TARTSATSI 27

Advertisement

Paga 27*

******************

Daga hafsa har salma ba Wanda yace da wani kanzil, har suka shiga cikin gida, koda suka shiga umma tana fitowa daga kitchen, ta kallesu taga kowace fuska ba walwala, ta dubi salma tace

“Ke yaushe kika fita bansani ba?”

Hafsa tayi saurin fad’in

“Ai umma Ashe wurinta ne yazo, yamace in fad’awa Abba yanaso yazo su gaisa”

Salma tayi saurin kallon Hafsa tana so su had’a ido da ita, saboda itadai ta kasa tantance wannan lamari ya yake, Hafsa kam bata bata wannan damar ba, kawai ta Kwab’e hijabinta ta d’auki buta ta shige toilet d’insu dake waje abinta.

Umma tadubi salma dakyau tace

“Me ke faruwa tsakaninki da ‘yata, saboda na fahimci akwai wani Abu da kukeso ku b’oye Man, don haka kiyi gaggawar sanar dani tun kafin ingano dakaina, nasan Hafsa duk abunda kikaga ta nuna b’acin rai akanshi,to ko abun ba k’arami bane, don haka inma ke ke mata abunda bataso, to ki daina tun muna sheda juna nida ke, don wallahi akan Hafsa zanyi maki abunda bakiyi tsammani ba”

Salma bakinta yana rawa tace da umma

Advertisements

“Yanzu umma kinfi son ta fiye dani?”

“Umma tace ni ina goyon bayan gaskiya duk inda take, saboda haka ki kiyaye”

Salma ta yi hanzarin kallon umma, nan take taji wani kuka ya taso mata, aguje ta shige d’aki ta aza kuka, Da hanzari Hafsa ta fito toilet din, wanda itama da ka Kalli fuskarta zaka gano tayi kuka,saidai tayi k’ok’arin wanke fuskarta don kar agane, saboda duk abunda umma take fad’a akan kunnenta, tana fitowa ta ajiye butar taje kusa da umma tace

“Umma me akayiwa aunty salma take kuka?”

Umma fuska ba walwala tace da ita

“K’yaleta gaskiya ce bataso, duk abunda zatayi taje tayi tayi”

Ta dubi Hafsa da kyau tace

“Ki daina bari salma tana sanya ki kuka, don nasan halinki da sanyin Hali, in har bazaki rama ba, to kar ki kuskura inga k’wallah a idonki”

Tana k’are maganar ta shigewarta d’aki, batareda ta jira taji abunda Hafsa zata ce ba, don tasan halin ta yanzu ne zata karya mata zuciya, itama tasa tayi kukan.

Hafsa jiki ba k’wari ta nufi d’akinsu, tana shiga taje kusa da salma ta zauna cikin dusassar murya dagaji itama tasha kuka tace da salma

“Aunty salma me yayi zafi shi ba wuta ba, yaanzu saboda namiji zaki iya juyan baya, kar fa kimanta ke ‘yar uwatace wadda mukasha nono tare,tunaninki ya daina baki cewa wai zan iya yin abunda nasan zai cutar dake”

Salma ta d’ago daga risgar kukan da take tace

Advertisements

“Hafsa tausayin kaina ne yake sani kuka, Don zuciyata tana zargin wani Abu, wanda idan har abun nan ya zama gaskiya, to tabbas rayuwata tana cikin garari”

Ta k’are maganar, tareda zubowar wasu hawaye masu zafi.

Hafsa ta kalleta, itama hawayen suka gangaro mata, tace da ita

Aunty salma ina so ki yarda da k’addara mai kyau ko akasin ta, ki kasance mai tawakkali ga dukkan lamurranki, insha Allahu zakiga komi yazo maki da sauk’i, amma kin tsaya kina ta tada hankalinki akan abunda baki tabbatar ba”

Salma ta taso daga inda take zaune, tazo kusa da Hafsa ta rik’o hannunwanta duka tace

“Hafsa ina son kiyiman alk’awali d’aya”

Hafsa kace “kamar me fa”

Salma ta share hawayen fuskarta tace

“Don Allah duk rintsi duk wuya kada ki bari soyayyar, wannan mutumen ta shiga acikin zuciyarki”

Hafsa da sauri ta kalleta, ba shiri ta k’wace hannuwanta ta, tashi tsaye ta juya mata baya tace

Alk’awali guda ne zanyi maki, zanyi iya k’ok’ari na, wajen ganin na k’ulla soyayya a tsakaninki dashi, amma fa kar ki mance komi sai in Allah ya k’addara in akayi dace akayi sa’a zan tayaki murna, in kuma har ya yaki amincewa, to gaskiya Shikenan zan fidda hannuna”

Salma Tayi hanzarin tashi tsaye Itama ta zagayo ta fuskanci Hafsa farin ciki d’auke a fuskarta tace

“In kika yiman haka, kin gama man komi mangata”

Ta Kare maganar tareda ruk’unkumeta, Hafsa hawaye masu zafi suka gangaro mata afuska, tayi k’ok’arin sharesu Don kar salma ta gani.

Umma dake jikin k’ofar su, tana saurarensu, itama bata san lokacin da ta share nata hawayen ba, domin azahirin gaskiya tana cikin rud’ani ba kad’an ba, saboda irin wannan tartsatsi da ya afkowa yaranta.

 

Nima na ajiye alkalamina, domin in share nawa hawayen😢

 

Akafta🤸🏻♀

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 17

Advertisement 17 Washegarin da akayi hutu shine ranar birthday na, mun fito don na kai su yusseer islamiyya,daga…
KALLABI
Read More

KALLABI 4

Advertisement *<Babi Na Huɗu>* _Soyayyar gaskiya tana faru ce a bisa wasu manyan ginshikai! Imma ƙaddara ta haɗa…