TARTSATSI 25

Advertisement

*Page 25*

*********************

Aliyu yayi murmushi yace

“‘yan biyun umma, k’anne na ne, kuma k’annen Auwal ne ciki d’aya amma azahiri ba ‘yan biyun gaske bane”

Daganan Aliyu ya bashi labarin matsayin Hafsa a wurinsu, tareda gutsura masa kad’an daga halayen ta na Kirki, jikin sadauki yayi sanyi sosai, yaji wani so da tausayin Hafsa ya lullub’eshi saboda shi arayuwar shi, mutum ne shi Mai matuk’ar tausayi sosai, Wanda duk da kasancewar shi jarumin namiji idan yaga abun tausayi baisan lokacin da k’walla zata zubo masa ba, saidai yaga Ashe hawaye ne yake.

Cikin mutuwar jiki yace sadauki yace

“Aliyu ka bani shawara, taya zan bayyana kaina wurin a Hafsa?”

Aliyu yayi saurin cewa

“Ka Bari kawai zan gayawa Daddy, saboda nasan zaiyi farin ciki idan har yaji wannan magana,Daddy ko wani wuri ne, zai iya yin ruwa yayi tsaki sai ya nemo maka auren, ballantana Abu a cikin gida tuwo na maina”

Sadauki yayi hanzarin dakatar dashi da cewa

Advertisements

“A’a Aliyu kar ka fad’awa Daddy, ka bari kawai ni zanyi yak’ina saboda banison a nuna k’arfi ko isa ko mulki acikin k’wato Mani zuciyar Hafsa, nafiso ta soni don kanta ba tareda an tilas ta mata ba, nasan in ta Daddy ne ko a gobe nace inaso a d’aura man aure da Hafsa zai iya bani, amma dai ka bari kawai ni zanyi yakina na da hannu na”

Ya k’are maganar yana murmushi

Aliyu yace “to Allah yayi taimako, don nasan Kai mai sa’a ne”

Dukansu sukayi murmushi Sun d’au lokaci suna hira kafin suyi sallama.

Sadauki yayi wani murmushi yace

“Allah kabamu sa’a”ameen

Ya tashi ya saka jallabiyyar shi ba’ka, ya saka wasu takalmi masu gashin mussa suma bak’ak’e fito sashen shi, yana tafe ‘yan aiki suna ta gaidashi, yana amsawa cikin sakin fuska har ya shiga b’angaren umma.

Da sallama ya shiga k’aton falon na umma, akayi dace k’anwar shi zakiyya tana saukowa daga up zata shigo main Palon dake mak’are da saitin kujeru kala uku, sannan da wani k’aton Diny Table agefe sai d’aukar ido yake.

Ya samu d’aya daga cikin kujerun ya zauna, itama zakiyya ta k’araso kusa dashi ta zauna tace dashi

“Blood bros ina kwana?”

Yayi murmushi yace

“Lafiya lau mummy fa?”

Advertisements

Zakiyya tace “yanzu na je gaidata, tana cen tana ta aikin nata, na jan carbi, ko magana bansamu ba yau d’aga man Kai kawai Tayi, shine na fito in had’a maka breakfast kar inyi latti ko in bari ladi ta had’a maka? ”

Ta kare maganar tana ‘yar karamar dariya, saboda tafi kowa sanin yanda yake kyankyamin abincin ‘yan aiki, in ba mummy ko zakiyyar sukayi ba, da wuya yaci abincin su shiyasa take tsokanar shi.

Yana murmushi ya Fara tafiya yacee

“A’a ladidi, ni kinga bari inje in sameta kar ki b’ata man lokaci”

Zakiyya ta dafe baki tana dariya, ta nufi sashen da kitchen d’insu yake, shi kuma ya haye sama wurin mummy.

Da sallama d’auke a bakinshi, saida ya tabbatar ta amsa sallamar shi, sannan ya shiga da’kin ya samu gefen gado ya zauna, minti biyar a tsakani sannan ta k’arasa laziminta, tayi addu’a ta shafa ta juyo da murmushi a kamilalliyar fuskarta.

