TARTSATSI 22

Advertisement

Page 22*

**********************

Ashe ba salma kad’ai ba mata da mazan dake wurin, ya tafi da tunaninsu, Hafsa kam taji ajewar motoci amma bata juyo ba tana cen tana k’ok’arin ganin amarya ta daidaita.

Shikam gogan naka basar wa yayi don dama ya saba da irin wad’annan kallon, kasancewar shi mutum ne shi wanda sabgar dake gabanshi kawai ya sa gaba ba ruwanshi da damar da kanshi akan k’ananun abubuwa ba shiyasa bai damu da kallon kowa wurinba Amma karaf idonshi suka Kai kan gefen da ya hango amarya mazai gani hannun Hafsa da yasha Jan lalle dake gyarawa Asma’u zaman d’aurin d’ankwalin da akayi mata, akayi dace itama ta juyo caraf idanunsu suka sarke da juna, kasancewar fitulun dake haske wurin tangaram suke, da sauri Hafsa ta janye nata idanun tayi k’asa da su, amma fa jikin ta sai rawa yake,zuciyarta sai k’ara k’arfin gudu take, gogan kam basarwa yayi ya maida idon shi wani guri, amma fa zuciyarshi sai lugude take masa,yana ta so yabi umurnin zuciyar shi, yaso ya k’ara kallon k’wayar idon Hafsa, amma yayi jarumtar hana kanshi Hakan.

Yaya Aliyu da sauri yazo wurin shi sukayi musabuha da juna, shima wanda sukazo tare da mai kamar balaraben yazo suka gaisa, daga nan Aliyu yayi masu jagora suka mike hanyar shiga hall d’in, mai kamar balarabe da Aliyu da wanda suka zo tare suna gaba bodyguard suna biyar su a baya har suka shige hall d’in.

Salma kam gabaki d’aya k’wak’walwar kanta ta tsinke, saboda suman tsaye ne tayi, batareda ta sani ba, ta bishi da kallon k’urullah har sai da ya shige Hall din, bata dawo hayyacinta ba saida raliya ta tab’o ta, sannan hankalinta ya dawo jikinta, jiki ba kwari.

Daga nan aka umurci kowa ya shiga hall d’in,duk mutane suka shiga su salma kawai aka Bari sai k’awayen Asma’u, Anko ne a jikinsu baki d’ayansu, sai amarya kawai da nata kayan suka sha ban ban, sai daifa itama nata kayan kalar ankon ne.

Akayi arranging na Hafsa da salma su shiga gaba saboda wani d’an box dake hannun Hafsa, sai salma rike da wata kwalba da alama ta turare ce komi oho, ango da amarya suna a bayansu, sai sauran kawaye suma da suka biyo baya, da sauran abokan ango.

Dama ansanar da cewa ga ango da amarya nan sunzo, habawa suna shiga Mr DJ ya sauya wata Waka mai d’ankaren dad’i, mc ya Fara sanarwa ga ango da amarya nan zasu shigo, kowa ya maida hankalinshi a inda ake tsammanin tanan ne zasu shigo hall yayi tsit sai faman kid’a ke tashi cikin natsuwa.

Sannu A hankali Hafsa ta fara shigowa Tana tafiya tamkar mai tausayin k’asa, abunka da ba’a saba zuwa irin wad’anga wuraren ba, nan take ido suka yi mata yawa kafafunta suka hard’e,tafiyarta ta canza, aiko saiga shi tafiyar ta bada wani style wanda baisani ba sai yace dagangan tayi, a hakan ta daure ta fara debo wani k’yalk’yali dake cikin box din, ta fara watsawa sama nan take kyalkyalin ya zaga ko ina Cikin hall din, sai faman sauka yake ajikin mutane yana wata walwalniya.

Advertisements

Gogan kam jin yayi kamar ya cire malunmalun shi, yaje ya rufe ta ruf adaina kallar mashi kaya.

Salma dake biye da ita da wata kwalba itama, sai d’aga ta take sama tana fesa abunda ke ciki, shima wani kyalkyaline tareda wani kamshi mai dad’i, suke tartsatsi cikin Hall d’in.

Ango da Amarya suka shigo, aka Fara tab’i, salma da hafsa suka kaisu wurin zamansu suka zaunar dasu,daga nan sauran k’awaye suka shigo da abokan ango, kowa ya samu wurin zama ya zauna.

Aka fara gudanar da dinner Aka kira k’awayen Amarya suka fito, suka nuna farin cikinsu, daga nan shiri yayi nisa, bansan ya akayi ba kawai sai naji ankira ‘yan biyun umma, suzo su taka rawa suma, aiko sai gasu sun fito tsakiyar fili aka Fara wasasu, k’irjin biki k’awayen amarya k’annen ango, saiko ga salma ta Fara taka rawa, Hafsa kam juyi kawai take don bata iya rawa ba, nanfa Ango da amarya suka zo suna masu liki, bayan sunkare ne aunty umaima tazo Tayi masu Nata, daganan ‘yan uwa da abokan arziki sukayi ta masu lik’i.

