A BAKIN WAWA 36

Advertisement

36

Da Asuba bayan sunyi sallah suka koma suka kwanta, ya kwashe duk yarda sukayi da Alhaji Munir ya fada Mata,

yace’ yanzu na rasa mafita,bansan ya zamuyi ba,

Nitro Pro Enterprise Crack 

Shiru tayi tana sauraran sa kafin ta dago,
tace’ ya kake gani idan aka ninka masa kudin orphanage din, idan yaga zunzurotun kudi zai yarda,

Yace’ kina ganin hakan zaiyi kuwa?

Tace’ sosai ma,Abu na farko da zakuyi ba bakar fata zaku sa ba, a Kira Wanda yake Felix Wanda yake Kula da companyn Paris kaga komai zai zo da sauki, tunda yasan Abban mu, kuma shin Abban idan yaga farin fata kuma yaga kudi da gudu zai yarda,

Yace’ yarda kika ce hakan za’ayi,

Tace’ idan kun dau shawara ba? Amma a ganinka ba kuwa wani business din yake zuwa ba? Wanda Baya so a sani? Yake fakewa da zuwa company?

Shiru yayi Yana jiya maganar ta,
yace’ banyi tunanin wannan ba,

Advertisements

Tace’ yanzu kayi,

Tace’ companyn Abuja shine next target, Dina,

Yace’ mezakiyi?

Kawai kudai ku dai ku zauna ku zuba ido, ku kula da komai,
Tace’ Amma a Naga 40 million muka ansa taya Ka sai company nan?

Yace’ ina ruwanki, kawai ki zuba ido kiyi kallo, ki Kula da aikin da kikeyi,

Murmushi tayi tace’ time will tell,am sorry,

Shima murmushi yayi,kawai ya rungumeta,

Tace’ Bana Jin ya bar mana wannan companyn, dole zaiyi wani Abu akai,

Yace’ kamar ya?

Tace’ kamar yarda da na fada ma,dole Yana Shirya wani Abu,

Shiru yayi yana tuno abinda ta fada masa Yana hadawa wuri guda, ya ilahi,

Da safe tana bacci ya Shirya zai fita, Baya so ya fita ya barta Amma ta Zama dole ya fita tsab ya Shirya abinsa har yazo bakin kofa sai kuma ya juyo ya ganta kamar ya kamar ya dawo yakeji sai dai idan ya tuna aikin da zaiyi sai kawai yasa Kai ya fice Yana tunanin ta, key din ya Bari a jikin kofa, yarda zata gani sannan ya fice, wurin mota ya kalla anan ya tuna su Mas’ud girgiza Kai kawai yayi ya fita, ya kulle Mata kofar gate din,ya fara takawa a kasa gashi unguwar shiru babu kowa a Layin duk Yan makaranta sun tafi Baya gahaka kuma Layin su duk wayanci Amareni da sabbin zuwa a Layin su, tafiya yake har ya karyo kwanar da zai sada Shi da babban titi Yana tafiyar sa, mota ya gani tayi parking a gaban Shi ya dago,yaga waye, su yusseer ne kallo Daya masu ya gane su,

Advertisements

Yusuf yace’ Ka shigo mu tafi,
Murmushi yayi zaiyi magana yaseer ya fito ya koma baya, shigowa yayi suka tafi,

Yusuf yace’ ina zaka je?

Yace’ kunga ku ajjeni ma a bakin hanya don wurina da nisa kuma school zakuje Kar ku makara,

Yaseer yace’ ai lecturer bazai zoba shiyasa ma yau bamu fito da wuri ba,

Yusuf yace’ ina ne?

Yace’ Ida kasan Tsohon M&M to nan,

Shiru yusuf yayi, yaseer ne yabada amsa da yasani,

Yaseer yace’ yanzu ai ya koma Ummu,

Ummu tace’ ehh sabida sunana akasa shiyasa Abubuwan su suke da dadi, ba?

Yaseer yace’ kaga shirme, wayace maki haka ne to?

