TARTSATSI 26

Advertisement

*Page 26*

********************

Salma ta zaro ido waje tace “Kai usman fad’i gaskiya Hafsa kaji yace a kira ko dai ni? ”

Usman bakinshi yana rawa, saboda son ya jaddada mata abunda yaji sadauki ya fad’a, yace

Wallahi aunty salma saida ma ya tambayeni, ni k’anen aunty Hafsa ne nace masa eh, yace mani shi mijin aunty Hafsa ne, inje in kira masa ita, baki ganshi ba Mai fara’a dashi”

Salma nan take ta dafe zuciya, saboda wani zafi da zuciyarta takeyi mata, ido rufe ta shak’o wuyan usman ta d’aga hannu da niyyar ta zabga masa Mari, umma ta rik’e hannunta tareda jawo usman ya dawo kusa da ita, tace da salma

“Kina hauka ne? me akayi na duka anan da zaki dokeshi? ”

Hafsa dai tana tsaye baki a sake tana kallon su ba tareda tace kanzil ba, saboda ita kanta tajita a wani yanayi, wanda bata taba jin irinshi atattare da itaba,jikinta duk yayi sanyi, umma ta maida kallonta ga Hafsa tace

“Kinyi tsaye me kike jira, kinji ance ke aje kira kije kigani wanene”

Jiki ba k’wari Hafsa ta shiga d’aki, ta d’auko hijabinta tasaka, tana tafe amma zuciyarta sai faman bugu take, tana isa bakin k’ofar get d’in nasu, ta d’an lek’a ta hangoshi a bakin motar sai faman duba agogon dake sanye a tsintsiyar hannunshi yake, da alama yana duba lokacin da Hafsa tayi ne bata fitoba, wanda duk wani second dake tafiya jinshi yake tamkar shekara d’aya.

Advertisements

Tana ganinsa tayi saurin komawa jikin k’ofar ta dafe kirji gabanta sai k’ara dukan lugude yakeyi dama jikinta ya bata cewa shine cikin zuciyarta tace itakam ina zata tsoma ranta ne ta d’auki tsawon minti biyar anan wurin ta kasa tafiya wajenshi, tana tunanin meye mafita, a haka dai tayi jarumtar fitowa ta tunkareshi, gogan kam yana hango ta sai faman murmushi yake har ta iso kusa dashi, kanta a k’asa ta gaidashi, haka kawai takasa bari ta had’a ido dashi, saboda jikinta sai faman rawa yake.

Sadauki afakaice Ya dubeta tun daga sama har k’asa ya lura da yanda jikinta yaketa tsuma yaso yayi dariya amma ya waske ya kalleta yace

“Hajiya tsumar fa tame ce?”

Taso ta kalli fuskar sa amma ta kasa ta daiyi jarumtar fad’in

“Me kagani”

Ta k’are maganar bakin ta yana rawa ya kalleta yayi dariya yace

“Ki rufaman asiri kar ki fad’i ki jazaman aiki in tsayuwar ce ta gagara muje daga ciki ki shimfid’a muna tabarma, kada kisa mutane su zargi ko satar ki nazoyi, kisa su had’a man jini da majina”

Hafsa ta k’ume dariyarta.

Ya k’ara da cewa

Ni kuma hannu na akai ina ta kiran

“Wallahi neman aure nazo ba sata ba”

Ya Kare maganar tare da aza hannu akai, yana ta kwatanta yanda zaiyi.

Advertisements

Ba shiri Hafsa
dariya ta kub’uce mata, Tayi kokarin sanya hannunta a baki tana kokarin toshe dariyar kar ta fito.

Sadauki ya bita da wani lafiyayyen kallo saboda bak’aramin burgeshi tayi ba sannan ga Jan lallen ga nata dake tafiya da tunaninshi, arayuwarshi yanason yaga Mace tayi jan lalle.

Ya fad’a zurfin tunanin duk randa mummy tayishi kullum bayada Aiki sai faman kallon shi, mummy tayita masa dariya Tana cewa Allah ya bashi matar da takeson jan lalle, tayita yimaka kana kallo, yayi dariya yace ai dole mane taso shi tunda inaso, aiko sai gashi ya had’u da Hafsar shi, gwanar son jan lalle.

Hafsa da taji shiru ta d’ago Kai ta kalleshi ba shiri ta mayarda kanta ak’asa saboda ganin ashe ita yake kallo.

Ya sauke ajiyar zuciya yace

“Abba fa?”