Bayan sunje sun zauna ne, kawai sai akaji mc yana ta kiran Hafsa fito tazo ta tsaya tsakiyar fili, cikin mamaki ta fito jikin ta sai faman rawa yake me za’ayi aiko sai salon kid’a kawai ya canza, dauke da wak’ar nan me taken fall in love, Haba wak’a ta dau zafi Hafsa ta Fara d’an juyi kwatsam saiga abokin tafiyar mai kamar balarabe ya fito, ya nufo Hafsa aiko sai kallo ya koma sama, yana zuwa ya b’arke rafar dubu sai lika mata yake saida rafar ta k’are ya jawo wata rafar itama saida ta k’are sannan yaje ya zauna.

Nan take hall ya rude kowa sai albarkacin bakinshi yake fad’i, Hafsa ta fito jiki a sanyaye don abun ya bata mamaki tana tambayar kanta miye had’in ta da wannan mutume.

Salma kam duk wani motsin mai kamar balarabe akan idon ta ne, daga nan ango da amarya suka fito suma sukasha lik’i aka aka koma wajen yanka cake, suka ciyar da junansu suka sha, daganan aka rukuce sai faman cashewa , sai aka fara service salma jiki har rawa yake taje kusa da mai kamar larabawa, shikam baimasan tanayi ba, don shikam zuciyar ta cika taf da k’aunar hafsa, don har ganin yake duk matan dake wurin fuskar Hafsa ce garesu.

Ana cikin casun ne kowa hankalinshi ya d’auku, kawai saiga Hafsa ta biyo ta kusa dashi, d’auke da khadija sabe a kafadarta, da alama rarrashin tane take don kuka ne takeyi, bata sani ba kawai sai Tayi tuntube tayi tangal tangal zata fadi, kawai sai ta jita jikin mutum daga ita har khadijar yana rungume dasu, hannunta cikin nashi ga wani daddad’an turarenshi mai narkar da zuciya da ta Shaka, ba shiri ta sakar mashi khadija, taja da baya, jikinta sai rawa yake, shikam dariya ta bashi, amma ya gimtse baiyi ba, yadai wanketa da wani tsadadden murmushi, cikin rawar baki tace nagode tayi gaba har ta fara tafiya, cikin muryarshi nutsatstsa yace

“Babyn fa kin barman ne”

Ta juyo bata ce komi ba yaje har kusa da ita ya ajiye khadija a k’asa, ya ciro wani sweet a cikin aljihunshi ya bud’e ya Mika mata a hannu ya sunbaci kuncinta, ya d’ago ya K’ara bin Hafsa da wani murmushi wanda ita kanta Hafsa sai da taji wani yarr ajikinta, kafin ta dawo dai dai har ya b’ace mata da Gani, koda ta waiga ta hango shi yana shirin barin Hall d’in bodyguard d’inshi suna biye dashi a baya.

Ana cikin haka saiga salma ta k’araso wurin Hafsa da sassarfa tace da Hafsa

“Hafsa me ya hadaki da hayaty?”

Advertisements

Hafsa cikin rashin inda ta dosa tace mata “wanene hayatyn naki?”

Salma tace “wancen baturen da ya wuce sai naga kamar daga wurinki ya fito?”

Hafsa sai ta tsinci kanta da cewa

“Khadija yagani tana kuka shine naga yabata sweet”

Salma tayi doguwar ajiyar zuciya tace “Ayya wato abokin shi ne ke sonki kenan don naga shine yayi maki b’arin kud’i d’azu ko? ”

Salma bata jira amsar da Hafsa zata bayar ba, ta duk’o saitin khadija ta karb’i sweet d’in da yasha miyau da guntuwar majina, ta Kai bakin ta tagutsura, ta lunmshe idonta cikin shauk’in so, irin na zuciyar da Tayi muguwar kamuwa da tsatsar so tace

“welcome to the world my hasashe”

Hafsa ta zaro ido waje, ba shiri tabar wurin, tana dafe da saitin zuciyarta tace

“Me ke shirin faruwa dani nida ‘yar uwata?”

tofa😳😳

Akafta 🤸🏻♀

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 46

Advertisement page 46* ******************* Hafsa hankalinta ya dawo ajikinta, koda ta waiga bataga Salma da khadija ba, nan…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 14

Advertisement €pisode 14…………… Bayan ya gama shiri tsaf ya dawo ya zauna gefen gado tare da jawo wayarshi…
Read More

TARTSATSI 10

Advertisement *Page 10* *************** Umma da hafsa suka bita da kallo har ta shige daki, Hafsa Tayi hanzarin,…
KALLABI
Read More

KALLABI 22

Advertisement BABI NA ASHIRIN DA BIYU Zaro idanu Innayoh tayi, cikin tashin hankali tare da rufe bakin ta.…