Yusuf yace’ kawai dantaji ance Ummu,

Tace’ bawani nan sunana ne, Ummusalma Ummu nan gani nan Bari,
Tace’ daman ma Baku dawo ba da bakina ya huta da masifa,

Dakwa har yanzu kina nan a rame ai, kamar a hure ki hantsala,

Rama bata Hana mutuwa,

A tare suka ce first time in history,

Banza tayi dasu bata tanka ba, sai kuma can, tace’ laaaa mu gaidar dashi ba,
Yaya ina kwana,

Shi dariya ma suke bashi,kawai de yayi shiru, da lafiya kawai ya amsa Mata, sude shiru sukayi Basu gaida dashi ba tunda sun san sun Zama abokai,

Lokacin suka karaso wurin, godiya ya masu zai fita,
Yusuf yace’ Dan Allah nace ko kasan Wanda ya siya companyn nan?

Murmushi ya masa Mai kyau yace’da damuwa ne?

Yusuf yace’ a,a bakomai kawai de ina San sani ne Dan Allah,

Binaif yace’ nine, da matsala?

Yusuf yace’ innocent you? Besan a fili ya furta ba,

Binaif yace’ lafiya kuwa?

Yusuf yace’ ah bakomai inasan numbern Ka Dan Allah,

Beyi musu ba ya ansa wayarsa ya saka masa ya Kara masu godiya ya fita.

 

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

‘ya’yan Hajiya ne dukan su suka zo kwansu da kwarkwartar su tamkar yaune ake bikin kowa kaga ni Yana cikin farin cikin zuwa gida, sukan zo akai akai sai dai ba dukansu suke faruwa irin na yau ba wasu sun haihu wasu kuma har yanzu Allah be Basu ba wasu kuma Daya haka de suka zo, babbar su wacce ta girme su,

tace’ Hajiya ya kamata muje muga mu ga matar Binaif,

Mebinta itama ta girmeshi,
tace’ wallahi kuwa hakan ya kamata,

Hajiya idan kunje sai ma ku kwana Dan ku muzguna Mata daman ‘yar kauye ce,

Saima tace’ nidai babu inda zani, bazani gidan ‘yar kauye ba,

Wata daga cikin su, tace’ Haba Anty Mariya da Anty zakiyya ba wallahi ba yi bane hakan Yakamata Ku San fa yanzu kun girma kuma kuna da yaran da zaku aurar nan gaba gaskiya hakan beda riba Sam wallahi,

Anty Mariya tace’ ke Dan gidanku kema yanzu kin girma ko? Har zaki ke fada min magana haka?

Tace’ Ai gaskiya ce na fada,ko Baki da ‘ya ai kinda kannai baza kiso ayi masu haka ba,

Anty Mariya tace’ ikon Allah yau ni Mariya Hudaya take fadawa magana haka, Kauwar kauwata cab,kefa kauwata ce ta wurin hudu fah imagine,

Anty zakiyya tace’ Ai kina da akusa Dani take sai mangareta marar kunya,

Hajiya tace’ kunga ya isa haka kedaman tun kina karamar ki kike kawo musu cikas idan bazaki ba ki zauna a idan ba lalle ba dole, sude dukan su zasuje harda yara ma kuwa manyan yaran ne kawai baza’aje da su ba kima ji dawai atoh bana San shashanci banza Dana hofi,

Hudaya shiru tayi batayi magana ba,

Anty tace’ Ai ni lamarin Hudaya wallahi Yana Bani mamaki Sam sai kace Bani na haifeta ba,
Zarah’u tace’ ahh mu ai zuwa dole ne wannan muje muci uwar ‘ya wallahi ko ya kukace,

Khadija tace’ wanna hakkun ne wajibine kafin ma yarinya tazo ta rena mu gwara take Baya Baya idan anzo abin dangi a to,

Aneesa da Ameera suka ce suma baza suce ba haka ma Saima,Fati kuma bata nan tana school haka suka Shirya tsab suka fita,

Hajiya tace’ haba wallahi muma ma huta da hayaniyar yaran nan,

Anty tace’ wallahi kuwa,sai dai drivern kuwa yasan gidan?

