuna,

 

Yace’ to,wata rana naje wellcare ina tafiya sai ga wata yarinya a that time bazata wuce 13-14 ba a shekaru tana sanye da Pakistan a jikinta me makon ta yafa mayafin sai ta daura Shi a Kai tasa earphone tana Danna waya tana tafiya, kawai tayi Karo da wani mutum, ya dago ta kalle Shi suka kurawa juna Ido ita ce ta fara dauke idanta daga gare shi tasa Kai zata wuce shikuwa ya riko ta, mema yace ma ta? Na manta de,Amma ita ca tace make kallan gabanka ba Ka tuhumi mutane ba, ta wuce ta barshi da Baki a bude, ko kinsan labarin?

 

Tashi tayi zaune tace’ kasan me yace’? Haka yace’ can’t you apologize? Or you don’t know how to apologize?

Murmushi tayi tace’ Kai Baka manta tuwa ko?

 

Yace’ kusan hakan,indai moment yamin dadi bana mantawa dashi,

 

Murmushi kawai tayi masa ta kwanta,

tace’ what’s your mom?

 

Yace’ ke kika fara fada min zancen mahaifiya ta, sannan kinyi gaskiya da kika ce dole za’a samu ‘yan uwanta, dole tana dasu,Amma abinda lurar anan shine yarda suka barni basa nemana Nima bazan neme su, yarda suka kyaleni Nima haka Zan kyalesu,

 

Tace’ to idan kuma mahaifiyar Ka tana da Rai fah?

 

Murmushin takaici yayi,

Yace’ Mi Amor kidena damuwa da damuwa ta,Nima kaina na dena damuwa bare kuma ke, kisawa zuciyar ki salama kidena bin al’amari na,Kinji ko? Idan ina da uwa har yanzu a raye to Yakamata a ce ita ce zata nemi ni,bani  ba,itace tasan gidan Mahaifina itace tasanni, tace zata iya nemana,ba Nima,taya Zan fara nemanta duniya fa da fadi,waya sani ma ko kasar da bansani ba taje? Kauyika suna da yawa garuruwa suna da yawa unguwanni suna  dayawa,kasasge suna da yawa to yakike so Nayi?

 

Tace’ at least ya kamata Ka fara,

 

Yace’ kinga Dan Allah kiyi hakuri Dan Allah karma ki Kara min zancen na dena Karna dena kin gane ai?

 

Ganin kamar ranshi ya baci abinda kuma bata so Kenan ta bata masa Rai, zuciyar Shi har wani bugawa take alamar abin na masa ciwo, Rasa abinda zatayi tayi kawai ta hade bakinsu daga nan kuma aka Lula.

 

 

 

 

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

 

 

 

Suna zaune kowa da system a gaban Shi ana fama da aiki,

 

yusuf yace’ wai ni ina Alkhakin namu ne, a kawo mana munayi muna ci muna korawa,

 

Yaseer yace’ taab ai tunda bakaje ba Anyi ba Kai,

 

Ummu tace’ wallahi kuwa, kaidai Bari,

 

Yusuf yace’ yanzu de rowa za’amin ko?

 

Ummu tace’ to muma iya Cincin din nan na dazu aka bamu da alawa kuma mun cinye,sai gobe tace muje mu ansa,

 

Yusuf yace’ kai karku Rana min hankali mana, wannan cincin din Naga Anty ce tayi,kawai kuce Baku jeba,

 

Yaseer yace’ to sai me ba’aje ba din,

 

Ummu tace’ munje basa nan Amma gobe Insha Allah zamu koma,

 

Yaseer yace’ exactly ‘yar gidana gobe zamuje idan mun dawo daga school yarda zataga irin mun gaji a zubu dayawa ace ku kaiwa Mamanku,

 

Yusuf yace’ kun Shiga uku da kwadayi kudai wallahi kuma Allah ya yaye maku,

 

Hakkin mune fah,

 

Haka yake Dan gidana hakkun maganar Ka gaskiya ce,

 

Zaiyi magana akayi sallama aka shigo Sameera ce ta shigo,dukan su Ido suka zuba Mata, ta Galla masu harara,

 

tace’ ba amsa sallama sai zuba min Ido,

 

Ummu tace’ Yaya Sameera lafiya?

 

Anty da ta shigo tace’ ba’asani na ina ruwanku kunku tazo?

 

Sameera tana shigowa tace’ mama Dan Basu taba ganina bane,

 

Shiru sukayi basuyi magana ba ita kuma suka gaisa da Anty,Abie ya dawo suka gaida shi Anty ta tashi ta tafi,

 

Sameera dawowa tayi kusa dasu inda suke a kasa ta zauna tace’ yusuf yaseer ina ta jiranku Naga kun dawo kunki nikuma bacci nake ji,

 

Yusuf yace’ to meya faru yau kuma?

 

Tace’ tambayar ku zanyi?

 

Yaseer yace’ munaji,

 

Tace’ Zaku iya tuna Yaya salama?

 

Yusuf yace’ meya faru kuma ?

 

Tace’ na manta da ita sai yau da wani yazo,

 

Yaseer yace’ wani Mai mota latest CRV, Baka ?

 

Tace’ eh, Shi,kasan shinee?

 

Da zamu shigo muka gan Shi,

 

Tace’ shine,daga na fada masu yarda sukayi,

Tace’bansan ya akayi na manta taba,Sam na manta abin mamamk yake bani kuma har yanzu ban iya tuna kamarta ba ko kadan,

 

Yusuf yace’ Kin fadawa Mama?

 

Yace’ Kar na fada masu kawai muyi aikin mu biyu sai ku dana fadawa……

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 65

Advertisement BABI NA SITTIN DA BIYAR Kamar yadda ake abisa al’ada ajiye sarauta yayi ya raka Gidado, duk…
KALLABI
Read More

KALLABI 5

Advertisement *<Babi Na Biyar>* EWF “`Wannan shafin gaisuwarki ce Mammyn Afreen ki more pagen da gasken gaske… Ina…
KALLABI
Read More

KALLABI 63

Advertisement BABI NA SITTIN DA UKU Make hannun shi, tayi cike da matsanancin kunya dan sai yanzu ta…