Sadauki yayi saurin d’an rank’wafawa ya gaisheta, ta amsa cikin sakin fuska ta dafa kanshi tana tofa mashi addu’o’i tareda sa masa Albarka.

Bayan sun k’are gaisawa ne, ya d’auko wayar shi ya kamo photon Hafsa ya mikawa ta, mummy ta karb’a tana dubawa tace

“Tubarkallah Masha Allah wannan mai kyaun fa?”

Sadauki ya Fara susar kai yace

“Itace mummy….”

mummy tayi murmushi tace

“Itace wa?”

Ya Fara bata labarin da Aliyu ya bashi dangane da Hafsa tareda bayyana mata yanda sukayi da Aliyu akan kar Daddy yasan maganar.

Mummy ta tsurawa photon Hafsa ido sosai, saboda a lokaci guda taji yarinyar ta burgeta, nan take taji Tana yiwa sadauki sha’awar Hafsa ta zamo matarshi, saboda tunda suke dashi bai tab’a kawo wata Mace yace yana so ba, itama ma ce a kullum take masa zancen auren, amma shi yana shashantar da zancen, saboda tafi kowa sanin wanene d’anta, shiyasa tayi saurin amincewa da Hafsa, don tasan bazai kawo b’ara gurbi ba,cikin natsuwa irin ta kamilar uwa tareda nuna masa tsantsar soyayya irinta uwa da d’anta tace dashi

“Na baka dama kaje ka nemo soyayyar Hafsa, Allah ubangiji ya sanya alkhairi cikin lamarinku.”

Cikin farin ciki sadauki yace “Ameen mum”

Daman yasan mummy mutum ce Mai sauk’in hali, bazata k’i abunda yake so ba, in har tasan abun yana kan hanyar kwarai.

Nan suka ci gaba da hira tana d’orashi akan hanyoyin da suka dace yabi, har zakiyya ta shigo take fad’a mashi ta k’are, ya bata umurnin ta kawo masa nan d’akin mum, ai kuwa haka akayi saigata rike da wasu ladi amintacciyar mai aikinsu d’auke da sauran kayan, suka ajiye zakiyya ta had’a masa komi yace itama ta zauna su karya, tare suka karya suna ta hira irin ta yaya da kanwarsa.

Nan ya gwada mata pic d’in Hafsa, itama ta rud’e tana ta faman murna, sai rok’onsa take akan ya kaita wurin Hafsa, yace zai kaita amma ba yanzu ba.

 

Ab’angaren su salma kuwa sun k’are ayukkansu kowace ta koma bacci, saboda ramakon Wanda basu samu sukayi ba da dare, dama ga gajiyar kacaniyar biki atare da su.

misalin karfe hud’u na yamma sai ga usman da guda ya fito daga waje yana ta haki, duk su umma suna tsakar gida dukansu suka maida kallonsu kanshi, umma ta kalleshi tace

“lafiya kake wannan gudu haka, baka tsoron ka fad’i kaji ciyo? ”

Usman yana maida numfashi yace

“Umma wani D’an indiya ne nagani a kofar gidanmu ya aje motarshi, yace inkira masa aunty Hafsa”

To fa mun shigo tartsatsi😱

Akafta🤸🏻♀

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 40

Advertisement BABI NA ARBA’IN CIF Please subscribe Shiru yayi na wani lokaci kafin ya dauke kan shi, cikin…
Read More

TARTSATSI 37

Advertisement *page 37* ******************* Salma cikin farin ciki, taje ta adana kud’inta, zuciyarta fal farinciki, don ganin takeyi…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 8

Advertisement €pisode 8……………………. Cikin daƙiƙa uku Tsuntsu Bilbil ya sauka gabansu na Naheela. Cikin kakarin jini ta shiga…
Read More

TARTSATSI 54

Advertisement *Page 54* ******************* Azaba iya azaba Raliya tasha ta amma ta kafe k’am da cewa ita ba…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 10

Advertisement €pisode 10…………….✍️ Barhana da sarki Zawatundma ya aika zuwa garin Mubanuwa kuwa da sauri ta fara keta…