Tace’ Ai shine ya Kai Alhaji yagani,

Hudaya tace’ ni Anty zanzo na wuce sai wataran kuma,

Anty tace’ Allah ya kiyaye,

Hajiya tace’ kekam zuwanki beda amfani ma Sam,

Bata tanka masu ba ta Kira mijinta tace ya sameta a gidan Anty safiya, tashi tayi ta Shirya ita da yaranta su biyu suka tafi.

Anty tace’ wannan yarinyar Allah de ya shirya,

Hajiya tace’ ameen,

 

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_Lagos_

Yana kwance ko aikin ma be fita ba, sabida an Basu hutu besan na mene ba jiya yaga message kuma ya tambayi manager da PA suka tabbatar masa hakan yasa Shi bajewa Yana ta kwasar bacci abinsa, wayar sa dake kara ya lalubo ya daga bema ga sunanan ba kawai dagawa yayi ya Kara kunne,

Daga can bangaren,
tace’ Hello!
Yarda akayi maganar da yarda salanta ya fita yasa Shi mikewa zaune yane mi bacci ya rasa zuciyar Shi na bugawa,jiya fah message kawai ya Mata na iso lafiya yace shine mas’ud haka kawai yace Amma shine yanzu harda Kiran Shi da masa muryan munafinci( 🤦♀️)

Jiya yayi ankuma cewa’ hello? Bakajine? Ko bacci kake?

Dakyar ya samu ya lalubo magana yace’ uhm,

Tace’ bacci?

Uhm,

At this time?

Uhm,

Shidai da zata kyaleshi ta dena masa wannan munafurcin Daya huta, zuciyar Shi tasan bugawa take ba a dari dari ?

Tace’ wai Kai komai uhm uhm uhm, shikenan ma Tou,idan Ka tashi Ka kirani,daman na kirane kawai mugaisa,

Yace’ a,a na wannan nace na ma ai wannan na tashi ma ai,

Tace’ really?

Eh maan,

To ya kake?

Runtse ido yayi gam, zuciyar Shi na tsananta bugu,
yace’ kamar yarda kike,

Nifa Banda lafiya,

Kwanciyar sa ya koma ya gyara,
yace’ Nima haka,

Meke damunka?

Bekawo komai a ransa ba,
yace’ I miss someone special, important to me,

Really?

Yeah,

Can I know her? She’s your Girl right?

Shifa har zuciyar sa Mus’ab yake nufi Basu taba irin wurin kwana daya basa nan ba sai da suka fara aiki kullum sai sunyi video call suke kwanciya wataran ma ahaka suke bacci Sai da asuba idan sun tashi su gani su sannan Daya ya tashi Daya sai kuma a tashi shima ba kullum ba kusan kullum ne hakan, gashi yanzu tazo tayi masa wannan fassarar,

Tace’ hello Bakaji ne?

Yace’ am ina ina ji, kauwata nake nufi,

Kana da kauwa daman?

Yace’ yeah, she’s mean alot to me, I love her more than I my self,

Tace’ woww, inasan kauwa mace but Banda sai kannai Maza guda biyu,

Yace’ hmm, nikuwa ina da su Duka,

Tace’ hakan nada kyau,
Amma kana da GF ko?

GF?

Ohh I mean girl friend,

Dariya ma ta bashi wai girl friend,caab batasan wai yanzu ma dauriya yake da ita ba ne?

Yace’ bantaba ba,

Impossible, as smart as u are ? Ace Baka da, Kai gaskiya bazan ma yarda ba,

Yace’ to shikenan,

Tace’ ehh shikenan,

Shiru sukayi bashi da abince Jin shiru tace’ to sai anjima,

Yace’ ok,

Tace’ bye take care of yourself for your future wife,
Ta kashe wayar,

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke yace’ wai Masha Allah, zuciyar sa a hankali ta fara dawo normal ga wani uban gumi da ya hada, sai dai ya daidai ta kansa Sannan ya turawa Ummusalma recoding din hiran su, ya kirata,

Tana kwance a daki har lokacin bata tashi ba, wayar ta ce ta tasheta daukowa tayi ganin Chatty ta daga batayi magana ba,

Yace’ ke, dalla tashi kinzo kina wani bacci har wannan lokacin kinsan nawa kuwa? To yarinya goma da kusan rabi shadaya ta kusa,kina baccin asara ( kamar ba yanzu ya Gama ba 😂 ) nasan ma mijinki ko abinci Baki masa ba, bare ki gyara gida,wayace maki Amarya na bacci to Amarya tun karfe bakwai take tashi kune de salan naku yazo da haka dalla can tashi ki kintsawa mutane gida,kina jina Dan tsabar renin wayo bazaki min magana ba?
Ohhh ga marenin wayonki ko? Wai ba magana bake maki ba? Ke Bana San San fa reni kifi fa a idona na rufe taam,yimin magana, wai bazaki yi ba eh?