Ta k’ara duk’e Kai a k’asa tace

“Bai dawo gida ba”

Sadauki ya furzar da iska bakinshi yace

“In kika shiga gida ki fad’awa umma, ace da Abba ina so yabani lokaci ina son inzo ingaidashi”

Hafsa tace “to insha Allah zan fad’a mata”

Har ta Fara tafiya da hanzari ya kalleta yace

“Ina zuwa kuma hajiya? bafa muyi sallama ba”

Ta waigo tace “eh nasani jirani minti biyu”

A b’angaren salma kuwa, fitar hafsa dai dai yake da fitar nutsuwarta, ta shige d’akinsu zuciyarta tamkar ta yage saboda tsantsar sukar da take yimata, takai gauro takai mari sai faman safa da marwa takeyi a tsakiyar d’akin su, tana sak’a wadda zata fissheta, inhar da gaske hasashenta ne yazo wurin Hafsa, ta lek’a tsakar gida ta samu taga umma ta shige d’akinta, aiko adari taja hijabi Tayi waje, tana zuwa ta d’an lek’a kanta yanda baza’a ganta ba, ai kuwa saigata a durk’ushe tayi saurin dafe zuciyarta dake k’una, sai hawaye sharr sharrr.

Akayi dai dai hafsa tana shigowa ta ganta durk’ushe a wurin, da sauri ta isa kusa da ita ta d’ago ta,ta tayar da ita tsaye tace

“Aunty salma lafiya meke damunki?”

Salma ta ture hannunta dake saman kafad’unta dakyar tace

“Kiji da kanki malama, ba ruwanki da abunda ke damuna”

Hafsa kanta ya d’aure sosai ta kalleta dakyau, don tanaso ta gasgata abunda taji ya fito a bakin salmar, amma ta kasa ta riko hannunta tace

“Menayi maki ne mai zafi har haka aunty salma?”

Salma ta k’wace hannun ta da karfi Tasa hannu biyu ta ture Hafsa ta ai kuwa kanta ya bugu da karfen hannun get yace gum, hafsa ta dafe wajen tace

“wash….”

Cikin jin zafin abunda salma Tayi Mata, muryarta cikin fushi ta fara magana

“Indai Don hasashenkine kike man wulak’anci haka, to kije gaki gashi, daman Ashe wajenki yazo ba wurina ba”

Tana k’are maganar tayi fuuu, ta shige ciikin gida.

Salma ta bita da kallo wani sabon farinciki ya ziyarci zuciyarta, Tayi d’an tsallen murna, tayi sauri ciro d’ankwalinta, ta goge fuskarta da ta b’ace da jirwayen hawaye, ta maidashi ta d’aura akanta ta fita.

Tana fita sadauki yayi hanzarin maido idonshi wurin, yana murmushi don a tsammaninshi Hafsa ce ta dawo, salma kuwa tana ganin ya fara murmushi itama ta bishi da wani k’ayataccen murmushi, mai saurin sace zuciyar Wanda aka yiwa, sai dai shi yana gano bafa Hafsa bace, sai kawai ya rage Girman murmushin shi, Tana zuwa kusa dashi ta gaidashi, ya amsa ba yabo ba fallasa yace da ita

“Kece tawainiyar mu ko?”

Salma ta kalleshi tayi murmushi, ba tareda tace komi ba don ita sam bata gano inda ya dosa ba.

Yak’ara kallonta yace

“Na kawo maku bak’unta dafatar zaku karb’eni hannu bibbiyu”

“Salma ta k’ara washe baki tace ai Kai na daban ne, ko a ina kaje ina Mai tabbatar maka aguje za’a karb’i bakuncinka”

Sadauki ya kalleta a karkace yace

” Hafsar fa? ko wani aiki takeyi zuwana na katse ta?”

Salma ta kalleshi da wani bugun zuciya da dirar mata, don ta kasa gano me yake nufi, bakinta yana rawa tayi hanzarin fad’in

“Ban..ga..ne.. ba ”

Sadauki ya kalleta dakyau, yace mata

“kice tazo muyi sallama ni zan wuce”

salma ta Fara Jan k’afarta kamar mai koyon tafiya, Don itafa Sam bata gano kan wannan mutumen ba.

Tare suka fito da Hafsa, ba wani sakin fuska atattare dashi, yayi masu sallama har ya tada motarshi yace da Hafsa kar ta mance da sak’onsa afad’awa Abba.

Yana tafe yana wasiwasi a ranshi saboda shifa ya karanci wani Abu acikin lokaci k’ank’ani, yayi saurin kawar da tunanin, don bayaso ya damar da kanshi, akan abunda bai tabbatar ba.

Tofa me ka fahimta😱

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 82

Advertisement *Page 82*   **********************   Acikin tashin habkali maryam ta fara kuka,tana baiwa Daddy hak’uri, amma Daddy…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 7

Advertisement 7 A bangaren Abba kuwa,yaji takaicin bada motar da tayi,Amma ba yarda zaiyi tunda ta Riga da…