Tace’ taya zanyi magana? Bayan Babban Yaya Yana magana? Kasan idan Nayi magana zaka ce Banda kunya,

Darwaje Baki yayi ance masa Babban Yaya, yace’ ehh kuma da wannan, fah,

Tace’ Ai Shi idan ya kama magana ba comer ba full stop,bare a tari numfashin sa haka yake idan ya fara zuba kamar an bude fanfo za’a cika sea,

Daure fuska yayi yace’ ke na taba wasa dake?

A,a koda wasa,sai dai ko a mafarki,

Wallahi kicigaba, idan kina haka baza kizo min gidana ba,

Tace’ to,

Yace’ kiduba what’s app na turo maki Abu,

Tace’ to,

Yace’ yau fah bamuyi aiki ba,

Tace’ akan me?

Wallahi bansani ba,Nayi Nayi naji amma banji ba,

Tace’ Ka Shirya kaje company din,

Ance idan an hanani shiga fah, ance ba aiki,

Ka nuna ID card kace kaima tare da Kai za’ayi,

Yace’ Insha Allah yanzu kuwa Zan Shirya,

Amma fa idan kaje ba shiga zakayi ba, kasamu kayan ‘yan aiki kasaka bayan Ka Shiga companyn har p cap, zaka sa Kar a gane ka,

Yace’ kefa matsala ce dake meye wani p cap ni bansan taba,

Ai daman bazaka sani ba, Dan kauye kawai,
Ta kashe wayar ta,

Yace’ wannan aljanar ina, mijinta zaiyi fama ba barama da Mai jinnu, tashi yayi yayi wanka ya shirya tsab cikin kanan kaya yasa farin glass ya rataya jaka ya fita.

 

✨✨✨✨✨✨✨

Data kashe wayar missed calls dinsa tagani dayawa sunfi goma da messages, murmushi tayi,data bude messages din, acikin awanin da Basu fi hudu ba zuwa uku,ya Mata wannan, harzata masa reply ta Bari, ta tashi ta fita Gidan ta Yana nan tas kamar jiya sai abinda ba’a Rasa ba,sai da ta zagaye iya cikin gidan nata sannan ta dauko mopper tayi mopping ta kawai tare da dusting din abinda ya dace amma iya dakinta kawai da nashi sai parlour shikenan, ta kunna burner tayi turaren wuta gidan ya dauki kamshi sannan ta kulle windows ta saki labulaye ta kunna acn ta kuma fesa Freshener dadi gidan ga kamshi Ka sanyin ac wanka taje tayi ta Shirya cikin wani material hadadde dashi ta coka dauri bawai Dan ta iya ba,sai Dan tasan anayi sanda take taken big girl ada, ita kanta ta turara jikinta kamshin take na daban, kitchen taje taga bakomai indomie kuma ba attarugu Rasa abinyi tayi ta bude fridge ta ciro abincin jiya dayasa Shi, shine tayi warming ta daba,ta dawo parlour ta dauko wayarta tana ci tana korawa da tea tana Jin recording dinsu sai da tagama ji tsab zata kirashi ta tuna da maybe yanzu ya fita, bugun kofa taji na hauka ko tace gate,Bana hankali ba, tashi tayi,
tace’ lafiya? Ko an buga a hankali banji ba, gaskiya a zo a Nemo Mai gadi ni banzan iya ba, tashi tayi tana gunguni ta zaro key ta fita……

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 2

Advertisement   2   Bayan sallahn magriba kowa Yana gida amma banda Ummusalma tana dakinta tana assignment yaran…